Chapter 5
by @barista
BIYU A ƊAYA
***
YOTA 13
Team of FIVE INK legends
I called you my pen🖋️ Na'ima SARAUTA 👸🏻
Page 5
Fitowa yayi daga toilet ɗaure da blue towel, ya iso wardrobe ya buɗe ya fiddo da ɗan ƙaramin white towel sannan ya rufe, ya tako zuwa gaban mirror yana kallon kansa cikin madubin yana goge duk inda ruwa yake a jikinsa, sai da ya kammala sannan ya shirya cikin ƙananan kaya, ya feshe jijinsa da turare, nan da nan ƙamshi ya baɗe ɗakin.
A nutse ya fito kai tsaye ɗakin Mamie ya wuce, yayi nocking tare da sallama, ya shigo ta amsa ya zauna tare da gaida ta
"Ina kwana Mamie"
Ajiye wayar dake hannunta tayi, saboda shigowarsa yasa ta katse wayar. Cikin kulawa ta amsa da
"Lafiya lau, yanzu nake shirin zuwa ɗakin ka kuma sai ka shigo "
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya kai hannu ya ɗauki Dabino dake ajiye akan plate ya ɗan saka haƙori ya raba gida biyu ba tare da ya sake mai da shi baki ba ya ce
"Lafiya Mamie? Wani abin ne ya faru?"
"To a kan maganar fitar da Hajjiya ƙasar waje ne, mun yi magana da mahaifin ka akai, ya ce ka ce su dakata"
"Eh Mamie daman....
"Look Waahab, fitar da ita shine mafita, batun a jinkirta kaita ma bai taso ba"
"Shikenan Mamie a fitar da ita, abin da yasa na ce a bari sai wani lokacin shi ne na sake bincike sosai akan larurarta na samo mafita"
"A'a Waahab is too late ace za a jira ka, kaga tafiya ce ka saka gaba, tun da dai abu yaƙi ci yaƙi cinyewa kawai a fitar da ita"
"Ba damuwa yanzu zan je na sake duba jikinta sai na wuce wajen Daddy mu tattauna"
Ya saka Dabino a bakinsa yana tunawa a hankali, yayi masa daɗi, ya ɗebi gudu uku ya mik'e tare da cewa
"Sai zuwa anjima Mamie, bari na duba jikinta"
"To Jamila ma ta dawo"
Ya ɗan juyo tare da cewa
"Sauƙar yaushe?"
"Jiya da yamma, saɓani ma ku kayi, kana fita wajen aiki ta iso"
"Uhm yau zan sha gori"
"Ato da gaskiyarta mana, kuna shekaru ɗaya tana da yara kai kana nan har yanzu ba zancen aure"
Yayi murmushi sosai ya ce
"Lokaci ne"
"To Allah ya nuna mana lokacin, amma dai ka dinga sake wannan fuskar taka ko za ka samu mata"
Murmushi yayi ya ce
"Mamie kawai ina jina haka ne amma fuskar fah babu laifi ina sake ta"
"Fuska kamar wanda ake aikowa mutuwa, kullum gum da ita, baka da lokacin kowa da aikin ka sai kuma ka maƙale a ɗaki"
Yayi dariya ya fice, kai tsaye zuwa ɗakin Mommie yana isowa ya tura ƙofar ya shigo tare da sallama, ganin Jamila na zaune tana tofa wa mommy addu'a yasa bai ce komai ba, ya zauna har ta idda addu'ar sannan ta dauko tare da cewa
"Barka da safiya Doctor"
"Barka dai Jamila, ya hanya?"
"Sai godiya tun jiya nake cigiyarka ashe kana night duty"
"Eh fah da safen nan na shigo"
"To ya aiki?"
"Sai godiya"
Ya duba jikin Mommie da sauƙi, a lokacin Suhaima ta shigo da sallama a bakinta ta ajiye basket dake hannunta ta ce
"Ya Waahab ina kwana?"
"Lafiya Suhaima"
Bai sake cewa komai ba, Suhaima ta dubi Jamila tare da cewa
"Aunty Jamila ruwan zafin sai yanzu na ɗaura"
"Ba damuwa, ina mujaheed?"
"Yana wajen Ya Sageer"
"Ai kawai sai mun ganshi in dai yana tare da Sageer"
"Shi kaɗai kika taho dashi?"
Cewar Doctor Waahab yana duba magungunan mommy, ta amsa da
"Eh sauran na barsu cen wajen Baban su"
"Da kin yi zaman ki ai, jikin nata ma da sauƙi"
"Hankalina yaƙi kwanciya shiyasa na taho"
"Suhaima na shigo da magungunan mommy ma suna ɗakina ki je ki ɗauko su, suna kan bedside"
"To Ya Wahaab"
Ta mik'e ta fito.
Suna hira da Jamila sannan yayi mata sai anjima ya wuce wajen Daddy.
*******************************
GHANA
Mashin Ocada ya sauke ta a daidai gate ɗin restaurant ɗin, ta ba shi kuɗin sa sannan ta shigo, farfajiyar restaurant cike da motoci wasu na ƙoƙarin parking wasu kuma suna ƙoƙarin fitowa, ta shigo ta wuce ciki, main kitchen ta shiga ta tadda sai aiki suke yi, bata yi wa kowa magana ba, ta sami gurin zama ta zauna, tana bin su da idanu. Babu wanda yayi mata magana don sun santa ba kasafai take shiga lamarin kowa ba, tagumi ta rafka tana kare musu kallo tana tuna abin da Majada ta faɗa mata a kansu, kenan kallon ƙitse take yiwa rogo? Yanzu duk sun ɓata rayuwar su...
"Bilqees yaushe kika shigo?"
"Ko kallon ta ba tayi ba, kuma bata ko motsa wa daga inda take ba, idanunta akan sauran ma'aikatan...
"Wai yau me yake damun ki ne? Kin makara sosai a gida ba ki fito ba, nazo ina yi miki magana ma...
"Majada"
Cewar Bilqees ba tare da ta kalleta ba, ta ci gaba da cewa
"Babu abin da ya shafe ki da makarata, ki yi abin gaban ki"
"To Allah ya baki hakuri"
Tana fadin haka ta yi tafiyarta...
"Ke Bilqees Alaja tana kiran ki"
Ta ɗago ta kalli Jummai dake tsaye, ta sauke numfashi jiki a sanyaye ta tashi ta wuce ta zata fito Jummai ta ce
"Sabar raina ma ko gaida ni ba ki yi ba, sannan kin tashi kin fito ɗin ina za ki je? Kin san inda Alaja take ne?"
A hankali ta juyo ta kalli Jummai ba tare da ta ce komai ba, Laraba ta iso tare da cewa
"Kin ganta nan tun da ta shigo bata ce mu ci kan mu ba, sai zuba mana manya manyan idanunta kamar na mujiya tayi mara kunya kawai"
Bata ce komai ba, tana ci gaba da kallon su, Jummai ta ce
"Ai ba laifin ta bane yanzu idanunta son buɗe, ta san duniya, dole ta haɗa kanta da mu, to ki sani Bilqees"
Cewar Jummai tana tafa hannayenta waje guda sannan ta dakata ta nunata da yatsa
"Kin yi kaɗan ki haɗa kan ki damu, ƙaramar ƴar iska kawai, kada ki ga Alaja tana wani ji dake kina ganin kin fi kowa, to ki sani tattaka ki zan yi"
Ita dai Bilqees kasa cewa komai tayi, tana bin su da kallo har ba ya isanta, to ko dai tuna ni suke yi ita ma irin su ce..
"Wuce ki bamu guri"
Ta juyo ta barsu suna ci gaba da zaginta, ta wuce Corido inda Alaja take zama tana ganin shige da ficen kowa amma bata ganta ba, ta dawo dakin da Alaja ke hutawa, tayi nocking ta buɗe mata, ta shigo ta wuce ta zauna, Bilqees ta iso ita ma ta zauna daga gefe tare da yin ƙasa da murya ta ce
"Bonjour Maa"
Tana gaida Alaja, barka da safiya. Alaja ta sauke numfashi tayi shiru ta kurawa Bilqees idanu na wani lokaci, jin shiru Alaja bata amsa gaisuwar ta ba yasa ta ɗago idanunta suka sauka cikin na Alaja, da sauri ta sudda kai...
"Have you end it?"
Girgiza kanta Bilqees tayi a hankali ta buɗe baki ta ce
"Ki yi hakuri, ba zan sake ba"
"Kin ce za ki kawo ƙarshen komai dake sakanin mu, shine na ce kin kawo?"
"A'a ki yi hakuri"
"Yanzu ki kalli tsabar idona ki ce na tura ki iskanci wajen wani, ko wani ne ya faɗa miki ai ba za ki yarda ba, amma ke ce kika faɗa da bakin ki. Faɗa min me na ce ki kai hotel ɗin?"
"Abinci"
"Na waye?"
"Alhaji mukhtar"
"To bayan shi na ce wani abu?"
"A'a"
"To ki buɗe kunnen ki da kyau ki ji ni, cewa yayi ya ganki kuma yana sonki, na ce a'a ba ruwana sai kin amince, to kin ji yadda mu kayi, ashe ɗan iska ne"
Bilqees tayi shiru kanta a ƙasa bata ce komai ba tana jin zancen Alaja wanda ya sha banban da na Alhaji mukhtar, shi da ya nuna ma bai san wacce aka turo ba, bai san ita ce ko wata ce su kayi ciniki da Alaja ba, shine za ta ce ya ganta sonta ya ke yi....
"Ai da nasan halinsa ba zan tura ki wajensa ba, duba har nono na kin tsosa duk da a lokacin babu ruwa a ciki, da mamanki da Babanki in sun fita sun bar min ke sai ki ta kuka ni kuma na sanya ki a nono na kina ta tsosa har kiyi bacci. Ai kin ga ni uwa ce ba zan cutar dake ba"
A hankali Bilqees ta sauke numfashi tare da ajiyar zuciya
"Je suis de'sole Maa"
Ta bata hakuri I'm sorry Maa, tana me kallon ta, riƙe take da nonuwanta tana nunawa Bilqees saboda da tabbatar da abin da take faɗa mata gaskiya ne, sauke numfashi Alaja tayi tare da sake gyara zamanta tana sake cewa
"To amma ai ba za ki zauna haka nan ba, dole ki yi aure, ko ba ki son auren?"
"Ba yanzu ba"
"Uhm I see, to anan kuma za mu sami matsala dake, ko saurayi babu?"
"I'm still young Maa"
Ta kare mata kallo, tayi murmushin da ita kaɗai ta san ma'anar sa, tare da girgiza kanta alamun mu je zuwa, sannan ta ce
"Focus on your work"
"Merci"
Godiya tayi mata thank you kenan, sannan ta ce
"Me zan yi yau?"
"Za mu yi meeting, ki haɗa min kan dukkanin ma'aikatan"
"To Maa"
Tana faɗin haka ta mik'e ta fice, Alaja ta kece da dariya ta furta
"In kin san wata ba ki san wata ba"....
************************
Maiduguri KIRAWA'S FAMILY
Yana barin ɗakin mommy ya wuce wajen Daddynsa, ya tadda su a main palour suna karyawa, yayi sallama ya iso ya zauna kan carpet ganin su ma a zaune suke kan carpet sun yi ɗaiɗai suna cikin abinci hankali kwance suna hira...
"Barkan ku da safiya"
Ya gaida su cikin girmamawa, Abbie ne ya amsa da
"Likita bokan Turai, lafiya kalau, ya aiki?"
"Alhamdulillah Abbie"
"Doctor ƙarso kai ma ka karya na san ba abin da ka ci tun safe"
Cewar Abba, sauke numfashi Wahaab yayi a hankali ya ce
"A'a Abba ku ci nawa yana cen ɗakina dana koma zan ci"
"Ai in dai Abdulwahab ne kuna ɓata bakin ku, bai ɗauki cikin abinci da muhimmanci ba"
Murmushi Wahaab yayi tare da cewa
"Daddy zan je na dawo sai mu tattauna"
"A'a ba damuwa faɗi muna jinka, ai cin abinci ba zai hana sauraro ba"
"Uhm haka ne, daman akan rashin lafiyar Mommie ne, a fitar da ita outside ɗin"
"Ko kaifa, ba damuwa zan fara shirye shiryen fitar da ita, za mu yi magana da Alhaji Shareef sai mu ga yadda abin zai kasance, kai kada ka wani damu ka ci gaba da shirin tafiyar ka"
"To Daddy na gode"
Bai jima a wajen ba ya fito, ya haɗu da Ya Sa'eed, nan kuma suka kama hira, Ya Sa'eed ya ce suje ɗakinsa, Dr Waahab ya biye masa suka tafi, nan fa sabon hira, tare su kayi breakfast, suka ci gaba da hirar su daga bisani Dr Waahab yayi masa sai anjima ya fito ya wuce ɗakinsa, ya faɗa kan bed nan da nan bacci ya ɗauke sa...
************************
Turo ƙofar da Suhaima tayi ne yasa suka ɗago dukkanin su suna kallonta, tayi sallama suka amsa. Ta zauna bakin katifa tare da cewa
"Morning ladies"
"Ke tun da Aunty Jamila tazo shikenan kika ƙaurace mana"
Cewar Ashfat, a hankali Suhaima ta sauke numfashi tana lumshe idanunta da suke nuna alamun jin bacci a tare da ita ta ce
"Aunty Ashfat ba haka bane, kwana biyu jikin Mommie ba daɗi"
"Haka ne jiya da daddare mun shiga a lokacin kina wanka Aunty Jamila ce ke tare da ita"
"Eh ta faɗa min, a bani abinci na ci"
"Suhaima ya jikin Mommy yanzu"
"Da sauƙi Aunty Hauwa"
"Allah ya bata lafiya"
"Amin"
Teemah ta ce
"Aiko ga abinci nan sai wanda kika zaɓa, ga na safe cen an ajiye miki ga kuma na rana"
"A bani kowanne ma zan ci yunwa nake ji ga bacci ma"
Nan suka zuba mata suna ci suna hira, Teemah ta ce
"Sis Ashfat rana tayi ba za ki kai wa Ya Waahab abinci ba?
"Lah kunga bari nayi maza na tashi na kai masa, yanzu haka ya tashi daga bacci"
"Ah mu namu gani ne ba mu da bakin magana"
Cewar Hauwa, su kayi dariya ita ko Ashfat ko a jikinta ta yafa mayafi tare da sake feshe jikinta da turare ta ɗauki basket ɗin ta wuce ɗakin Dr Waahab, tana isowa tayi nocking yana kwance, tashin sa kenan daga bacci tayi sallama tare da turo ƙofa ta shigo, ganin yana kwance yasa ta wuce kai tsaye in da breakfast ɗin yake, ta ajiye basket da ta shigo dashi tana ƙoƙarin ɗaukan na breakfast ɗin taji da nawi da mamaki ta ɗago sai taga ya iso inda take sanye da dogon wondo da riga me gajeriyar hannu, kwarjinin sa yasa ta kasa furta ko da kalma ɗaya ne, ta kura masa ido kamar yadda shima yake kallon ta a hankali ya sauke numfashi tare da cewa
"A ɗakin Sa'eed na yi breakfast shiyasa banci wannan ba"
Wani abu ya tokare mata maƙoahi, yanzu duk yadda ta ɓata lokacin ta amma ko takan abin da ta girka bayyi ba...
"Ki baiwa Baba Musa abincin"
"Uhm to"
Ta faɗa a hankali jiki ba kwari ta nufi ƙofar fita taji ya kira sunanta
"A'isha"
Dif ta tsaya, a hankali ta juyo ba tare da ta ce komai ba, ya ce
"Ki tafi da wannan ma, bani jin yunwa kada ya ɓaci"
Kamar tayi kuka, ta tako ta iso ta ɗauka, ta juya da sauri kamar ta kife don ɓacin rai taji ya sake kiran sunanta
"Ashfat"
A ranta ta ce "sai kayi kuma, mutum sai shegen miskilanci"
Ta ce
"Na'am Ya Wahaab"
Takowa yayi zuwa inda take tsaye, yayi magana kamar bakinsa nayi masa ciwon
"Ba sai kin sake wahalar da kanki ba, wajen girka min abinci ba don ban fiye cin abinci ba wani lokacin, amma dana buƙata zan faɗa miki sai ki girka min"
Ta haɗiye abin da ya tsaya mata a maƙoshinta ta ce
"Na ji"
Ya sauke numfashi yasan ranta ya ɓaci to amma hakan shine daidai ba zayyu ta wahala wajen girka masa abinci kuma bai ci ba ko abincin ma ya ɓaci ayi asara, a hankali ya ce
"Na gode da gyaran ɗaki"
"Uhum"
Ta juyo kamar ta kife ta iso ɗakinsu da basket har guda biyu ta tadda ƴan'uwanta su uku daga ɗayan side ɗin sun shigo, tana ƙarasa shigowa ta dire basket ɗin a ƙasa ta ajiye cikin ɓacin rai, ta zauna bakin katifa sai hawaye....
Comments and share fisabilillah