Chapter 1
TARIHIN DAULAR KILA
Shekara Dari Biyu da Talatin da Biyar da Suka Gabata (1790)
Daular Kila ta kasance ɗaya daga cikin tsofaffin masarautun da suka yi suna wajen adalci, jarumtaka da kuma kare mutuncin al’umma. An kafa ta ne a cikin wani kwari mai yalwar noma, kiwo da kasuwanci, wanda ya haɗa hanyoyin matafiya daga gabas da yamma. Sunan Kila ya samo asali ne daga wani tsohon jarumi mai suna Kilan Dabo, wanda shi ne ya fara haɗa ƙabilu daban-daban ƙarƙashin tuta guda.
Tun kafin kafuwar masarautar, yankin ya kasance cike da ƙananan ƙauyuka masu cin gashin kansu. Sai dai yawan rikice-rikice tsakanin shugabanninsu ya hana zaman lafiya. A lokacin ne Kilan Dabo ya tattara dattawa da mayaƙa, ya sasanta su, sannan aka kafa Daular Kila bisa ginshiƙai uku: adalci, gaskiya da haɗin kai.
Kafin kafuwar Daular Kila, yankin ya kasance ƙauyuka ne da dama da suke rayuwa dabam-dabam. A wancan lokaci, yawancin al’ummar yankin suna bin addinin gargajiya, inda suke bautar iskoki, manyan itatuwa, duwatsu da rafuka. Akwai wani babban tafki da ake kira Ruwan gujus, wanda ake ɗauka a matsayin wurin tsafi. Kowace shekara ana kai hadaya a bakin tafkin domin neman ruwan sama, kariya daga annoba da yalwar amfanin gona.
Dattawan ƙauyukan sun yi imanin cewa ruhun tafkin ne ke ba su albarka, saboda haka duk wanda ya karya dokokin tsafin, ana ɗaukar cewa zai jawo masifa ga ƙasar baki ɗaya.
Shekaru da dama bayan haka, wasu malamai masu yaɗa addinin Musulunci suka iso yankin Kila ta hanyar ayarin ‘yan kasuwa daga ƙasashen sokoto da Borno. Sun fara wa’azi cikin hikima da haƙuri, suna koyar da tauhidi, ibada da kyawawan ɗabi’u.
Da farko mutane da dama sun ƙi karɓar saƙon Musulunci saboda tsoron barin al’adunsu. Amma a hankali, sakon ya fara shiga zukata. Dattawa da matasa suka fara musulunta, aka fara gina ƙaramin masallaci na laka, sannan aka fara koyar da Alƙur’ani ga yara da manya
Lokacin da Sarki Kilan Dabo ya hau karagar mulki, ya rungumi Musulunci tare da manyan fadawansa. Ya bayyana cewa addinin Musulunci shi ne zai zama ginshiƙin shugabancin Daular Kila. Ya rusa wuraren bautar gumaka da tsafe-tsafe, ya hana yin hadaya ga rafuka da itatuwa, sannan ya umarci a gina Babban Masallacin Juma’a a tsakiyar masarautar.
Duk da haka, bai tilasta wa kowa musulunta ba. Ya yi amfani da hikima da adalci, lamarin da ya sa al’umma suka riƙa shiga Musulunci sannu a hankali har addinin ya bazu a faɗin Daular Kila.
Bayan tabbatar da zaman lafiya da haɗa ƙauyuka goma sha biyu ƙarƙashin tutar masarauta guda, Sarki Kilan Dabo ya kafa tsarin mulki na farko na Daular Kila. Ya kafa Majalisar Dattawa, rundunar mayaƙan fada, da dokokin da suka haramta zalunci, cin hanci da kwace haƙƙin talakawa.
Saboda hikimarsa da adalcinsa, ana kallon Sarki Kilan Dabo a matsayin Uban Daular Kila, kuma har bayan rasuwarsa ana ci gaba da ambaton sunansa a matsayin sarkin da ya kafa masarautar tare da shimfiɗa tubalin Musulunci a cikinta.
Masarautar ta bunƙasa ƙwarai ta fuskar noma, kasuwanci da ilimi. A kowace shekara ana gudanar da bukukuwan gargajiya da na addini cikin haɗin kai, lamarin da ya sa Daular Kila ta zama abin koyi ga sauran masarautu.
Daga cikin manyan al’adun masarautar akwai Hatimin Sarauta, wanda ake ɗaukarsa a matsayin alamar halaccin mulki. An ce tun daga Sarki na farko aka ajiye wannan hatimi a wani wuri na sirri a cikin fadar masarautar. Ba wanda zai iya taɓa shi sai wanda jinin sarauta na gaskiya ne . Duk lokacin da aka samu rikici ko ruɗani game da magaji, wannan hatimi ne ke tabbatar da gaskiya.
Tun daga wannan lokaci ne Daular Kila ta fara samun jerin sarakuna masu ɗauke da tarihi daban-daban, wasu sun yi fice wajen yaƙe-yaƙe, wasu wajen ilimi, wasu kuma wajen shimfiɗa adalci har sun bar tarihi da ba zai taɓa gogewa ba.
A haka ne Daular Kila ta ci gaba da bunƙasa ƙarƙashin jagorancin zuriyar Sarki Kilan Dabo. Karagar mulki ta riƙa gadon jini daga uba zuwa ɗa, ko kuma ga wanda ya fi cancanta daga cikin gidan sarauta, bisa shawarar Majalisar Masarauta. Tsawon shekaru masu yawa, sarakuna goma sha huɗu suka yi mulki, kowannensu yana ƙara wani tubali na cigaba, adalci da ɗaukakar Daular Kila.
A ƙarshe, bayan rasuwar Sarki na goma sha huɗu, Allah Ya nufi mulki ya koma hannun Mai Martaba Alhaji Sarki Salim Jalaluddeen Kila, wanda ya zama Sarki na goma sha biyar a tarihin Daular Kila.
Sarki Salim ya yi fice da hikima, adalci da tsoron Allah. A zamaninsa ne Daular Kila ta kai wani matsayi na cigaba da zaman lafiya da ba a taɓa ganin irinsa ba. Jama’a daga masarautu daban-daban suna kawo ƙorafe-ƙorafensu zuwa fadarsa saboda sun yi imani da adalcinsa. Haka kuma ya mayar da ilimi, addini da jin daɗin talakawansa a matsayin ginshiƙan mulkinsa.
DAWOWA LABARI
A cikin babban fadar Masarautar KILA shiru ya ratsa ko Ina a cikin masarutar . Bayin fada suna tafiya a hankali cikin dogayen zauruka, kamar suna tsoron ko ƙarar takun su zai iya tayar da wani abu da bai kamata ya tashi ba. tsuntsayen lambun fadar ma sun yi shiru, kamar an rufe musu baki.
---
SASHI NA ɗAYA
YARIMA JALAL
A saman bene a daya daga cikin sashekan cikin masarautar, Yarima Jalal yana tsaye a bakin doguwar taga , yana kallon birnin Kila daga nesa.
Shi wani irin mutum ne mai nutsuwa da idan ya shiga wuri, ko ba ka san shi ba, sai ka ji yanayi ya sauya.
Fata mai ɗan duhu, dogon jiki mai cike da ƙarfi, idanu masu zurfi kamar suna ɓoye sirrin da ba ya son kowa ya taɓa. A fuskarsa akwai natsuwa amma ba ta lafiya ba. Natsuwa ce ta mutum da ya koyi ɓoye zafi.
Bayan sa, wata murya yajiyo
"Ranka ya dade
Allah ya ja zakamin sarki mai jiran gado ... Sarki yana Neman dukkan 'ya'yansa maza."
Jalal bai juyo nan take ba.
Sai ya ɗan matse yatsunsa a gefen taga.
"Dukkan 'ya'ya maza," ya maimaita a hankali.
Ya ɗan yi shiru.
Wannan na nufin Yarima Fahad ma.
Jalal ya juyo.
"Ya ce me ya faru?"
Bawan ya sunkuyar da kai ƙasa. "A'a ranka ya dade. Amma... dattawan fada sun riga sun taru."
Idanun Jalal suka ɗan tsuke.
Taron dattawa ba tare da sanarwa ba yana nufin abu guda: wani hukunci mai girgiza masarauta
---
YARIMA FAHAD
A ɗayan gefen fadar kuwa,Yarima Fahad ne
Ya jingina da wani babban ginshiƙi, yana riƙe da kofin abin sha mai daɗi, yana murmushi kamar duniya ba ta taɓa damunsa ba. Kyawunsa yana da sauƙin lura amma halinsa ya fi jawo hankali.
"Su taru kawai," ya ce yana murmushi. "Dattawa suna son hayaniya fiye da yadda mata ke son zinari."
Abokinsa ya dubi shi da damuwa. "Ranka ya dade... wannan taron ba kamar na yau da kullum ba ne."
Fahad ya ɗan sha abin shansa.
Dole mu fara sabawa da wannan lamuran na fada domin ko mu dade ko mu jima tsakanin ni da Yarima jalal dole za a samu sarki.
---
BABAN DAKIN SARAUTA
A tsakiyar fada, Babban Dakin Sarauta ya tsaya chak
Wurin da ba a rubuta tarihi da tawada sei dei da yanke shawara.
Wurin kujerar Sarki babu kowa a kai.
Amma dattawa sun riga sun zauna.
Lokacin da yayan sarauta suka shigo daga bangarori biyu dabam.
Shiru ya mamaye dakin sarautar
Lokacin da dattijo mafi tsufa a cikin majalisar ya miƙe, dukkan idanu suka koma kansa. Hannunsa na rawa kaɗan---ba saboda tsufa kawai ba, amma saboda nauyin abin da zai faɗa.
Ya kalli kujerar sarauta da babu kowa a kai.
Sannan ya ce:
"Wannan masarauta ba ta cikin natsuwa."
Wata ƙaramar hayaniya ta ratsa dakin, amma ya ɗaga hannu ya dakatar da su.
"An samu alamar cin amanar cikin gida saboda an San Sarki salim yana kwance bashi da lafiya
Nan take, idanun Yarima Jalal suka canza na tsananin kulawa, Kamar wanda wannan magana ta shafi shi kai tsaye.
A ɗaya gefen dakin, Yarima Fahad ya ɗan karkata kai, yana kallon dattijon kamar yana jin labarin wasa ne.
Amma a ƙasan murmushinsa, akwai wani abu.
Dattijon ya ci gaba:
"Daga cikinmu ... akwai wanda ake zargi da haɗin kai da masu neman rushe mulki."
Shiru ya sake mamaye dakin
Nan take, ƙofofin dakin suka buɗe da ƙarfi.
Wani soja ya shigo da sauri, ya sunkuya ya ce:
"Ranka ya daɗe... an gano wani mutum a cikin harabar fadar. Yana ƙoƙarin shiga ɗakin takardun sirri."
Dattawa suka tashi cikin firgici.
Jalal ya matsa gaba nan take.
Fahad ma ya tashi, amma a hankali, kamar wanda yake kallon abin nishadi.
A waje, iska ta yi sanyi furanni sei kadawa suke yayin da bishiyoyi suma suke ta rawa, Sojoji suka fito da wani mutum a daure.
Amma kafin a kai shi gaba... Mutumin ya ɗaga kai ya kalli Yarima Jalal kai tsaye.
Ya faɗi kalma ɗaya:
"Ba ni kaɗai ba ne... Daga cikin ku... akwai wanda ya saka mu sato hatimin sirrin kila da sayar da shi ga wanin da ba dan sarautar ba.
Hayaniya ta kaure a dakin
Jalal ya tsaya cak.
Fahad ya yi shiru gaba ɗaya, murmushinsa ya ɓace.
Nan take Yarima Fahad ya matsa gaba. Idanunsa suka yi ja da fushi yayin da yake kallon bawan da aka kama.
Lebbensa suka motsa a hankali, amma muryarsa ta fito da ƙarfi.
"Sarkin Dogarai!"
Cikin sauri, Sarkin Dogarai ya fāɗi ƙasa yana kwasar gaisuwa.
"Ranka ya daɗe, Yariman Yarimomi. Allah Ya ja zamaninka."
Fahad ya ɗaga hannu kaɗan.
"A ɗauke shi. A kai shi ɗakin tsaro. A tsare shi sosai. Kuma a yi masa horo mai tsanani har sai ya faɗi gaskiyar da yake ɓoyewa."
"An gama, ranka ya daɗe."
Sarkin Dogarai ya amsa cikin biyayya.
Nan take dogaran fada suka yi gaba, suka kama bawan daga hannuwansa. Ya yi yunƙurin magana, amma kafin ya furta komai aka janye shi daga cikin zauren.
Muryarsa ta ci gaba da amsa kuwwa a cikin fadar.
"Na rantse ban yi laifi ba! Wallahi akwai abin da ba ku sani ba!"
Amma babu wanda ya saurare shi.
Da ƙofofin zauren suka rufe, shiru ya sake mamaye wurin.
Dattawan fada suka kalli juna.
Wasu suna cikin tunani. Wasu kuma suna cikin shakku.
A gefe guda kuwa, Yarima Jalal ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci.
Sai ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya.
"Ya Allah..."
Ya furta a cikin zuciyarsa.
Akwai wani abu game da mutumin nan da ya hana zuciyarsa samun natsuwa. Tun lokacin da aka kama shi, Jalal yake jin kamar akwai wani ɓangaren gaskiya da har yanzu ba a gano ba.
Amma bai da hujja. Ba zai iya magana ba.
---