BABI NA HUƊU
💎🌹 Haula Habeeb🌹💎
Story Written By
Amdeey Tejj d'Unique ✍️
BABI NA HUƊU
HAZ Construction Company
Habeeb
Idanunsa da suka fara sauya kala ya zuba masa, yana kallon yadda yake aikin gabansa ya yi banza da shi kamar bai san Allah ya yi ruwan halittarsa ba. Ransa ya fara ɓaci da wulaƙancin da Salim ɗin yake yi masa. Tun a gida ya je ya same shi yana shirin fita, yana kallo ya san wajensa ya zo amma ya yi banza da shi. Yanzun ma zuwansa Construction Company ɗin kenan, kuma don shi ya zo, don shi ko baƙo ne ya zo da yaushe yake zuwa ba, sai abu muhimmi ko patrol ya kawo shi. A yanzu da ya zo tun ɗazu yake zaune, amma Salim ya ƙi ya yi masa magana. Shi kuma ya ma rasa ta inda zai fara, ya rasa abin da zai ce masa, kuma Salim ɗin ya san ya rasa abin faɗan ne, amma ya yi ɗibar shara da shi.
Tashi ya yi ya nufi ƙofa ya fice, rai a ɓace. Bai tsaya ko ya bi takan masu gaishe shi ba, ya nufi lift ya sauko last floor, ya fito daga liftar. Har ya wuce sai kuma ya dawo, ya ɗaga hannunsa da ya cika da wani yanki na fushin da ke ransa, zuciya na tafarfasa, ya sauke a kan ɗaya daga cikin mutane ukun da ke tsaye cikin reception ɗin Company ɗin suna magana.
Dum! haka mutumin ya ji jin sa ya ɗauke, kafin ya yi wani tunani ko hasashen abin da ya same shi, numfashinsa ya yi sama ya dawo, raf ya zube a sume.
Shi kuwa Habeeb da jajayen idonsa masu kama da garwashi, ya nuna sauran biyun da ɗan yatsansa alamar gargaɗi yana tauna baki. Su kuma suka ja da baya a tsorace. Bai ce wa kowa komai ba, ya fice daga reception ɗin baki ɗaya. Yana fita ya nufi motarsa ya shiga, already mai gadi ya san ba ya jira, don haka da ya gan shi ya nufi mota, a rikice ya nufi gate. Tun kafin ya tada motar ya wangale gate ɗin, shi kuma da mugun speed ɗin da ya zarce ƙa’ida, ya fice daga Company ɗin.
Salim
Ya ɗago da nufin ya yi magana, don dama ba wai ya yi banza da shi ba ne, don ya san tun da ya tako ya zo, to yana so su shirya ne. Shi kuma dama sam ba shi da riƙo, ƙin kulashi da ya yi a gida ma sauri yake yi. Kuma idan ya tsaya za su ɓata lokaci sosai, idan bai kawo project ɗin da yake aiki on time ba kuma ya yi ta yi masa masifa. Yanzu ma barinsa ya yi sai ya gama sai su yi magana. Bai ma san ya fita ba saboda yadda ya maida hankalinsa a kan aikin, duk da da ƙarfi ya rufo ƙofar, amma sam bai ji ba. Ya ɗago kenan kuma ya ga wayam baya nan.
A rikice ya miƙe ya nufi ƙofa, hankali a tashe don ya san da fushi ya fita, kuma ya san akwai matsala. Jikin lift ya je, lokacin kuma Habeeb yana ciki bai sauka ba. Ganin zai ɓata lokaci ya sa bai iya jira ba, ya nufi stairs da sauri, bibbiyu yake haɗawa don ya yi sauri. Yana saukowa last floor, motar Habeeb na ficewa. A rikice ya ƙarasa zuwa wajen mutumin da ke sume, bai tsaya bin ba’asi ba, don ya san aikin wane ne, ya ba da umarnin a yi maza a kai shi asibiti.
Ficewa ya yi ya hau mota shi ma, dama already mai gadin bai gama kulle gate ba, hakan ya sa bai jira ba ya kulle, shi ma ya fice, hankali a mugun tashe, lokaci guda yana gwada lambar Habeeb ɗin.
HAZ Mansion
Haula
Ta sake turo browny lips ɗinta gaba tana bin uniform ɗin da Gwaggo ta watsa mata a jikinta. Ta kau da kai kafin ta ce, “Ni fa Gwaggo ba zan sake zuwa waccan baƙar makarantar da ba su san darajar iyaye ba. Tsakani da Allah sai su ajiye yaran mutane su yi ta zaginsu. Dama wancan satin ma da na ƙarasa zuwa ƙawayena na je yi wa sallama in gaya musu na bar zuwa makarantar. Kawai ki canza min makaranta shi ne magana.” Ta ƙarashe zancen tana tura baki.
Takaici ne ya sa Gwaggo ta kasa magana, sai bin ta da ido kawai da take yi. Tuna ta bar girki a wuta ne ya sa ta fice daga ɗakin tana faɗin, “Ki bari in dawo in same ki ba ki shirya ba, ki ga yadda za mu yi da ke.”
Oho, ko a jikinta. Ita dama makarantar ta ishe ta, dole ya sa take zuwa ba don tana so ba. “Haba makaranta sai Turancin tsiya, ai ko sarauniyar Ingila ma sai ta sara musu, ko ma ya sunanta, oho dai ni ma na manta.” Ta furta a fili ita ma tana barin ɗakin.
Waje ta fito harabar gidan tana kallon yadda ma’aikata ke kai-kawo. Ji ta yi kamar ta je wajen mai gadi su yi hirarsu yadda suka saba, to amma Salim ya hana ta. Lambu ta nufa, a ranta tana fatan Allah ya sa Salim na can.
Mommy
“Innalillahi Wa Inna Ilaihirraji’un! Alhaji! Alhaji!! Alhaji!!!” Cewar Mommy kenan da ke saukowa daga stairs, hankali a mugun tashe. Kallo ɗaya za ka mata ka fahimci hakan, kamar za ta kifa ta ƙaraso cikin parlour ɗin, da har kowa da ke cikinsa ya miƙe tsaye yana jiran jin abin da za ta ce, don wannan kiran kam ba lafiya ba.
Tana ƙarasowa ta fashe da kuka tana faɗin, “Ya mutu Alhaji, wallahi ya mutu! Wayyo Allah na shiga uku, shikenan!”
Daddy da bai gane inda zancen ya dosa ba ya ce, “Wai wa ya mutu ne iye? Ki yi min bayani yadda zan fahimta.”
“Son, Alhaji son ne, Son!” ta kasa ƙarasawa saboda kukan da ya ci yota.
Nan fa kowa hankalinsa ya tashi. Daddy cikin saurin nutsuwarsa ya ce, “Me ya samu Son ɗin? Ina yake?” Bai ƙarasa maganar da ke shirin yi ba, wayar Mommy da ta yar ta ɗauki ruri. Da hanzari ya ɗauka kasancewar yana kusa da wayar, sunan likitan su ya bayyana a screen ɗin wayar. Da sauri ya ɗaga yana faɗin, “Doctor, what happened to my son? Where is he?” Sama-sama yake jin maganar, saboda network ya hana ya ji abin da yake cewa.
Ajiye wayar kawai ya yi ya miƙe tunda ya fahimci abin da ke faruwa. Kallon Uncle Bulama da yanzu yake shigowa parlour ya yi, ya ce, “Mu tafi asibiti, Son ba lafiya.” Daga nan ya fice, Uncle Bulama ya bi bayansa. Wuf! Mommy ta tashi ta bi bayansu ko mayafi babu.
Tahir ya yi tsaki ya fice daga parlour yana faɗin, “Zancen kenan, kullum Habeeb Habeeb mtswww. Allah ya sa daga can ma sai dai a kawo labarin mutuwarsa.”
Mami ta taɓe baki tana mai komawa kan kujera, ta ci gaba da abin da ke gabanta.
Salim
“Mr Salim, sorry, amma ya kamata ka samu wuri ka zauna. Sir Habeeb In Sha Allah will be fine, because now everything is okay, so muna hoping zai farka lafiya.” Cewar likitan kenan bayan ya fito daga A/E room, ganin yadda duk hankalin Salim ya tashi, tunda suka shigo asibitin ya kasa zama sai kai-kawo yake yi.
Girgiza kai Salim ya yi ya ce, “I can’t, Doctor. Hankalina ba zai taɓa kwanciya ba bayan ɗan’uwana yana cikin wannan yanayin.” Maganar su Mommy ne ya sa dukkansu suka mai da hankalinsu gare su.
Daddy ya ƙaraso ya ce, “Dr, ya ake ciki? Ina shi Son ɗin?”
“Alhaji ku kwantar da hankalinku, mu je ciki.” Cewar likitan yana mai musu iso zuwa office ɗinsa.
Bayansa suka bi, dukansu zuwa office ɗin. Zama suka yi banda Salim, wanda ya jingina da bango ya lumshe idonsa. Shi fa tun ɗazu kawai zargin kansa yake yi da ɗora wa alhakin faruwar komai, don gani yake da bai share shi ba, da komai bai faru ba.
“Muna sauraron ka,” Daddy ya faɗa yana kallon likitan.
“Calm down, Alhaji. The accident is minor, Allah Ya kiyaye. Kuma ba rauni ba karaya, kawai dai da alama he was angry during the time he was driving, and he was shocked. Yanzu mun ba shi bed rest, In sha Allah idan ya farka za ku iya tafiya gida. And don Allah a kiyaye ɓata masa rai, don kun san condition ɗinsa. Ban yi expecting ma ciwon shi ba zai tashi ba.” Ya ƙarashe maganar da ɗan murmushi yana kallon Mommy, a ransa yana mamakin da shi kaɗai ya san abin nasa.
Ajiyar zuciya suka sauke baki ɗaya su, kafin Daddy ya ce, “To, ma sha Allah, thank you Doctor. Tunda an tabbatar da komai lafiya, zan wuce. Idan ya farka sai ka yi noticing ɗina, don dama na zo ɗaukar abu ne. Sai ku bar shi da Salim, ku zo mu je.” Daga haka ya miƙe.
Mommy cike da damuwa ta ce, “Amma Alhaji, ka san ba zan iya tafiya in bar yaron nan ba. Amma likita, zan iya ganin shi?” Ta mayar da maganar zuwa ga likitan.
“Yes, za ki iya ganin shi amma sai nan da thirty minutes.”
Shi dai Salim da ido kawai yake bin su, don tun bayan gama bayanin likitan ba fahimtar abin da suke cewa yake yi ba. Kawai shi dai yana tsaye ne a wajen, ga shi nan dai.
Haula
“Haula! Haula!!” Cewar Gwaggo kenan tana mai shigowa cikin parlour ɓangarensu.
Haula da ke zaune kan kujera da sauri ta kwanta jiki a rufe, a dole ita tana barci.
Gwaggo ta ƙaraso ta tsaya a kanta tana kallonta. Daga yadda take mammatse ido, ta san ba barci ta yi ba, iskance ne kawai. Girgiza kai ta yi kafin ta ce, “Za ki tashi ne daga wannan baccin ƙaryar taki ko sai na yi miki duka?”
Ta maƙale murya can ciki don a yarda da ita, ta ce, “Gwaggo, ba ni da lafiya ne fa, tun ɗazu sai rawar sanyi nake ji, ni kamar ma zazzaɓi nake yi.” Ta yi maganar tana ƙifƙifta ido.
Cike da haushi Gwaggo ta ce, “Dallah! Tashi min in ga wuri. Ba kin ƙi zuwa makaranta ba? To dama in ba ki yi sharan masallaci ba, za ki yi na kasuwa, don haka tashi ki wuce mu je kitchen.” Ta yi maganar tana nuna mata hanya da ɗan yatsanta.
Ai ko tana jin an kira kitchen, ran ta ya yi baƙi. Ita fa ta tsani duk wata harka da ta shafi girki, ta fi gane a dafa a kawo ta ci. Kamar za ta fashe da kuka ta ce, “Don Allah Gwaggo ki yi haƙuri, wallahi ba ni da lafiya. Taɓa jikina ma ki ji kamar wuta.” Ta miƙe tana ƙoƙarin kamo hannun Gwaggo.
Ja da baya Gwaggo ta yi tana faɗin, “Kin san Allah, ko mutuwa kike sai kin je kitchen ɗin nan don haka wuce mu tafi. Ba dai kin ce ba za ki makaranta ba? To mu zuba da ni da ke, wanda ya fasa, shige mu tafi in ga wuri.”
Ta zumɓuro baki gaba kamar za ta ture Gwaggo da shi, ta yi gaba fuuu. Gwaggo ta bi bayanta, a ranta tana yi mata addu’ar shiriya.
Suna isa kitchen ɗin, suka hau aiki. Ta na yi tana baƙin rai, ita kuwa Gwaggo kamar ba ta san ta na yi ba, aikin gabanta kawai take yi.
Yanka kabeji take yi, ta dage sai faskara take yi kamar za a ba dabbobi. Gwaggo ƙuri ta yi, ta zuba mata ido tana kallonta. Ita kuwa ta yi fuska kamar ba ta san tana kallonta ba, can ta nisa kafin ta ce, “Yanzu Haula, haka ake yanka kabejin?”
Ta ƙara turo bakin gaba ta ce, “To ai kin san ban iya ba, kika ba ni.”
“Ki ci gaba Haula. Ke ba kya jin magana ba, ki yi, akwai ranar da za ki gane abin da nake faɗa miki. Ke ki ce ba kya son girki, to bari ki ji. Duk wani isa da ’ya mace take ji da shi, idan ba ta iya girki ba aikin banza ne. Ki bar ganin wannan kyan naki kamar ’yar Aljanu, wallahi Allah idan ba ki iya girki aikin banza ne. Mummuna da ba ta fi ki komai ba daga ƙirar halitta, sai ta fi fada a wajen mijinki. Ki ci gaba, za ki tuna da zancena watarana ko ba na raye.”
Faɗin Gwaggo kenan, wanda da ta san abin da ke jiran Haula nan da lokaci kaɗan, da ta janye kalamanta masu kama baki a rayuwar Haula. Sai dai kash! Sirrin Allah sai Lillahi, ba wanda ya san gaibu, ba ka san ranar da tsautsayi zai faɗo maka ba, balle ka guje shi.
Ita kam Haula taɓe baki ta yi ko a jikinta. Ita da za ta auri mai kuɗi, me zai haɗa ta da kitchen? Ai sai dai ita ma ta dinga irin na ’yan gayu, ta wanke goma ta tsoma biyar. To in banda abin Gwaggo, yanzu ba ga matan gidan nan ba, ba wacce take shiga kitchen, amma ko kishiya ba su da ita, to ai su ba su damu da wannan ba.
Tunanin Haula kenan, ba tare da ta san ƙaddarar da ke jiranta ba nan da wani lokaci kaɗan.
Nabila ce ta shigo kitchen ɗin ko sallama babu balle gaisuwa, tana faɗin, “Wai kin gama abincin Yaya? Wai ki fito da shi za a tafi kai masa asibiti.”
Gwaggo ta ce, “To gani nan, na gama, barin ƙarasa kwashewa.”
Nabila ta fice daga kitchen ɗin ba tare da ko amsawa ba, dama Nabila akwai raini.
Waye kuma ba lafiya? Haula ta tambayi kanta. Da sauri ta miƙe ta nufi Gwaggo tana tambayarta waye ba lafiya, ba tare da ta kalle ta ba ta ba ta amsa. Tsalle ta yi ta dire tana faɗin, “Haba mutane sun samu su sha iska mana. Yau kam akwai hira ni da Yaya Salim, shi kuma ya je can, Allah ma ya sa asibitin su yi ta riƙe shi kar ya dawo.” Dukan da Gwaggo ta kai mata a kan baki ne ya sa ta yi shiru ba ta ƙarasa abin da take son cewa ba.
Cikin takaici Gwaggo ta ce, “Wai ke wata irin mutum ce? Ki ci gaba, ba shi ɗin maƙiyinki ne ba. Idan masu gidan suka ji ki, kya yi musu bayani.” Daga haka ta ja basket ɗin da ta shirya abincin a ciki ta fice daga Kitchen ɗin.
Ita kuwa Haula ta taɓe baki, a ranta ta ce, “Oho dai makaranta ce ba za ni ba, idan abin daɗi ne mutum shi ma ya je mana.” Ita ma ta fice daga kitchen ɗin, kafin ta dawo ta sake ba ta wani aikin.
HAZ Clinic and Maternity
Habeeb
Ya sake damƙe hannun Salim da ke cikin nasa, lokaci guda yana sake rintse idonsa, ya haɗiye, ya tauna leɓɓansa da mugun ƙarfi, zufa sai tsattsafo mai yake yi daga duk wani lungu da saƙo na jikinsa.
Salim da ya kwantar da kansa gefen gadon da Habeeb ɗin ke kwance a kai, hannunsa ɗaya cikin nasa, ya ware ido da cikin azaba da sauri jin ana shirin markaɗa hannunsa. Ƙoƙarin fara zame hannun nasa ya fara, ganin yadda Habeeb ya yi musu wani irin damƙa, sai dai ya kasa. Ganin idan ya dage za su ɓalla hannun ne ya fara ƙoƙarin tashinsa, don ya fahimci wannan mafarkin nasa ne yake yi.
Ganin halin da yake ciki, tuni ya manta da zafin da yake ji, ya fara ƙoƙarin tashinsa. Jijjiga shi yake yi da ƙarfi yana kiran sunansa, a wani irin zabure kamar an yi masa allurar ƙarfi, ya wani irin rungume shi da sai da ya ji kamar zai raba masa ƙasusuwa, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri. Shi dama Salim kusan ya saba da irin wannan azabar a duk lokacin da ya shiga irin wannan hali.
Sun ɗau lokaci suna a haka, kafin ya sake shi don karan kansa. Komawa ya yi ya kwanta ya rufe idonsa ruf, kai ka ce barci yake. Sannu Salim ya yi, amma ko alamar ya ji bai nuna ba.
Bai damu da yadda ya rufe idonsa ba, don shi ya san dalilin da ya sa ya rufe idanun nasa. Suna a haka, likitoci suka shigo. Sai da suka gama duba shi, yana kwance kai ka ce barci yake. Ganin bai motsa ba ne ya sa likitan tambayar Salim ko bai farka ba.
“A’a, ya farka,” Salim ya ba shi amsa.
Kai kawai likitan ya jinjina, don shi ma ya san halinsa, tunda ba baƙo ba ne a asibitin, asali ma dai asibitinsu ne. Sallama ya yi musu, ya ce idan ya gama hutawa za su iya tafiya gida, daga haka suka fice.
Suna fita, su Mami suka shigo da gaba ɗayan su, da su Mommy dama ta ɗan fita ne.
“Sannunku da shigowa,” cewar Salim.
“Yauwa Salim sannu, bai farka ba ne?” cewar Mommy.
“Ya farka, Dr ma ya ba mu sallama.”
“To Alhamdulillah ai, ashe jikin ba sosai ba ne,” Mami ta faɗa tana neman wuri ta zauna, lokaci guda tana faɗin, “Sannu Son, ya jikin?”
Bai ko motsa ba balle ya dubi waɗanda suka shigo. Mommy ce ta ƙarasa gaban gadon ta zauna ta kamo hannunsa, kafin ta ce, “Son, ko akwai inda yake maka ciwo ne a kira likitan?”
Ba tare da ya buɗe ido ba, murya can ciki kamar ba ya son maganar ya ce, “Mu tafi gida Mommy.”
Ɗan murmusawa ta yi, kafin ta ce, “Dama yanzu za mu tafi ai, tunda an sallame mu, amma sai ka ci abinci.” Ta kai hannu ta ɗauko basket ɗin da su Mami suka zo da shi.
“No need Mommy, mu je kawai.” Ya miƙe zaune yana kau da kai gefe don kar ya haɗa ido da kowa.
Mommy za ta yi magana, ya riƙo hannunta ya matsa. Shiru ta yi ta fasa maganar don ta fahimci abin da yake nufi.
HAZ Mansion
“Haula, ki je ki gyara wa Alhaji Ƙarami ɓangarensa, Hajiya ta ce an ba su sallama za su dawo yanzu. Kin ga yau aikin nan ya caɓe min, ke kuma idan na bar ki da shi ba iya yi za ki yi ba. Kuma kin san ba ya so wani ya gyara masa ɓangarensa ba ni ba.” Gwaggo ta faɗa tana mai yin aiki cikin hanzari, don lokaci ya riga ya ƙarato, ga masu gidan da mita idan ba a gama abinci da wuri ba. Duk yawan aikin abincin gidan ita kaɗai take yi, wanda kuma ita ta zaɓar wa kanta hakan, don akwai ma’aikata da yawa a cikin gidan. Duk wani aiki da ya shafi kitchen ita take yi, hatta shara, wanke-wanke da goge, haka zalika gyaran ɗakin Habeeb. Duk iya yawan aikin da zai sha mata kai, ko da an yi baƙi aikin gidan ya ƙaru, ba ta bar wani ya je ya yi ba. Su ma kuma masu gidan sun sakar mata, don sun yarda da ita sosai, kuma sun bari a kan cewa don ta saba hidimar Habeeb ɗin ne tun yana yaro kasancewar ita ta rene shi.
“Ni fa Gwaggo ba zan je ɗakin wancan mai kama da muzurun ba, mutum sai shegen masifa ya dinga yi wa mutane bala'i da wannan manyan idon nashi masu kama da marufin ƙwanƙwalati. Ki dai gama aikin ki je, haka kawai ya ce na yi masa wani abu a ɗaki. Alƙur’an ya yi min sharri, ba zan yarda ba. Ni sam ban ma san dalilin da ya sa asibitin nan suka sallame shi ba, da sun yi ta riƙe shi har...” Dukan da Gwaggo ta kai mata a baki ne ya sa maganar ta koma ciki, ba don ta shirya ba.
Cikin faɗa Gwaggo ta ce, “Wai ke mutum ce ko aljana Haula? Sam wannan kunnen naki ba ya jin bari ko yi, sai dai abin da kika ga damar yi shi za ki yi. Mutumin da kike ci kike sha a ƙarƙashinsa, ki kwana ki tashi a inuwarsa, amma kike fatan ya daɗe a cikin ciwo. Ba don shi ba, da an daɗe da korata har ke ma a gidan nan, don ba za su iya jure irin wannan mummunan halin naki ba. Kar ki tashi ki je ki yi abin da na sa ki, ki ci gaba da zama kin ji. Dama ina da cikinki wallahi Haula, sai kin ga yadda za mu yi da ke a gidan nan. Daga nan in tattara in mayar da ke can ƙauye, ki je ki ci gaba da yawo tsakanin mangoro da giginya, don ba zai yiwu in zauna in zuba ido a kore ni a aikin da nake yi shekara da shekaru tun ba ki zo duniya ba saboda ke.” Daga haka ta juya ta ci gaba da aikin gabanta ba tare da ta sake bi ta kanta ba.
Jin wannan maganar a bakin Gwaggo, ta san ranta ya yi matuƙar ɓaci ne. Jikinta ya yi sanyi ba don komai ba, sai jin za a mayar da ita ƙauye. Ta daina cin kaza da shan lemun roba kenan? Ta miƙe kamar munafuka, sumi-sumi ta fice daga kitchen ɗin.
Sai da ta fito ta nufi hanyar ɓangaren nasa, ta tuna da dalilin da Gwaggo take mata faɗa. Saboda wannan mutumin, Gwaggo har take cewa za ta mayar da ni ƙauye, wato ta fi sonsa a kaina kenan. Saboda shi Gwaggo ta ɓata mata rai, bayan wanda take ciki na saka aikin dole da aka yi. Wani tunani ya zo kanta, ta murmusa ta ce, “Ai ko, ya sin akanka zan rama.” Ta furta a fili, daga haka ta ƙara da sassarfa ta isa ɓangaren nasa.
Habeeb
Motar su tana parking, da sauri securities suka zo suka buɗe musu ƙofa. Yana fitowa bai bi takan kowa ba, ya nufi ɓangarensa.
Mommy ta yi saurin tsayar da shi ta ce, “Son, ina za ka je? Ba ka ci abincin ba, sannan ba ka jin daɗi, bai kamata ka je can ba.”
Slowly ya juyo ya kalle ta a gajiye, don hayaniyar ta ishe shi, cike da ƙosawa ya ce, “Mommy! Zan je, but go first, I want to refresh.” Daga haka bai jira cewarta ba ya wuce.
Mami ta taɓe baki ita ma ta wuce tana jan hannun Nabila. Ita kuwa Mommy za ta rufa masa baya, Salim ya dakatar da ita. “No Mommy, ki tafi kawai, bari in bi bayansa, za mu zo.”
“Bai fa ci komai ba tunda ya farka.”
“Kin fa san halinsa, ki kwantar da hankalinki, zan kawo shi.” Sai da ya lallaɓata ta tafi, sannan ya bi bayansa.
Habeeb
Yana shiga ɓangarensa, ya zare sun-glasses da ya sa tun a mota ya ajiye a kan centre table, ya zauna a kan kujera ya lumshe ido. Sai kuma ya miƙe ya fara cire rigarsa don ƙyamar jikinsa yake yi, dama shi ya tsani zaman asibiti.
Salim ne ya shigo, bai juya duba wane ne ba don ya san wane. Sai dai ya tsaya, ƙarasowa Salim ɗin ya yi sannan ya ce, “Am so sorry Dude, na san komai ya faru ni ne sila, don da...”
Cike da gajiya da jin maganar kowa ma a kusa da shi, ya juyo ya ce, “Why did you want to disturb me, Salim?” ya katse shi.
“Ba komai, kawai dai...”
“Please,” kawai ya ce. Daga haka ya ci gaba da tafiya, har ya kai hannu zai tura ƙofar ɗakin, sai kuma ya tsaya ya ce, “Wannan mutumin, hope an yi masa abin da ya dace?”
“Eh, na bar securities sun yi abin da ya dace, don hankalina a tashe yake a lokacin, amma a asibiti na je duba shi, sun kawo shi su ma. Sannan an kira familynsa, a taƙaice dai komai normal.” Don ya fahimci wa yake nufi.
Bai ce komai ba ya tura ƙofar ya shige. Kai tsaye bathroom ya nufa, cire kayan jikinsa ya yi ya watsa a laundry basket, sannan ya fara abin da ya kawo shi.
Haula
Fitowa ta yi daga cikin closet ɗinsa, hannunta riƙe da wasu English perfumes na kaya, a ranta tana ta ta’ajibi da mamakin ƙamshinsu, don tunda take a duniya ba ta taɓa jin turare mai ƙamshinsu ba. Ai ko ta samu na fesawa in za ta je makaranta, dama ita... Motsin ruwa da ta ji da kuma alamar motsi kamar na mutum, ya katse mata zancen zuci da ɗaukin da take yi. A tsorace ta juya don a tunaninta aljani ne ya shigo. Sai dai abin da ba ta yi ko tsammanin gani ba ne ta gani, wani uban ihu ta ƙwala tare da zubar da kayan da ɗibo a hannunta, wanda ya jawo hankalinsa gare ta.
Duk da abin ya zo masa a bazata, amma ko alama bai nuna ba. A natse ya juya ya kai dubansa gare ta, cikin sa’a kuma caraf idonsa cikin nata.
#amdeey_tejj_dunique
#haulahabeeb.