RIGAR ARO

9

by @pherty001







Bayan sun iso harabar makarantar, wannan karon tare suke da driver, shi ya fito ya buɗe musu kofa suka fito, Fadila ta kalli Nurayyah tana murmushi,  kafin su soma tafiya duk wanda ya dube su zasu burge shi ance akwai abotar da idan tayi yawa har kama da juna ake kusan haka ne a wurin su musamman Nurayyah less din ba qaramin fito da ita yayi ba ko dan bata taba saka abu mai tsada bane? ya fito da cikar dirinta da kyan siffa, tafiya take cikin natsuwa, Idanuwanta manya-manya masu tsantsar haske da fari kalar madara sun fito radau, idan ta ɗago su tana kallon mutane sai kaga kowa ya shagala wajen kallon karsashi dake cikinsu, hancinta siriri ne mai tsini wanda ya zauna daidai tsakar fuskarta tamkar an zana shi da fensir saboda tsari, bakinta ɗan ƙarami idan tana magana ko murmushi kwarjinin fuskarta yana ƙara bayyana ne gaba ɗaya, ga fararen haƙoranta dake jere gwanin ban sha'awa, fatar jikinta kuma  ta fito da wani irin sheƙi a hakan ma dan bata sami hutu da kulawa ba, Nurayyah kyakkyawar halitta ce ta gaske.

Fadila bata kyaleta ba har sai da ta rakata lucture hall din su, sanda suka shiga kowa ya zuba masu ido yana kallon su musamman mazan class din cos basu saba ganin su a ajin ba, abin ka da mata masu kishi nan da nan wasu na soma bata fuska suna yatsina fuska sanda suka ga Nurayyah musamman da suka ga hankalin mazan ya koma kansu,

Fadila ta raka ta har ta sami guri ta zauna inda ba kowa, Nurayyah ta zauna ba tare da ta damu da irin kallon hargitsawa ko kishin da matan suke jifar ta da shi ba, ta gyara zaman ta tana kallon gaban ajin cikin natsuwa da nuna aji na gaske, a nan ne fadila ta dube ta tana murmushi tace, "Alright babe, you are good to go, I have to run to my own class now, see you after lectures, take care!"  tayi mata bye-bye  ta fice ta nufi nata sashen karatun.

​Tana  zaune bayan tafiyar fadila tana jiran isowar lecturer, sai ga wani kyakkyawan saurayi ya taso daga inda yake zaune ya nufe ta, yana tafiya cikin wata irin izza matan hall din suka soma kallon sa cos da yawa a ciki sun jima suna crushing din sa bai taba kula su ba amma yau da ganin bakuwar fuska shi da kansa ya tashi zai je gurin ta, Kai tsaye ya nufi inda Nurayyah take zaune  ya zauna a kujerar kusa da ita daidai yana satar kallonta, Nurayyah ta juyo ta ɗago manyan idanuwanta ta kalle shi da wani irin kallo na basarwa dake nuna he is not welcome gaba ɗaya cos tana son ta nuna masa tana da aji, ya dube ta  yace, "Honestly, I couldn't resist coming over, you look absolutely breathtaking, my name is Faruq, what's yours?" Nurayyah ta yi jim kamar bazata yi magana ba tace  Nurayyah, ganin tayi masa magana ta kula shi sai ya soma jan ta da hira sama sama yana tambayar ta yaushe ta fara karatu a ina take da sauran su, wani ta amsa wani ta mashi shiru,


​A yau kam Nurayyah ta tsinci kanta cikin tsantsar farin ciki da nishadi mai yawa ba irin na jiya dake cike da tsarguwa ganin yau ta dauki attention na mutane da yawa sai zuwa ana mata magana tana basarwa, bayan sun gama lectures na ranar, suka fito harabar makarantar tana tsaye tare da fadila suna jiran isowar driver, Faruq yana hango ta tsaye da fadila yaxo gurin su da murmushi a fuskarsa yayi sallama fadila kawai ta amsa Nurayyah kuwa sai wani jan aji take yi tana kawar da fuskarta gefe kamar bata san da zamansa a wurin ba, fadila tana tsaye a gefe tana kallonta da mamakin yanda Nurayyah ta canza lokaci ɗaya, faruq yace "Please Nurayyah, just give me a minute, I just want your digits, please!" Nurayyah  ta yi masa shiru cos tana kunyar fito da wayar ta ma ya gani, shiyasa tun da take zaune a aji bata yi yunquri fitar da wayar ta ba kamar yanda taga sauran dalibai kowa da wayarsa a hannu.


​Bayan driver ya zo suka shiga motar, Faruq ya ƙaraso da sauri ya tsaya a jikin gilashin motar yana mata magana akan ta bayar da number ta, iskanci irin na Nurayyah sai ta dauke kanta gefe taqi kallon sa sai fadila ce tace masa "kayi hakuri with time zata baka rashin sabo ne" faruq ya gyada kai cikin murmushi kafin ya hakura ya bar wurin, sun dauki hanya Nurayyah ke bata labarin irin yanda ake ta kallon ta da yanda maza suka yi ta crushing din ta sai dai wannan faruq din ya fiye naci duk yanda take share shi yaqi ya hakura da ita kuma sam ita bai burge ta ba bai mata irin namijin da take son kasancewa da shi ba, fadila tayi murmushi tana jin dadi a ranta ganin Nurayyah ta saki ranta yau ba kamar jiya ba wanda hakan ke nufin babu wata damuwa zata cigaba da karatun ta.

​Sun iso unguwarsu, Nurayyah ta fito daga motar cike da farinciki ta nufi gida da sauri, bayan taje gida ta cire kayanta ta zauna a gaban kakarta tana ta bawa Jaddi labarin abubuwan da suka faru na yadda taji daɗin shigar da tayi a yau cos hakan ya siya mata mutunci a idon abokan karatun ta har take bata lbr mazan da suka ce suna son ta yau, Jaddi sai dariya take cikin farinciki ganin Nurayyah yau na dariya abinda ta jima bata yi ba tun a shekaru biyu da suka wuce wai Nurayyah ta zauna gabanta haka tana bata labari tana dariya sam har ta manta da wannan, Nurayyah ta cigaba da faɗin , "Jaddi wallahi kuɗi suna da daɗi sai yau na tabbatar da hakan, idan baka sanya sutura mai kyau kana riƙe waya babba a hannunka ba kai ba kowa bane a idon mutane."

Washe gari allah kawai tayi ta tashi ta shiga wanka tana fitowa ta soma shiri, cikin kayan da fadila ta ba ta ta shiga duba su ɗaya bayan ɗaya har idanuwanta suka sauka a kan wata atampa mai kyau da zane masu ɗaukar hankali wadda aka yiwa dinki na zamani wato riga da skirt na kece-raini, ta sanya kayan jikinta ya karbi atampar, rigar ta matse ta daidai saitin ƙugunta wanda ya fito da sirrin kunkuminta ya bayyana cikar mazaunanta da tsayin kafafunta, ta ɗauki wani ɗan ƙaramin gyale ta ɗora shi a kafaɗarta kamar yanda ta ga mata yan gayu a TikTok suna yi, Jaddi dake zaune a parlo tana gyara eggs ɗin kaji da ta kwaso ta dube ta, ta cika da mamakin ganin yanda Nurayyah ta koma da irin kyau da tayi har ma tafi jiya, wallahi sai taji ta kasa dauke idanun ta akan Nurayyah lallai Nurayyah idan ta sami hutu da kudi ba qaramar mace bace.

Nurayyah ta lura da yadda Jaddi ta bude baki tana kallon ta hakan ya sanya ta yin wani murmushi tana kallon kanta a jikin qaramin madubin dake ɗakin kafin ta juyo ta dubi Jaddi cikin gamsuwa da yanda tayi kyau,tace "ni kaina nasan nayi kyau Jaddi, ke dai kawai ki bari kuɗi suna da daɗi, kuɗi sune mutum" tana maganar tana juyawa a gabanta, Jaddi ta gyaɗa kai tana murmushi cike da farinciki har Nurayyah ta fice.

Ko da ta fito su fadila basu iso ba tukun taja ta tsaya tana kokarin kira ta a waya taji ko me ya tsaida ta, malam Musa ya fito daga gidan sa, har yazo ta gabanta ya wuce ta ya sake kallon ta kafin ya cigaba da tafiya cikin mamakin lallai idanunsa ba gizo suke masa ba Nurayyah ce, yarinyar da ya sani da nutsuwa da kamun kai yau itace da wannan shigar ta rashin mutunci, anya Jaddi ta ganta kafin ta fito kuwa, and abinda ya qara daure masa kai yanda Nurayyah ta nuna kamar bata ganshi ba taqi ta gaida shi, ga mamakin sa sai yaji tace "Baba an tashi lfy" ya amsa fuska a sake yana qare mata kallo daga sama har qara, ta lura da irin kallon da yake mata sai ta yatsina fuska kafin ta dauke kanta gefe shi kuma ya fice cike da mamakin ta.

Tana gurin a tsaye har su fadila suka iso tun da suka doso ta fadila ke murmushi a mota suna tsayawa gabanta ta sauke glass din tana kallon ta,

tace, "Oh my God, girl! You look so cute dear, gaskiya sai na dauki photo na turawa yaya ya gani!" tayi mgnr cikin farin ciki gami da fito da wayarta ta soma ɗaukar ta, already dama ƴaƴan fadila ya jima yana son ta tun ranar farko da ya soma ganin ta tare da fadila and Nurayyah ta sani sai dai ita ko a lokacin da suke secondary duk wani mai son ta bata maida hankali sosai akan sa shiyasa ko ƴaƴan fadila dake son ta bata taba bashi hadin kai 100% ba shi kuma yana kallon hakan a matsayin ƙuruciya lokacin har yazo ya bar qasar zuwa Spain inda acan yake karatu, fadila ta dauke ta pics masu kyau, sanda Nurayyah ta bude motar ta shiga ta dube ta tana faɗin "Don Allah karki tura masa kinsan halin yaya, he is so persistent and annoying sometimes," fadila ta kyalkyale da dariya tana cewa, "Come on, he's just crazy about you, let me just make his day with this gorgeous view, shi yayan nawa kike ma wulaqanci ban son iskanci fa,"  driver ya ja motar ya bar unguwar suka ɗauki hanyar makaranta.

Hanya take kallo kafin ta juyo tana kallon fadila da hankalinta ke kan wayar ta tace, "Seriously fadila, I never knew that changing my wardrobe would totally shift how people perceive me at school, kowa kallo na yake yi jiya tamkar ni ƴar wani babban mutum ce a garin nan," fadila ta juyo tana murmushi tace, "That's the power of appearance, sweetie, in this modern society, your outfit represents your status before you even speak a single word, nobody cares about your background as long as you look classy and sophisticated, sutura itace mutunci mutum a yanxu shiyasa fake life yayi yawa zaki ga mutane kowa yana so ya saka sutura mai tsada ko ta wace hanya, wani da bashi wani kuma ko da zai rasa abinda zai ci ya fi so ya hada kudin ya siye sutura mai tsada ya sanya" Nurayyah ta jinjina kanta cikin ga suwa wanda kusan hakane idan ta tuna wata maqociyar su dake TikTok yarinyar wani lokaci har gidan su inda Jaddi tana zuwa ta bata abinci taci idan basu girka gidan su ba amma idan ta hau live a TikTok sai ka dauka wata shegiya ce saboda ba'a gidan su take yi sai taje gidajen friends din ta, ga wayar hannunta ma babbace.

Fadila tayi murmushi tana sake kallon Nurayyah tace, "Nurayyah! You look like a literal runway model today, I bet Faruq will lose his mind completely when he sees you walking down the hallway," Nurayyah ta yatsina fuska kaɗan data tuna faruq ita har ta manta dashi, tace, "I don't even care about him or any of those guys, they are just trying to get my attention because of how I look yesterday," fadila tace, "Well, that's what high society is all about, you attract the finest things when you look like the finest option, so just embrace the attention and enjoy every bit of it,".