Chapter 3
BA SO BANE.
Story📃 writing
by
Hafsat waziri
Yota
Page 3
Shigowar Oga Fahad cikin hall ɗin ne ya sa ta ɗago kai ta maida idanunta kansa. Shi kuwa, da zarar ya hango duk ma'aikatan suna zaune suna ta surutunsu kamar babu wani abu, sai ya tsaya cak a bakin ƙofar hall ɗin.
Wata irin fusata ce ta bayyana ƙarara a fuskarsa.
Cikin tsagaggen murya ya ce,
“Duk ba ku iya gaisuwa ba ne?”
Ya ƙarasa maganar yana takowa zuwa ciki.
A razane ma'aikatan suka miƙe tsaye gaba ɗaya, suka haɗa baki wajen cewa,
“Barka da yamma, Oga!”
Oga Fahad, wanda ke ƙoƙarin mayar da wayarsa cikin aljihun wandonsa, ya ɗan dakata. Ya bi su da wani irin kallo kafin ya juya ya kalli inda take zaune.
Sai ya sake kallonsu.
“No... ba ni ba.”
Nan take wajen ya yi tsit.
Su kuwa ma'aikatan suka tsaya suna kallonsa cike da ruɗani, kamar waɗanda aka yi wa magana da wani yaren da ba su fahimta.
Ba tare da ya sake cewa komai ba, ya fara takowa zuwa gare ta.
Sai duk suka zuba masa.
Har ya isa inda take zaune. Ya tsaya a gefenta, ya nuna ta da hannu sannan ya ce,
“Ita za ku gaisar, ba ni ba.”
Kalaman nasa suka faɗo a kunnuwan ma'aikatan kamar tsawar aradu.
Wani sabon shiru ya mamaye hall ɗin. Su dai sun san
tun bayan buɗe wannan kamfani watanni uku da suka gabata, babu wani shugaba da suka sani sai Oga Fahad. Shi suke girmamawa, shi suke ɗauka a matsayin mai kamfanin.
Don haka maganarsa ta gigita su matuƙa.
A hankali suka mayar da hankalinsu kanta.
Tana zaune cikin isa da natsuwa. Ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, hannayenta a haɗe, idanunta kuwa na yawo a kansu ɗaya bayan ɗaya.
Tamkar sarauniya da ke duba bayinta.
“Wai ba ku ji abin da na faɗa ba ne?”
Muryar Oga Fahad ta sake kaɗa hall ɗin.
Ya bugi teburin da ke kusa da shi da ƙarfi.
“Ko duk iskanci ne wannan? Ina magana kuna kallona kamar ba ni nake magana ba?”
Muryarsa ta biyu ta fi ta farko tsanani.
Cikin firgici ma'aikatan suka shiga rige-rigen cewa,
“Barka o...”
Sai dai kafin su ƙarasa, ta ɗaga musu hannu.
Wani ɗagawa da ya haɗa isa, iko da umarni.
Nan take bakunansu suka rufe.
Kamar waɗanda aka dannawa maɓallin tsit.
Oga Fahad ya yi musu alamar su zauna.
Kowa ya koma mazauninsa cikin sanyin jiki.
Shi ma ya ja kujera ya zauna kusa da ita.
Sai wajen ya sake nutsewa cikin shiru.
Shirun da har ana iya jin bugun zuciyar mutum.
Tsoro da fargaba ne suka mamaye zukatan ma'aikatan.
Dukansu suna jin kamar wani babban bala'i ne ke shirin sauka a kansu.
Musamman bayan abin da ya faru a ɗazu.
Habu, wanda ke zaune a sahun gaba, ya ɗan ɗago kansa ya kalleta.
Da sauri ya sake sunkuyar da kansa.
Kirjinsa na dukan tara-tara.
Gumi kuwa ya jika masa goshi duk da sanyin na'urar AC da ke aiki a hall ɗin.
Abin da ya faru ɗazu ya ci gaba da dawo masa a rai.
A idanunsa komai ya faru.
Kuma ya san idan har da gaske ita ɗin budurwar Oga Fahad ce, to tabbas akwai matsala.
Ko da yake dai Aziz ba ya wajen a yanzu.
Ya lumshe idanunsa a hankali.
A zuciyarsa yana tunanin ko ya kira Aziz ya roƙe shi ya zo ya ba ta haƙuri kawai domin a rufe maganar.
Sai dai kuma ya san halin Aziz.
Ko da duniya za ta taru a kansa, ba zai taɓa zuwa ya ba da haƙuri ba.
Oga Fahad ya ɗan matsa daga yadda yake zaune.
Ganin shirun ya yi yawa ne ya sa ya gyara zamansa.
Sannan ya juya ya kalleta.
Wata irin kulawa da tsantsar ƙauna ce ƙwarai ke yawo cikin idanunsa.
Ya sauke muryarsa ƙasa, cikin taushin da ba kasafai ma'aikatan suka taɓa ji daga gare shi ba, ya ce,
“Sweetheart... ga su nan duka. Ki yi duk abin da kike so a kansu.”
Ta ɗago kanta ta kalle shi.
Kamar mai son gano wani abu daga cikin fuskarsa.
Shi kuwa ya gyaɗa mata kai a hankali.
Alamar ya tabbatar mata cewa ikon yanke hukuncin yana hannunta gaba ɗaya.
A hankali ta janye idanunta daga kallonsa, ta sunkuyar da kai ba tare da ta ce komai ba. Oga Fahad ya yi shiru yana nazari. Ganin ta ƙi yin magana, tare da sanin halinta na cewa ba ta cika faɗar abin da ke damunta ba sai dai ta aikata, ya sake tabbatar masa da zargin da ke cikin zuciyarsa. Wato dai da gaske akwai abin da ya faru tsakaninta da ma’aikatan kamfanin tun bayan zuwanta.
Nan take wata dabara ta faɗo masa. Cikin sauri ya miƙe tsaye, idanunsa suka sauka kan Habu, mai aikin Courier.
Da sauri Habu, wanda ke zaune, ya miƙe tsaye. Zuciyarsa na bugawa da sauri saboda tsoro.
Cikin sigar bada umarni, Oga Fahad ya ce,
“Go and get my laptop from my office.”
“Yes, Sir.” Habu ya amsa, sannan ya fita daga hall ɗin da sauri kamar wanda zai faɗi.
Bai jima sosai ba ya dawo ɗauke da jakar laptop. Kai tsaye ya ƙarasa gaban Oga Fahad ya ajiye masa ita, sannan ya koma wajen zamansa ya zauna.
Cike da ƙwarewa, Oga Fahad ya buɗe laptop ɗin ya fara dannawa.
A nan ne ya ga duk abin da ya faru. Ya zuba ido yana kallo tare da girgiza kai. Fuskar nan tasa cike take da ɓacin rai. Sai da ya kalli komai tun daga farko har zuwa lokacin da Suhairat ke magana da ita.
Da ya gama kallon komai, sai ya rufe laptop ɗin. Ya ɗago kansa cikin matsanancin fushi fiye da wanda yake ciki a da.
Wai ƙanwarsa?
Ƙanwarsa mafi soyuwa a gare su za a yi wa irin wannan cin mutuncin?
Ya ɗaga jajayen idanunsa yana bin ma’aikatan da kallo. Nan take duk suka sunkuyar da kawunansu ƙasa kamar wasu masu babban laifi.
Daga bisani idanunsa suka tsaya kan Habu, wanda ke zazzare ido kamar an kama ƙwarto. Ya gan shi a cikin bidiyon lokacin da Aziz ke ƙoƙarin fita, yana tsayar da shi yana magana da shi.
Cikin sauri Oga Fahad ya nuna shi da yatsa.
Cike da tsoro, Habu ya ɗaga hannunsa yana nuna kansa alamar, “Ni?”
Wani mugun kallo da Oga Fahad ya watsa masa ne ya sa ya miƙe da sauri kamar zai kife.
Ya fito tsakiyar wajen.
Gaba ɗaya idanun mutanen hall ɗin suka koma kansa, har ya fara jin kamar zai faɗi ƙasa.
A zuciyarsa wata shawara ta zo masa da ya gudu ya fita waje kawai. Amma nan take wata zuciyar ta tuna masa irin wahalar da ya sha kafin ya samu aikin.
Don haka ya yanke shawarar ya tsaya, ko da kuwa biyo baya ba mai kyau ne.
A hankali yake takawa kamar wanda ƙwai ya fashe masa a ciki.
Da ya isa gaban high table, ya tsaya kamar almajirin da ke jiran umarni.
Oga Fahad ya kalle shi da idanunsa masu tsoratarwa, sannan ya ce,
“Call him.”
Ba tare da musu ba, Habu ya ciro wayarsa daga aljihu. Ya san wanda ake nufi da ya kira ɗin dama. Hannunsa har rawa yake yi saboda tsananin tsoro, dama can shi matsoraci ne kuma ba ya son tashin hankali.
Bugu biyu kacal aka yi, wanda ake kira ya ɗaga.
Habu ya kai wayar kunnensa ya yi shiru. Shi ma wanda aka kira ɗin ya yi shiru.
Kamar munafiki, Habu ya ɗago ya saci kallon Oga Fahad, wanda ya kafesa da ido.
Oga Fahad ya juya ya ɗan kalli Suhairat na wani ɗan lokaci, sannan ya dawo yana kallon Habu.
“Ka ce masa ya zo.”
Da muryar da ke rawa, Habu ya ce,
“Hello Aziz, ni ne... Dama a wajen aiki ne... A, aka ce ka zo.”
Shiru Aziz bai ce komai ba.
Sai Habu ya sake cewa,
“Hello Aziz, kana jina? Daga kamfanin S and S Sardines ne...”
Bai ƙarasa ba, Oga Fahad ya yi masa alamar ya ba shi wayar.
Ba tare da gardama ba, Habu ya miƙa masa wayar sannan ya ja baya kaɗan.
Da zarar ya karɓi wayar, Oga Fahad ya kara ta a kunnensa. Yana shirin yin magana, Aziz ya rigaya da cewa,
“Amma ka san bana son ana damuna idan ina barci ko?”
Ya faɗi hakan da muryar barci.
Sannan ya ƙara da cewa,
“Kana ji? Ko wanene ke nema na, ka faɗa masa ba yanzu ba.”
Kittt!
Ƙarar katsewar wayar ta ratsa kunnen Oga Fahad.
Cikin tsananin mamaki ya cire wayar daga kunnensa.
Ya ɗaga kansa yana kallon ma’aikatan da ke cikin hall ɗin kamar mai son tabbatarwa ko sun ji abin da Aziz ya faɗa.
Bayan wasu daƙiƙu kaɗan, ya sake danna lambar.
Bugu ɗaya kacal aka ɗaga.
Cikin zafin rai da daga murya, Oga Fahad ya ce,
“CEO na kamfanin S and S ne ke magana. Ka tabbata ka bar duk abin da kake yi, ko menene shi, ka zo yanzu! Ina nufin yanzun nan!”
Daga nan ya katse wayar yana huci da fushi.✍️✍️