CHAPTER 7
by @deejasmah
Jin ta daki garun ɗakin ya sanya ta gane ya iso ƙarshen bango, yayinda yarinyar ta matso gaban ta tana ƙoƙarin kai hannu kan cikin ta. Ji tayi duk wani ƙarfin jikin ta ya ƙare gabaɗaya musamman da ta ji wani sanyin da yake fitowa daga hannun yana nufo cikin ta.
''Nana me kike yi haka ne jikin garu?".
Da sauri ta buɗe idanu jin muryar Umman ta yana mata amsa kuwwa, duban gaban ta tayi babu yarinyar babu dalilin ta babu alamun ma ta taɓa wanzuwa a cikin shi sai Umma da ke bin ta da kallon tuhuma. Ajiyar zuciya ta saki ta na dawowa gaban gadon ta na jinya ta zauna har lokacin ba ta daina sakin numfashi ba. Sake maimaita tambayar ta Umma tayi da sauri Nana tace '' babu komai fa Umma kawai ina kallon ɗakin ne, ban son bacci ya ɗauke ni jiya da dare ban iya bacci ba''.
''Allah sarki Auta, kin san dama haka lalura take balle naku na masu juna. Allah dai ya inganta ya ba ki lafiya mai ɗaurewa ya sauke ki lafiya''.
''Ameen Umma ta'' ta amsa tana fara'a don ba ta jin wani kunyar Umman tata akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakanin su kasantuwar ta auta. Dariya Umman tayi tana '' Ƴar tusa, amma kin daɗe a gida babu lafiya ne ko? Duk kin ɗashe kamar mara jini a jiki? Na yi mamaki da ba su ce zasu ƙara miki jini ba ma''.
''Ai ba'a cika son ƙarin jini ga mai ƙaramin ciki ba ne Umma sai in ya zama dole, amma ina da lafiya fa ciwon farar ɗaya ne kin san yana saurin zugar da mutum''.
''Haka ne, gobe zan samo ganyen ugwu in dafo miki taliya yana ƙara jini sosai har da ruwan ma zan haɗo miki ki yi ta sha''.
''Yawwa Umma, nagode'' daga haka suka cigaba da hira har sauran ƴan dubiyan ma suka dawo cikin ɗakin. Kamar jiya yau ma da magriba suka watse aka bar ta da Inna Yabi, Aunty Mariya wacce Nana ke bi ce ta kawo musu abincin dare. Khaleed kuma da zai dawo ya kawo musu nama da yoghurt ita dai Nana shayi ta sha ta kwanta.
Saɓanin jiya yau kam ta samu bacci sosai sai dai gabanin asuba ne wani mugun fitsari ya tada ta, farkawa tayi a gaggauce ta sauka daga kan gadon ta nufi bayi. Sai ji tayi ana gudu cikin ɗakin na su ga kuma gifcin inuwa ta gefen ta, tsayawa tayi hannun ta dafe da marar ta da take jin kamar zai tsinke tsabar fitsari da fargaba.
Jin sanyi a bayan ta ya sanya ta waigawa karaf idanun ta ya faɗa kan na yarinyar ɗazu tana zaune a bakin gadon ta akasin ɗazu da gashin ta ke nannaɗe kamar gammo yanzu kam an sake mata shi ne ya barbazo ya rufe mata fuska sai dai abin mamaki kana ganin idanun ta da mummunar hancin ta, ga kuma magen jiya tayi matashi da ƙafafun Inna Yabi duka suna kallon ta da wani irin mugun kallo. Ji tayi fitsari yana bi mata ƙafafu saboda firgici yayinda ƙafafun ta suke mata rawa kamar mazari, ɗukewa tayi a wurin har lokacin tana dafe da marar ta idanun ta a runtse fitsari yana cigaba da zuba.
''Subhanallahi, Nana Lafiya?". Da Inna Yabi ta furta ne ya kuma taimakon ta daga yanayin da ta shiga a dararen nan biyu wato jiya da yau, tahowa tayi da sauri gaban ta tana ƙoƙarin ɗaga ta idanun ta ya faɗa kan fitsari. Da sauri tace '' Fitsari kuma Nana?".
''Inna wallahi ban san ya fito ba, jin shi nayi yana bin jikina''.
''Subhanallah, anya babu matsala a cikin nan naki? Mai ƙaramin ciki ba ta iya riƙe fitsari? Ina aka taɓa yin haka? Mu je ciki ki ɗauraye jikin ki yanzu zan fita neman likita ya duba ki'' ta ƙarashe tana kama ta, da taimakon Inna ta cire kayan ta tayi tsarki ta wanke jikin ta. Kafin ta ɗaura zani suka fito waje, wani kayan ta nema ita kuma ta gyara wurin ta wanke wancan da ta ɓata ta ajiye su a bokiti a cewar ta zata shanya da safiya. Tana fitowa ta fita neman likita wanda inda tana da hali da tace kar ta fita amma ya ta iya sai rufe idanun ta tayi duk shagalin da ake yi cikin ɗakin ba ta kalla ba duk da dararrakun da ake yi ya tsaya mata a rai da zuciya amma tayi dauriyar ƙin kallo har Inna ta dawo da likita.
Tambayoyi ya dinga jera mata kan cikin ko akwai abinda yake mata ciwo ita kuma tana ba shi amsa da babu komai, fitsarin ya matse ta ne. Cewa yayi '' ki daina bari sai fitsari ya matse ki zaki je yi, don yana saka ciwon mara mai tsanani kuma matsala ne ga mai ciki''.
''Zan kiyaye In Shaa Allah likita''.
''Toh ma Shaa Allah, sai da safe'' daga haka ya juya ya fita, Inna dai bata koma bacci ba a cewar ta asuba ta gabato sai ta ɗauro alwala ta fara jera nafila hakan ba ƙaramin natsuwa ya haifar mata ba musamman da hayaniyar ɗakin ya ɗauke ɗif sai salama da kwanciyar hankali.
Yau da Khalid ya zo ya same ta idanun ta biyu suna hira ita da Inna Yabi ta yi wanka abun ta ta zura ƴar doguwar rigar material, zama yayi bakin gadon yana duban fuskar ta yace '' Eh lallai jiki ya samu, har da hira''.
Inna ce tace '' Wallahi fa, ga ta nan tayi shar kamar amarya''.
''Kayya dai Inna, ina kwana? Ya masu jikin?''.
''Jiki Alhamdulillah, ya ƙoƙari ''.
''Ai ku ke da ƙoƙari Inna, Allah ya ƙara girma ya bada lada''.
''Ameen ɗan nan''.
Maida idanun shi kan Nana yayi yana cewa '' Madam ya dai? Ya jikin?".
Tsulum Inna ta tashi ta fita kamar an tsikare ta ta bar su su biyun zaune.
Narke idanu tayi tana jin yanda yake ba ta kulawa har ɓargon ta tace '' Ina kwana? Ya gajiya?".
''Gajiya babu, zaman kaɗaici ya kamata ki tambaye ni ba wannan ba. Duka dai mun gode Allah ya jikin?'' ya kuma maimaita tambayar shi.
Murmushi ta saki a hankali tace '' Yayi sauƙi, marar ta daina min nauyi. Jiya kaman dutse haka na ji ta''.
''Duka ma zai daina gabaɗaya, Allah ya baki lafiya. Na yi magana da Mama kan batun Iyami ta kuma bamu ita da an sallame ki daga nan can zamu tafi''.
''Toh Yaya, Allah ya kai mana rai''.
''Ameen Jannah, akwai abinda kike so?".
''A'a ba abinda nake so, baki na ne dai yake min ɗaci sosai ban san ko akwai abinda ake ci ba''.
''Ni ma ban sani ba kam, amma zan tambayi Inna in ina dawowa sai in kawo miki. Bari in zo in tafi kar in yi latti''.
''Toh Yaya, Allah ya tsare hanya ya bada sa'a'' ta furta cikin sanyin murya.
''Ameen ta Yaya, sai na dawo''.
Da idanu ta raka shi tana jin tsoron zaman shirun da aka bar ta, gudun mutanen nan su dawo. Sai ga Inna ta dawo ɗakin kamar jira take Khaleed ɗin ya fita, wani farinciki ne ya cika mata zuciya ta gyara zama suna cigaba da hira. Har Iyami ta kawo abun kari, bayan zuwan ta ma Umma ta zo da matar babban yayan su Nana Anty Adama. Yinin yau ba a bar ta ita ɗaya ba saboda yanda ƴan dubiya suka yi yawa, daga wannan ya shiga sai wannan ya fita ciki harda ƙawayen ta na makaranta da ta shaidawa jiya da aka kawo mata wayarta. Bayan azuhur ne ta samu bacci mai ɗan tsayi.
Duƙe take a bayin tsakar gidan su ta gama fitsari kenan ta ji motsi a bayan ta, da sauri ta miƙe tana duban bayan nata suka haɗa idanu da wani baƙin maciji sai shawagi yake yi tsakar bayin. Juyawa tayi zata fita ta ga ya sha gaban ta ba tare da ta san ta ya aka yi ba, ja da baya ta fara yi shi ma yana biyo ta tayi tuntuɓe da ƴar dutsen kankare da aka ajiye don wanka. Ɗan ƙaramin ihu ta saki ta zubewa a wurin, macijin ne ya tsaya gaban ta ya buɗe ƙaton bakin shi. Wani abu mai kama da tukan goro ya watsa mata a fuska wanda saukar shi ya zame mata kamar na ruwan zafi, yanzu kam da ƙarfi ta furta '' Wayyo Allah na............''
Deejasmah