10
by @pherty001
Nurayyah ta jinjina kanta batare da tayi magana ba, sun kusa zuwa makaranta ta dubi fadila tace "Gobe a canza mana wata motar fadila, I mean ya ɗauko Maybach ɗinnan ta yayan ki ya kaimu school da ita gobe, because we really need to upgrade our presence on campus muma aga muna canza mota ko,"
Fadila tayi jim cikin mamaki kafin dta dubi Nurayyah tana murmushin yaqe cos bata son abinda zai bata mata rai tace ta fasa karatun amma tana mamakin yanda tun ba'a je ko ina ba Nurayyah ta ɗauki kanta wata daban, tace "Shikenan as you wish, anything for you to feel comfortable," ta tuna ta zo da abu tana son bawa Nurayyah ta miqa hannu ta dauko ledar inda ta ajiye ta ɗora ta akan cinyar Nurayyah, Nurayyah ta dube ta kafin ta bude ledar tana faɗin "menene a ci..... tayi shiru sakamako wayar da ta gani a ciki iphone 16, ta ciro da sauri tana jujjuya ta kafin ta dubi fadila cikin neman qarfin bayani, fadila tayi dariya sosai ganin yanda Nurayyah tayi tace "is for you dear" Nurayyah ta zare ido cikin son gasgasta abinda fadila din ke faɗa kamar bata yarda ba, fadila ta karbi kwalin wayar ta bare tana nuna mata komai dalla dalla kafin ta bata cikin murmushi tana faɗin "Look it matches your vibe completely, Nurayyah Allah wayar ta maki kyau kalar kice!" Nurayyah da ta tabbatar da gaske fadila take ta fashe da kukan farin ciki tace "Oh my God, fadila, thank you so much! I don't even know what to say, you have completely changed my life, bansan da me zan saka maki ba wallahi ina matuqar son ki" fadila tana dialling number daddy kafin ta bawa Nurayyah wayar tana "Shine ya siya miki shi zakiyi wa godia, tell him how much you love it," Nurayyah ta karbi wayr hannunta yana ɗan rawa ta som gaida shi cikin girmamawa kafin ta fara mashi godia da mashi addu'a a rayuwar sa, fadila sai murmushi take tana kallon Nurayyah, Daddyn fadila ganin yanda Nurayyah ta rude take zuba mashi godiya sai yayi dariya cikin dattako yace " ba komai Nurayyah fadila tana son ki kuma kina sanya ta farinciki duk abinda fadila take so ina taya ta son shi kuma kome tace in maki insha Allah idan bai fi qarfina ba zanyi, a tabbatar anyi karatu da kyau banda biye wa qawaye banza kuma kada ko bari kowa ya shiga tsakanin ku har ku sami matsala kinji". Nurayyah ta gyaɗa kai cikin murmushi kamar yana ganin ta kafin tace "insha Allah babu wanda zai shiga tsakanin mu kuma zamu yi karatu sosai" yace " Allah shi maku albarka" kafin ya tsinke wayar.
Driver ya na ajiye su a harabar makaranta kowa ya nufi faculty din sa, yau ma kmar kullum Faruq yn tare da ita a gefenta yana ta faman damun ta da surutu da sam hankalinta baya gunsa yana kan sabuwar wayar ta da take qoqarin ganin ta iya ta, sai basar dashi take da taga ya soma damun ta ta dube shi tana fadin "Faruq, please, I have a long day ahead, don't stress me," yana murmushi yace "Just your voice is enough to make my day Nurayyah, so I don't mind the attitude," sai ya tashi ya bar gurin taja qaramin tsaki kafin ta tashi ta fice daga hall din taje ta sami wuri daban inda babu wanda zai dame ta ta zauna tana cigaba da danna wayarta, lokacin cin abinci yayi fadila ta kira ta a waya cos taje bata ganta lecture room din su ba babu jimawa tazo ta sami fadila din suka nufi wurin cin abinci The Academy Lounge wanda wurin cike yake da mutane sosai, mata da maza masu aji ne a wurin kowane yana jin shi wani shege ne, suna zaune suna jiran abinda suka yi order sai ga wani guy yazo gurin su ya tsaya a gaban teburinsu yana wani kallon nu, kallo daya Nurayyah tayi masa ta dauke kanta cos ta gane shi yana daya daga cikin mutanen da suka dame ta jiya, ganin irin kallon da Nurayyah tayi masa a wurin ya saka ransa baci matuqa ya buga teburin gaban su cikin bacin rai wanda ya sanya daga fadila har Nurayyah sai da suka tsorata, sauran mutanen dake wurin hankalin su ya dawo kan su, cikin bacin rai ya soma magana, "Wai me kike taqama dashi? Na lura tun jiya da kika zo kike wani shan qamshi kina kyale mutane, dan kina da kyau shine me? Zaki zo kina man girman kai, dole ki kula mu a school ɗinnan wallahi baki isa ki kyale ni ba ki tambaya kiji koni waye a school ɗinnan!" Nurayyah taji tsoron a zuciyar ta sai dai bata nuna a fuska ba kada ta bayar da kanta a wurin ganin yanda hankalin kowa ke kansu a sanyaye ta dubi fadila alamar su tashi daga wurin duk da bata yi magana ba fadila ta fahimce ta,
tace "Kada ki kula shi kinji, ire iren su basu da hankali a makarantar nan, they are just looking for trouble," Tayi mgnr a hankali yanda bazai ji ba, ganin sun qi kula shi yaji ransa ya qara baci musamman da yaga sun tashi zasu bar wurin, ya sha gaban su yana nuna su da yatsa, yace "Wallahi bazaku bar nan ba sai kin gayamin ke yar gidan uban waye ce da ake maki mgn kina kyale mutane! Wannan fuskar da kike taqama da ita sai na bata miki ita da ruwan acid wallahi idan baki yi hankali ba!" jin kalmar acid ya sanya fadila jin tsoro sosai jikinta ya dauki rawa ta soma roqon guy ɗin tana cewa "Please, stop this, we are sorry, let us go," Nurayyah ta dauke idanunta gefe cike da takaici da fargaba duk da har lokacin bata nuna tsoro a fuskarta ba, idanun ta suka sauka akan wata poster ta siyasa da aka manna a wurin ta soma kallon poster ɗin bata san shi ba bata taba ganin sa ba, sai dai tana jin sunan sa a bakin mutane wani lokacin shine mai neman gwamna a yanzu, ALQASEEM A. BINNANI ta karanta sunan a zuciyarta, kafin ta juya ga guy din dake ta fama ɗaga masu murya duk akan taqi kula sa, "ba kana tambayar ko ni ƴar gidan waye bace to ni matar ALQASEEM A. BINNANI ce!"
Wannan kalmar na kiranta matar Binnani ya saka duk mutanen dake wurin kallonta da tsantsar mamaki da firgici har da fadila ma wadda ta saki baki tana kallon Nurayyah, fadar haka ya sanya guy ɗin dake ta kumfa yin baya da sauri yayi mata wani kallo na firgici da tsoron kar a lahanta shi ko kuma a turo ace zaa kama shi cos kowa yasan Binnani shine mai neman takarar gwamna a yanxu kuma yana da masoya a Kaduna saboda alheri da kyautatawar sa, ya taimaki matansa da yawa a Kaduna, yace "Hajiya ki yanda kike so, ashe ni ne ɗan iska ban sani ba, kiyi haƙuri wallahi ban sani ba," ya juya da gudu ya bar wurin, a take gurin aka soma kallonta da wani kallo na maximum respect da mamaki kowa yana cewa ashe matar babban ɗan siyasa ce, fadila ta cika da mamakin ta sanda suka fito suka soma tafiya zuwa motar su tace "Kinsan me kika yi? Qarya fa Nurayyah! Idan suka gane kin masu qarya zaki raina kanki wallahi, ai ba a irin wannan karya a garin Kaduna musamman ma a jami'a wallahi idan suka gane kin masu qarya har suna zasu saka maki dan suci zarafin ki kuma duk inda kika je sai an tsokane ki..." Nurayyah ta katse ta tana kallon cikin idanunta tace "Idan fadar sunan sa da nayi zai siya min respect da girma haka to ni matar sa ce da gaske koda a mafarki ne," fadila zata yi magana don ta sake fada mata hadarin dake cikin abinda take yi Nurayyah ta hana ta hanyar ɗora hannunta akan lips ɗin ta tana murmushi, "ki bar zancen kawai".
Suka shiga mota suka bar school ɗin, har suka iso gida babu wanda ya sake magana acikin su, Nurayyah hankalinta na kan wayar ta why fadila tana tunanin halin da Nurayyah zata shiga idan aka gane ƙaryar da ta shuka cos bata son wani abu ya sami Nurayyah indai bana alheri bane gashi Nurayyah taqi ta fahimce ta ko zata gane illar abinda tayi yau.
Ta sami Jaddi tana allah sai ta wuce dakin ta, ta cire kayan jikinta ta shiga bayi bata jima ba ta fito sai bayan tayi allah ta nufi inda Jaddi tana murmushi kafin ta ɗora mata wayar a jikinta tana faɗin "mahaifin fadila ya siya min Jaddi" Jaddi ta dauki wayar tana juya ta cikin mamaki cos bata taba ganin irin wayar ba, cikin farinciki ta soma yi wa mahaifin fadila godiya tare da yi wa Nurayyah Allah ya sanya alheri, ta cigaba da faɗin "Dazu Malam Musa ya zo bayan tafiyarki school yayi ta magana a kan shigar da kika yi wai bai dace da tarbiyyar gidan nan ba," Nurayyah ta yatsina fuskarta cikin nuna rashin damuwa tana faɗin "Ki kyale shi Jaddi kawai baƙin ciki yake min don yaga rayuwata ta fara canzawa yana ganin zan fita daga cikin talaucin da muka dade a ciki," Jaddi ta yi dariya tace "Nima wallahi nawa tunanin ke nan shiyasa nace masa kawai zan miki magana shikenan ya wuce," Nurayyah taji wani ƙwarin gwiwa a gurin Jaddi suka jima suna hira kafin ta tashi ta nufi ɗakin ta.
Washe gari babu school sai ta shirya ta nufi gidan su fadila, Fadila ta kasa jure fargabar da ta kwana da ita, ta juyo ta dube ta kafin ta maida hankali akan busar da gashinta da take yi da dryer "Kinsan bana so na ganki a cikin matsala Nurayyah, honestly I am so scared for you, tsoro nake ji kada ƙaryar da kika yi a school jiya ta sanya ki a cikin matsala mai wahala, shine naje nayi bincike mai zurfi a kan shi wannan governor Alqaseem Binnani da kika ce ke matar sa ce kada labari ya jewa matar sa a gida wani case ya tashi tayi tunanin ko ke budurwar sa ce, wai kinsan wa yake aure? Kinsan wacece matar sa?" Nurayyah ta girgiza kanta tana kallonta cikin rashin damuwa kafin tace "Wacece ita? I don't really care to know her or her name, na dai san bata haife ni ba tunda na ganshi a hoton poster dinnan so young, he looks so handsome and energetic, ba zai wuce shekaru 40 ba idan ma ya dade a duniya ke nan," fadila ta ja numfashi mai zafi sannan cikin sanyin murya tace "Waleeda yake aure, mijin Waleeda ne wallahi kin ji na rantse miki!"
Wannan kalmar ta sanya jikin Nurayyah yin sanyi da mamaki, how confused Nurayyah is, ta shiga shocked sosai ta juya tana kallon fadila don son gasgasta abinda ta faɗa tace "Bangane ba? Wace Waleeda kike magana a kai?" Fadila ta dube tace "Waleeda Aminu da muka yi makaranta da ita, har kin manta da muguwar yarinyar nan da ta tsane ki babu dalili wacce ta kwace maki scholarship da qarfi nasan kin gane ta kawai kina son gasgasta wacce nake nufi ne, Wai ashe kafin ta je karatu mahaifinta yayi mata auren gata da Alqaseem Binnani saboda shi yaron abokin sa ne da ya rasu aka ce kuma yana so yayi amfani dashi a siyasa kinsan shima baban Walida yana takarar senate yanxu, mahaifin ta yana son Al'Qaseem sosai kuma yana son yaci takarar gwamna, to shine da aka daura auren ta tafi karatu bata qasar, a yanda naji ma kamar shine yake zuwa ya same ta wai tun da ta tafi shekara biyu a yanzu sau daya ta taba dawowa sai dai shi yaje ya same ta acan.
Nurayyah ta yi mamaki da jin bacin rai na tuno abinda Waleeda ta yi mata wanda ya tarwatsa mata future, ta rintse idanuwanta tana tunani da yanxu fa itace acan tana karatun ta kusa kammalawa may be, ta buɗe idanunta waɗanda suka canza launi zuwa wani irin mischievous kallo dake cike da ramuwar gayya, ta saki wani lafiyayyen murmushi mai cike da ma'ana ta kalli fadila dake kallonta tace "Kinga ashe banyi ƙarya ba! Da gaske ni matar sa ce yanzu," fadila ta zuba mata ido cikin tsananin mamaki tace "Kamar ya? I don't understand you Nurayyah, what are you trying to say?"
Nurayyah ta gyara zamanta tace "Da shi zan yi amfani na cimma burina akan ta wallahi haka kawai naji ina so na rama abinda tayi min, ina so na sami kusanci da Binnani, I just want to be with him ba dan ina son sa ko neman wani abu a gurin sa ba just to snatch him from her na hana ta farinciki kamar yanda ta hanani na shekara biyu ko sau daya ne naji ta shiga damuwa saboda ni, my heart will be free na rama quncin da ta sanya ni, I lost my dream but I found a way to take back my power through the hearts of a girl who destroyed me, ba tana ganin t kwace scholarship taje tana karatu da shi ba? I will use her husband na mayar da abinda na rasa a rayuwata and show her the power of talakan mutum ba abin raina wa bane!" tana gama fadar haka ta cigaba da latsa wayar ta batare da ta saurari abinda fadila zata ce ba.