HAULA HABEEB

BABI NA BIYAR

by @amdeeytejjdunique587

💎🌹 Haula Habeeb🌹💎


Story Written By


Amdeey Tejj d'Unique ✍️





BABI NA BIYAR





Haula






Kwance take cikin bargo, ta duƙunƙune, har yanzu jikinta rawa yake, don ta tsorata sosai. Abu ne da bai taɓa faruwa da ita ba tunda take a rayuwarta. Ta sake matse jikinta da mugun ƙarfi, don har yanzu hoton yana wucewa a idonta, sai flashing kanshi yake yi. Duk yadda ba ta son sake a rangama da abin da ta yi yau ko a mafarki, duk da ba ta tsaya ta ƙare masa kallo ba, amma sam ta kasa nutsuwa. Kirjinta sai duka yake.

A haka Gwaggo ta shigo ta same ta. Da farko ba ta lura da halin da take ciki ba, sai daga baya, da ta yi mata magana ba ta ko iya amsawa ba ma, sai Gwaggo ta watsar da ita, don a tunaninta iskanci ne ya motsa. Ta yi kwanciyar ta, ba ta sake bi ta kanta ba. Cikin dare jikinta ya ɗauki zafi sosai, zazzaɓi ya hau ta.

Salim

Ya sake juyi a karo na biyu, kafin ya kai hannunsa kan bedside drawer yana laluben wayarsa da ta karaɗe ɗakin da ƙara alamar ana kiransa. Ya ɗora a kunnensa ya ɗauka ba tare da ya duba mai kiran ba, saboda baccin da yake yi har yanzu bai sake shi ba, idanuwansa ma a rufe suke. Muryar da ya ji ne ya sa ya buɗe ido tangaran haɗe da mamaki, don ya san in dai lafiya ne ba za ta kira shi da sassafen nan ba.

Zaune ya tashi, kafin ya ce, “Lafiya kuwa Gwaggo?” ya tambaye ta hankalinsa a ɗan tashe.

Daga can Gwaggo ta ce, “Barka da safiya, Babban Mutum. Ka kwantar da hankalinka, ba wani abu ba ne. Dama mutuniyar taka ce ba ta da lafiya, kuma ka ce in dinga sanar da kai idan ba ta da lafiya, ba securities ba.”

Wani ɗan ajiyar zuciya ya sauke, kafin ya ce, “Gwaggo, ciwo ai ya wuce a ce ba wani abu ba ne. Ga ni nan zuwa.” Daga haka ya yi saurin gimtse wayar, kafin ta fara wannan godiyar tata da ba ya so. Miƙewa ya yi, ya zira jallabiyarsa, ya fice daga ɗakin.

Gwaggo

Bayan ta katse wayar tata ƙirar Nokia, ta mayar da ita mazauninta, wato haɓar zaninta ta ƙulle ta. Sannan ta juya ta kai dubanta ga Haula da ke kwance lulluɓe cikin bargo. Ta sake kai hannunta gefen wuyanta a karo na ba adadi, har jikinta da zafi. A jiya da ta shigo ta same ta kwance, sam ba ta yi zaton zazzaɓin da gaske ba ne, da yake tunda ta tura ta sharan ɗakin ba ta sake dawowa ba. Dama kuma ta san fushi za ta yi da ita, shi ya sa ba ta bi ta kanta ba, ta yi kwanciyar ta. Sai da asuba ta zo ta tashe ta yi Sallah ne ta kai hannu jikinta ta ji yana da zafi. Tun lokacin ta so kiran Salim, sai kuma ta fasa ganin cewa maybe shi ma yana masallaci. Duk da hankalinta ya tashi, amma haka ta daure, tunda shi Salim ɗin ya hana a dinga ba ta magani sai an binciki abin da ke damunta. Ba don haka ba ai tana da ‘yan magungunanta na zazzaɓi da ta ba ta, ko ɗan ƙaramin clinic ɗin da ke gidan da aka yi shi don ƙananan ciwuka ya hana a dinga kai ta, sai shi ya zo.

“Sannu Haula,” cewar Gwaggo.

Ba ta ko iya amsawa ba, sai jikinta da rawar sanyi.

Tura ƙofa aka yi, Gwaggo ta kai dubanta ga ƙofar, Salim ne ya shigo. Sallama ya yi, sai da ta amsa kafin ya ƙaraso. “Sannu Gwaggo,” bai jira ta amsa ba ya ɗora da tambayar, “Me ke damunta?” Nan Gwaggo ta ba shi labarin yadda ta zo ta same ta jiya zuwa.

Tashi ya yi ya fice daga ɗakin, can ya dawo da abun awo da sauransu. Da ƙyar aka lallaɓa Haula ta tashi, aka yi mata abin da ya kamata. Ba abin da ya ba Gwaggo mamaki sai yanda ko raki a yau Haula babu. Idan dai an ce yi, ba za ta yi ba; in kuma an kamata a yi mata, to ba musu ko ja-in-ja. Hatta allura da aka yi mata, bayan ta ɗan sha tea kaɗan, ko motsi ba ta yi ba. Kai, ba ka ce Haula ba ce.

Tun daga ranar, kullum da safe sai Salim ya zo ya duba ta, ya ba ta maganin safe idan ya dawo daga masallaci, kafin ya wuce ɓangarensu. Gwaggo ma ba ta sake sa ta aiki ba, ko ta ce ta je makaranta. Shi ma bai ce ta je ba, da kansa ya je makaranta, ta ba da uzurin ba ta da lafiya.

Hotel, VIP Side

Wata irin shegiyar dariya ya tuntsure da ita, har yana sauka daga kan kujera, kasancewar VIP ne, wajen su kaɗai ne. Zaman daɓaro ya yi tsabar dariya.

Sagale ta yi tana kallon ikon Allah, da kuma mamakin dariyar da yake. Yo, ina ma’anar dariyar take? Tana yi masa magana hankali, amma shi ya mayar da ita mahaukaciya. Tsaki ta yi, cike da haushi ta ce, “Dalla, ni ba na son iskanci. Ina maka maganar damuwarmu, kai kuma kana min dariya. Wato ga mahaukaciya ko?” Ta yi maganar tana wurga masa harara.

Ɗaga hannu ya yi alamar surrender, sai da ya miƙe ya zauna a kan kujera kafin ya ce, “Wow, good idea. Ya yi, ba ke kin yarda ba? To ai shikenan, ba wata matsala, Allah ya kai mu ranar biki.” Ya ɗauki kofi ya kai bakinsa bayan ya tsiyaya ɗaya daga cikin kwalbar giyar da ke gabansa.

Numfashi ta sauke kafin ta ce, “Na san ka, na san waye kai. Wannan dariyar da kake akwai alamar tambaya a cikinta.” Ta kai dubanta kan agogon hannunta, kafin ta ce, “Please, kada ka ɓata mana lokaci, ka ga time ya tafi, sannan akwai abubuwa da yawa a gabana. Idan da matsala, mu yi solving ɗinta tun da wuri.”

“No, ba wata matsala, ai kina da kwanya, ke ma.”

“Ka ga Malam, idan da shawarar da na yanke ta ishe ni, da ban zo nan ina ɓata lokacina ba. Please, take it serious, don Allah.”

Gyara zama ya yi, kafin ya ce, “Yanzu ke, saboda Allah, da kika yarda da wannan abu, ta ina kike ganin mafita?” Ya yi maganar yana ƙure ta da ido.

“Ni a ganina, tunda na rasa, ban damu ba a kai shi dawa kawai, kowa a gidan ya rasa. Shi ya sa hukuncin ya yi min daidai, ko a jikina. Na san dai a ƙarshe, ko ma mene ne abin da ya biyo baya, ni na san mafakata.”

Murmushi ya yi sannan ya ce, “Duk abin da aka yi da jaki dai sai ya ci kara. Yanzu banda ƙaramin tunani irin naku na mata, ina mafita a nan? To bari ki ji, kina zaune ba ki ankara ba, sai dai ki ji gafara sa, kafin ki farga kuwa wani zancen ake yi ba wannan ba, ya zama kin yi zuwa zomo kasuwa, kin zo a banza, kin tashi a banza.” Sigari ya jefa a baki, ya sa lighter ya kunna. Sai da ya zuƙa sannan ya fesa mata hayaƙin a fuska.

Hannu ta sa ta kaɗe, kafin ta ce, “Wai mene ne haka ne don Allah? Sai sani a duhu kake yi, ka ƙi ka fito ka yi min maganar da zan fahimta.”

Sai da ya sake fesa mata hayaƙin kafin ya ce, “Auu, sorry. Har yanzu ba ki fahimta ba ko? To bari in yi miki dalla-dalla.” Ya ajiye guntun sigarin, tunda already ya riga ya shanye ta tun a zuƙa ta biyu.

Gyara zama ya yi, ya tattaro hankalinsa waje guda, kafin ya fara magana: “Ina magana ne a kan hukuncin da kuka yanke a kan ɗanku, ko ‘yar ƙanwar ki Salmai za a ba shi. To fa abin da muke buƙata ba zai samu ba, domin ita ma kada ki manta tana da nata ƙudurin a kai. A lokacin da ta samu wannan damar, yadda muka so mu yi a farko, ita ma haka za ta yi, ta tattare komai ta bar ki a tsaye. Da zarar kin yi wani yunƙuri kuwa, fallasa ki za ta yi a duniya. Dama za ta yi miki fallasa yadda kowa halinsa zai fito fili ne, maybe da sauƙi tunda an yi mutuwar kasko, amma ke ce za ki fito idon duniya. Kin fini sanin wace ce Salmai. Ya lafiyar kura bare ta damƙi akuya da ‘ya’yanta a ramin ta? Ai idan rasawa za a yi ba gaba ɗaya ya kamata ba. Ba ‘yar Ummi za a ba wa ba, waje za a nemo a dawa, tunda ita tana da alaƙa da ‘yan gidan.” Ya sake kai kofin giyarsa bakinsa yana sha, yana kallon yadda yanayinta ya sauya lokaci guda.

Handkerchief ɗin da ke hannunta ta sa ta share zufar da ta tsattsafo mata a goshi, kafin ta kai dubanta gare shi. Cikin rashin sanin abin yi, ta ce, “Lallai Smart, ka cancanci sunan naka. Sai yanzu ka hasko min abin da ni ko a hasashe ma ban hasko ba. Gaskiya ne da aka ce aikin mai shawara ba ya ɓaci. Yanzu da ban zo ba, na zauna da tunanina, da kwaɓa ta yi ruwa tsalolo fiye da ruwan kogi, tsabar tsinkewa.”

Taɓe baki ya yi bai tankata ba, sai cup ɗin giyarsa da ya sake kai wa baki.

“Yanzu meye abin yi? Ga shi ba lokaci, muna da buƙatar komai cikin gaggawa. Sannan satin da ya wuce aka je tambayar auren, kuma sun bayar. Maganar da nake maka bai fi saura sati uku da kwanaki ba auren, don ana buƙatar komai cikin gaggawa.”

Sake gyara zama ya yi, wanda da gani hakan al’adarsa ce idan zai yi magana. “Mafita ɗaya ce,” ya faɗi yana kallonta.

“Mecece mafitar?” ta tambaya.

“Dole ce yarinyar da za a aura mai ta zama ‘yar ƙauye.”

“‘Yar ƙauye kuma?” ta faɗi da alamar tambaya.

Ya jinjina kai, yana faɗin, “Yeah, ƙwarai ‘yar ƙauye, ƙayau ma kuwa. Jahila wacce ba ta da ilimi ma kuwa, ba ta tantance A da B, ‘yar talakawa wacce kuɗi kawai suke so, marar wayo, yarinya.”

A wannan karon, ita ce ta gyara zama, cike da mamaki, da kuma tunanin ta yadda wannan lamarin da yake faɗa, mai kama da tatsuniya, zai kasance. “Wai ka san abin da kake faɗa kuwa? Ta yaya jahila ‘yar ƙauye da ba ta san kanta ba ma za ta yi mana amfani? Ba wannan ba ma, ta yaya kake tunanin za su yarda, ko shi kansa zai yarda ya auri ‘yar ƙauye? This statement doesn’t make sense. Wai ma yarinya!” Ta kau da kai gefe tana faɗin, “Wannan batun naka ba shi da masauki a nan.”

Murmushi ya yi, sannan ya yi al’adar tashi, wato gyara zama. “A yanzu kike ganin shi haka, amma bari in haska miki kaɗan daga cikin alfanunsa.”

Sai da ya yi gyaran murya, ya miƙe tsaye yana kai-kawo a cikin wajen, kafin ya soma magana kamar wani mai jawabi: “Jahila ‘yar ƙauye ce kaɗai za ta saka miki hannu a kan takardar da kike buƙata, ba tare da ta san a kan abin da ta saka hannu ba, saboda ba ta san abin da fallen takardar ta ƙunsa ba. Jahila ‘yar ƙauye, ‘yar talakawa, ce kaɗai za ki juya ta yadda kike so, saboda tana kwaɗayin abin da za ki ba ta, wanda idan kin ci ribar, bai fi ki watsa mata ‘yar tsaba ba, ta kwashe ta tafi tana murna da godiya. Jahila ‘yar ƙauye, marar wayau, ita ce za ki raina mata hankali, ki yi yadda kike so da ita, kuma asirinki ya rufu ruf. Ko ta yi wani motsi ma, kin fi ta power. Cikin ƙanƙanin lokaci za ki iya kawar da ita har zuriyarta, a ɓatar miki da su a doron ƙasa.”

Numfashi ya ja, ya nemi wuri ya zauna a kujerar da ke kallon nata, yayin da ita kuwa ta yi sagalo tana bin sa da kallo kamar wawiya.

Ya kalle ta, ya yi ‘yar dariya, sannan ya ci gaba: “A ɓangare ɗaya kuma, wayayyiya ‘yar birni mai ilimi, take opposite ɗin jahila ‘yar ƙauye. Wayayyiya ‘yar birni, lokacin da kika buɗe mata ƙudirinki, har kika miƙa mata fallen takardu, hmm, to a lokacin za ku yi kunnen doki. Bari in yi miki misali da ‘yar wajen Ummi, don kin san barewa ba za ta yi gudu 'yarta ta yi rarrafe ba. Yarinya ce wayayyiya, wacce ta san duniya, idonta a buɗe yake. Da zarar wannan fallen takardar ta shiga hannunta, ta ga abin da ta ƙunsa, to fa ki sani alƙiyamarki ta tsaya, don ba ke ba, ko mahaifiyarta, sai kun zama ita ke juya ku. Kin ga kuwa muddin hakan ne, to ba sai na yi miki bayani ba, domin yarinya ce wacce take gogayya da maza manya masu madafan iko a hannunsu na ƙasar nan, suna ji da ita, wanda kin san wannan na sani. Daga wannan lokaci kuma, kara za ta ajiye miki. Da zarar kin tsallake, ba sai na yi miki bayanin wannan ba. Kin ga kin haƙa ramin binne kanki da kanki kenan. Yanzu sai ki tantance ki san na kwatanci.” Ya sake kai cup ɗin giyarsa bakinsa. 

Ƙura masa ido ta yi, kamar mai son tantance shi ne, ko ba shi ba ne. Mamaki take ta yadda ya gano abin da ita, da ta kwashe shekaru tana wannan aikin, ta kasa ganowa, har take ƙoƙarin binne kanta da kanta. Yo, wannan ai ba iya rami ta tona ba, har kanta ita za ta binne. Lallai Smart ya wuce inda duk take tunani ko hasaso shi. An ya ƙudurinta a kansa bayan kammaluwar aikin nan kuwa zai yiwu?

Ruwan da ta ji saukarsa a fuskarta ne ya ta da ita daga tunani. Shi kuma ya kalle ta, ya ɗan murmusa, don ya san tunanin da take.

“Na ga kamar kin yi suman zaune ne, shi ya sa na watsa miki don ki farka,” ya faɗa ganin tana kallonsa.

“Bari kawai Smart, mamaki ne ya kama ni, ganin yadda ka gano abin da ni ko a hasashe ban hango ba. Amma ta yaya ka gano hakan?”

Murmushi ya yi sannan ya ce, “Wannan ba abin mamaki ba ne, abu ne a bayyane ai. Sannan ba yau kika san Smart ba. Kin ga kuwa, maybe za ki ga fiye da wannan ma. Mance da wannan, don muna da abin da ya fi shi muhimmanci.”

“Haka ne kam, amma shi ma yana da nashi amfanin. Meye mafita yanzu?”

Gyara zama ya yi, kafin ya ce, “Mafita ɗaya ce. Sai dai akwai risk, kamar yadda kika faɗa ne, bai zama lallai su yarda a ɗaura masa aure da ‘yar talakawa ba. Amma dole sai an yi hakan muddin muna so mu tsira.”

Ajiyar zuciya ta yi, kafin ta ce, “Akwai sauƙin faɗa a baki kam, amma a ai kace akwai wahala, musamman wannan babban nasu. Ka san shi da kafiya, sannan kuma ga wayo. Yanzu muna wani motsi kaɗan, sai ya sa mana question mark, ya fara zargi. Sannan ita kanta yarinyar da za a samo ɗin fa?”

“Yarinyar da za a samo ba abu ne mai wuya ba, don kuɗi ne za su yi aiki. Shi ma wancan zan san yadda za mu yi. Ke kuma za ki yi holding cikin gidan ku. Matso ki ji yadda za ta kasance.” Ta matsa kamar yadda ya buƙata, magana ya fara mata ƙasa-ƙasa kamar mai gudun a ji su.

Haula

Duniya sabuwa a wajen Haula, abin nema ya samu, don tun daga ranar da wancan abin ya faru ba ta sake zuwa makaranta ba. Salim da kansa ya je ya ba da uzurin ba ta da lafiya a makarantar. Aiki ma Gwaggo ta daina sa ta, sai dai ta ci ta kwanta, a dole ita ba ta da lafiya. Aiki sai ta ga dama ta share iya ɗakin kwanciyar su, anjima kaɗan ta ce jiki ya dawo, wanda a zahirin gaskiya kuma ba haka ba ne. Ta warke, ba abin da ke damunta. Abin da ya faru ma ta manta, musamman da ya kasance tun daga ranar ba su sake haɗuwa ba, don ba fita take ba daga ɗaki, sai lambu idan ta gaji da zaman. Salim kuwa kullum shi yake ba ta magani, sai sun sha hirar su yake tafiya office, haka zalika idan ya dawo da dare. Shi ya sa take da ɗan noƙewa don kada ta yi aiki ko ta je makaranta, don ta sha alwashin ba ta sake zuwa sai an canza mata makaranta.

Tun Gwaggo ba ta fahimta ba, har ta gane ta warke zallar iskanci ne kawai. Nan ita ma ta ga wautar kanta, don da alama ta mance da wacce take tare. Ai ko ba shiri ta farga. Don haka yau ta ɗaura ɗamarar yin maganinta.

Habeeb

Dawowarsa kenan daga morning exercise ɗin da yake fita kullum. Securities biyun da suke biye da shi as usual ne suka buɗe masa gate. Ya kawo kai zai shiga, dai-dai lokacin shi ma Tahir zai fito. Kallon kallo ne ke gudana a tsakanin su, cikin su an rasa wanda zai ba wani hanya. Kusan 50 seconds, zuciyar Habeeb ta motsa, ransa ya fara ɓaci. Shi ma Tahir jira yake Habeeb ya ba shi hanya ya wuce, don gani yake bai kai wanda zai matsa ya ba shi hanya ba. Shi kuwa Habeeb, ganin Tahir ɗin ba zai ba shi hanya ba, zuciyar kuma ta riga ta kai limit, Tahir bai yi awo ba sai jin sa ya yi nesa daga inda yake, sakamakon saukar wani mari da ya ji a kuncinsa, ba tare da ya yi zato ko tsammani ba.

Shi kuwa Habeeb da ƙafa ya ture shi ya shige ciki, ko takan shi bai bi ba, ya nufi side ɗinsa.

Ta wutsiyar ido ya bi bayansa da kallo, yadda yake tafiyar ƙasaita, da yadda damatsensa ke motsi, ya san ko ya bi bayansa da niyyar su daku, shi zai ji jiki. Dole ta sa ya haƙura da bin nashi, amma zai ga munafurci. Silalewa ya yi a wurin ya suma.

Haula

“Yauwa Babban Mutum, idan kun gama shan maganin, sai ka sauke ta a makaranta, ko kafin ka wuce aiki, idan ba a takura ka ba, tunda na ga kwana biyu jikin da sauƙi, ya kamata a koma makaranta ko?” Cewar Gwaggo kenan da yanzu shigowarta ɗakin, ta tarar da su suna hira.

Salim ya murmusa kaɗan, ya ce, “To, Gwaggo, ya kamata kam, tunda an kai sati biyu rabon ta da makaranta. Ba komai ai, bari in je in shirya sai mu wuce.” Tashi ya yi ba tare da ya kalli inda Haula take ba, ya fice.

Yana fita Haula ta koma ta kwanta tana faɗin, “Ni Gwaggo, wallahi dauriya nake yi, amma ban warke ba, kaina ma ciwo yake yi yanzu.” Ta koma ta kwanta.

Gwaggo ta kalle ta ta ce, “Na rantse Haula, idan ba ki tashi kin shirya kin tafi makaranta ba, zan ba ki mamaki.”

Tura baki ta yi, ta ce, “Ni fa Gwaggo, idan kina so in je makaranta, sai kin cire ni a waccan makarantar da ake zagin, don ba zan je a dinga zagina ba.” Ta ƙarashe maganar tana ƙunƙuni.

Gwaggo ba ta ce mata komai ba, ta fice daga ɗakin. Ita kuwa juya baya ta yi, ta ci gaba da magana cikin ƙunƙuni, tana shan alwashin komai za a yi, wallahi ba za ta je makarantar ba.

Bayan wasu mintuna da ba su wuce goma ba, tana kwance a inda Gwaggo ta bar ta, ba zato ba tsammani ta ji murya da za ta ce ta manta mai mallakinta, ana tambayarta da shi.

“Uban me ya sa ki ke cewa ba za ki je makaranta ba?” tambayar kenan, da ta ji shi kamar saukar aradu.

Wuf! Ta miƙe zaune, tana bin sa da kallo, zuciyarta kamar za ta faɗo daga kirjinta na dukan cassa’in da tara. Caraf idonta sai cikin na Habeeb da ya tsare ta da nashi idon da suka yi ja. Wanda ba ita ba, idan ka kalli ƙwayar idonsa, ba za ka so ka sake kalla ba a karo na biyu.

#amdeeytejjdunique
#haulahabeeb