12
by @gureenjoh
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.
GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
*SHAFI NA GOMA SHA BIYU*
Cikin hanzari ya riƙe wuƙar wanda take ya yanke hannunsa jini ya shiga zuba, da ƙarfi ya riƙe hakan ya sa ta kasa fusga sai idanunta ta zubawa nashi da suka rine zuciyarta na wani irin bugu da ta rasa na jin daaɗi ne ko na menene?
"Yanzu aka barki sai ki kashe ni?"
Tambayar ya zo mata wani iri ga idanunsan nan masu cike da masifar kwarjinin da bata taɓa ganin irinsu ba tsaye cikin nata kaman da gayya ya zuba mata saboda sanin tasirinsu da kaifin su ga duk mai kallon cikinsu.
"Kana raina abin da Diva za ta iya aikatawa kenan, saƙe wuƙar ka ga idan ban tsayar da numfashinka ba."
"Baki tsoron haɗuwarki da ubangiji a ranar gobe? Baki tsoron abin da zai iya biyowa baya? Wace iriyar kangarewa zuciyarki tayi da baki tunanin komai sai na zalunci? Kin san makomar ki kuwa da zarar kin kashe rai?"
Jikinta tsuma yake yi Dukda tana jinshi amma ba har chan ciki ba saboda already kwayar da ta sha ya ɗauki effect.
Shi kuwa har ga Allah tausayi da wani irin karaya akan tarbiya ne ya rufe shi, menene amfanin wannan rayuwar, motsa wuƙar da ya riƙe ta yi wani irin azabar zafi ya ratsa har kwanyarshi da ya sa ya saki wuƙar ta faɗi ƙasa saboda itama ta saki, saurin duƙawa tayi za ta ɗauka ya sa kafarshi ya taka ta ɗago tana kallonshi.
A karo na biyu ya nufi yi mata nasiha bayan haƙuri da ya kudurta zai bata
"A cikin littafin tirmizi an ibn Abbas (RA) Manzon Allah yace mutumin da aka kashe zai zo da wanda ya kashe shi a ranar alkiyama, wanda aka kashe zai riƙo gashin kai da goshinshi yana janyo shi jiyoyinshi a waje suna zubar da jini har wurin Allah madaukakin sarki zai ce ya Allah ka tambayi wannan me na mishi ya kasheni? Sai dalibai suka ce idan ya tuba fa? Man qatala mu'iminan muta'ammidan.....sai ya ce wannan aya tana Nan ba'a share ta ba ba'a sauya ta ba duk wanda yayi kisan kai da gangan sai ya dauki zunubinsa na har abada.."
Ashe baki tsoron gamuwarki da Allah cikin wannan yanayin?"
Zuciyarta rawa yake da ta rasa dalilin durkushewarsa, kafafunta sanyi ne ke shigar su tamkar wacce aka jefa cikin tsakiyar ƙanƙara sai kuma a hankali kwakwalwarta ke juyawa a saninta bata da imani, Meyasa mere kalaman bakin wannan ke neman rushe duk wani ƙwarinta?
Ya taka da kafarsa ɗaya gabanta yana kallon cikin idanunta da tsantsar gaskiya a kan harshensa da ya tafi ya ratsa zuciyarta ya furta
"Idan har don na mareki ne kike neman ɗaukan haƙƙin raina ki rataya a wuyanki ki yi haƙuri! Ina baki haƙuri daga zuciyata bisa kuskuren da na yi..."
Waennan kalmomi guda uku na ki yi haƙuri su suka rusa ta gabaɗaya zuwa ƙasa, hawayen da bata san daga ina ba suka cika kurmin idanunta. Tabbas raɗaɗin abin da yayi mata bai kauce nan take ba domin rauni ma yana da nasa lokacin warkewar amma tabbas ta ji saukin nauyin zuciyarta.
Dayawa ɗora waennan kalamai kan harsunanmu sun yi mana nauyi.
"Shehi!! Shehi!!!"
Muryar Ammar ne ke kiranshi don shirun yayi yawa hakan yasa ya biyo bayansa, sauƙe idanunta tayi bata yi magana ba ta zubawa hannunsa da ke ɗigar jini.
Hannun ya ɗan kalla ya ɗago sai suka haɗa idanu.
"Leave!"
Ya faɗa a hankali don ba ya so Ammar ya zo ya sameta wurin, duk wani bibiyar rayuwarsa da take yana so ya ƙare anan, ba kaskantar da kai ba ne a wurinshi kalaman da yayi mata yayi hakan ne saboda duk wanda ya san rayuwa ya kuma san duniya ta fuskar ilimi ba ya barin mutane su zama abokan gabansa, ko da ko akwai wanda ke gaba da shi ma zai yi kokarin chanza sa domin ya dawo masoyinsa makiyinka zai iya zama mai matukar amfani har ma ya ceceka daga cikin wani bala'in shiyasa ake son kyautata zato da alaqa da kuma zamantakewa a dabi'ance da kuma addinance.
Ko kan Ammar ya iso ta bar wurin, duƙawa Irshad yayi ya ɗauki wukarta da ta bari nan ya naɗe a hanky ya saka cikin aljihu.
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun Irshad! Me zan gani haka? Me ya faru?"
Ammar Yayi maganan yana kamo hannunshi.
"It's an accident ba wani Big deal ba ne in shaa Allah"
Zai yi magana Irshad ya wuce daidai suna zagayowa ta enterance na hall ɗin motarta na ficewa daga wurin.
Ammar malam bala ya kira a waya akan su zo su kai Irshad asibiti.
Duk yadda suka so su samu wani bayani ma ko magana daga bakinshi bai ce komai ba kuma sun san ba zai ce ɗin ba ne tunda bai faɗa ba tun farko. A haka suka yi asibiti aka shiga yi masa dressing na ciwon da kokarin tsayar da jinin.
***
Dukda yadda ta fito cikin rashin sanin yanayin da ta ke ciki hakan bai hanata sake sauƙe idanunta kan jar motar da ta kula yadda take tailing Irshad haka shima yake tailing ɗinta ba, bata damu ba don ta san kila Jagaban ne da wannan aiki don haka da wani irin speed ta isa gida.
Ko da ta shiga parlor baya nan, ɗakinshi ta je ta yi knocking...
"Sohana! Lafiya kuwa na ga yanayinki wani iri?"
"Baba ba na ce ka kyale min Irshad na san yadda zan yi da shi ba? Then Meyasa ka tura mutanenka suke bibiyata?"
Da ɗan mamaki ya ce
"Ban tura wasu mutane su bibiyeki ba Sohana, tun da kika nuna kin fi son handling situation ɗin da kanki na bar zancen"
"Then Meyasa sai ta hanyana suke gane inda Irshad ya nufa?"
Ta faɗa da mamaki don ta san babanta ba zai mata karya ba.
"Ko kuma su ma wani abin daban suke bibiya dangane da shi ba, idan dai har kin fahimci shi suke bibiya ina zaton su ma da nasu 'yar tsamar da shi"
Kai ta gyaɗa kawai ta juya ta nufi ɗakinta, a yadda ta ke ta tsaya ƙasan shower babu abin da ta cire saboda yadda take jin wani kunci a ranta, kaɗaici ya ziyarci jikinta Dukda tana zagaye da mutane amma ganin shadows take yi musu basu da wani impact a rayuwarta...
Ko da ta fito bata ji daidai ba sai da ta bugu iya buguwa kan ta zube sai bacci kuma.
***
Zubash ce zaune ɗaure da towel bayan ta fito wanka tana gyara jikinta, matashin saurayin mai ji da kuɗi ya zuba mata idanu.
"Kina da kyau"
Ta kalleshi ta madubi ta san tatsuniyar gizo dai ba ta wuce ta ƙoki don haka ta ce.
"Na sani"
Yayi murmushi
"kowani irin magana kina da amsar ta"
"hakan ce daidai da ma"
"Zuby wlh tallahi da za ki amince da na aureki"
"ko?"
Ta faɗa tana sanya kayanta.
"Da gaske nake yi komai kike so zan yi miki shi muddin za ki killacemin kanki ki zama matata wallahi ba zan kama ki da laifukanki na baya ba"
Hannun da ta miƙo masa ya riƙe ya ja ta ta zauna gabansa suka zubawa juna idanu
"Sallameni Khalil in wuce, aure ne kake so ka je ka nemi wata ban shirya aure yanzu ba"
Ta faɗa tana Miƙewa, a kalaman ta ya jiyo zafin ƙasan zuciyarta daga furucin.
Zai kara magana ta juya kawai ta fice.
Yana da account number ɗinta don haka yayi mata transfer ɗin kudi masu kauri.
Da kafa take ta tafiya hawaye na zuba mata duk dakiyar zuciyarta bata jin za ta iya danne hawayen.
"Rayuwar da Mama ta zaɓa min kenan kuma shi zan yi har sai ta fahimci kuskurenta, ba zan taɓa tafiya in bar Nana ta faɗa irin halin da na faɗa ba..."
Hawayen ta share ta tari machine zuwa gidan Jagaban, jin Diva bata available suka baje a wurin suna lido da shaye shayensu ana ta shiga da fice na sayan kwayoyi da sauransu.
Wani irin jiniya ne ya karade unguwar kan ma kowa ya motsa a gidan wasu jami'ai suka fara shigowa da gudu gudu.
Babu wanda ya tsorata ko ya firgita har sai da suka shiga cikin parlor suna bincike, abunsun bai taɓa kai wa nan ba kuma sun tsatsare su da bindigu manya a hannayensu.
"Ina shugabanku?"
Shadow ya ce
"Baya nan"
"Ƙarya ne! An tabbatar mana yana cikin gidan nan ko ku fito da shi ko mu shiga mu fiddo shi da kanmu"
Ɗayan ya faɗa, babu wanda ya sake magana suka nufi dakunan gidan suna tura murfin farko, na Diva suka buɗe mutum uku suka shiga suka kunna haske ta bayyana a gabansu...