RIGAR ARO

11

by @pherty001


*RIGAR ARO*




©️Fertymerh Xarah💞





11






Wani irin kallo fadila take yiwa Nurayyah, kallon da ke cike da tsoro, fargaba, da kuma matsanancin mamaki mai al'ajabi, yayin da take ƙoƙarin karanto me ke cikin ƙwaƙwalwar ƙawar tata. Ta kurawa kyakkyawar fuskar Nurayyah ido tana ayyana abubuwa da dama a ranta, zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, cos a halin yanzu Nurayyah tsoro take bata ta canza daga yanda aka santa a baya, gaba ɗaya yanayinta ya sauya zuwa na wata daban. Idanun Nurayyah sun yi lamo, suna kallon wuri ɗaya ta tafi duniyar tunani batare da tasan me take kallo ba, sai murmushi take  lokaci bayan lokaci idan tayi wani tunani, abin da ya tsoratar da fadila har ya sanya ta fara tunanin ko Nurayyah ta fara zaucewa, me take ayyanawa a zuciyar ta me yake sanya ta murmushi, like she was completely losing her mind or out of her senses. Ganin halin da Nurayyah take ciki ya sanya fadila ajiye dryer dake hannunta ta taso ta zauna kusa da Nurayyah tana faɗin, "Kina son yin rayuwar da ba taki ba saboda wata banza can, wannan shine RIGAR ARO domin halin da kike son ɗorawa kanki ba naki bane, aro ne zaki yi, dan Allah ki daina tunanin komai Nurayyah ki manta da ita na roqe ki."

​Nurayyah ta jiyo muryar fadila kamar daga sama cos bata ma san ta dawo kusa da ita ba ta juya tana kallon fadila kafin ta dauke kanta tana cigaba da girgiza kafafunta, fadila ta cigaba da faɗin "Ta yaya ma zaki ganshi har kiyi tunanin ƙulla alaqa dashi, and wait, what if Walida taji labari tazo Nigeria saboda ke, bakya tsoron abinda zai je ya dawo?"

​ Tambayar fadila ta daki tsakiyar ƙwaƙwalwar Nurayyah, maimakon ta nuna tsoro ko ku kuma fargabar haduwa da Walida kamar yanda Fadila tace, sai kawai ta yi shiru na wasu daƙiƙu, ta tsurawa yatsun ƙafafunta ido cike da tunani kafin taja numfashi mai nauyi tana kallon fadila da idanun ta da suka rine saboda bacin rai tace, "Koma me zai faru ya faru idan tazo wannan karon, yanda nake jin xuciyata da karfi bana jin tsoron tunkarar ta, ba tana can tana karatu da scholarship ɗina ba, ni kuma zan maye gurbinta a idon mutane wannan shine RIGAR ARO ta sanya nawa nima zan sanya nata." Nurayyah ta qarasa maganar cikin bacin rai da jin wani confidence akan zata iya ko da zata cutu sai tayi sai ta sanyawa Walida tsoro da bacin rai, ta cigaba da faɗin "Dama da yawan mutanen gari basu san ta ba, zan nuna kaina a matsayin ita a duk inda naje, daga haka zan sami kusanci da Binnani cos sai ya nemi sanin wacece ni, wataqila ma ya saka yaran sa suje dani har gaban sa, kin gane?" Fadila sai kallon Nurayyah take cike da tsoro cos tayi nisan da bata jin kira duk yanda zata yi da ita bazata saurare ta ba a yanzu illah ta barta har zuwa wani lokaci idan ta sauko daga zafin da ta ɗauka, Nurayyah ta tashi ta sanya hijab din ta tana kallon fadila "sai kin jini", kafin fadila tayi magana tuni Nurayyah ta fice da sauri, fadila ta bita da kallo ba tare da ta motsa ko iya mata magana ba saboda yanda jikinta yayi sanyi gaba daya daga lamarin Nurayyah, ba dan ta san ita kaɗaice qawar Nurayyah ba kuma Nurayyah bata zuwa ko ina kullum tana gida da tace Nurayyah ta fara bin qawaye banza ko kuma ta fara shan wani abu dake gusar mata da tunani cos kwata kwata abinda Nurayyah take shirin yi abune mai hatsari babba, babban mutum ɗan siyasa a Kaduna take so tayi qarya da sunan sa tayi wasa da hankalin sa me yasa ba za'a neme ta ba a cutar da ita?

Washe gari, da wuri fadila tazo ɗaukar Nurayyah ko da Nurayyah ta fito ta cika da mamakin ganin fadila ta canza mota ta dauko wata daban, sosai taji dadi shiyasa take son fadila cos duk abinda take so shi take yi, ta bude motar ta shiga ta zauna fadila ta tayar suka fice, babu wanda yayi magana acikin su binni binni fadila kan juyo ta dubi Nurayyah da ta mayar da idanun ta a window tana kallon titi, daga sanda Nurayyah ta shiga school zuwa yau ta kasa gane kanta gaba ɗaya ta canza tsoro take ko dai Nurayyah na da wata qawa daban a school bata sani ba, nooo tasan bazata taba boye mata ba, da wannan har suka iso makaranta taje tayi parking inda take ajiye mota suka fito tun da suka doso haraba school ɗin fadila ta lura da wani irin kallo da mutane suke masu wasu har nuna su suke, ta dubi Nurayyah sam hankalinta baya gun su yana kan wayar ta, cikin sanyi fadila ta qara matsawa gare ta tana faɗin  "Wataqila sun gano ƙarya kike, kinga sai kallon ki ake ana nuna ki." Nurayyah ta ɗago daga kan wayar ta tana kallon mutanen da fadila take magana, tabbas duk inda suka bi sai taga an juyo an kalle su sai ta fara tsarguwa tana jin wani iri ba daɗi, sanda zasu rabu ta dubi fadila tana faɗin "bye bye" fadila ta gyada mata kai kawai batare da tayi magana ba tana kallo Nurayyah ta fice taja numfashi kaɗan kafin ta nufi wurin karatun ta, abinda yafi bawa Nurayyah mamaki tana shiga hall wadanda ke tsaye a hanya duk suka jaye mata ana kallon ta, kallo na ban mamaki ake binta dashi bata damu ba ko a jikinta saboda wani qarfin hali da ta dorawa zuciyar ta ta cire tsoro kada su gane ta, taje ta zauna ta lura wasu daga wurare har zuwa ake ana leqen ta duk bai dame ta ba, mata sarakunan kishi wasu suka fara qananun maganganu akan basu yarda matar Binnani bace kishi da baqin ciki ya sanya suka soma qananun maganganun akan Nurayyah "Ta ya wannan yarinyar zata ce ita matar ɗan takarar gwamna ce, kamar Binnani ace matar sa tana yawo babu jami'an tsaro ko guda a tare da ita, sannan kuma babu ayarin manyan motoci da ke biye da ita kamar yadda aka saba gani da matan manya, gaskiya wannan abin akwai alamar tambaya a sake dubawa."

​Wasu kuma suka ce, "A'a, zai iya yiwuwa fa, it may be sun yi hakan domin boye kansu daga surutu mutane kowa yana son privacy musamman mutum dan siyasa kamar Binnani so ba dole sai an ganta da guards ko manyan motoci ba, and abinda zaku duba yarinyar deserve cos ta haɗu tana da kyau tana sanya kaya masu tsada me ya rage, ai karatu tazo yi ba neman suna ko siyasa ba, wata qila idan kuka bibiya idan zata je unguwa duka ana mata waɗannan school ne kawai bata zuwa dasu dan bata raayi may be,"

Wasu kuma suka ce"Wataƙila ma sai sun ci zaɓe zata fara yawo da securities da motocin gwamnati, yanzu tunda kamfe ake yi, dabarar siyasa ce ta sanya aka barta tana yawo kamar kowa don kar a janyo mata hankalin abokan gaba na wata jam'iya kun san mu mata da nuna fi'ili babu yanda zaa yi matar gwamna guda a gari ta riqa yawo haka idan ba wani target suke son cimmawa ba."  Ire iren wannan maganganun ne kawai suke tashi a hall din wasu suna qarya ta zancen wasu kuma na qoqarin kare ta duka Nurayyah tana jin su babu wanda ta kula ko ta dago ta dube su ta mayar da hankalinta akan wayar ta cike da tunanin abin yi, ana haka sai ga faruq yazo cos abinda yake ji yana yawo bai gasgasta ba a ganin sa duka ya fi su kusanci da Nurayyah duk da bata bashi fuska bata kula shi amma sam babu wata alama dake nuna ita matar aure ce yana son ji daga gareta dalili kenan da ya sanya shi zuwa ya ce, "Wai da gaske ne Nurayyah, kina da aure kuma ke matar mai takarar governor ce Binnani?" Taji gabanta ya faɗi a karo na farko kamar bazata yi magana ba sai ta dago tana kallon sa da kyawawan idanuwanta ta gyada kai alamar eh batare da tayi magana ba, jikin faruq yayi sanyi duk wani burin sa akan mallakar ta yanxu babu shi yaji wani qunci a ransa Allah ne shaida tun ranar farko da ya soma ganin ta yaji yana son ta kuma yana son auren ta, batare da yayi magana ba ya juya ya bar wurin da sauri saboda yanda mutane suka zuba masu idanuwa suna kallon su.

Bayan sun dawo daga school tana kwance a saman gadonta sai tunani take da nazari akan maganganun da ake a makaranta wanda gaskiya ne, matar gwamna zaa ganta da securities da manyan motoci, ko guards masu take mata baya, tabbas idan tana son ɗauke hankalin mutane su yarda da ita dole sai ta nemi waɗannan abubuwan amma ta ina, ina zata samu, wacce ko keken hawa bata da shi kuma bata taba mallakar shi ba bare wata aba mota? And ina zata samu mazan da zasu zame mata security, kanta ya dauki zafi ta shiga tunani sosai da jin karayar zuciya akan abinda take son yi, idan har babu waɗannan babu amfanin nuna kanta a matsayin matar Binnani kuma tabbas bazata qara fita school ba saboda kunya da abinda zai biyo baya na tozarci idan aka gane ta.

​Ta dade tana juyi a kan gado tana lissafin hanyoyin da zata bi, kafin faruq ya fado mata a rai, to ko shi zata tunkara ta gayamasa gsky may be ya taimake ta da wani abu tun da yana son ta da gaske, idan kuma yaji gskyr cewa qarya take ya tona mata asiri fa, bata tunanin faruq zai iya tona mata asiri saboda ta yarda yana son ta da gaske ko a idanuwansa abinda take gani daban ne kuma ta tabbata tun da yana so ya same ta kome tace zai mata dan ya faranta mata.