JODAH

12

by @sadisakhna


 

 

 

______👑 *JODA* 👑_____ 

 

              

 

 

 

Na  

 

*Sadi-sakhna* 

 

Ƴar mutan Jama'are 

 

 

 

 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

 

@sadisakhna on Arewapen 

@SAKHNA03 On Wattpad 

*** on Whatsapp 

 

 

LITTAFI NA 1 

 

 

 

 

*Harƙa ta (12)*👑 

 

 

 

 

**** 

 

 

 

A yamma da Babbar fadar Babban Sarki Mansa Kaita Fasih, Hamshaƙin sarki a zamanin da babu kamarsa a kaf faɗin duniya ballantana kuma yankin Habasha. 

 

 

 

Wata fadace wanda tafi ɗaruruwan fadojin sarakuna da dama,amma idan aka kamanta ta da fadar sarkin daular mali duk da haka itama ƙaramace.  

 

 

 

Fadar Keita Hammarou (Hammar) kenan babban ɗan sarkin Masarautar Mali Mansa kaita Fasih. 

 

 

 

Dukkan shafenta anyishi ne da ɗanyen zinare,walwali da ɗaukar ido ba'a cewa komai a wannan wajen. Katafariyar fada ce da zata iya ɗaukar Mutane fiyeda 200 banda Babbar turakar Ɗan sarkin Wanda shi kaɗai yake rayuwa aciki amma ko hamshaƙai goma ma sai sunce wajen yayi musu yawa. 

 

 

 

Matashin gwarzon Jarumine mai shekara Goma sha Takwas a duniya amma kwarjini da kuma jinin mulkin dayake gudana a cikin jikinsa zai sa mutum yayi masa kallon ɗan shekara 25 . 

 

 

Sauran matan sarki sunyi ta gutsuri tsoma ganin sarki yabashi Fadar Keita Mansa tun kafin yacika shekara ashirin bayan anyi masa aure, wanda shikuma yayi masane saboda jin daɗin wata gagarumar nasara da yayi a aikin daya sakashi yanada shekara goma sha Bakwai. Kuma hakanne yake hura wutar tsanarsa a zuciyoyinsu,ganin an maida ƴaƴansu tamkar masu jira suyi masa hidima a gaba. Bayan kowa a cikinsu batada burin daya wuce nata ɗan yazama a sama fiyeda na kowa. 

 

 

 

Mahaifiyarsa Musso Maleeka ta rasu yanada shekara goma,kuma itace Matar Mansa kaita ta farko,hakan yasa yajashi a jiki ya koya masa dabaru na mulki da kuma horo na yaƙi sosai,domin roƙonta na ƙarshe kenan shine yayi amfani da dukkan ƙarfinsa wajen kare mata rayuwar ɗanta daga abokan gaba. Kuma kasancewar itace matarsa ta farko kuma wacce yafiso,sai ya ɗauki wasiyyar tata da muhimmanci,kuma yake iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya cikata. 

 

 

 

A bangare ɗaya kuwa Keita  Hammar  mutum ne mai matuƙar izza,da ganin manyan mutane ma ba abakin komai ba ballantana kuma bayi dayake musu kallon dabbobi. 

 

 

 

Ƴaƴan sarakuna da manya babban burinsu shine ya karbi ƴaƴansu mata koda a matsayin ƙwarkwara ne bama sai ankai ga mata ba. Amma har yau da ake sauran Shekara biyu dayi masa aure babu wata mace daya taba kallo,domin a ganinsa babu wata mace data cancanci har ya kalleta ballantana kuma bata lokacinsa. 

 

 

 

"Labari ya iskemu yanzunnan,Keita Sunjata yadawo daga yaƙin daya tafi ɗauke da kambun nasara. Hasashenmu ya zamo gaskiya Rishe yana shirin sake juyewa da mujiya a karo na biyu. 

 

 

 

Shine labarin da wani mutuminsa yakawo masa,yana cikin Fadar tasa a ɗakin karatu. Jinjina lamarin yayi kafin yayi murmushi. 

 

 

Alƙalamin gashin ɗawisun dayake rike a hannunsa ya ajiye a cikin wata kwalbar tawada ta zinare, Numfasawa yayi cikeda ƙasaita,batareda ya kalli inda bai mai kawo masa saƙon yake ba yayi magana kaman bazai ba. 

 

"Da alama waɗannan Halittun bazasu daina ingiza ƴaƴansu ba wajen yin abu mai hatsari ba domin samun babban matsayi ba." 

 

Tashi yayi daga kan kujerar ya nufi hanyar fita daga ɗakin karatun,bayi kaman guda biyar suna binsa a baya har ya isa wani hamshakin ɗaki banda walwali na zinare babu abinda yake,dukka bayin a wajen sukakaja burki,iya wata dattijuwar baiwa ce kawai tabi bayansa mai suna Inna Aneesa farar balarabiya wacce takasance baiwar mahaifiyarsa da ta taho da ita,kuma wacce tazame masa tamkar uwa ta biyu. 

 

Rawanin dayake kansa ya ware,dogo kana baƙin gashinsa ya zuba a gadon shimfiɗaɗɗen bayansa. Ban ɗaki ta nufa ta haɗa masa ruwan wanka wanda aka zuba turarruka kala kala daya kasance ya saba da ƙamshinsu tun tashinsa. Sake rigar da take jikinsa yayi ta faɗi a ƙasan wajen ya nufi banɗakin,ita kuma ta tattare kayan ta kaisu inda ya dace kafin ta kawo wasu da ajiye masa akan wani Mulkyakykyen gado da ko ganinsa mutum yakeyi ya isa ya sakashi yaji duk gajiya da sauka masa yana buƙatar ya kwanta ko zai huta. Daga haka tabar turakar bayan ta tabbatar ta haɗa masa dukkan abinda yake buƙata. 

 

Ɗan sarki guda ɗaya kenan da bai yarda da wanzuwar bayi ko yaushe ba a cikin rayuwarsa,ya tashi dayin abubuwa da dama da kansa,ciki shine shiryawa wanka da kuma wasu abubuwan dasuka kasance sirrinsa. Ko Inna Aneesa Bakomai yake bata izini tayi masa ballantana wani. Kowa yasani dokace wata baiwa ko bawa basa shiga turakarsa bayan Inna Aneesa,koma menene saidai mutum ya sameshi a majalisa inkuma bawane a inda yake karatu. Ko kaɗan baya shiga sabgar abinda yake faruwa a gidan sarautar saidai idan ya shafeshi,yayinda a nasu bangaren na gidan sarautar kuwa kowa yadamu da rayuwarsa,shiɗin ciwon idone a wajen mutane dubbai a gidan.  

 

Da safe da kuma yamma akwai majalisinsa a matsayinsa na babban Yarima,sauran ƴayan sarki da kuma ƴayan manya daxasu kasance manyan gobe sukan halarta kowa aji yanayin fasaharsa da kuma inda yake buƙatar gyara ko tuni. Sannan akwai bangaren horo na yaƙi,shima anan wajen kowa burinsa shine yaka ya kada shi ko yaci nasara akansa ko yaya ne,amma ganin hakan yasa yaƙi yarda yabawa kowa damar hakan. Ko yaushe rayuwarsa ta ƙare a wajen Horo dakuma karatu. Domin shikaɗai ne yake ɗauke masa wasu tunane tunane,kuma yakejin kaman an halicceshi dansu ne. Kowa nayi masa kallon mai matsayine kafin yayimasa kallon mutum,ciki kuwa hadda mahaifinsa,wannan dalilinne yasa ya kulle zuciyarsa daga kowanne irin shauƙi ko nuna gazawa................hakan kaman kuma yafara cin rayuwarsa a matsayin abinci sannu a hankali. 

 

 

 

 

A hankali yasamu bakin gadon ya zauna  bayan ya fito daga wankan,ƙirjinsa ya riƙe gamm yana cije jan lebensa wanda kaman ka matsa jini ya fito. Kallo ɗaya zakayi masa kasan yana cikin matsanancin hali. Ya ɗau wasu daƙiƙu a haka kafin ya kaɗa wata ƙararrawa ta gefen gadonsa. Inna Aneesa ce tashigo,ganinsa yana dafe da ƙirjinsa yasa ta karisa da sauri cikin kulawa. 

 

"Hasbunallah yallabai yadai ko ciwonne kai" 

 

Tayi maganar tana ƙarisawa inda yake. Daurewa yayi ya ɗaga mata kai kafin yace. 

 

"Inna Aneesa ko zaki haɗamin wannan shayin yau ma,kwana na uku kenan bana samun bacci" 

 

"To yallabai taya zaka samu sauƙi bayan ko yaushe kana cikin ƙure zuciyarka da gangar jikinka da abinda yafi ƙarfinsu. Ka dunga sararawa ranka sannan kasamu koda mutum ɗayane a wannan duniyar wanda zaka iya faɗamasa damuwarka. Yanada kyau ka dunga jin cewar ba kai kaɗai bane a wannan duniyar,yin hakanne kaɗai zaisa zuciyarka ta samu sukuni idan ka tuna da cewar akwai wani daka yarda dashi" 

 

Jinta kawai yakeyi domin wannan maganganun nata ta daɗe tana yinsu kuma kullum yana saurara amma ko kaɗan bai taba yin aiki dashi ba. 

 

Tashi yayi ya cigaba da shiryawa da alamar fita zayyi,da mamaki inna Aneesa tasake kallonsa kafin ta kuma cewa. 

 

"Yallabai badai fita zakayi ba a cikin wannan halin ko?"  

 

"In kinsani Inna Aneesa meyasa kike tambaya,jinya ko wani wahala indai bawai na kasa tashi ba bazai taba hanani gudanar da aikin daya kasance nawa ba. Domin gazawa ta na nufin na miƙa matsayina da hannuna ne ga abokan gabata,hakan kuma abune da bazan taba yiba matuƙar ina numfashi." 

 

"Yaushe zaka bar gabar daka saka a ranka ta wucene yallabai,wanda ya mutu bazai taba dawowa ba,sannan kowa yayi da muni kansa yayiwa. Sannan a ciki baka san wacece tayi sanadin mutuwar mahaifiyarka ba,dukka kayi musu jam'i kake gaba dasu,ko gaishe dasu bakayi,sannan ƴaƴansu ai yan uwanka ne idan kana ganin su barene. Suma ka yanke katangar alaƙa tsakanin ka dasu. Ko wani abu daya kasance zai haɗa alaƙa tsakaninka dasu yankewa kakeyi. Ina mai tabbatar maka matuƙar bazaka bar ƙiyayyar dake cikin zuciyarka ta narke ba,to babu wani ɗan adam dazaka yarda dashi,kuma hakan shine fetur ɗin dayake rura ciwon zuciyar dayake damunka. Ka gafarce ni amma lokaci yayi dazan sanar da Mai girma mansa halinda kake ciki. Niba babbar mai magani bace,shekara biyar kenan ina taimakonka da wannan lalurar taka amma abu yaƙi warkewa,ina tsoron yayi nisan da bazaiji magani ba har takai rayuwarka tashiga hatsari" 

 

Bin bayanta yayi da sauri amma tayi hanzarin ficewa daga cikin turakar,komawa yayi ya zauna akan gadon yana jujjuya hannayensa alamar wanda yashiga cikin tunani. 

 

A rayuwa tunda ya tashi baisan wani mutum dayake masa kallon shima mutum ne kaman kowa ba bayan mahaifiyarsa da inna Aneesa. Kowa yana shiga rayuwarsa ne da niyyar akwai abinda yakeso daga gareshi. Sannna kowa kallon wanda bazai yi kuskure ba ko ya gaza ba yake masa. Hakan yasa rayuwarsa take wanxuwa a matsayin wanda zai yi komai koda yafi ƙarfin gangar jikinsa da ruhinsa wajen ganin yayi abinda mutane suke zata daga gareshi. Bashida gefen dazai kalla ya nuna rauninsa ko ya yada makaman yaƙin rayuwarsa ya huta na ɗan wani lokaci.  

 

Ya rasa mahaifiyarsa wacce yake ganin tamkar itace danginsa kaɗai a wannan babbar duniyar dake cike da mutanen dayake rayuwa dasu amma ko kaɗan bai taba banbancesu da sabin mutanen daya haɗu dasu a karon farko ba. 

 

Kawar da tunanin dake cikin kansa yayi ya shirya cikin wata riga ruwan jibi dakuma baƙin wando,sai ya saka adon zinare kaɗan bamai nauyi ba,kasancewar baya jin daɗin jikinnasa. 

 

Majalisi ya fita a cikin fadar tasa inda daukkan wasu ƴaƴan manya da kuma sauran ƴayan sarkin ke wanzuwa a tattauna sha'ani na harkar ƙasa wanda yashafi iya su magadan mulkin gobe. 

 

Cikin taƙama kafaɗarsa a tsaye wuyansa ya ɗage yafito kaman bashine yagama riƙe ƙirji ba ɗazun. Bayin dake babbar harabar bakin turakarsa suna ganin fitowarsa suka take masa baya har zuwa ina majalisin yake kasancewa. 

 

Bayan ya ƙarisa wajen kujerar da aka tanada domin zaman sa ya nufa,amma kafin yaƙarisa matasan samari guda biyu suka yi masa magana. 

 

"Ran magajin Sarki mansa ya daɗe?" 

 

Ɗagowa yayi ya kallesu kaman bai taba ganinsu ba,amma hasalima dasune yayi wasan ƙasa. Rayyan ne ɗan gidan waziri Da Umar Ɗan galadima,dukkansu ƴayan manyane wanda suma anan cikin fadan suka tashi. Bai tsayaba duk da sunui masa magana,amma yarage saurin tafiyarsa domin yaji damai suke tafe. 

 

"Hammarou bansan mai mukayi maka ba baka bamu damar ganinka ko kaɗan,kuma nasha rubuta maka wasiƙa akan cewar ina son yin magana dakai. Akan ƙanwata ne Hamrah kai kanka masani akan yanda take mutuwar sonka ka daure ka zabeta a gasar zabar gimbiya daza'ayi nan..........." 

 

"Wanne matsayine dakai a daular mali daya baka damar tsaidani kayimin tayin kanwarka,sannan ka ƙira sunana garangatsau batareda girmamawa ba, Ina son a sakamin laifinsa a cikin kundin rahoto na yau. Ƙanwarka kuma kace tunda tana so tabi layi idan bata samu ba a gyara mata turaka ɗaya a sashen kuyangu takare rayuwarta a can" 

 

"An gama ranka ya daɗe,da sannu wannan gagarumin laifi daya aikata zai shiga kundin na rohoto a yau ɗinnan. Dan haka hattara ɗan waziri sarkin Daular mali na gobene gabanka ba sa'an wasa ba." 

 

 

Dukkansu sakin baki sukayi suna jin furucin keita Hammarou,sun san yanada izza da ɗagawa,ga mungun miskilanci amma basu taba tunanin zai sauƙe matsayinsu kaman haka ba ya maidasu tamkar basuda maraba da bayi a wajensa. 

 

Har aka gama zaman majalisar aka watse jikinsu a sanyaye yake,shikuwa ko a jikinsa haka yayi kaman bai jisu ba ya cigaba da gudanar da lamrinsa,sunyi zaton zai manta da abinda yafaru. Kwatsam suka jiyo ya bawa Rayyan dokar rashin zuwa majalisa na tsawon sati uku sannan ya zauƙeshi akan matsayin sa na cikin majalisar na wucin gadi a matsayin horo ga raini da yayi ga Sarkin gobe mai jiran gado. 

 

Masu mamaki suka shiga yi,wanda dama sunsan zai aikata kuwa ko kaɗan hakan bai basu mamakin ba. 

 

"Ɗan uwa baka ganni bane na dawo dsga karatun dana tafi tsawon shekara uku?" 

 

Hamad ya faɗa cikin fara'ah ga keita Hammarou lokacin daya tashi daga kan kujerar zai fita.  

 

Kallo ɗaya yabi Hamad ɗin dashi kafin yace. "Uhmm to sannunka kayi ƙoƙari,da fatan abinda ka koya zai taimaka maka wajen wasa makaminka a yaƙin dakake ciki" 

 

Dariyar daya keyi ya rage amma bawai fara'ar fuskarsa ta kau ba kana yace. 

 

"Babu wani makami a hannuna,sannna ni babu wani yaƙi dana shiga,dan haka babu wani makami dazan wasa a sanadin yaƙi. Nayi ne domin rayuwata badan na kashe kaina da yaƙi ba. Wanda suke ciki ma Allah ya rayasu" 

 

Ɗan tsayawa yayi kaman zaice wani abu jin furucin Hamad ɗin,amma sai ya ɗan jijjiga kai tareda yin guntun murmushi yayi gaba abinsa. 

 

 

"Ummah ni wlh na gani,tsawon lokaci tunda nayi wayo nakejin ana cewa ni mallakinsa ce,alhalin shi ko tsuntsun daya kwasoni ma bai sani ba. Ranar fah aikana yayi dana shiga sashensa wai yana ce ni baiwa ce. Wlh ummah walaƙancin keita Hammarou na dabanne,ni bazan auri mijinda ko kallo ban isheshi ba ballantana nasaka ran zai kulani." 

 

"Ke dallah rufemin baki marar hankali kawai keba mace bace,idan bai karkato hankalinsa ba ke bazaki karkato dashi ba. Idan Allah yasa kika haihu dashi bakya ganin shikenan Allah ya taimake mu,a ce tsatsonmune zai cigaba da mulkin daular mali. Kedai ki kwantar da hankalin ki Allah yakaimu nan da shekara biyu azo zaban gimbiyar daular mali. Kiyi amfani da kusancinki dashi kici gaba da yin ƴan dabarunki na mata. Harki samu shaƙuwa tashiga tsakaninku. Namijine fah......har ya isa ya tsallake kyakkyawar mace kamarki?" 

 

"Hmmm umma kenan bakisan labarin sa bane,tunda yake bai taba kula mace ba wai sunan so,mai zuciyar dutse sauran mutane suke cema masa" 

 

"Idan bai kula mace ba sai akace baxai kula a gaba ba. Kika sani ko kece wacce zuciyarsa take jira ta narke da isowarta" 

 

Fari Hamrah tayi da manyan fararen idonta cikin jin daɗin yadda ummannata take yabon kyawunta a kullum. 

 

"Fasih....ni ya labarin Hillah ne,tun lokacin da ummanta idan tazo ganin umma take zuwa da ita, data rasu basu sake zuwa ba,ko yaya take yanxu?" 

 

Da rawar jiki wanda yaƙira da Fasih ɗin ya ƙariso inda yake yanayi masa kallon mamaki" 

 

"Yallabai dagaskene kunnuwana daidai sukaji sunan mace waɗannan labbannaka suka furta,kuma kamar da alamar bege?" 

 

Ɗan murmushi yayi yana cigaba da kwafar wani rubutu daga cikin wani ƙaton littafi. 

 

"Ranka ya daɗe ko a tura mata wasiƙar gayyata kai?" 

 

"Ahah ba iya wannan ba inaso ka tura musu saƙo cewar nace inaso tashiga gasa na zama sarauniya a wanda za'ayi nan da shekara biyu" 

 

Zuwa wannan karon zamewa Fasih Yayi harda faɗuwa jin surutan da keita Hammarou yakeyi,anya kuwa kansa ɗaya yau? Kodai kai an bashi wani magani mai saka sambatu yauɗin ya sha. 

 

Fasih yayi wannan tunanin har sannan yana kallon Hammarou wanda yake ta aikin rubutunsa batareda ka kalli Fasih ba,kamar bashine silar sakashi cikin halin ba.  

 

"Waiiihh!!  Gimbiya Hillah ashe kece sarauniyar mata wacce taciri tuta a fadar keita Mansa Hammarou" 

 

 

 

Sadi-sakhna ce ✍🏼 

 

Comment  

Like  

Share  

Follow