BABI NA TAKWAS
by @maidambu41
KARFE DUKKA KARFE NE...!!!
{Zanen ƙaddarar Falilah}
BABI NA TAKWAS.
A little apologize 😹🫀😍🥰
Shiru nayi na wani lokaci, kafin naji saukar hawaye. Ba zan iya tuna kome akan rayuwata ba. Bana son na tuna bayana, domin nasan ba wani kyau yayi ba da zan ishe kaina da son lallai sai na tuna. "Amma dai kin san an hana ki tunani me zurfi haka?" D'ago kai nayi na kalleta kafin na ce mata."Aunty Sadiya tsakaninki da Allah kina zaune da ni ne don Allah ko akwai abin da yake kasan ranki?" Sake baki tayi tana kallona kafin ta ce min. "duk yadda ya miki haka ne" daga haka bata kuma min magana ba, kuma can dama ba zata yi maganar ba, domin a cikin Yaran Hajja Warisa ita ce ba me yawan fara'a da magana ba amma kuma bata da dadi duk yadda kaso a zauna lafiya, ban san me yasa ta makale min ba. Wasa wasa zamana a asibiti yayi mugun addabata, Dr Mu'awiya da Barak sun addabi rayuwata da kara kaina, musamman mara kunya Barak sam yaki yarda na ga idanunsa babu abin da yake d'aga min hankali kamar yadda suke abin kamar hauka, takaba nake wanda kowa yasan haramun ne, fisabilillahi idan ba jahilci ba yaushe mijina ya mutu da suke wannan tashin hankalin da me yayi kama, baki daya sun mai da min rayuwata wata iri, naji da begen mijina ko naji da tashin hankalin da nake kwana da shi, Subhanalillahi mutane basu da dad'i, sai dai ya turo min kayan dubayya. Yau Dr Mu'awiya da kansa ya zo duba ni da wasu rundunar likitoci. "Queen jininki ya koma daidai, amma ki rage tunani." Banza nayi da shi, kamar na tsinka mishi mari. "Dr Mu'awiya ka amshi case ɗinta mana." Inji Zuhrah, wani irin haɗe rai nayi, ina dauke kai. Shafe kansa yayi yana faɗin. "Queen ba zata yarda ba" kunshe dariya Zuhrah tayi, kasa kasa naji an ja tsaki. "waye yayi tsaki." Sanin Dr Mu'awiya bai da mutunci yasa ni jan tsaki kamar nice nayi. "Nurse Zuhrah kin ga ni ba" "Ai dole idan ta haihu ta gama takaba, na tsaya maka niman Queen nan" kamar an ce na d'ago kai, ya juya tare da barin dakin, Ruth Joshua ta ce. "Dr Mu'awiya, ina tare da Nurse Zuhrah." Ganin zasu manna min hauka nace musu. "amma kusan haramun ne ko?" "Sayyadah Falilah, bari mu je." Fita suka yi ban da Zuhrah da ta rage tana cike-ciken takarduna. "Falilah idan kin nutsu ina son muyi magana." "Ki bar maganar nan!" Kamar zai b'alla kofar ya shigo. "Wai me kika dauke ni?" Kallon shi muka yi har da Aunty Sadiya da tashigo da abincin. "Tambayar ki nake Aunty Aishatou Mustapha Liman? Ko dan bamu da arzikn? Ok I guess why kike wulakanta ni, domin duk mazanki babu faƙiri irina ko? Da na fito niman soyayyar ki." "Takaba nake fa! Kuma ko da na gama sai na haihu, idan na haihun ma babu aure a tsarina, please kayi rayuwarka nayi tawa." Na fada mishi sigar lallashi, bana son tashin hankali sam, wani kauda kai yayi yana faɗin."takaba? Yes na yarda takaba kike ni kuma sonki nake da aure." Kallonsa nake baki sake, kafin na girgiza kai ina faɗin. "Baka san meye rayuwa ba, har yanzu baka san halin rayuwa ba. Don Allah ka tafi bana son magana." "Sai kin gaya min me yasa kike rejected ɗina?" "Saboda kai Yaro ne, baka da abin da zai gamsar da ni, ni mace ce da nake son azabtar da zuciyata da so da kulawa, kai kuma Yarinta da shiririta sun ishe ka, idan soyayya kake bukata ina da Yar shekara goma sha uku, ka tafi ka nime ilimi da duniya, ka dawo na baka Humaidah idan har da gaske so na kake na baka Humaidah!" Ba iya shi bane ya shiga firgici hatta Ya Man da ya shigo dakin. "Kin sake rejected dina, sannan kika saka Yarki a tsakanin mu! Me na miki da zafi haka?" "Kayi hakuri gaskiya ta gaya maka." Juyawa yayi ya kalli Ya Man, "Malam yanzu haka zan!" "Ka amshi Humaidah idan har da gaske Falilah kake so!" "A'a bana son wata mace ita nake so, ita nake muradi. Ta gama Idda da takaba zan aure ta." Ya fada da sauri yana me barin dakin, kaina a sunkuye na "Ya Man zan koma wurin Dady da zama kawai." "Mahaifiyarki fa?" Ya tambaye ni, "zan na zuwa dubata, bana son damuwa ne." Fita Nurse Zuhrah tayi jikinta yana kara sanyi, kusan asibitin sun kwantar da ni ne, domin idan cikina ya isa wata bakwai a cire minshi, sai gashi baki daya na gundura da asibitin. Haka kwanaki suka yi ta, gudu a hankali Ahmadi ya cika wata biyu da rasuwa. A ranar Ya Jamal da Matarsa suka zo gani na. Duk da sun sauka a gidan mu, sai da suka tawo har asibitin duba ni. "Sannu Falilah ya karin hakuri?" Inji Ya Jamal "Alhamdulillahi." Na fada, ina karban Ammar. "Maman Ammar ya Hajiya da jiki!" Tabe baki tayi tana faɗin. "da sauki sosai, ita ce ma tasa Honey a gaba yazo ya duba baki." "Allah sarki, Ubangiji ya bata lafiya." "Amin" wani irin yanayi ta shiga, ganin har lokacin babu abinda ya sauya a kaina, sai dai rashin walwala. Dake mazan sun fita şuna da wani abokinsu likita a cikin asibitin. "Falilah na zata zaki zubda cikin nan ne." D'ago kai nayi sannan na ce mata, akan me zan zubda cikin? Ai ko shege ne ba azubda shi ba, balle d'a me cikakken Uba irin Ahmadi." Tabe baki tayi tana faɗin. "Na zata don hajiya bata sonki zaki datse alakarki da zuri'arta ne!" "Ni Ahmadi na aura ba Hajiya ba, cikin Ahmadi ne ba na hajiya ba, so mu bar maganar haka" domin haka kawai sai naji raina yana b'aci, Allah na tuba cikin Ahmadin zan zubda? Ashe kaunar karya nake mishi. Dawowa Mazan bai wani dame ni ba, sai ma maganar da Jamal ya min. "Ance nan da sati biyar zasu cire miki babyn ko? " "Eh" "Alhamdulillahi, in sha Allah zamu zo ayi aikin akan idanun mu. Da Fatan babu matsala a tare da ke ko?" Girgiza kai nayi, "idan da matsala ki gayawa Bana, sannan office din mijinki sun bukaci a bada wani ya maye gurbinsa, shi ne na samu Malam da Bana, yanzu ke muje jira idan kin samu kanki lafiya sai a tattauna asan yadda za ayi." "Amma lamido babu matsala ko?" "Babu wata matsala ita ta dace da office din mijinta, kuma zata fi kowa bawa Basmah kulawa, sai dai idan falilar da nasani ta sauya. Amma fatan Ahmad akanta gaskiya ne, ta rike office din har lokacin barinta aiki yayi."
Gyada kai Ya Bana yayi, "dalilin zuwana kenan, sannan daga ni har Babangida muna aikin mu, ba zai yiwu mu sake aikin ba, matan suma kowacce da tana aikin. Ita falilar ta dace da matsayinsa." "Tow Allah yasa haka shi ne mafi alkhairi." "Amin Ya Allah." Kuka ne yazo min, a hankali ina yi ina karawa. Domin wannan lokacin mutuwarsa ya dawo min sabo fil, gani nake kamar yana raye, kawai boye min ake. Nasiha suke min tare da bani hakuri, hakuri sannan suka bar asibitin. Ashe koda suka koma gida, takarduna da suke wurin Ya Nafi'u, Ya Man ya kira Dady ya turo mishi, shima kuma ya gaya mishi yana zuwa nan da jibi. Zai tashi ranar Juma'a kenan, haka kuwa aka yi Yayuna baki daya suka taru aka hada conference meeting a kaina, a lokacin da Ya Bana ya gafarta musu da bukatar UNICEF da abin da dangin Ahmadi suka yanke, ya musu dad'i musamman Ya Nafi'u da yake ta zabga murmushi yana faɗin. "Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, Ubangiji me kyauta da kari, dama ina shirin gaya mata an mai da ni lagos. Shirin tashin nake babu lokaci ashe itama nata nasarar tana hanya." "Alhamdulillahi, ban san dai inda zasu turata ba, amma ku saka idanu akan inda za a tura ta." Inji Ya Man, "Ya Man haka xata zauna babu aure?" "Inji Hajja Mama da ta zo wucewa. "Zata yi mana, kawai dai zuwa yanzu ta samu nutsuwa koda nan da shekara biyar zuwa shida, yawan auren yayi yawa idan ta kuma aure na takwas kenan fa." Ya Man ya fada a hankali, "eh amma dai shine mutuncinta, idan ta samu mijin tayi auren." Hajja Mama da dai Kinyi hakuri da maganar auren nan, Allah ya zaba mata abin da ya fi alkhairi" maka mishi mafifici tai, tana harararsa. "Sakarai." Da haka suka ajiye zancen inda Ya Man ya kashe zancen auren da lallai Hajja Mama ta ce sai nayi ka da, gata ya min yawa ga kudi ga rashin aure na fada wata rayuwa, kunsan me? Dole Hajja Mama ta ji tsoro, domin mu dai yan gidan mu, muna da wani irin yanayi ne,na bukata shi yasa duk inda nayi aure sai sun bayyana cewa ai ban san kome ba, sai bukatar namiji, bani mantawa lokacin da Ahmadi ya dawo rayuwata domin na zata yazo yaudara ta ne, na gaya mishi cewa. *Malam ba zaka iya aure na ba!* Ware idanu yayi kafin ya ce min. *Akan me? Ba zan iya aurenki ba* *domin ni harija ce* na gaya mishi haka, saboda wannan dalilin yasa ba a ganin laifin Mazan da suke sake ni, sai a bani laifi ace jarabata ce ta kaso auren...
***
Ana saura sati daya a min aiki, Barak ya zo har dakin da nake, ya zauna ga Aunty Sadiya da Nutse Zuhrah. "Na zo ki gaya min me yasa ba kya sona?" Murmusawa nayi sannan na ce mishi. "Kasan me?" "Bari na gaya maka wace ce ni, ruwan ka ka zauna da tunanina ruwanka ne ka rabu da tunani na."
***
Kamar yadda kowa ya sani nice karama a cikin gidan mu, sannan zan iya cewa kusan shalele domin na taso cikin soyayya da gata. Musamman Yaya Nafi'u wanda ya kasance Babba a cikin gidan mu. Mahaifiyarsu Yaya Nafi'u ta rasu, inda rikon su ya dawo hannun Hajja Mama, don matan Ya Man hudu ne, Hajja Mama ita ce Uwargidansa auren saurayi da budurwa, sai Hajja Salamatu, Mahaifiyar su Ya Nafi'u, sai Hajja Jume, sai Hajja Warisa. Hajja Mama Allah bai bata haihuwa akan lokaci ba, sai bayan auro Hajja Salamatu, ta haifi Ya Nafi'u, da Aunty Shatu. A lokacin Hajja Mama ta haifi Aunty Zahra, kafin Ya Bana, sai Ya Kabiru Zainab ta rasu, Ni auta, sai Hajja Jume ita ta haifi Ya Hamza da Aunty Sa'adatu da Jamil, dakin Hajja Warisa. Ya Muhammad, Ya Fahad, Ya Haris, sai Aunty Sadiya. Kasancewar yayuna duk sun girma, dole na koma gidan Ya Nafi'u domin can akwai yan wasa, ni kuma gidan mu babu yan wasa, kuma wani abin sha'awa shi ne, Yayuna Bala'in sona suke, both wadanda muke Uba daya, idan na cire muku mutum daya wacce ban san laifin da na mata ba. Allah ya daura min niman fada, gashi bani da karfi. Hanifa da Safiya sune kawayena, kusan makarantar mu ma Yaya Nafi'u yake biya, sannan ban da Yaranta, kallon su Ya Man da Hajja Mama nake a matsayin kakanina, domin yadda na bude idanu naga Yaya Nafi'u yana hidima da ni, a yadda nake jin labarin ranar bikinsa aka haife ni. Shekarata takwas a duniya amma kaf layin mu, babu wanda be sannin ba a wurin niman fada da tsokanar tsiya. Bani mantawa mun fito islamiyya wasu yara guda biyu, suka tsokane ni da Falilah tsigai, wato ina da baki da masifa amma bani da karfi ko kaɗan, haka yasa suke kirana falilah tsiga. Gashi bana son sunan, don Allah cikin jin haushi na dauki dutse garin na jefe su, ai kuwa na samu wata mata da take ajiye a wurin, ai kuwa glass din motar ya fashe. Ware idanu nayi, a lokacin baki daya yaran suka watse ban da Hanifah da Safiya. Rike hannuna suka yi, tare da jana muka gudu. A tunanin mu za a nemi gidan mu, amma har yanzu lokacin babu wani labari, a bakin Yara daliban Ya man suka ji labarin barnar da nayi, koda aka bi sawun inda aka yi abin babu alamar abin ya faru, sai ma wani irin tsoro da ya dirka min. Ya Man ya kira ni ya min fada, ranar banci abincin dare ba. Fushi nayi da kowa. Ashe akwai tashin hankali, washi gari mun yafi school. Sai ga motar nan har kofar makarantar mu, juyawa nayi na fara niman Hanifah ina samun ta na ce mata. "Kin ga motar jiya tazo!" Juyawar da zamu yi babu motar babu alamarsa. "ina motar?" "Yanzu fa na ganshi a nan fa!" Na nuna mata inda motar yake tsaye, "hala motar aljani kika fasa " tabbas na tabo bala'i, domin ba iya ni, duk wanda yake tare dani yasan na cilla rayuwata cikin tashin hankali. Abin mamakin anan shi ne yadda iya Ni daya nake ganinsa babu wanda yake ganinsa da wannan Ya Man yake ta fadar cewa gamo nayi, domin idan ba gamo ba ne taya iya ni zan na ganinsa. Sosai aka yi ta min ruki'a ko zan daina ganinsa, sai dai abin ya ci tura domin ganinsa nake sosai, kuma abin sai nice nake ganin. Bani mantawa lokacin Ya Man har Maiduguri ya kai ni, babban family house ɗinsu. Ana aka ta bani Addu'oin da su rubutu, har na dawo daidai kamar sauran Ƴaran. A hankali nayi ta girma ina kara samun kaina cikin rashin ji, kasancewar nice karama yasa babu me iya tankwara ni, sai Hajja Mama domin kaf duniya bani da wacce nake mugun shakka da tsoro irinta, akwai wani bikin sallah da aka yi. A ranar sallah kayan mu iri daya da Ya Nafi'u, shadda ce fara kal yadda aka Mishi aikin Surfani haka nima aka min, muka dawo idi, Hajja Jume ce take ta faman kaiwa da komowa, wani abun da yake kafe a cikin gidan mu,shi ne har kwanan gobe masu aiki wanke-wanke kawai suke a cikin gidan mu amma basu abinci, sannan abincin gidan baki daya matan Ya Man suke haduwa su yi tare baka iya banbance wace ce da miji wace ce mara miji. Haka ya sanya muka taso da hadin kai, har yau baka tab'a tantance mu domin baki daya muke kama da juna,idan ka cire ni da nake da duhun fata. Iyayen mu nada haɗin kai. Ana ta rabon abinci aka zuba mana namu, sai ga Mubin d'an Ya Bana, ya shigo cikin mu. Ai kuwa na ce mishi. "Ba zaka ci abinci da mu ba, kaje wurin yan uwanka maza" tashin da zai yi kawai ya tunkuda ni kan tuwon shinkafa da aka zuba mana, Allah yaso da sanyi babu zafi da na kone, ai kuwa na bata kayan sallah ta, yadda na fasa ihu haka na fadi a kasa ina burgima abin da ya bawa Hajja Mama haushi kenan ta dauko bulogari tayi ta muka min, sai da Ya Man ya fito ya ganta tana shirin kashe ni ya ce mata. "Wallahi kika kashe min y'a kotu ce zata raba mu dake, tunda ba kya kaunarta" taji haushi sosai, har da guntun fushinta. Duk da haka Ya Nafi'u sai da ya kai ni asibiti aka bani maganin zazzaɓi, cikin dare nayi ta ihu da firgita ina fisge-fisge. Dakyar aka samu kaina, tun daga lokacin Hajja Mama ta daina duka, kuma dama ba dukan take ba, haushi na bata.
*Bai zama dole nayi update kullum ba, koda sau uku zuwa hudu zaku samu, zan na skipping kwana biyu saboda hidimar Yara da gida, idan bai muku ba, sai dai a hakura wallahi*
#Mai_Dambu