RIGAR ARO

12

by @pherty001





Washe gari da Nurayyah ta tashi da wata irin kasala da gajiyar tunani da suka hana ta samun cikakken barci cikin dare, duk da haka ta shirya kamar yadda ta saba, da fadila tazo suka nufi makaranta, zuciyarta cike da wani nauyi da tun jiya yake danne mata kirji. Tun da suka isa school take ta raba ido inda zata ga faruq har suka gama darasin farko bai shigo ba sai tayi tunanin ko bai zo school bane, bayan sun fito tana kokarin zuwa inda fadila ta hango shi saman motar sa tare da wasu abokan sa guda biyu, kenan yana school shine bai shiga lecture ba, jiki a sanyaye ta nufi inda shi ke, sanda ya hango ta tana zuwa gurin shi yayi mamaki cos bata taba neman sa ba wacce ko magana yake mata sai ta ga dama take amsawa, mamakin sa ya qaru sanda tayi masa alamar yazo, tace tana da aure to neman me take masa, kada fa a dauka tare suke aje a gayawa Binnani wani abu ya same shi, kamar ba zai je ba ya diro daga saman motar bayan yayiwa friends din sa magana ya nufe ta, yana zuwa yace 

"lfy Nurayyah?" A sanyaye tace "Ina son magana da kai" Mamaki ya ƙara bayyana a fuskarsa amma bai nuna  ba sai ya gyada kansa kawai, "Okay"

Faruq ya bi bayanta cikin sanyin jiki da mamaki, har suka sami wani kebantaccen guri a ƙarƙashin bishiyoyin dake bayan school auditorium, wurin babu hayaniyar ɗalibai. Suka zauna a kan dakalin siminti dake wurin, Nurayyah ta yi jim sanda taga alamun ita yake saurare kafin ta ɗago idanunta da suka ɗan sauya launi saboda rashin barci tace,

"tambayar ka zan yi please, meyasa kake bibiya ta tun ranar farko da ka soma gani na?" Kai tsaye yace "saboda ina son ki kuma auren ki nake son yi, but tunda kina da aure kuma ke matar babban mutum ce na haƙura"  ta sauke ajiyar zuciya a hankali sannan taja numfashi kafin ta sake gyara zamanta ta dube shi tace "idan na gayama gaskiya ba zaka tona asirina ba, zaka rufa min asiri?"

Faruq ya yi shiru yana kallonta cikin tsananin mamaki dake nuna cewa bai yi tsammanin jin wani abu daban daga gare ta ba kafin daga bisani ya gyaɗa kai alamar  gaskiya da amincewa, Nurayyah  tace "ka min alƙawari ko abokin ka ba zaka gayawa wannan gaskiyar ba idan har kana sona da gaske, ni kuma na yi maka alƙawari zan kasance da kai a kullum" Faruq dake son jin menene wannan take son faɗa har take cewa zata kasance dashi bayan tasan tana da aure cikin sauri yace "insha Allah, menene?"  Nurayyah ta yi jim tana tunanin yadda zata fito da zancen kafin ta daure tace "ni ba matar Binnani bace, in short ban taɓa ganin sa ba, ban san shi ba sai a ranar da na ganshi a poster, na faɗi sunan sa ne saboda kawai wannan guy ɗin kada ya cutar da ni yace zai watsa min ruwan acid ya bata fuskata shiyasa naji tsoro nace masa ni matar Binnani ce"

Yanda Faruq ya cika da tsananin shock da mamaki abin ya kasa musaltuwa cos maganar ta zo masa a ba-zata, ya gyara zamansa da kyau yana kallon kwayar idanunta don tabbatar da abinda yake ji yace "ƙarya kike da sunan babban mutum, ke ba kya jin tsoro ya saka a kama ki ko kuma ƴan adawar sa su cutar dake, baki san akwai anan school ɗin ba?" Idanun Nurayyah suka yi rau rau ita bata duba hatsarin dake cikin abinda suke magana shi da fadila kawai ita yanda burinta zai cika take so, ganin yanda jikinta yayi lagwas faruq yace "yanzu me kike so ni na yi maki?" Ta dube shi tace "domin tabbatar da cewa da gaske ni matar Binnani ɗin ce dole sai na haɗa da manyan motoci da securities da zasu riƙa bina a duk inda zan je, bani da manyan motoci and ban san inda zan sami securities ba" sai faruq ya fashe da dariya for the first time, dariya sosai cikin mamakin ta kafin ya tsagaita yana mata wani kallon raini yace "dole sai kinyi ƙarya, ba karatu kika zo ba, malama ki maida hankali kawai ga karatun ki babu ruwan ki da wannan ƙaryar domin duk ranar da aka gane ki wallahi am sorry for you, ina baki shawara saboda ina son ki da gaske, and yanda school ta dauka cewa ke matar Binnani ce a yanzu idan kina so I know how to handle it na gayamasu gaskiya batare da kin tozarta ba ki cigaba da normal life din ki kamar kowa" Nurayyah ta yi shiru ta kasa magana cos ba haka take so ba, ita ba karatun bane a gabanta yanxu, tunda bata da raayi a wannan fannin babu abinda zai saka ta karatun Mass Com, ba dan tana so ba cikin rawar murya da tsanani damuwa ta gayamasa komai da waleeda tayi mata da kuma dalilin da yasa take son yin hakan, ta nuna masa bata son ta haqura ita tana so ta rama abinda Walida tayi mata ta hanyar samun kusanci da Binnani, irin kukan da take masa ya saka jikinsa sanyi cos mace bata taba sanya shi a gaba tana kuka ba musamman kukan Nurayyah da yake jin yana son ta yana jin kukan har cikin ransa, ya zuba mata idanu yana nazarin yadda take roƙonsa kafin yace "na yarda zan taimaka maki but sai kin min alƙawari zaki aure ni" Nurayyah ta yi shiru tana kallonsa yayin da zuciyarta take bugawa da sauri da sauri, faruq kuma ya kafe ta da idanuwansa, domin cimma burinta idanun ta sun riga sun rufe har bata hango wata matsala a gaba kai tsaye ta gyada kai ta amince da zata aure shi, faruq yaji dadi sosai ya yarda zai taimaka mata, nan suka zauna suka tsara komai akan idan sun zo school ba ruwan su da juna tunda ana mata kallon matar aure, idan suna wajen school zasu riqa fita yawon shakatawa tare da sauran su, ya gayamata baban shi babban ɗan kasuwa ne bai cika zama Nigeria ba yafi yin business din sa a China so kullum cikin tafiye tafiye yake idan bayanan yayi mata alqawarin zai riqa dauko manyan motocin sa yana arama ta tana zuwa school dasu da duk inda zata je mgnr guards kuma masu masu gadi da mahaifin sa ke bari guards shidda ne zai yi magana da uku su riqa bibiyar ta shi zai yi settling da shi, Nurayyah taji dadi kamar an mata albishir da gidan aljanna, irin dadin da taji kamar ta rungume faruq take ji a wurin, shi kansa ya lura da yanda taji dadi.

A daren ranar, Nurayyah ta sanya Faruq ya zo domin ya ga unguwar su wallahi yayi matuqa sosai da ganin irin unguwar da ta fito da kuma gidan da take zaune amma take son yin wannan ƙaryar.

Wallahi da matukar mamaki da al'ajabi ya bar unguwar a daren , cos zuciyarsa ta kasa amincewa da abin da idanunsa suka gani, yarinyar tana da wani irin gutsy character. A cikin inner thoughts ɗinsa, ya kasa daidaita hoton Nurayyah da yake hangowa makaranta idan ta sha kwalliya tayi kyau da irin gidan da ya ganta a ciki shi wallahi ya dauka ƴar wata shege ce a garin ashe ashe...... Kuma a hakan Yarinyar take son nunawa duniya ita matar wani babban mutum ce mai fada a ji, matar wani high-profile personality, da Mamakin hakan ya yi barci.

Washe gari da , da Fadila ta zo ɗaukar ta, Nurayyah ta fito bata ko shirya ba, fadila na ganin ta ta sauke glass tana kallon ta tace "Beb what's wrong na ga baki shirya ba? Nurayyah ta qago murmushi yaqe kafin tace "Fadila ki wuce kawai."

Wani irin mamaki ne ya cika Fadila, she was totally caught off guard, cikin tsananin surprise ta ce, "Meyasa bazaki je ba Nurayyah? Is everything okay?"

Nurayyah ta ce, "Zan zo daga baya akwai abinda zanyi wa Jaddi ina gama zan shigo, Just wuce kada kiyi latti."

Fadila ta dube ta na wasu dakiku, "To shikenan, sai kin zo," Fadila ta faɗa kafin taja motar ta wuce, Nurayyah ta saki wani boyayyen murmushi ganin fadila ta tafi bata tsaya bincike ta ba, a smirk of victory. Ta juya da sauri ta koma cikin gida, Direct akwatin kayanta ta nufa, ta dauko wani tsadadden lace mai ruwan madara (cream-coloured), dinkinsa ya zauna daram a jikinta. Lace din yana daya daga cikin kayan da Fadila ta bata da bata sanya ba, dinkin ya fito da kowace sura ta jikinta, ya kara mata wani irin regal and sophisticated look.

Kwalliya sosai tayi kuma tayi kyau ta baza turare ta ko ina a jikinta, ta dauko wata hadaddiyar jaka da takalmi mai tsini, high-end designer stilettos, duka cikin kayan da fadila ta bata ne, a tsintsiyar hannunta na hagu, agogo ne  na mata masu aji, a gold-plated luxury watch. 

Ta dubi kanta sosai ta mirror ita kanta ta san tayi kyau sosai takoma kamar wata infant princess.

Tana qoqarin fitowa daga dakinta taji dirar motoci kamar a qofar gidan su, a gurguje taje ta yi wa Jaddi sai anjima kafin ta fito, turus ta ja ta tsaya tana kallon motocin dake qofar gidan su guda biyu, baƙaƙe sol, kirar Prado V6 na zamani, Gilashin motocin gaba daya baki ne (fully tinted), suna ta sheki, Karar injin motocin da tsarinsu ya tayar da hankalin mutanen unguwar. Yara kanana na layin har biyo motocin suke yi suna ihu irin yanda yaran unguwa suke su biyo mota,

Malam Musa yana tsaye a kofar gida, idanunsa cike da taraddadi yana kallon yadda motocin suka daidaita a daidai kofar gidansa dana Jaddi.

Nurayyah ta qarasa jikin motar da aka bude mata tana tafiya cike da jiji da kai da tinkaho, radiating pure confidence and arrogance, Ganin yanda mutanen unguwa suke kallonta da mamaki bata ko damu ba ta shiga motar aka rufe.

Layin gaba daya ya rude ba ga samarin ba, baga matan ba aka shiga tsegumi da surutu a kanta. Malam Musa dake tsaye ya ji wani irin daci a zuciya ganin yanda Nurayyah ta koma yanzu babu kunya,

sanda suka iso school aka bude mata motar ta fito, ta fito cikin wani irin taku na daukar hankali, dalibai da ma'aikatan dake kusa suka zuba mata ido, Tana yin wata irin tafiyar qasaita kamar matar governor da gaske tafiya ce ta mutane masu kuɗi, mulki, da aji, an elitist composure sai wani yatsina fuska take tana bin mutane da kallon banza irin ga matar governor nan.

Abin da ya fi ba kowa mamaki shi ne, yau da jami'an tsaro (securities) take inda aka soma tunani may be dan anyi magana ne akan su yau tazo da su dan ta tabbatarwa mutane da cewa da gaske ita matar Binnani ce, duk inda ta saka qafa suna take mata baya fuskarsu ba annuri ga baqin glass da suka manna a ida uwansu, duk inda ta bi ana nuna ta da yatsa, creating a ripple of whispers. Shigar ta aji ya sanya malamin dake tsaye da sauran dalibai duka suka yi shiru ana kallonta, ta nemi guri ta zauna guards din suka koma bayan ta suka tsaya kowane fuskarsa ba annuri, malamin ya kasa magana cos duk sun ji lbr matar Binnani ce, a hakan ya cigaba da darasi har ya gama ya fito, tun daga nan kowa ya shiga tsoron ta ko kuma abinda zai haɗa su da ita, bayan sun gama duka lectures na ranar ta fito her guards trailing closely behind her. Fadila da taji lbr yanda maganar ta bi school yasa tazo ta ganewa idanun ta for the first time ta kasa gane Nurayyah saboda wani irin kyau da tayi da kuma wata tafiya ta ɗaukar hankali da take sai ka rantse dama Nurayyah yar babban gida ce idan baka san asali ta ba wallahi mutuwar tsaye tayi har sanda Nurayyah ta qaraso gare ta tana mata murmushi cikin yin far da ido, fadila ta bata rai eyeing her up and down with sheer disbelief kafin ta ce, "Ashe da gaske ne abin da ake fada, wai matar governor ta shigo makarantar nan yau! Ance kin zo da securities yau ma... but wait Nurayyah, wadancan manyan motoci guda biyu da wadannan mutane guda uku dake take maki baya a ina kika same su? Me kike shirin yi da rayuwarki are you feeling happy da abinda kike yi yanzu?"

Nurayyah ta hade girar sama da ta kasa, ganin yadda idanun mutane ke kansu, ta sa hannu ta riko hannun Fadila, suka matsa jikin wata bishiya a gefe guda inda babu cinkoson mutane, seeking a moment of absolute privacy. Nurayyah ta tsaya tana kallon Fadila dake ta faman huci, ta daidaita tsaiwarta cikin natsuwa ta ce

"Duka a gurin Faruq na same su, motocin gidan su ne, wannan mutanen kuma guards ɗin babanshi ne. Yace babanshi baya nan yayi tafiya shine ya kira uku daga ciki suka zo And shi zai biya su duka, it's a financial deal, ai babu wata matsala insha Allah just pray for me ke kin cika tsoro wlhy."

Wani irin bacin rai mai zafi ne ya mamaye zuciyar Fadila, a wave of pure frustration. Ta ji jikinta gaba daya yana rawa saboda takaicin yadda Nurayyah  ta nutsar da kanta cikin kogin karyar da zata iya halakar da ita a kowane lokaci. Fadila ta kura mata ido,  jikinta har rawa yake saboda bacin rai ta ce, "Lallai Nurayyah, baki da hankali ko kadan! Wannan wace irin rayuwa ce ta hauka da kika dauko wa kanki? Karyar da kika sani sarai zata zo ta bayyana gobe ko jibi? Kina so ki nuna wa duniya abin da baki da shi? Menene abin burgewa anan, the luxury cars or the securities guards, sunan ki kike so ki bata da mutuncin ki a idon mutane saboda fake life ko kuma saboda wata banza dake can tana rayuwar ta and ta manta dake! Wannan hanyar da kika dauko ta karya ba zata kai ki ga nasara ba, rayuwar bogi ce wacce zata ruguje miki at anytime, and your facade will crumble into pieces! Ranar da ta ruguje, zaki zama abin tausayi a idon kowa, ni dai har ga Allah banji dadi ba kuma bana son wannan rayuwar!"

Nurayyah ta lumshe idanunta a hankali, absorbing every sharp word, tana sauraren maganganun Fadila, if not fadila then who? Waye zai gayamata maganganun nan marasa dadi ta haqura ta kyale shi fadila kaɗai ta kai wannan matsayin, ta saki wani gajeren murmushi na gadara da nuna isa, a cold, prideful smile, ta ce

"Kwantar da hankalin ki Fadila, zan daina idan lokaci yayi, ba zan dauwama a haka ba. But for now, yanda na zama wata a makarantar nan kowa ke girmama ni har malamai na ɗanɗana wannan daɗin da respect, gaskiya bazan iya dainawa yanzu ba, idan na daina mutane zasu gane qarya nake yi dama ni kuma bana son haka so I have to sustain this high status profile, dole in karasa abin da na fara."

Fadila ta ce, "Wace irin girmamawa Nurayyah? Malamai da suka girme ki wasu suka haife ki kike jin dadin su baki girma dan kawai kudi da mulki na qarya, bakya tsoron ranar da asirin ki zai tonu? Idan Faruq ya tona miki asiri ko mutane suka gano gaskiyar ki fa? Your reputation will be utterly ruined!"

Duk yanda Fadila taso nuna mata gaskiya tare da hujjoji, Nurayyah taqi ta gane taqi ta saurare ta, da ta ga fadila zata bata mata lokaci da surutu da bazai amfane ta ba sai ta katse ta " idan mun je gida zamuyi maganar shikenan yayi maki ko" kafin fadila ta bata amsa ta soma tafiya cikin izza fadila ta bita da kallon mamaki, tana kallo aka bude mata mota ta shiga aka rufe, kusa mutuwar tsaye tayi a wurin sanda motocin suka fice daga school ɗin, da kyar ta iya jan qafafunta da suka mata nauyi zuwa motar ta.