BIYU A ƊAYA

Chapter 6

by @barista

BIYU A ƊAYA 

***
YOTA 13 
Team of FIVE INK legends 

Dedicated to princess Nimcyluv 👸🏻


GHANA 

Page 6

Shiru su ka yi suna zaune duk sun yi tagumi kamar waɗan da ke zaman makoki, babu me magana a cikin su, tun safe suke wajen har zuwa wannan lokacin ba su motsa ba, ƴar wasan nan da suke yi ma yau babu ita. Aicha ce dake zaune kamar wacce aka yi wa mutuwa ta ɗago tayi tozali da matar da ta taimake ta jiya, da sauri ta ce

"Lah ga tanan yau ma"

Suka ɗago dukkanin su suna kallonta, ita ma su take kallo, tun jiya da ta koma gida take bin su cikin ranta, tana mamakin me suke yi a gefen hotel? Abin al'ajabin ma yara ne babu me cikakken hankali a cikin su, komai zai iya faruwa da rayuwar su.

Takowa tayi a hankali zuwa inda suke zaune, ga mamakinta ko motsa wa ba su yi ba ballantana ma su ji tsoron ta, a hankali ta zauna ita ma kan dakali dake fuskantar nasu, ta yi magana cikin siririyar muryarta me daɗin sauraro

"Sannun ku yara"

"Ki bamu abin da kika kawo sai ki tafi"

Cewar ɗaya daga cikin su, wanda shine ya fi su ɗan girma, da mamaki take duban su, ta basu abin da ta zo dashi kuma?....

"Ko kema nema ki ka zo yi?"

Yadda suke magana babu ko tsoro yasa tayi mamaki, ta kalli Aicha ta ce

"Me kuke yi anan?"

"Sadaka muke karɓa"

Cewar ɗayan yarinyar, abin da ya faɗa ya gigita ta, what sadaka?" Da ƙyar ta numfasa sabar tashin hankali da kaɗuwa ta ce

"Wane irin sadaka?"

"Ko mene ne ma muna karɓa"

Gasu yara ne ƙanana amma kuma babu ko tsoro a tare dasu, a hankali ta sauke numfashi tare da cewa 

"To gashi ban zo da komai ba, ballantana na baku"

"Ni Alawa nake so"

Cewar Aicha, ta miƙawa Aicha hannun akan ta iso gare ta amma ta girgiza kanta alamun a'a, ta sauke numfashi tasan tsoron niqabin da ta saka ne take ji shiyasa taƙi tahowa gare ta. 

Ta mik'e tana dube dube ko zata hango shago amma bata hango nan kusa ba dole sai ta tsallake titi, haka ta mik'e ta iso bakin titi ta sallake ta sayo musu biscuits da Alawa sannan ta dawo ta ce su yi layi, su kayi suna murna ta raba musu sai tsalle su ke yi, ta sauke numfashi tausayi suka bata to ina iyayensu? Musamman ma Aicha wacce ita kaɗai tasan sunanta a cikin su, a hankali ta rage tsawonta daidai na Aicha ta ce

"Ina ne gidanku?"

"Mu bamu da gida"

"Bangane ba, ina mamanki?"

"Ta mutu"

Daram ƙirjinta ya bada, tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya tazo kan yaron da ya fara yi mata magana a lokacin da tazo, 

"Ya sunan ka?"

"Muneef"

"Muneef, nice name, ku tafi gida kada ku sake zuwa nan"

Ga mamakin ta suka kece da dariya dukkaninsu har da Aicha wacce bata san ma kanta ba, ta dinga binsu da kallo har suka zauna suna shan Alawa, bata ce komai ba ta juya cikin sauri tana duba agogon wayar ta, tayi sauri ta hau ɗan mashin ta bar wajen......


************************

Tun da Bilqees ta bar ɗakin Alaja ta dinga bin kororo² lungu² sako² tana neman ma'aikatan tana sanar dasu Alaja tana neman su a ɗakin taro, duk da ba wani amsa mata suke ba kawai faɗa musu take yi tayi gaba abin ta. Ba a ɗauki lokaci ba duk suka hallara nan Alaja ta gabatar da jawabi, akan anyi sanyi a restaurant ɗin, ba a tarɓan customers yadda ya dace, cikin ɓacin rai tayi magana 

"Naga kamar kun gaji da aikin ne shine kuke yadda kuke so, to ku sani duk wacce ta kuskura ta zama sanadiyar jawo daƙushewar wannan restaurant ɗin to wallahi sai ta fuskanci tashin hankalin da bata taɓa sanin akwai shi a duniya ba, ni za ku maida shashasha ban san abin da nake yi ba.

Suka haɗa baki wajen bata hakuri 

"Ki yi hakuri Alaja ba za mu gyara kuskuren mu"

Tsaki taja sannan ta ci gaba da cewa

"Na gani a aika ce ba wai a faɗan baki ba, na kula har wani haɗa kafaɗa kuke yi dani sabar bushewar ido, to ku sani duk iskancin ku a ƙarƙashina kuke...

Ba su ce uffan ba, ta wanke su tas da soso da sabulu, ba tare da ta bari sun sake yin magana ba, sannan ta ce

"Gobe za ayi baƙi tun safe nake so kowacce ta fito aiki a fara shirye-shiryen tarɓansu, kuma manyan mutane ne, don haka ku kashe kanku wajen ganin sun samu farin ciki a cikin wannan restaurant ɗin"

"Za mu yi ƙoƙarin ganin hakan ya faru"

Suka haɗa baki wajen faɗan haka, amma Alaja ta daka musu tsawa tare da cewa 

"Ba ƙoƙari nake so ku yi ba, ku aikata da ƙarfin ku"

Tayi ta musu balbalin bala'o'i sannan ta ce su ɓacewa ganinta. Kowacce tayi hanyar ta, Bilqees ta mik'e ta koma kitchen duk abin da ta san aikinta ne ta kama yi......


*******************************

Nigeria Maiduguri KIRAWA'S FAMILY 

Zuba mata na mujiya su ka yi suna kallon ta, ganin ta shigo da basket har guda biyu ta ajiye ba tare da ta ce da su komai ba take hawaye. Runtse idanunta tayi tana jin ƙirjinta yana yi mata zafi da raɗaɗi, kamar ta ƙwala ihu ko za ta ji sauƙi amma ina babu hali, Hauwa ce ta yi magana 

"Sis Ashfat me ya faru? Kin fita kina farin ciki yanzu kin dawo kuma kina hawaye"

Ba ta ce komai ba haka kuma bata daina zubda ƙwalla ba, Suhaima ta yi magana duk da a lokacin bacci take ji ta ci ta ƙoshi ta kwanta bacci ya fara ɗaukanta ta ji shigowar Ashfat shine ta buɗe idanunta ta ɗan ɗago, a hankali ta yi magana 

"Aunty Ashfat, mene ne?"

"Uhm"

Kawai Ashfat ta iya cewa, Teemah ta ce

"Ko dai ciwon kanta ne ya tashi?"

"Ba shi bane, sis Ashfat wa ya ɓata miki rai?"

"Ku kyale ni"

Shine abin da Ashfat ta iya cewa, ta kwanta kan katifa tana sauke numfashi, Hauwa ta janyo basket ɗin duka biyu ta buɗe ɗaya bayan ɗaya taga yadda Ashfat ta zuba abinci ta kai haka ta dawo dasu, ta sauke numfashi wato Ya Wahaab ya nuna mata halin nasa kenan, to me yasa take kuka don bai ci ba....

"Sis Hauwa me kike kallo cikin basket ɗin?"

Cewar Teemah, sauke numfashi Hauwa tayi ta  gyara zamanta tare da cewa 

"Ya Wahaab bai ci abincin ba"

"Shine take kuka?"

Cewar Suhaima, Teemah ta ce

"Shine mana tun da kin ga ta shigo ɗauke da basket ta dire ta soma hawaye"

"To wa ya sani, in dai Ya Wahaab ne kin kama aiki, ki ma tashi ki wassake ya fi miki, ba kasafai abu yake burge shi ba, maybe baya ra'ayin abin da kika girka ne...

Cewar Hauwa, Ashfat ta katse mata magana ta hanyar cewa 

"Who told you?"

Murmushi Hauwa tayi tare da cewa 

"Ai kin san alaƙar dake sakaninmu hakan ma ya ishe ki amsa"

"To ba haka bane, cewa yayi, ya ci abinci a side na Ya Sa'eed shine bai samu ya ci wanda na girka ba"

Murmushi Hauwa tayi, ta koma ta kishingiɗe, Suhaima ta lumshe idanunta da su kayi mata nawi, tayi magana a hankali 

"To sis Hauwa abar magana, da wanne za ta ji"

"To na bari amma da kanta za ta biyo ta hannuna"

"Ke kika sani"

Cewar Ashfat ta ci gaba da hawaye....

*******

Dr Waahab Waseem KIRAWA, Ashfat tana fita ya zauna bakin bed ya sauke numfashi, bai ji komai ba, don shi komansa a faranti yake yinsa, in zayyu to zayyu, in kuma ba zayyu ba haka ma ba zayyu ba, ya mik'e ya faɗa toilet ya watsa ruwa ya jima yana wanka sannan ya fito, ya shirya cikin ƙanana kaya ya gabatar da sallah azahar sannan ya ɗauko system nasa yana dubawa, yana nan zaune har lokacin sallah la'asar, ya idar sannan ya shirya ya fito ya yi wa Mamie sai ya dawo ya wuce parking space ya shiga motar sa ya tada kai tsaye sai Teaching hospital TH.

Yana shigowa cikin hospital ɗin ya wuce parking space, bayan yayi parking ne ya fito tare da ɗauko white coat nasa ya rataye a hannunsa bayan ya saka side bag nasa, ya sanyawa motar key kai tsaye ya wuce office nasa, yana isowa ya buɗe ya shiga, fes an gyara masa komai tsaf ya zauna tare da sauke numfashi ya ajiye white coat nasa ya kunna system nasa yana dube dube...

Turo ƙofar da aka yi ne yasa ya dago, aka yi sallama ya amsa, sannan ya ƙaraso tare da cewa 

"Our special Medical doctor har ka shigo?"

Ya sauke numfashi tare da cewa 

"Yanzu shigowa na, have a seat"

Ya zauna tare da cewa 

"Tun ɗazu nake jiran shigowar ka"

"Dr Faisal da fatan dai ba laifi nayi na?"

"A'a akan batun tafiyar ne, ni na ma kammala shiri sai dai Madam ta ce ba zayyu na tafi ba sai da ita"

"Dr Faisal wannan ai abin da ya shafe mu ne ban da ita, how comes ta bimu"

"Kasan Amarya ce, to gashi kuma yarinyar ce, barinta ita kaɗai har tsawon 3 months abin bai yi ma'ana ba"

"Na fahimta wannan ra'ayinka ne, bana amarya ba"

Murmushi Doctor Faisal ya yi tare da cewa 

"Let's go straight to the point, naga kuna ɗasawa da Dr Ɗayyab kuma kaga shine jagoran tafiyar ma baki ɗaya, kayi masa magana in zayyu na tafi da mata ta"

Murmushi Dr Waahab yayi sosai tare da cewa 

"Ango"

Dr Faisal ya sosa keyarsa tare da cewa 

"Ba zaka gane ba"

"To kada dai kayi min gori, zan yi magana da shi amma ina ga tafiya da ita ba zai zamo matsala ba, duk da haka zan yi magana dashi"

"Yawwa na gode sosai, ya shirye shiryen tafiya?"

"Kasan meye?"

"A'a sai ka faɗa"

Cewar Dr Faisal yana gyara zaman sa, Dr Waahab ya ci gaba da cewa

"Ni ko fara shiri ban yi ba gashi tafiya saura 5 days abu kamar wasa"

"To Ya kamata ka fara shiri fah kwanaki kaɗan suka rage"

"Gobe in sha Allahu zan shirya komai na"

"Ya fi kam, bari na koma office, sai zuwa anjima"

"Ok sai anjima"

Dr Faisal ya wuce, Dr Waahab ya ci gaba da ayyukan sa.....


******************

"Ke Ashfat tashi lokacin sallah la'asar ya yi"

A hankali ta buɗe idanunta tare da turo baki ga kanta da yayi mata nawi, ta dago za tayi masifa saboda katse mata bacci da take yi sai taga Ammie ce mahaifiyar ta, ta tashi ta zauna tare da sake ware idanun tana bin ɗakin da kallo taga ashe ita kaɗai aka bari a ɗakin, zuwan Ammie ne ma yasa ta tashe ta..

"Tashe za ki yi ba wai zama ba, baccin ya isa haka"

"Ammie ban ma san nayi bacci me nawi haka ba"

"Ina za ki sani tun ɗazu na turo a tashe ki amma sai ace kina bacci"

Ta mik'e tare da yin miƙa ta ce

"To Ammie zan watsa ruwa sai na gabatar da sallah"

"Da ya fi miki kam, sai ki hanzarta wankan ki samu ki gabatar da sallah don lokaci na ta tafiya"

"To Ammie"

Ammie ta fice, Ashfat ta rage kayan jikinta ta faɗa toilet ta watsa ruwa sannan ta ɗauro alwala ta fito ta shirya cikin doguwar riga ta lace ta feshe jikinta da turare sannan ta gabatar da sallah, bayan ta idar ne ta shirya ta fito kai tsaye kitchen ta nufa tasan a wannan lokacin ƴan'uwanta suna kitchen suna aiki.

Ta shigo ta tadda su sun baza ko ina sai faman girke-girken abincin dare suke yi, ta iso tare da cewa 

"Yanzu a rasa wacce zata tashe ni, kun san lokaci ya tafi sosai shine ba za ku tashe ni ba, har sai da Ammie ta tashe ni"

Suka ɗago dukkanin su suna kallonta, ta sauke numfashi ta zauna tana haɗe fuska, murmushi Aunty Jamila tayi tare da cewa

"Gaskiya ba ku kyauta mata ba"

"Aunty Jamila ai zan rama"

"Sis Ashfat ni kam gani nayi kin kwanta cikin wani yanayi shiyasa ban tashe ki ba"

Cewar Suhaima, Hauwa ta ce 

"To tun da dai kin tashi ai shikenan, komai ya wuce"

"Bai wuce ba har sai kun karɓi laifin ku"

"Tabɗi ni dai ban yi wani laifi ba, shikenan kina bacci sai mu katse miki bacci"

"Ke Hauwa bana son shashanci kuma wallahi sai na rama ke ma kin sani ba a yi min na kyale"

"Ki yi hakuri Aunty Ashfat in sha Allahu ba za mu sake yi ba"

Cewar Teemah, Ashfat ta sauke numfashi tare da cewa 

"Ke ai ba ki da matsala an yafe miki, da sauran nake"

Ba su ce komai ba, ta mik'e ta zuba abinci a plate wanda ta gani cikin food flask rice and Stew shi already sun kammala sun ajiye a gefe sun maida hankali ga dafa tuken semo da miyar yauƙi...

Ta zauna sai da ta kammala ci sannan ta mik'e tare da cewa 

"Aikin ma ya kammala ba sai na tayaku ba, kun ga tafiyata"

"Ya Ashfat aiki fa har yanzu da saura kinga akwai ƙulla semo fah"

Cewar Teemah, tayi murmushi tare da cewa 

"I'm patient"

Ta fice tana ji suna ta mita, ta wuce side na Mamie, ta turo ƙofa tare da sallama, Mamie ta amsa a lokacin tana ƙoƙarin fitowa daga toilet dake ɗakin. Ashfat ta zauna kan carpet cikin girmamawa ta ce

"Barka da yammaci Mamie?"

"Yawwa barka dai A'isha"

Ta faɗa tana me isowa wajen wardrobe, ruwa ta watsa don taji dama dama saboda ji take jikinta wani iri haka, ta ɗauko doguwar riga mara nauyi ta zura ta iso ta zauna bakin gado tare da cewa 

"A'isha da fatan lafiy"

"Lafiya kalau Mamie, yau tun safe ban ji motsin ki ba"

"Ai yau wuni nayi a kwance, fitar ma wuyanta nake gani"

"Aike Mamie, ba ki son fita kin fi son ɗaki"

"To muna da ku ina zan fita? Me zan yi? Ai gara dai nayi kwanciya ta"...

Turo ƙofar da Hauwa tayi ne yasa ta ɗago ta katse maganar da take son yi....

"Sis Ashfat ashe dai nan kika zo?"

Murmushi tayi tana sudda kai ƙasa ta ce

"Eh Hauwa, ba dai kun gama aikin ba?"

"Na kawo wa Mamie fruits ne zan koma mu ƙarashe"

"To yayi kyau, ni ma ba shigo na gaida ta ne"

Ta mik'e tana shirin fitowa Hauwa ta ce

"To an gode surka"

Ta juyo ta harareta irin na wasan nan sannan ta fice, dariya Hauwa tayi...

"Surka kuma?"

Cewar Mamie, Hauwa ta ajiye plate dake ɗauke da yankakkun fruits ta ce

"Eh Mamie surkar ki ce"

"To ki ce ita ce zaɓin Wahaab"

"Yaya da ra'ayi"

"Aiko in dai haka ne nayi farin ciki"

"Ɗazu ma ta gama hawaye"

"Subhanahu! Hawaye kuma?"

"Eh tayiwa Ya Wahaab breakfast bai ci ba haka ma lunch"

"Gaskiya bai kyauta ba, aiko kaɗan ne sai ya taɓa"

"Mamie zan koma na ƙarashe aikin"

"To in kun gama aikin sai ki ɗaura min green tea"

"To yanzu kuwa"

Saurin barin bakin ƙofar tayi saboda jin motsin fitowar Hauwa, ta ɓuya a bayan Corido ta sauke numfashi, da farko ta karaya akan soyayyar ta, amma tun da Mamie na farin ciki da hakan sai in da ƙarfinta ya ƙare. Ganin Hauwa ta shige kitchen yasa ta fito daga maɓuyarta ta wuce ɗakin Ammie tana shiga ta taddata zaune suna hira Aunty Nazeefa ta gaida ta sannan ta kwantar da kanta a kafadar Ammie...

"Ke ba ki san kin girma bane?"

Cewar Aunty Nazeefa, ta turo baki tare da cewa 

"Kai Aunty Nazeefa kawai don na kwanta a jikin Mamata ya zama laifi"

"Ya ma zama tashi ki barta ta sarara"

"Uhm"

Ta faɗa ta mik'e ta fice zuwa ɗakinsu, tasan gulma ce ta kawo Aunty Nazeefa ko me kuma ya faru a ɗayan side ɗin......





Comments and share fisabilillah