RIGAR ARO

13

by @pherty001

*RIGAR ARO*




©️Fertymerh Xarah💞




13



Suna fita daga school direct gida suka nufa da ita, suna ajiye ta kuma suka fice kamar wancan karon da suka shigo aka taru ana kallon su haka ma wannan karon, Nurayyah ta girgiza kanta tana tsaki kafin ta shiga gida cike da takaici yanda ta taso cikin getto area da sam basu san wayewa ba, motoci ne duk aka taru ake kallo haka sai kace jirgi ne ya shigo unguwar.

Da yamma ma da faruq ya kira ta zai zo haka tace ya jira ta ba sai ya shigo layin su ba kada tsegumi yayi yawa, sanda yazo ta fita daga unguwar taje ta same shi inda yayi parking, ta bude motar ta shiga, sun jima gurin suna hira and laughing kamar wasu masoyan  gaske dake kaunar juna, cos faruq ya dauka da gaske Nurayyah son sa take yi, sai wani kallo yake jifanta dashi a jikinta yana mata kallon sha'awa yace, "You looked incredibly gorgeous yesterday at AFIT Nurayyah, kowa sai magana yake yi akan ki you completely dominated the environment", murmushi Tayi ta lumshe idanu ta kafin ta bude tace "what do you expect from a high-class lady like me? kai dai nagode sosai da securities da komai ma cos everything went yanda ya dace ni kaina na sani". Ya matso kaɗan cikin dabara ya saqala hannunsa cikin nata yace "Kome kike so zan miki Nurayyah indai zaki kasance tare da ni saboda I am deeply falling for you", Nurayyah tayi murmushi kawai batare da tayi magana ba cos ta san deep down in her heart ba ta jin sonsa ko kadan babu ko digon kauna a tare da shi a cikin zuciyarta, tana nuna masa alamar so ne dan kawai to protect her dark secret, she was just carefully manipulating his emotions to sustain her high-profile status ba don tana kaunar sa ba.

Bayan tafiyar faruq, salla magrib kawai tayi ta nufi gidan su fadila, a lokacin tana kwance tana waya da wanda zata aura cos auren ya kusa sai ga Nurayyah ta shigo, kallo daya Nurayyah tayi mata ta dauke kanta fadila na kallonta sanda ta nufi closet din ta tana fito da kaya, fadila ta cika da mamaki har bata understanding me ma wanda take wayar yake cewa, ta katse kiran tana faɗin "2 minutes pls ina zuwa" bata jira amsar sa ba ta tsinke wayar ta jefar akan bed ta tashi tana kallon Nurayyah tace "Lafiya kika ciro min kaya haka ba ko tambaya Nurayyah?"

Nurayyah ta dube ta kafin tace "wanda kika ga na ciro su nake so, wadanda kika bani sun kwana biyu ina so na canza already an gama sanina da su bazan zauna ina ta maimaita kaya ba bayan kin san matsayina a idon mutane yanxu". Cikin mamaki da takaici fadila ta matsa tana duba kayan tace, "Idan kika kwashe duk wannan kayan ni me kike so na saka and duka duka wannan ban jima da ɗinka su ba wasu ma ban taba sanya su ba, and wanda na baki last time babu abinda ya same su Nurayyah?

Nurayyah  ta juyo tana kallon Fadila da wani irin kallo dake cike da overwhelming desperation and greed ta ce, "you mean dan kin ɗinka sabon kaya ba zaki iya bani aciki ba? And laifine dan nazo na ɗauki wani abu naki duk yanda kike son sa? Ni bama wannan ba raina bazai baci ba ko wulakanci kika min cos nasan dan ina yin abinda bakya so ne, da bana wannan rayuwar da bakya so ko closet din gaba daya na dauka ba zaki ce dan me ba, ni yanzu bayan kayan nan ma Naira Million daya nake so ki aro min I swear zan biya ko yaya Sameer ne ki masa magana pls ina jin nauyin sa idan kuma kina da ki aramin zan biya ki kinji na rantse? A yanzu Nurayyah ta daina bata mamaki illah haushi da takaicin ta da take ji a yanxu, she was completely structuralized by the shock of the amount da take demanding yanxu, abin har ya kai haka ta zuba mata ido cikin takaici kafin ta girgiza kai ta ce, "1 Million? Me zaki yi da su? Kai tsaye Nurayyah tace "sabbin kaya zan ɗinka kamar yanda kika ɗinka wannan, ina buqatar shoes and bags, veils, ƴan kunne da sarqa da sauran abubuwan da bazata rasa ba, gwara ina yi ina canzawa na gayamiki irin kallon da mutane suke min yanzu wanda already kin sani kuma kina jin lbr ko a school ". Fadila cikin bacin rai tace "ni kaina ina maimaicin sutura bare ke, wai me kika dauki kanki Nurayyah, menene amfanin abinda kike, bakya tsoron ranar da zata baci maki? Wannan karon Nurayyah ta harɗe hannuwa a qirjinta tana kallon fadila cikin bacin rai tace "Ke ai Fadila ce ni kuma Mrs Binnani ai kinsu  banbanci a tsakaninmu dole zaki yi maimaicin kaya, how can a governor's wife repeat clothes? Kina maida ni baya fadila, ki aramin kuɗin idan zaki aramin".

Fadila tayi tsaki ta juya ta zauna akan sofa cike da bacin rai, Nurayyah ta juya tana kallonta ganin taqi mata magana ya saka ta tattara kayan da ta dauka ta dube ta, ta fice tana qunquni dole ta sami kudi ta ɗinka nata ta huta da gori fadila da alama fadila ta soma gajiya da ita shiyasa take mata wulaqanci a yanxu, banda ma fadila bata ganewa ba alfarma take mata ba ko ta manta matsayin ta gudan matar governor ta saka kayan sakawarta ai abin alfahari ne a gurin ta, zata zo ma ta daina saka kayan kafin mutane su ankara da sharing suke da fadila, su fara gane duk kayan da fadila ta sanya zaa ganta dasu.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Nurayyah tayi nisa da bata jin kira kullum da irin abinda take yi, mutanen unguwa sun soma surutu akan ta yarinyar da aka sani da nutsuwa yanxu duk babu a wurin Nurayyah idanun ta sun bude sosai a yanxu, sai dai kuma as the saying goes that every fake life has an expiration date, tana cikin rayuwar qaryar nan sai ga mahaifin faruq ya dawo qasar wanda hakan ya saka manyan motoci da securities guards suka koma bakin aikin su.

Dalilin haka sai ta daina zuwa school tun da ba motoci ba securities dama ba karatun ke kai ta ba nuna kanta da matsayinta, kuma duk wannan abin da take Jaddi bata da labari duk qananan maganganun da ake kai mata akan Nurayyah sai ta dauki fada da nuna zaa takura rayuwar jikarta dan an ga ta sami sauyin rayuwa yanzu ta shiga makaranta tana karatun ta ake so ayi mata baqin ciki.

Akwai sanda tana son zuwa school ɗin da ta kira faruq yace"Nurayyah ki yi hakuri daddy yana gari kuma yana amfani da motocin, bazan iya dauka na fito dasu batare da ya sani ba cos he tracks every single movement of the fleet, kuma da zarar ya lura babu daya daga cikin motocin a gida to wata fitina ce zata tashi wacce nima ba zan iya tunkararta ba tun da bai san ina fita da motocin ba sai saka min doka akan su, gwara ki haqura har ya tafi ai bazai jima ba zai koma", Nurayyah cikin jin zafi ta tsinke wayar batare da tace komai ba, haka ta share kusan sati bata leqa school ba, fadila tana sane amma bata taba tambayar ta dalili ba.

Ganin ta jima tana son fita school babu dama sai ta soma tunanin hanyar da zata sami mota taje ko guda ce ai ba a'a yi tunanin wani abu dan kawai an ganta da mota daya ba, zaa dauka may be yau bata raayi securities ne, kuma bazai yiwu taje tare da fadila ba a matsayin ta ai sai dai kawai a ganta ta tuqa fadila yanda zaa dauka itace ta rage mata hanya, ko dai zata je ta roqi fadila ta ara mata ɗaya daga cikin motocin gidan su ne, tunanin ta ya tsaya lokacin da take tunanin may be fadila zata iya ara mata tun da tana son ta, da sauri ta tashi ta shirya ta fita ko Jaddi bata gayawa ba, napep ta shiga zuwa unguwar su fadila, da taje wa fadila da zancen sosai fadila ta nuna mata tsoro akan umma bazata taba yarda da hakan ba ko daddy ma dan haka ta hakura, gaba daya a wannan lokacin Nurayyah ta karaya ji take kamar ta fasa ihu tayi kuka ko zata ji sassaucin da zafin da zuciyar ta ke mata haka dabara ta fado mata tace "to kira min yaya Sameer zan yi magana dashi ya aramin motar sa" fadila bata yi qasa a gwiwa ba ta miqa mata wayar ta alamar ta kira da kanta, Nurayyah ta karbi wayar tana dialling number shi kafin ta sami wuri ta zauna, babu jimawa ya daga kiran, sai da suka gaisa tana son masa magana kuma sai take jin nauyi, "ya dai kin yi shiru kuma kamar da magana a bakin ki? tace, "Yaya Sameer, dama wata alfarma nake nema a gurin ka idan babu damuwa, motarka nake so ka aramin na riqa zuwa makaranta da ita please?", Sameer yayi shiru na wasu mintuna yana nazarin zancen kafin yace, "kin iya mota ne Nurayyah? ", Nurayyah da sauri tace, "A'a  Yaya Sameer ban iya ba", Sameer ya sake cewa, "To ya zaki yi da ita idan na ara miki tunda baki iya tukawa ba kuma babu wanda zai riqa tuka miki ita a gida?", Nurayyah da sauri tace, "Zan sami driver da zai riqa driving dina zuwa school  cos sau da yawa ni da Fadila ba lokaci daya muke da lectures ba kuma idan ina da tawa motar abubuwa zasu fi tafiyar min daidai bazan takura ta ba and fadila ma tace zata koya min da kanta har na iya."

Sameer ya dinga mata tambayoyi tana amsawa da yake akwai dabara da wayo duk inda ya bullo mata zata bulla mashi nan daga qarshe yayi giving up yace "shikenan fadila ta karɓo miki key din hannu Umma, and ki bi a hankali kuma ki kula sannan duk dare ki maida motar ta kwana a gida saboda daddy tun da a gidan ku babu wurin ajiye ta," Nurayyah ta amsa da sauri tana masa godiya cike da farinciki, nan suka cigaba da soyayyar su kamar da gaske fadila na cin abinci tana kallon Nurayyah tana mamakin yanda Nurayyah take samun sa'ar duk abinda ta nema take samu cikin sauqi and ji yanda take magana da yaya cikin taushin murya kamar da gaske sonsa take, ta sauya rayuwarta gaba daya she was completely transformed into a different person, wallahi har da na sanin nema mata admission take cos gani take tana da alhakin tarwatsa rayuwar Nurayyah da bata matsa mata akan ta koma school ta cire damuwa ba da yanzu tana can gida tare da Jaddi cikin kwanciyar hankali, ga shi ko mgnr aure bata so ayi mata, ta rasa gane kan Nurayyah ko akan wannan ko sau daya bata taba ce mata tana son wani namiji ko wani ya burge ta ba, sanda suka gama wayar Nurayyah ta saka taje ta karɓo mata key ta kawo mata, bayan ta karbi key babu bata lokaci ta tashi ta tafi, tana isa gida ta kira faruq ta sanar da shi ta sami mota saura driver yayi mamaki sosai ya tambaye ta ina ta samu, ta gayamishi yayan fadila ne ya ara mata.

Washe gari sai ga faruq da sabon driver ko da ta dube shi ta yatsina fuska cos ita ba irin wannan take so ba, ta fison masu sanya suit da glass wanda zaka gansu fuskarsu ba alamar wasa a ganin ta su suke yin aiki da gaske, ganin yanayin ta ya saka faruq gane Lawal bai mata ba yace "Just manage with him for now kafin a sami irin wanda kike so."

Nurayyah tayi shiru bata ce komai ba amma ba haka taso ba, taje ta shirya ta fito suka je da motar faruq har gidan su fadila aka ɗauko motar Sameer kafin Lawal ya tuqa ta tana zaune a gidan baya suka nufi school, faruq na gaban su cikin tashi motar.