GADAR TSAUTSAYI 30
by @nusybee143
Page 30
💫
A Murtala Muhammad airport da ke Lagos jirginsu Shaheeda ya sauka, tunda jirgin ya sauka gaban Shaheeda yake dukan uku-uku, tsananin firgici da tashin hankali ya bayyana akan fuskarta
Ta san su wanene iyayenta, musamman mahaifinta,ta san yadda yake da zafi,kuma ba ya É—aukar wargi,tana tsananin fargabar abin da zata je ta tarar
Hotel É—in da suka kama lokacin da za su tafi Spain ita ta sake komawa,ta kama É—aki don ta huta, gobe ta bi jirgi zuwa Kano
A wannan daren ko sau ɗaya bacci bai kawo mata farmaki ba,banda tashin hankali da fargaba, sai tunane-tunane da suka cunkushe mata ƙwaƙwalwa,a ranta tana addu'ar Allah ya ɗora ta akan Abba, Allah ya sa hukuncin da zai yi mata ya zamo da sauki
A ranar dare ya yiwa Shaheeda tsawo,duniyar ta yi mata ƙunci, fargaba ta mamaye mata zuciya, tunani da taraddadi suka cunkushe mata ƙwaƙwalwa,ji take yi a duniya ta fi kowa shiga mawuyacin hali,kuma ta fi kowa shiga tashin hankali
Washe gari ma ko ruwa ta kasa kai wa bakinta,jiki babu ƙwari ta yi booking jirgin da zai nufi Kano,kuma ba tare da ɓata lokaci ba suka hau zuwa kano
Ta kai a ƙalla awa ɗaya tana nazarin yadda zata tafi gida, kafin daga baya ta yi shahada kawai ta tafi, bayan ta sauka ma taxi ta hau zuwa Maliya estate,tana tafiya a taxi ɗin banda matsanancin tunani babu abin da take yi,sai share hawaye
A bakin maliya estate ta sauka daga taxi É—in,ta sallame shi sannan ta ja akwatinta,amma ta kasa motsawa ko nan da can
Kamar daga sama ta ji Muyassar yana faÉ—in "Shaheeda!
Shaheeda daga ina haka?"
A firgice ta ɗaga kai tana kallon Muyassar da yake ƙare mata kallo,jikinta babu inda ba ya rawa,amma duk da halin da take ciki babu abin da ta ji kunya da muzanta irin ganin ta da ya yi da tsohon ciki, musamman da ta kula idanunsa suna kan cikin nata yana kallonta da wani irin yanayi
Da ƙyar ta lalubo nutsuwa,muryarta na rawa,kanta a ƙasa ta ce"ina kwana yaya Muyassar"
Maimakon ya amsa sai ya ce"tsayuwar me kike yi anan?
Wuce ki shiga ciki mana"shiru ta yi bata tanka ba,ya sake faÉ—in "wuce mu je na kai ki,kin zo kina tsayuwa a nan"ya wuce gaba,ta bi bayanshi jikinta a sanyaye,suka nufi cikin gidan
Shaheeda ta sake muzanta ganin duk ta inda suka wuce sai an kalle su kafin su isa sashen Ummeey,suna zuwa ta ja ta tsaya tana lafewa a jikin bango, Muyassar ya kalle ta yana faÉ—in "ya dai?
Ki wuce mu shiga ciki mana"
Hawaye suka zubo mata,ta ce "ka bar ni a nan kawai,ina tsoron Ummeey"
Yar dariyar takaici ya yi,ya ce"Shaheeda kenan!
Wasu abubuwan kafin mu aikata su za muyi tunanin yadda makomarmu zata zama ba sai mun aikata ba, yanzu misali, menene amfanin wannan abu da kike yi yanzu?
Ummeey mahaifiyarki ce,ke kaÉ—ai ta mallaka wadda zata kalla ta ji sanyi na cewa eh tana da zuri'a a duniya,amma ba ki tuna hakan ba kika yi abin da zata yi kuka, why Shaheeda?"
Ita dai Shaheeda bata tanka ba, sai kukanta da ya fara tsananta, Muyassar ya kwantar da murya ya ce"alright,komai ya wuce, na san ba za ki sake irin wannan aikin ba, Allah ya kyauta ya kiyaye gaba,tashi mu wuce ciki"babu musu ta miƙe, jikinta duk babu ƙwari suka nufi cikin sashen Ummeey
Ummeey tana zaune a parlour tana shan tea a hankali sai ta ji sallama,a gigice ta ɗago tana kallon Shaheeda wadda gaba ɗaya ta fita hayyacinta, Shaheeda ta kasa jurewa ta taho da gudu ta faɗo jikinta tana kuka mai gunji, Ummeey bata yi wani yunƙuri ba sai kukan da ta fashe da shi ita ma, tana bin tilon ƴar tata da kallo, wadda gaba ɗaya ta fice a hayyacinta tamkar ba dirarriyar ƴarta Shaheeda ba,mai kazar kazar da yawan surutu
Yanzu duk ta yi sanyi ta canja,ta rame sosai,mafi girman tashin hankalin da ta gani a tare da ita shine tsohon cikin da yake jikinta
"Ummeey don Allah ki yafe min!na yi kuskure!na bijirewa maganarki,a ƙarshe ban samu sakamako mai kyau ba,don Allah Ummeey ki yafe min,don Allah Ummeeyna"kunnuwanta suka ɗauko mata sautin Shaheeda cikin gunjin kuka
Da ƙyar Ummeey ta iya ɗaga harshenta ba tare da ta kalli Shaheeda ba,ta fara magana cikin karayar zuciya
"Shaheeda! Allah ne shaida,a tsawon lokaci tun da na haife ki ƙoƙarina shine na ba ki tarbiyya,bani da kowa a kusa da ni daga ke sai mahaifinki,ke ce kaɗai ƙwan da Allah ya ba ni, wanda nake saka ran samun walwala daga gare ta,amma a ƙarshe a dalilinki na yi nadamar haihuwa,wasu mutanen suna kuka saboda ba su haihu ba,wasu mutanen suna alfahari da ɗaya ko da yawa da Allah ya ba su,amma ga ni ina kuka saboda na haihu,ina nadama saboda ɗaya da Allah ya ba ni, meyasa Shaheeda?me nayi miki da zafi haka?"
Kukan Shaheeda ya tsananta, cikin kuka ta sake rungume Ummeey tana faɗin"don girman Allah Ummeey ki yi min rai, Ummeey ki yafe min, wallahi na yi nadama, ba zan sake ba,don Allah Ummeey kar ki juya min baya, wallahi ina sonki Ummeey,ke ce....."a fusace Ummeey ta hamɓare ta daga jikinta tana aika mata da wani mugun kallo,hawaye bai tsaya a idanunta ba ta ce"kina so na Shaheeda?a hakan? ƙarya kike yi!!!
Da kina so na da ba ki so raina ya ɓaci ba ko yaya ne
Shaheeda da kina so na da ba ki guje ni ba,da ba ki jefa ni a cikin baƙin ciki da tashin hankali ba!
Shaheeda kin san a halin da na samu kaina da na rasa ki a kusa da ni kuwa
Meyasa? meyasa za ki yi min haka?me na yi miki?"ita dai Shaheeda wannan karon babu baki,sai kukan da ita ma take yi cikin tsananin tashin hankali, fargaba da damuwa
Sun kwashi mintuna a haka, kafin Ummeey ta dubi Shaheeda fuska babu rahama ta ce"sai abu na gaba! wanene ya yi miki cikin jikinki?"
Muryarta a shaƙe saboda kuka ta ce"Arnold ne"
Shiru Ummeey ta yi gabanta yana faÉ—uwa,ta ce"wanene Arnold?"daidai nan Muyassar ya dawo parlourn da sallama, fuskarsa babu walwala
Kanta a ƙasa,tana jin wata muzanta da nadama, muryarta tana rawa ta ce"wanda na aura "
"Kika aura?"a cewar Muyassar yana kallonta da wani irin yanayi,"yaushe kuka yi auren?kuma wanene ya É—aura miki auren?"
Kanta a ƙasa ta goge hawayenta ta ce "kafin na tafi, wajen malami muka je aka ɗaura mana auren"
Shiru Muyassar ya yi yana bin ta da kallo cikin tsananin mamaki da takaici,ya ce"wanne malami ne haka da kuka je ya É—aura muku aure ba tare da ya yi tunanin abin da zai je ya zo ba"
Tana shashsheƙar kuka ta ce"ku yafe ni don Allah, Ummeey don Allah ki yafe min"
A fusace Ummeey ta kalle ta ta ce "tambayarki ake yi amma kin zauna kina shirme!kin san tsaf zan lakaɗa miki duka a gidan nan?ba ki san a ƙule nake da ke ba ko?"
Jikinta yana rawa ta fara ba su labarin abin da ya faru tana kuka,suka zuba mata idanu suka kallonta cikin tsananin mamaki,har ta kammala labarin,tun daga lokacin da suka yi aure da Arnold har zuwa lokacin da Diego ya saka ta a jirgi ta dawo Nigeria,da ƙyar ta kai ƙarshe kafin ta sake rushewa da kuka mai tsanani tana faɗin"don Allah Ummeey ki yafe min, zuciyata ciwo take yi min,don Allah Ummeey,zan mutu ki taimaka ki yafe min, Ummeey ki yi min addu'a don Allah,don Allah Ummeeyna"ta faɗa da ƙarfi cikin muryarta da bata fita sosai tana rungume Ummeey da ƙarfin tsiya, wadda itama zuwa yanzu kukan take yi sosai
Muyassar ne ya kama hannunta ya janye ta daga jikin Ummeey, wadda har yanzu bata yi wani yunƙuri ba, banda kukan da take yi kamar ranta zai fita,ya zaunar da ita yana faɗin "kukan ya isa haka Please,ki daina wannan kukan, abin da ya faru ya riga ya faru, Allah ya kyauta ya ba ki ikon cinye wannan jarrabawar,amma ke ma ya kamata ki daina taurin kai da gardama, Allah ya raba ku da abin da ke cikinki lafiya ya albarkaci rayuwarsa,ki kwantar da hankalinki kin ji?
In sha Allah komai zai daidaita,ki daina kuka"ya ƙarashe maganar yana goge mata hawaye
Cikin kuka ta ce"yaya ina tsoron abbana, Ummeey har yanzu tana cikin fushi da ni, tsoro nake ji yaya"
Muyassar ya ce"kin san dai ke favourite É—in abba ce ko?
To ki kwantar da hankalinki, in sha Allah ba zai ɓata miki rai ba, Ummeey kuma ki ba ta lokaci zata huce
Ya kamata zuwa yanzu a ce kin kwantar da hankalinki,kin fawwalawa Allah komai kin ji yar ƙanwata?idan ba haka ba kuma ba zan sake shigowa wannan sashen ba,idan ma na shigo to wajen Ummeey kawai na zo,ba wajenki ba"Shaheeda ta yi saurin goge hawayenta tana faɗin"na daina kukan yaya,na daina,amma don Allah ka cewa ummeey ta yafe min"Muyassar ya ce"ki kwantar da hankalinki,in sha Allah ta yafe miki ma,me za ki ci yanzu?"
Shaheeda ta girgiza kai ta ce"na ƙoshi yaya"
Muyassar ta É—aure fuska ya ce "okay ba ki huce ba kenan?"
Da sauri ta girgiza kai ta ce "a'a yaya,ka kawo min avocado,ina so zan ci"Muyassar ya yi murmushi yana lakace mata hanci yana faɗin "that's my little ƙanwa!
Sai na dawo,ki kula kin ji"ya miƙe ya fice daga sashen yana ɗaga mata hannu
Bayan fitar Muyassar aka fara zaman kurame tsakanin Ummeey da Shaheeda,sun kai aƙalla mintina goma kafin Shaheeda ta dubi Ummeey ta yi ta maza, cikin raunin murya ta ce"don Allah Ummeeyna ki yafe min
Kin ji Ummeey?ko zagina ne ki yi, Ummeey ki dake ni ko za ki huce,amma don Allah ki yafe min,ki yafe min don Allah,kin ga halin da ma shiga a sanadin fushin da kika yi da ni,don Allah ki yafe min na samu sassauci kin ji Ummeeyna?"
Duk da yadda zuciyar Ummeey take zafi,amma abinka da ɗa da uwa,sai ta ji zuciyarta ta karye, tausayin Shaheeda ya rufe ta,ta dube ta, cikin sanyin murya ta ce"Allah ya ƙara ganar da ke, Allah ya raba ku lafiya , Allah ya ba ki lafiya, tashi ki je ki yi wanka ki sauya kaya,me za ki ci?"
Murmushi ya ƙwacewa Shaheeda,ta rungume Ummeey tana faɗin "na gode Ummeeyna, Ummeey ko menene kika dafa zan ci, Allah ya saka miki da alkhairi Ummeeyna"daga haka ta miƙe ta shige zuwa ɗakinta tana farin ciki
Jikinta ya yi sanyi sosai lokacin da ta ga wasiƙar da ta rubutawa Ummeey a inda ta bar ta, Allah sarki Ummeey! yanzu haka don kar damuwa ta dame ta ne ta kasa shigowa ɗakin, Allah sarki Ummeey!ta goge hawayenta ta shiga wanka
A parlour kuwa Ummeey tana zaune sai ga Hajiya Atika kamar an hankaɗo ta, kallonta Ummeey ta yi gabanta yana faɗuwa,amma ta dake ta ƙaƙaro murmushi ta ce"a'a!
Maman Malika!ya yaran?"
"Yara alhamdulilla!sune suke gaya min wai Shaheeda ta dawo, menene gaskiyar maganar?"
Jikin Ummeey a sanyaye ta jinjina kai,ta ce"eh Shaheeda ta dawo,tana ciki ma, yanzu ta shiga"
Hajiya Atika ta jinjina kai ta ce "to kenan gaskiya yaran suka faÉ—a da suka ce ta dawo da tsohon ciki kenan?"
Ummeey ta kalle ta jiki a saɓule kafin ta yi ƙasa da kai, Hajiya Atika ta ce "tambaya nake yi Hajiya,da gaske ne?"
Ummeey ta ce"da gaske ne,ta dawo da ciki"Hajiya Atika ta rafka salati tana rike haɓa ta ce"oh Allah ka dube mu!
Wai cikin shege a gidan Alhaji Yusuf Maliya duk da tarin tsaro da tarbiyyar gidan?
To Allah ya sawwaƙe,da kika ce mata ta dawo yau ai alhajin nan da abin da bai wuce sati guda ba ma zai dawo,shi da kanshi ai zai yi abin da ya dace,don dai mu ma muna da ƴaƴa mata, gaskiyar magana kenan"ta juya fuuu ta fice daga parlourn
Ummeey ta bi ta da kallo kawai ba tare da ta iya ce mata komai ba,ta sani hakan zata faru, fiye da haka ma zata iya faruwa, gashi Hajiya bata nan ballantana ta tura ta gidanta,amma zata yi magana da Hajiya Jamila,zata je gidanta ta zauna,don ba zata iya wannan tashin hankalin ba,ba za'a yi haka da ita ba
Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci maganar dawowar Shaheeda ta bazu a maliya estate,da yawa sai zuwa ake yi a ganta, musamman idan an faɗi da tsohon ciki ta dawo,babu wanda yake da tunanin ya tambaye ta daga ina ta samo cikin, banda wanda Muyassar ya yi mata,shi kuwa Muyassar ya ce mata kar ta damu da kowa, Allah ma ya sani ba zina ta yi ba,ba ɗan shege bane a jikinta don haka kar ta wani damu,idan ta haihu ma shine zai zama baban yaron
Hakan ya sa ta yi kuka sosai,ta yi nadama,amma ta san auren Muyassar ya fi ƙarfinta,don ta ji an ce watanni uku ne suka rage a yi aurensu da Arfa, wadda tun da Shaheeda ta zo bata ganta ba,alamun tana gidan iyayenta
Kwanan Shaheeda biyu da dawowa,da daddare suna zaune a parlour, Shaheeda tana cin avocado da yanzu ita ce abincinta,yau ma through out ta kasa cin komai saboda jikinta da ya motsa sai da Ummeey ta kai ta asibiti,ba su juma da dawowa ba ma
Wayar Ummeey ce ta yi ƙara,sai da gabanta ya faɗi ganin wanda yake kira, Abba ne
#Nusy_bee