HAULA HABEEB

BABI NA SHIDA

by @amdeeytejjdunique587

💎🌹 Haula Habeeb🌹💎

Story Written By

Amdeey Tejj d'Unique ✍️







BABI NA SHIDA






Ta miƙe tsaye a tsorace, kai a ƙasa. Tunowa da abin da ya faru ranar ya sa cikinta ya ƙara ɗurar ruwa, don dama ta san shirun da ya yi, bai ce mata komai ba, ba yana nufin ya bar ta ba ne. Yo, wannan mugun ne fa.

A ranar, a lokacin da ta shiga ɓangaren, ta yi niyyar har ta gama lissafin ɗakin ne ta fito kawai abinta. Tunda shi ya ce ɗan ganin arahar gabas ce. In ba haka ba, duk yawan ma’aikatan da suke cikin gidan nan, wasu ma da alama biyansu kawai ake yi ba don akwai aikin da suke yi ba, amma sai Gwaggo ce za ta yi masa gyaran ɓangarensa bayan na kitchen, saboda shi mugu ne. Ai ko, zai ga abin da za ta yi masa.

Amma a lokacin da ta shiga ɓangaren, sai lissafinta ya canza. Ta ɓige da kallon kyau da ƙawatuwar sashen, don tunda take ba ta taɓa ganin wani wuri a gida mai kyau da ƙawatuwarsa ba. A duk faɗin gidan, ba sashen da ta gani wanda ya kai shi kyau, duk da ba ko ina ta taɓa shiga ba. Shi ma ɗin ba ta taɓa shigowa wannan side ɗin ba sai yau, wancan na cikin gida take shiga. Haka ta yi ta kalle-kalle har ta kai bedroom ɗinsa. Nan ma ta baza ƙauyancinta har ta shige bathroom. Ai ko nan ta ƙara baza ƙauyanci, don ita ba don su shower da jacuzzi ɗin da ta gani ba, da ta ce wani sashen ne aka kawo ta.

Riƙe baki ta yi a fili ta furta, “Kai! Wannan mutumi da son kai yake. Ashe a nan filin gidan ya ƙare? Wannan duka wai a ce ban ɗaki ne, kuma shi kaɗai. Kaf gidan nan akwai ban ɗakin da ya kai wannan kuwa!” Ta faɗi cike da mamaki tana riƙe haɓa. Sai kuma ta taɓe baki tana sake baje hanci tana shaƙar ƙamshin da ke tashi a cikin ban ɗakin mai sanyi.

Nan ma taɓe-taɓen ta yi har ta kai closet. Ta tura ƙofar ta shiga. Tsayawa ta yi ta riƙe baki, a fili ta sake furta, “Oh ni Haule! Wannan mutum, abin mamakinsa na da yawa. Shi kuma har da kantin sai da kaya yake da shi a nashi ban ɗakin? To wa ya ba shi shawara ya buɗe kanti a bayi?” Sai kuma ta fashe da dariya.

Kafin ta ce, “Yo, in banda shiriritar irin tasa, wa zai zo siyan kaya a bayi? Ko da cewa wannan na ’yan ƙasar waje ne, to ai bayi dai sunansa bayi.” Wata dariyar ce ta sake fashewa da ita.

“Oh ni! Ana ganin Haula mai shirme mara kai, ashe ina da hankali. Don dai duk haukata, ba zan buɗe kanti a ban ɗaki ba. Abin mamaki! To wa zai zo siya?” Wata dariyar ta sake yi, kafin ta soma bin komai ɗaya bayan ɗaya. Ba abin da ya ƙara ba ta mamaki sai yadda kayan wurin duk kusan girmansu ɗaya yake. A ranta take sake tunani, to shi bai san akwai masu ƙaramin jiki da masu uwar ciki ba ne? A tunaninta ma iya kayan maza yake siyarwa tunda ba ta ga na mata ba. Komai ta ɗaga, wani ta mayar da shi wurin zamansa, wani ta yasar. Kwalaben turarukan kaya ta ɗauko ta ce, “Kai, ashe har da su turare ma.” Nan ta hau fesawa, sai da ta fesa kowanne.

“Kai, wannan turare da ƙamshi suke.” Har ta mayar da su mazauninsu, sai kuma ta ɗauko tana faɗin, “Ai ma tunda na sayarwa ne, bari in kai wa Gwaggo ta saya mana. Dama wannan turaren nata mai warin Binta Sudan ɗin ya ishe ni.” Sai kuma ta fashe da dariya, kamar wata zautacciya ta sake cewa, “Oh Haula gidan sharri! Wato turaren Gwaggo ne mai warin Binta Sudan ko? Hmmm, za ki yi bayani idan ta ji ki.” Ta tattaro duka perfumes ɗin, har wanda ma ba a buɗe ba.

Da haka ta fito, sai kuma idonta ya yi mugun gani, a lokacin da ta gan shi a wannan yanayi, iya matuƙar firgita ta yi, don ita ba ta zaci ma shi ne ba da farko. A guje ta koma ciki, jikinta babu inda ba ya tsuma don firgici. Can cikin kaya ta je ta ɓoye.

Shi kuwa a ɓangarensa, da ya juya ya ganta, ci gaba da abin da yake yi ya yi kamar ba abin da ya faru a zahiri. A ɓoye kuma, ƙoƙarin danne zuciyarsa yake yi a kan abin da take raya masa. Bayan ya gama, towel kawai ya ɗaura ya fice. Ruf da ciki ya kwanta ya kulle idanunsa yana ƙoƙarin controlling kansa ya samu calmness. Duk yadda ya kira sunan Allah, hakan ya gagara. Dole tasa ya ci gaba da zama a haka. Ya ɗau lokaci a kwance a nan ba tare da ya san abin yi ba, yana jin lokacin da ta fice daga ɗakin kamar munafuka, a tunaninta barci yake. Shi kuwa ba ƙaramin ƙoƙari ya yi ba wajen ya ga ya tashi ya yi ajalin wannan aljanar yarinyar ba.

“Ba na maimaita magana,” muryarsa ta katse mata tunani.

Shiru ta sake yi, ba ta ce komai ba. Tashi ya yi ya nufi ƙofar, ya murza key ya bar shi a jikin ƙofar. Cikinta ya ba da wani sauti, take fitsari ya cika mararta.

“Kneel down,” ta ji ya furta.

“Wallahi zan faɗa maka dalili, Yallaɓai ka yi haƙuri. Zagi malaman makarantar suke yi, shi ya sa na ce a canza min, ba do gangan na ƙi zuwa ba.” Ta yi maganar idonta na cika da hawaye, murya a karye, lokaci guda tana haɗe hannunta waje guda alamar roƙo.

“Kneel down I said, do not let me repeat my for the third time,” ya faɗi yana ɗora ƙafarsa kan centre table ɗin ɗakin.

Kwarjini ya mata. Duk da ba ta fahimci sauran abin da ya ce ba, amma ai ta san 'kneel down', kuma shi kaɗai ta gane a ciki. Ba ta ma san lokacin da ta kai gwiwarta ƙasa ba.

Magana ya fara cike da ƙasaitacciyar murya irin tasa kamar jinin sarauta, amma cikin sautin da ba nishaɗi ko wasa a ciki, wannan kaɗai ya isa ya sa ka shiga taitayinka. “Wato ke kin gagara ko? Ba kya jin maganar kowa, sai abin da kika ga dama shi za ki yi ko?” Ya ɗan yi shiru na seconds kafin ya ci gaba.

“Abun naki har ya kai kina bin mutane ban ɗaki? Kike bin mutane, ke gaki ’yar...” Fasa abin da ya yi niyyar faɗa ya yi.

“Start pumping,” kawai ya ce, ya fara kai-kawo a cikin ɗakin.

Nan ma “pumping” ɗin kawai ta gane, don shi ma ana sa su yi a makaranta. Kamar jiran cewarsa take yi, ai kuwa ta hau yi.

Iya jigata Haula ta yi. Hawaye da majina suka haɗu suka caɓe mata. Kuka kuwa har ta gode Allah. Roƙo kuwa da akwai kwando a kusa da ta cika ta mayar. Sunan Salim da Gwaggo da ke bakin ƙofa take ta kira. Salim na roƙonsa ya buɗe ƙofar don ita ta ƙi magana saboda nauyinsa da take ji. Da akwai iyakar kiran sunan mutum a duniya, da yau ya ƙare tsabar kiran neman ɗaukin da Haulat take musu. Har Mommy Salim ya kira ko zai buɗe, amma a banza, ya share su kamar bai san Mommy na wajen ba.

“Oya tsallen kwaɗo, ba ki yi laushi ba, tunda har yanzu bakinki bai mutu ba,” ya faɗa a gajiye, don shi kansa hayaniyar Haula ta ishe shi, kansa ma ciwo yake yi.

“Wallahi na yi, kai ne ka ce kada na sake faɗi, ka ga...”

“Shshhhh,” ya faɗi.

Shirun ta yi kamar yadda ya buƙata, har tana kama baki.

“Ba zance, kada ki sake ba. Ki yi kin ji, ni ma ina jiranki. Tashi ki je ki sa uniform.”

Da rarrafe da bin bango ta shige ban ɗaki. A tare suka fito, tana biye da shi a baya. Fuskar nan ta yi ja, ido ya kumbura, tana tafiya tana share hawaye. Ko da ya fito bai bi takan kowa ba ya yi wucewarsa. Ita ma tsoro ya hana ta tsayawa, ta wuce. Gwaggo ta bi ta da kallon tausayi cike da damuwa. Ta kai hannu ta goge ƙwallar da ke shirin zubo mata. Salim ya sha gabansa zai yi magana, kallon da ya yi masa ya sa shi yin shiru.

Kallonta ya yi, sumi-sumi kamar munafuka ta shige gaban mota, shi kuma ya shiga baya. Driver ya ja motar suka fice, suka bar Salim da ƙura, ya bi bayan motar da kallo.

Mommy ma ba ta ce komai ba, ta yi ɓangarenta.

Salim ya kalli Gwaggo, zai yi magana ta dakatar da shi, kafin ta ce, “Me za ka ce Babban Mutum? Kai ne kake biyewa Haula ai. Ita kuma da kake ganinta zuma ce, sai da wuta.”

Bai ce komai ba ya fice. Ita ma ta koma ciki, ranta ya ɓaci da tunanin halin da Haula take ciki.

Haula

Sukuku ta yini a makaranta, ba wani karsashi. Tunda ta zauna a kan nata desk ɗin ba ta tashi ta je ko ina ba, har fitar break aka yi. Ba kuma wanda ta kula. Hakan kuwa ba ƙaramin mamaki ya ba malamansu da sauran ɗalibai ba. Ana tashi ta fito ta ɗau hanyar gida, ko driver ba ta jira ba. Tana tafiya tana jin cinyoyinta kamar ana sara mata su. Ganin ba za ta iya tafiyar ba ne, ta nemi wuri ta zauna ta kama kuka. Kasancewar ba ta yi nisa da makarantar ba ya sa ko da driver ya zo bai ma ƙarasa ba, ya tsaya a inda take ya yi mata horn. Kamar mai koyon tafiya haka ta tashi ta shiga motar suka ɗau hanya.

Suna isowa ɓangarensu ta shige kai tsaye. Ko takan Gwaggo da ke kitchen ba ta bi ba, ta shige ɗaki ta kwanta.

HAZ Group of Company

Habeeb

“Yes, come in,” ya faɗi jin ana knocking ƙofar office ɗin daga waje, ba tare da ya ko kalli inda ƙofar take ba. Kuma har ya shigo bai ɗaga ido ya kalle shi ba.

“Barka da rana Sir,” cewar wanda ya shigo ɗin.

Bai amsa ba, bai kuma nuna alamar ya ji ba.

Bai damu ba, ya fara bayanin abin da ya kawo shi, tunda ba wai yau ya san halin mai gidan nasa ba. “Na je makarantar kamar yadda ka ce idan time ya yi in je in mayar da ita gida, amma na samu har an je an ɗauke ta.”

Kai kawai ya jinjina masa ba tare da ya ɗago ba, shi kuma ya fice.

Sai da ya gama aikin da yake yi, kafin ya ɗago ya jingina bayansa da kujerar da yake zaune a kai. Lumshe ido ya yi yana juyawa a kan kujerar sannu a hankali. Haka kawai Haula ta faɗo masa a rai. Ya tuna da abin da ya faru a bathroom, sai wani sabon haushi da takaici ya kama shi. Wa ma ya san kallon da take masa yanzu? Dama ba ta da kunya, kuma shi ta raina. Watakila ma duk san da ta ganshi sai ta tuna. A hankali ya buɗe idonsa, wani sabon takaici na ƙume shi. Huci ya furzar yana shafa suman kansa da ke gyare tsaf. To, wai ma, ko da gangan ta shigo? Ko ma tana bin maza ne, oho?

Ganin tunaninta da bai ga amfanin da zai yi masa ba, na shirin cike shi ne ya tashi ya fice daga office ɗin gaba ɗaya. Lift ya hau ya sauka last-floor. Kai kawai yake ɗagawa masu gaishe shi har ya fito harabar Company. Da sauri bodyguard ɗinsa suka taso. Hannu ya miƙa musu, already sun san abin da hakan yake nufi. Key ɗaya daga cikinsu ya ba shi, aka buɗe masa ƙofar mota ya shige. Slowly yake tuƙa motar cike da izza har ya fice daga Company ɗin.

Haula

Gwaggo ta shigo ta same ta kwance a kan gado, ko uniform ba ta samu arziƙin cirewa ba.

“Haula! Dama kin dawo?” Shiru ta yi kamar ba da ita take magana ba, ba don tana barci ba.

Ƙarasowa kan gadon Gwaggo ta yi, ta janyo ta. Kuka ta fashe da shi, ta rungume Gwaggo. Nan Gwaggo ta shiga rarrashinta tana mai da na sanin kiran sa da ta yi. Don ita ta kira shi lokacin da ta yi mata magana ta ce ba za ta je makaranta ba. Ta san Salim ba zai takura ta ba, sai dai ya rarrashe ta. Ita kuma idan kana rarrashinta, kamar kana zugata ne. Kuma shi kaɗai ne zai sa ta a gaba har makarantar ba tare da musu ba. Ita sam ba ta zaci zai ta horo haka ba.

“Lallaɓa ki tashi ki je ki cire uniform ɗin nan, ki gasa jikinki da ruwa mai ɗumi za ki ji daɗi.”

Sake langwaɓewa ta yi tana faɗin, “Wayyo Gwaggo, an sassaƙe min cinyoyina. Don Allah Gwaggo ki yi min wanka, ko ta bayana ne ki ɗan gaggasa min.”

Gwaggo ta yi dariya ta ce, “Daɗina da ke Haula raki. Ke, wai har yanzu ba ki san kin girma ba ne?”

“Gwaggo, ba zan iya tafiya ba. Allah, kuwa sai an je wanzamai sun duba ƙafar nan ko ta kwaɓe a mazauninta.” Ta yi maganar a shagwaɓe.

“Ni kin ga, kada ki karya ni. Aiki na kitchen ba yi min za ki yi ba,” cewar Gwaggo tana ture ta.

Sake lafewa ta yi sosai ta ce, “Zan taya ki fa Gwaggo.”

“Wa ɗin, ke Haula? Taɓ! Haka kawai, yaushe kika taya ni balle kin samu abin liƙe mawa?” Dariya ta yi ta ce, “Ba da ni ba, wankan jego jaka.”

Za ta fara roƙon da ta saba idan tana son abu, Gwaggo ta ture ta, ai ko ta maƙale mata. Da ƙyar Gwaggo ta ƙwace bayan ta rakata ban ɗaki. Ta fice ta nufi kitchen don ta kawo mata abinci kafin ta fito.

“Wayyo Gwaggo na shiga uku! Na mutu ni kam, shikenan! Innalillahi Wa Inna Ilaihirraji’un raji’un.” Kururwar Haula da ke tashi kenan ta karaɗe ɗakin da ihu.

Gwaggo da ke nufo ɗakin da sassarfa ta ƙaraso cikin ɗakin har tana tuntuɓe. Ganin yadda Haula ta kame jikinta tana kuka, har jikinta na tsuma, ya ƙara kiɗimata. Hankali a tashe take faɗin, “Me ya faru Haula? Me ya same ki?” Ta ajiye farantin abincin da ke hannunta har yana zuba. Ta ƙarasa inda Haula take ta riƙo ta tana sake maimaita tambayar abin da ya same ta.

“Gwaggo, na mutu. Yoyo nake yi.” Ta faɗi tana fashewa da wani irin kuka.

Cikin rashin fahimta Gwaggo ta ce, “Yoyo kuma?”

“Eh Gwaggo, yoyo nake, wallahi na jini ma. Shikenan, na kusan mutuwa. Dama a makaranta an ce idan ba ka da jini, mutuwa za ka yi. Shikenan ni kam.” Ta sake rushewa da sabon kuka.

Nan Gwaggo ta fahimci abin da ke faruwa. Ajiyar zuciya ta sauke tana bin ta da kallon tausayi, don ita ɗin abar tausayi ce. Saboda Haula sam ba ta da wayo. Shekarunta goma sha biyar, amma idan ta yi maka wani abu, ko ɗan shekara goma ba zai yi maka ba. A wannan zamanin da muke ciki da yara suke da wayewa, musamman a wannan ɓangaren, wata ma tun kafin ta kai matakin ta san komai. Wasu ma iyayensu ba su san lokacin da ’ya’yansu suka fara ba, don sun san yadda za su yi da kansu. Sai dai iyaye masu lura da duk wani motsin ’ya’yansu ne kaɗai su kan fahimci hakan tun a karon farko. Amma Haula ba abin da ta sani game da rayuwa sai shirme da shiririta. Lallai ba za a tafi a haka ba. A yanzu ita ce uwa a wurin Haula, don ma dai waɗanda suka zama uba, kuma yayyenta, wato Salim da Habeeb, duk da a zahiri Salim shi ne komai na Haula, shi ne mai ba ta kulawa. Amma a ɓoye za ta iya cewa Habeeb shi ne suka jingina da shi, ya hana su faɗuwa. Ya zama dole ta zage dantse, ta tsaya tsayin daka don ganin rayuwar Haula ta saitu ta dawo hanya. Ita ma ta zama kamar kowace mace, mai wayo da sanin kanta. Duk da aikin ba mai sauƙi ba ne, amma nauyi ne da ta ɗauka a kanta, kuma wajibi ta sauke. Don haka ta ɗaura ɗamarar kula da ita baƙin rai baƙin fama.

Tunanin Gwaggo kenan, kuma tsarinta kenan, ba tare da ta san abin da Mai kowa da komai ya tsara ba. Wataƙila ma wannan ce kulawar da za ta ba ta ta ƙarshe, ba ta sani ba. Wataƙila kuma akwai wata dama a nan gaba. Ƙaddara tana shirya lamarinta ne ba tare da ta yi shawara da wanda za ta wanzu a kansa ba. Gaban kanta take yi, ba ta jiran umarni ko jagoranci. Yadda ta so take yi da kai, ba yadda ka so ba.

HAZ Mansion

Ta sauke wayar daga kunnenta, a bakin gado ta ajiye. Ta goya hannunta a baya, ta yi ta kai-kawo, sai kuma ta koma bakin gadon inda ta zauna. Gaba ɗaya lissafinta a dagule yake, ta ma rasa ta ina za ta fara. Gaba ɗaya al’amarin ya zo mata ba yadda ta zata ba. Komai ya rushe, ga shi Smart ya sake jagula lissafi. Ajiyar zuciya ta sauke.

“Ya zama dole abin da nake so ya tabbata, ko da kuwa hakan yana nufin faruwar komai ne. Babu wanda ya san yaushe na fara, amma za a iya sanin tsakiyar labarin. Ƙarshen kuma kowa zai bar ni da shi, ni kaɗai zan ci moriyar kayana, kamar yadda na fara ni kaɗai. Ban damu da abin da zai faru ba, rai kuma ai ba yau aka fara asararsa ba, don ba za a iya lissafa adadin waɗanda suka salwanta ba zuwa yau. Abu ɗaya na sani, shi ne nasara, kuma ko ta halin ƙaƙa, za ki yi nasara! Za ki yi nasara!! Za ki yi nasara!!!” Da ƙarfi ta furta maganar, kuma cike da ba wa kanta tabbacin faruwar hakan.

Cikin wani sabon ƙwarin gwiwa da ya sake zuwa mata, bayan ta ba wa kanta tabbacin hakan, ta tashi ta nufi gaban wardrobe ɗin kayan sawarta. Ta ɗauko wata jallabiya mai hula ta mata ta saka. Ta dawo gaban madubi ta ɗan fesa turare da lip gloss. Ta kalli kanta a cikin mirror ta sakar wa kanta murmushi, sannan ta fice daga ɗakin ta nufi turakar mijinta...

HAZ Fashion House

Salim

“Excuse me, it’s an important call, 5 mins I’m coming.” Daga haka ya tashi bayan ya ɗauki wayar da ke ruri, yayin da sunan da ya yi saving ɗin lambar Habeeb ya bayyana a kan allon wayar. Ya fice daga meeting hall ɗin.

“Where are you?” Kalmar da ta fito daga bakinsa kenan bayan amsa sallamar da Salim ɗin ya yi masa.

“I went to HAZ Fashion House. You know the year-end financial statement of HAZ Company for this year has been postponed, because there are a lot of debts outside, sai next year. Kuma already dama time ya riga ya wuce, shi ya sa nake bi nake tattaro duk wani record in case. Duk da dai har yanzu ba wata gamsasshiyar amsa daga gare ka na cewar an fasa ɗin.”

“Ɗan’uwana, I don’t know the reason for this postponement. Idan ka bar Fashion House ɗin, come and meet me at home. And who ordered for the postponement?” Ya ƙarashe maganar da tambaya.

“No, ka bar komai sai na dawo ɗin, za mu fi yin maganar cikin natsuwa.”

“Okay,” kawai ya ce, daga haka suka kashe kiran.


#amdeey_tejj_dunique
#haulahabeeb.