Chapter 8
by @deejasmah
MAƘOFTAKA DA ALJANU
Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah) & Ameenah Abubakar Ƴandoma
CHAPTER 8
..."inna lillahi wa Inna lillahi rajiun! Nana lafiya?" Inna Yabi ta furta lokacin da ta rirrike Nana. Ita kuwa sai faman rarraba ido ta ke tana so ta gasgata shin da gaske ne ko kuma mafarki ne tayi, in dai ba tsorata ba ce ta saka ta jin zafi a fuskarta ba to kuwa abin da aka watsa mata da gaske ne.
"Nana magana nake lafiya? Ta ya za ki kwala uwar kara wadda bani da ke cikin dakin nan ba hatta wanda ke waje zai iya jiyo ki, amma sai magana muke kin lula wata sabuwar duniyar tunani.
Zabura ta sake yi sai da Yaya Adama ta rirriketa. "Ke Nana wai me ye haka kike yi?" A maimakon ta ba su amsa sai gani suka yi ta fashe da kuka.
Hankalin duk wanda ke wurin ba karamin tashi ya yi ba Musamman Inna Yabi. Tsoronta Allah kada cikin nan ya fice ta san zauci ne kadai Khaleed ba zai yi ba.
"Tsorata na yi" ta karasa maganar tana kuka. "Haba Nana! Ina ilimin ki kawai daga kin tsorata za ki hau kuka a maimakon ki kama addu'o'in neman tsari."
Yaya Adama ta karasa maganar tana shafa bayanta alamun rarrashi.
"Ke ma dai ita fada. Amma ni fa lamarin Nana ya fara bani tsoro anya kuwa?" Inna Yabi ta karasa maganar tare da rike haɓa.
"Anya kuwa me Inna?" Iyami ta fada cikin daure fuska.
" 'yar nan In tambayeki mana!" Inna Yabi ta fada tana mai kallon Yaya Adama.
"Allah ya sa na sani "
"Lokacin da Nana ta na gida bata taɓa yin wani ciwo haka ko kuma lalura da ke da alaka da Jinnu ba?"
Mummunar faduwa gaba Yaya Adama ta yi. Abin da ya faru shekaru ashirin ya dawo mata sabo fill tamkar a lokacin ya faru. Saurin ɗauke fuska ta yi. "Inna Yabi! Ban fahimci abin da kuke son fada ba"
Ganin yadda Yaya Adama ta amsa mata maganar ne ya saka jikin Inna Yabi yin sanyi. "Ina nufin lalura haka kota Jinnu?"
"Inna Yabi a bar maganar nan. Shi kenan mutum kuma mace mai ciki ba zata yi mummunar mafarki ba sai ki fara yi mata jaye-jaye. Kuma in ma aka ce za a bi daga-daga ai na kurya kasha kashi."
Zabura Inna Yabi Tayi "to ja'irar nan fadi ba a tambayeki ba. Yi mana shuru abin da ya saka na tambaya ina so ne in ji, In akwai ba sai a hau neman magani ba kuma ai na ga duk an riga da an zama daya"
Nana Ganin kamar abin na neman ya zama cacar baki mikewa ta yi ta fada toilet. Jingina tayi da bango tare da sakin ajiyar zuciyar da ita kanta bata san ta mece ce ba.
Ruf ta rufe idanunta mafarkin da tayi ya na dawo mata daki-daki Motsi ta ji alamar wani ya shigo cikin kewayen. Da sauri ta Kara rumtse idonta gam, tamkar tafiyar tsutsa haka ta ji saukar wani abu a hannunta.
Wurgar da shi ta yi idonta a rufe domin ta kwammace kome zai faru ya faru idanunta a rufe ba tare da ta gani ba.
Kukan Jariri ta rika jiyowa nesa da ita, a hankali sautin ya kara kusanto inda take. Kankame jikinta ta yi tana jiran ko ta kwana. Janyo ta aka yi a hankali tare da kiran sunanta. Jin Muryar mai kiran sunan nata saurin bude ido tayi tana mai kara shigewa jikinsa.
"me kike yi a cikin bayan gida, kamar ma kuka kika yi" Khaleed ya karasa maganar ya na duba fuskarta. "Aa hutawa nake yi" jin amsar ya yi banbarakwai wai namiji da suna Baraka. "Hutawa kuma? A cikin najasar? Ko dai kin manta da abin da kike dauke da shi ne" ya karasa maganar a kufule. Bata ba shi amsa ba, jin yadda ya fizgi hannunta suka fito zuwa dakin. Ba kowa duk sun fita waje daga ita sai Khaleed.
Girar sama data kasa ya hade. "Nana" ya kira sunanta cikin kaushin murya.
"Me kike nufi da Ni, me kuke nufi da sabbin halayen da kika ɓullo da su? Tun kafin in San kina da ciki na rasa gane me kike nufi da ni. Nana ko dai kin gaji da zama da ni ko dai haihuwa da ni ne bakya don yi?"
Kukan da take yi ne ta tsayar cak! Ba abin da kake jiyowa cikin dakin sai saukar numfashinta.
"Khaleed kai ne kuwa? Ko dai abin da na saba gani ne yau yake neman tabbata a zahiri?"
"Ke dakata!" Ya daka mata uwar tsawar da ta sakata hadiye sauran kukanta. "Ina mai rantse miki da girman Ubangiji idan kika yi kuskuren da cikin nan ya zube. Hmm! Bazan CE miki ga abin da zai faru ba amma za ki gane waye ainahin Khaleed" ya karasa maganar cikin zafin zuciya. Har zai miƙe tayi saurin riƙe masa hannun "Yaya ni ce fa Jannah dinka, ko a mafarki kada ka yi tunanin zan iya zubar da cikinka ko da bani kaunarka bare ma ina kaunarka. Wallahi ba laifina bane" ta karasa maganar ta rushe da kuka.
Mata da miji sai Allah. Wani irin tausayinta ya ji ya lullubesa, duk duniya idan akwai abin da baya so bai wuce ya ga hawaye a fuskarta ba. Komawa ya yi ya zauna. "Nana! Daina kukan nan kinji." Ya karasa maganar ya na share mata hawaye.
"Ina kaunar ki har cikin zuciyata. Nana na kasa gane me kike nufi, na kasa gane kanki zuciyata harta fara gaya mini ba daidai ba a kanki."
"Kada ka bari zuciyarka ta lalata fahimtar juna dake tsakanin mu. Nima na rasa me ke damuna, abin da ke damuna ko an tambayeni bazan iya cewa ga shi ba. Addu'a nake bukata kayi min addu'a ka ji"
Ta karasa maganar tana mai jingina da jikin Khaleed.
Tausayinta sosai ya ji ya na ratsa ilahirin jikinsa, tabbas ya na sonta amma ya kasa janye zargin da zuciyarsa ke saka masa.
Motsin da suka ji alamun wani zai shigo shi ya saka su saurin sakin juna. Iyami ce murmushi ta yi "brodaaa na fahimci matarka ta warke kawai mu tattara mu koma gida." Dariya suka kwashe da ita a tare.
"Ja'ira uwar sa ido. In fitsari banza ne kazama ta yi"
Cewar Khaleed
"Lalala! Su Broda abin hada gori? Kwantar da hankalinka kwana nawa ne mutumina ya na dawowa za a fara maganar aurenmu"
Shigowar Inna Yabi CE ta saka su barin zancen. Kasancewar magriba ta yi Khaleed tare da Iyami ya tafi yaya Adama ma sun tafi. Ya rage daga Inna Yabi sai Nana da tsoro ya jima da lullubewa. Saboda duk inda aka ce magriba tayi hankalinta ya gama kwanciya. "Nana ba ko da dan goro. Na wurina ya kare yanzu nake cewa idan Khaleed ya zo in ce masa ya siyo mini kinga Har ya fita.
"Inna Yabi babu, sai dai ko bakin get wurin masu saide-saide.
Hijabinta ta gyara ta fita neman goro.
Gyara kwanciya Nana ta yi tana tunanin abinda ya faru a tsakaninta da Khaleed.
Wayarta ce ta dauki ruri, bakuwar Number ta gani wadda tunda uwarta ta haifeta bata taɓa ganin irinta ba. Har ta ajiye aka sake kira, dauka tayi "hello!" Ta furta tare da kara ta a kunne.
Ƙarar tsoki taji an yi ƙit aka kashe wayar. Tsorata ta yi mayafi ta yafa ta fito daga dakin wanda tunda aka kawota bata saka kafarta wajen wurin ba.
Dakin kusa da ita taga an turo wani mutum saman gado dukkan alamu sun nuna gawa ce, saboda ga dangin mamaciyar nan sai kuka suke. Tausayin su ne ya kama Nana, a na kawowa daidai inda take farin mayafin da aka rufe Gawar daidai fuskarta ta bude. Wiƙil ta buɗe idanuwanta da suka fito ƙuru-ƙuru ta na kallon Nana....
Meenat A. 'Yandoma