14
by @pherty001
*RIGAR ARO*
©️Fertymerh Xarah💞
14
Tun daga ranar da ta sami mota a hannu shikenan bata da aiki sai yawo acikin gari, ta soma bin faruq yawon banza, basu wannan hotel bikin qawaye basu club, acan idanun ta suka qara bude wa da yanda ake dressing da sauran su, lamarin Nurayyah ya wuce tunani cos gaba ɗaya ta daina shiga aji lectures ko karatu kamar sauran ɗalibai tunda ta lura da yanda ake ba ta girma tun daga kan dalibai har malamai ma,shi yasa ko tests bata yi ko wani assignment da bata daukar shi da muhimmanci, presentation ma sai ta ga dama take yi, idan aka gama zata aika cikin guards din ta da cewa Binnani ya aiko shi yaje ya bada wani abu dan a gyara mata scores din ta, a significant financial settlement or heavy connection influence shikenan sai a gyara mata komai an ba ta manyan maki ba tare da ta sha wahala ba, exam ma da tazo taqi zama tayi batare da ta damu da abinda zai biyo baya ba, fadila har kukan baqin ciki tayi da ta sami labarin abinda ke faruwa kuma ko da tayi wa Nurayyah magana ko a jikinta bata damu ba, ta nuna tsantsar halin ko in kula with ultimate nonchalance and a cold shoulder, ta dubi Fadila ta ce, "Ke dai kiyi ta karatunki Fadila, leave me alone to manage my high-profile life, kin san dalilin da ya sa nake yin komai amma sai ki dinga damuwa a kaina, a time will come da duk wannan zan ajiye na daina, bazan iya karatun da ban taso da burin yin sa ba kin dai gane ko." Fadila ta jinjina kai batare da tayi magana ba ta fice ta barta.
Wasa wasa Nurayyah ta soma janye jiki da zuwa school ɗin, cos gani take kamar ma zuwan yana rage mata daraja a idon mutane, kamar ta matar Binnani me zata yi da karatu bayan kowa yana mata kallon su suke da gwamnati aiki ma suke badawa to saboda me zata shiga aji? Ta tattara karatun ta ajiye bata da aiki sai yawan club da hotels ita da faruq why shi a fakaice yana xuwa school ɗin sa ko yayi mata magana tace bazata je ba sai ya kyale ta, ta fi so tayi ta yawo a Kaduna tana qone mai a banza, tana zuwa gurare da dama cruising around the elite streets of Kaduna, visiting luxury boutiques, and high-end cafes Ko da bazata siye komai ba kuwa, idan ta gama yawon ta dawo gida ta cewa Jaddi daga makaranta take.
Yau da faruq yazo irin kwalliyar da tayi masa ta fito ya saka shi jin wani iri akan ta sanda ta shigo motar with deep romantic emotions ya kamo hannunta ya gyara zaman sa yace, "Noor, gaskiya naci burin aure sosai a kanki kuma yanzu na kasa samun natsuwa a zuciyata gani nake kamar zan rasa ki, shiyasa nake so in turo iyayena ga iyayenki ayi maganar auren mu, so we can formalize our union", nan take Nurayyah ta ji hankalin ta ya tashi gabanta ya fadi cos bata shiryawa auren ba kai ko ta shirya ta gwamace ta auri Sameer da ta auri faruq, yanayin ta ya saka faruq jin wani iri cikin fargaba yace " Nurayyah are you ok, Naga kamar kin canza daga maki mgnr auren mu? ta ja numfashi kaɗan kafin ta lalubo abinda zata gayamasa tace " just ina tunanin qanin babana wanda shi zai bayar da aurena a yanzu bashi da lfy gsky yana jinya so we just have to wait for his recovery Sai Ayi mgnr auren" faruq ya jinjina kansa yace" olryt ba damuwa I will wait long for you my baby, Allah ya bashi lfy" Nurayyah tace "Amin" tare da sauke numfashi a boye ganin ta sami nasarar shawo kansa.
Bayan tafiyarsa ta jima tana tunanin yanda zata yi idan faruq ya dage da son auren ta cos bata shirya auren a yanzu ba idan ma ta shirya Sameer zata zaba, faruq da bashi da aiki sai yawon club da hotels a hakan zata aure shi yana hulda da wasu matan a waje ita kuma ya killace ta a gida sam bazai yiwu ba, kafin faruq ya ankara ya fahimci bata son sa ya kamata ta motsa tayi wani abu da zai fara janyo hankalin Binnani zuwa gare ta cos shine target ɗin ta.
yanzu lamarin Nurayyah ya riga ya wuce duk yadda ake tunani cos faruq yake koya mata mota, kullum yake zuwa da yamma suje yana koya mata kuma da yake tana da kwakwalwar ganewa nan da nan ta soma iyawa cikin qanqani lokaci, she mastered the steering wheel with absolute grace and precision ta yadda ma take bin hanya tana tuqin sai ka dauka dama can ta iya, yau ma da suka dawo daga koyon motar faruq ya kasa haquri akan mgnr auren ya dube ta yana faɗin, "Nurayyah, seriously I can't imagine my life without you anymore, a kullum burina da tunanina bai wuce naga ranar da zan gan ki cikin gidana a matsayin matata ba, qanin mahaifin ki har yau bai sami sauqi ba cos am eager a matse nake kin san ina ta haquri fa, even hug ɗinnan bama yi". Nurayyah ta yi qoqarin boye damuwar ta kada ya gane, bata san meyasa kwanakinnan ya sanyo ta gaba akan su yi aure ba, tace "Faruq, kasan nima ina son mu kasance tare amma har yanzu jikin Abba ko jiya Jaddi taje qauye duba shi Kaga bazata fara masa mgnr aurena ba kada iyalin shi su dauka ciwon sa bai dame ta ba, ka qara lokaci pls". Yace "Nurayyah, fargabata daya kada ki zo ki canza raayi a kaina ko ki sami wanda ya fini kin ga duk inda naje dake sai anyi min magana akan ki, kina da kyau da diri Nurayyah I don't want to loose you please". Murmushi Tayi wanna karon kafin ta jinjina kanta tace "Babu abin da zai raba mu Faruq, trust me, nothing will ever come between us, ka kwantar da hankalinka i will be yours when am ready Idan na kammala abinda na fara." Ya jinjina kansa cikin gamsuwa da yarda da ita, tace
" Faruq ina son driver gaskiya, sai ka nemo min". Faruq ya dube ta da mamaki yace " me zakiyi da da driver ke da kin iya driving yanxu, Why do you need a chauffeur?", Nurayyah tace" ka taba ganin matar gwamna ta tuka mota da kanta ta fita unguwa? Have you ever seen a first lady behind the wheel herself? Koyon motar da nayi for a purpose ko da ta kwana ta baci", Faruq yace "ina driver da na kawo maki wancan lokacin? Tace "gaskiya ni bai min ba shiyasa na sallame shi bana son tsoho wannan ko laifi yayi min bayan iya masa faɗa ba and tsoho ne ta yaya zai iya kare ni idan wasu sun zo cutar dani? Yace " shikenan zan duba nagani". Bayan tafiyar faruq ta shiga gida kai tsaye dakin Jaddi ta nufa, sanda ta shigo Jaddi ta zuba mata idanu wa tana mata kallon mamaki, Nurayyah ta canza kamar ba ita ba, tayi wani irin haske har fatar jikinta wani sheqi take yi, ta lura akwai wata irin wayewa da bata san Nurayyah da ita ba a yanxu, ga sutura mai tsada da take saka wa, idan tasa turare qamshin sai ya dade a jikinta bai fita ba, mutanen unguwa yanxu sai tsegumi suke akan manyan motocin dake zarya a unguwar, tana kallo Nurayyah ta dauki abinda zata dauka a ɗakin ta juya zata fice ta kira ta, " Nurayyah!" Nurayyah ta juyo tana kallonta bayan ta amsa, kafin ta dawo ta zauna gabanta tana faɗin " kiran me kike min, tukunna ma zaman me kike da baki kwanta ba, ga dare yayi? Jaddi bata amsa ba, kai tsaye tace " Nurayyah tsoro nake ji a kan sabuwar rayuwa da kika daukowa kanki a yanzu, ina son ki tuna fa ke marainiya ce ba uwa ba uba sai ni kadai da kike da ita a duniya, duka danginmu suna can kauye zamane kawai ya zo da mu nan Kaduna da dadewa, yanzu naga kina son ki manta da asalin inda kika fito, kin dauko wata rayuwa daban wacce na jima ina sanya miki ido a kanta tun lokacin da mutanen unguwa suka fara kawo min tsegumi a kanki, ga Alhaji Musa ma ya soma cire hannunsa a kanki, tkunnan ma ina kike samun kudi, motoci da tsadaddun kayan da kike saka wa kullum kina canzawa kamar ma bakya maimaici a yanda na lura?
Nurayyah taja numfashi kaɗan tace "Jaddi, kinsan halina fa kinsan bazan taba zuwa nayi sata na dauki kayan wani ba, sannan kinsan bazan je na zubar da mutuncina ba, mace ce ni fa just 19yrs kema kinsan lokacina ne yanzu, mace kamata dole zan yi samarin and samarin zasu kashe min ko nawa ne dan su mallake ni kawai masu kawo maki magana akaina ki kyale su tsabar gulma da hassada ce ke damun su dan sun ga nafi ƴaƴan su, kin san me samarin ƴaƴan su suke kai masu duk bai ishe su ba sai ni na tsole masu ido nan zaki gane tsabar hassada ne kada nazo nafi ƴaƴan su, motoci da ake magana ai na gidan su faruq ne kin sani ko ranar na gayamiki da kika gani kika tambaye ni, wannan mota da nake hawa kullum kuma yaya Sameer ya aramin akan na riqa amfani da ita kafin ya dawo, sutura kuma kin san fadila take bani, bani ma da samarin da ake tunani suna kashe min kudi, mazan nan ne kawai guda biyu da kika sani bayan su bani da wani saurayi da har ake tunanin ina wata rayuwa can daban, mgnr maimaici kuma kece bakya lura ina nake da kayan da har zace bazan yi maimaici ba, kawai dai ina dadewa ban maimaita sutura ba idan na sanya". Jaddi ta sauke numfashi mai nauyi tana jin wani relief a zuciyar ta, sai dai tana kwankwanto akan ta tace "Amma Nurayyah, Fadila ta fada min kin daina zuwa makaranta, ina kike zuwa idan kika fita kullum?",
Nurayyah ta ji gabanta ya fadi ta kai hannunta goshinta ta shafa a hankali cikin tunani kafin tace, "Ki bar zancen Fadila kawai Jaddi, babu ranar da bana zuwa makaranta sai dai kullum idan naje ina da gurin da nake zuwa nayi karatuna saboda kada a dame ni ko kuma qawaye banza su ja raayina kin sanni tun ba yanzu ba yanda nake da karatu bare makaranta irin wannan da idan baka dage kayi karatu ba kora ne sakamakon ka meyasa zanyi wasa da karatuna? Sannan abinda nake so ki sani muna da banbanci da fadila, ajin mu ba ɗaya ba abinda muke karatu ba ɗaya ba sanda take da darasi ba lallai bane ni ina dashi sanda nake nawa ba lallai bane ita tana da shi, shiyasa yaya Sameer ya bani motar sa kin ga babu takura duk sanda take da darasi taje nima haka so ba lallai bane ace sai ta ganni school idan bata ganni ba tazo zuwa kawo gulma bana zuwa ni bana son haka, ni barci ma nake ji sai da safe". Kafin Jaddi tayi magana tuni Nurayyah ta tashi ta fice da sauri saboda gujewa tambayoyi Jaddi da ta saka ta a gaba, Jaddi ta bita da kallon mamaki tana jin wani rashin yarda akan Nurayyah a yau, wanda take ji ya kamata tayi bincike cos fadila bazata mata qarya ba ko yaya ne dole zasu hadu a makaranta komai rashin darasin su a tare, da wannan Jaddi ta tashi itama taje ta kwanta saboda dare yayi.