ALIYU HAYDAR

Chapter 21

by @nieemartullah


HAYDAR na gama waya da Mamy ya kira Zannur.

Bayan ya ɗaga ya ce masa " Mamy ta ce tana son ganin mu gobe."

" Amma lafiya Zannur ya tambaya?"

" Nima ban sani ba,kawai dai ta ce tana son ganin mu gobe."

" Toh shikenan, Allah ya nuna mana goben."

" Amma Zannur na tambaye ka mana."

" Ina jin ka,me ya faru?"

" Don Allah bayan mata ta da ta mutu ina da wata matar ne?"

Zagin shi Zannur ya yi ya ce " kai bana son iskanci,ita Safiyyah ce zaka ce baka san da ita ba."
Shiru HAYDAR ya yi sai kuma ya ce " ita ma Mamy sunan da ta kira kenan."

" Don Allah Zannur ko dai hauka nake yi ban sani ba?"

 Ganin ba bu wasa a yanayin shi, sai Zannur ya ce  " wai don Allah ALIYU da gaske kake baka san da zaman Safiyyah a matsayin matarka ba?"

" Wai ita Safiyyah ma wacece wallahi ni ban san ta ba."

" Shikenan ka kwantar da hankalin ka, goben idan muka je za mu ji ko ma menene."

Bayan sun gama waya ya yi ta tunanin to meyasa HAYDAR ya ke cewa bai san Safiyyah ba?

A ranshi ya ce kar fa abinda nake tunani ya tabbata.

Ganin babu wanda zai bashi amsa yasa ya watsar da duk wani tunani ya ce bari zuwa goben ko ma menene ai zai ji.
Suna dawowa gida hajiya Mama ta ce " au har kun dawo?"

" ai da na san ba daɗewa zaku yi ba da na bari kun tafi da ita."

Jay ta ce " ai shikenan dai tunda mun dawo."

Ɗakinta ta wuce don dama a gajiye take, gashi tana son ta shiga asibiti bayan sallar isha'i saboda akwai patients ɗin da zata gani.

Munarh ce ta biyo bayanta ta ce " Jay idan zaki je asibiti anjima zan bi ki,ina son naje na qara duba babe."

" Uhm su babe manya Jay ta faɗa tana juya idanunta."

Dariya Munarh ta yi ta ce " faɗi ki ƙara mace da mijinta ki ce bazan ce mashi babe ba?"

" Kedai kiyi ta zama,ni wallahi na ɗauka Ayaanah ma 'yar ki ce sai da Mom ta yi man bayani sannan na fahimta."

Dariya Jay ta yi ta ce " ban da lokacin ki ma ni."


Ganin Jay ta maida abin wasa yasa Munarh ta ce " Allah ba maganar wasa ba a farko da na fara ganin Ayaanah nayi tunanin 'yar ki ce."

" Wallahi Munarh banda wani ɗa namiji bai taɓa taɓa ko da farcen hannu na ba,dazan iya cewa tabbas Ayaanah 'ya ta ce."

" Abin yana matuƙar ɗaure min kai."

" Har yatsun ƙafafunta irin nawa ne,wasu lokutan ni kaɗai nayi ta kallonta."

" Ina ji a jiki na akwai alaqa me ƙarfi tsakani na da ita, shiyasa lokacin da aka kawo ta asibiti na ce wa wanda ya kawo ta ya barta a wuri na har zuwa lokacin da shi mahaifin nata zai dawo."

Munarh da taketa saurarenta ta ce " kuma kema kina da gaskiya, don ina da tabbacin kuna da alaƙa da Ayaanah."

" Alaƙa ko ta kusa ko ta nesa."
Miqewa ta yi ta ce " bari na ɗan zuba ruwa a jiki na ko zan ji sauƙin gajiyar nan sai mu tafi."

Toilet ta shiga ta dan watsa ruwa,bayan ta fito ta shirya sannan ta ce ma Munarh da ke zaune tana jiran ta ta gama shiryawa su tafi.

Suna fitowa parlour suka haɗu da hajiya Mama da Ummi a parlour suna hira.

Kallonsu hajiya Mama ta yi ta ce " amma dai ƙara fita za kuyi ba?"

Munarh ce ta bata amsa da " fita za muyi mana."

Taɓe baki ta yi ta ce " haka aka iya daga nan sai nan."

Jay da take ta jin su ta ce " to ko na zauna sai ki je asibitin ki duba marasa lafiyar?"

Ƙwalalo ido ta yi waje tana kallon Ummi ta ce " kiji man wannan zance ƴar nan, zata saka man jakar tsaba kaji suyi ta bi na."

" Na hana ku fita ne?"


" Daga yin magana zaki ce na je na duba marasa lafiya."

" Da shekaru na zan duba su?"

" Ni dai kar a saka man magana a baki, maza ayi ta tafiya sai kun dawo,a dawo lafiya."

Ummi dai sai murmushi take yi bata dai ce komai ba.

Ummi Jay ta ce wa sun tafi.

A dawo lafiya ta ce masu sannan suka tafi.

A hanya ma hira suka yi ta yi har suka je asibitin.

Suna qarasawa ta ce ma Nurse Habeebah ta raka Munarh ɗakin patient ɗin nan da ke sama room 234.

" Toh matar babe,je kiga mijinki kafin na gama duba patients ɗina."

" Ya ranki,ta faɗa tana dariya."

Girgiza kai Jay ta yi har ta juya zata wuce ta ƙara juyowa ta ce " Allahummah yahadikhi."

Dariya ta ƙara yi ta ce " Ameen wa iyyaki,don kema kina da buƙatar shiriyar."

Nurse Habeebah da ke ta kallon su ta ce " muje ma'am."

Layla ce riqe da waya tana ta kiran Sooraj a waya saboda tunda ya fita taji hankalinta gaba ɗaya yaƙi kwanciya.

Ta kira shi yafi sau uku amma bai ɗaga ba.

Sosai ta ji gabanta yana faɗuwa,number Hafsat ta yi dialling.

Bayan ta ɗaga ko gaisawa ba suyi ba ta ce " Hafsat kina gida ne don Allah?ina son gobe mu koma wurin malamin nan."

Hafsat da ke zaune tare da mijinta a paris ta ce " ƙawata ba na faɗa maki zamuje paris da babe ba?"

Layla dake sauraronta ta ce " wallahi na manta ƙawata."

" Hankali na ne gaba ɗaya a tashe,muna zaune da Sooraj wannan yar iskar cousin ɗin ta shi da bana so Saleemarh ta kira wai yazo gidanta mamanshi na kiran shi."

" Kuma kin san na faɗa maki sun zo lokacin ina kallo series film ɗina ko ruwa ban  basu ba na ce su shiga kitchen ai ba baƙi bane su."

" kin san fa dangin miji,kar naje wani makircin suka ƙulla man."

" Wallahi tunda ya fita naji gaba na yana ta faɗuwa."

" Na ma rasa wani irin tunani ma zan yi."

" Ki kwantar da hankalinki ƙawata ko ma menene suka ƙulla da na dawo zamu warware shi."

" Amma yanzu dai ki kwantar da hankalin ki, ko dawowa yayi kar ki nuna masa wani abu."

" Ko maganar kar kiyi masa sai idan shine yayi miki kinji."

" Tohm shikenan ƙawata sai ki dawo ɗin."

Sallama suka yi,sai a lokacin ta ji ta ɗan samu sauqi kaɗan.

Bayan ta gama duba duk patients ɗin ta ta wuce ɗakin mijin Munarh yake.

Knocking ta yi ta shiga bayan an bata izinin.

A zaune ta gansu suna ta hira kaman ba mara lafiya ba.

Ta ce " eyyeh lallai ne lovebirds daga ganinta shine har ka samu lafiya haka?." Ta faɗa tana dariya.

Shi dai murmushi kawai ya yi baice komai ba.

Munarh ce ta ce " eh mana ya ganni ba dole ya warke ba."

" An faɗa maki ni ɗin ta wasa ce."

Shi dai kallon su kawai yake bai ce komai ba kuma tun maganar farko da suka yi ya fahimci tabbas ita ce Jay ɗin da har kunnenshi ya gaji da jin labarinta.

Kallon Abdul Munarh ta yi ta ce " yawwa babe let me introduce her to you."

Kafin ta ƙara cewa komai ya ce " she's Jay,your best friend and the only sister you have."

Dariya ta yi sosai har hawaye na taruwa a idonta ta ce " kai babe wannan ai casting ne salon ma ta ce maganar ta nake yi kullum?" Ta faɗa tana hararar inda Jay take a tsaye tana saka hand gloves.

" Shi dama mutum in bai ganni ba hankalin shi baya taɓa kwanciya i don't even know how you survive all this years." Jay ta faɗa tana harararta ita ma.

Tana gama saka hand gloves ɗin ta ƙaraso inda suke ta ce " ɗan kwanta bari na ga ciwon."

Kwanciya ya yi ta cire bandage ɗin da aka rufe ciwon ta yi dressing wurin.

Bayan ta gama ta ce " ciwo yana ta warkewa."

" Ina ganin zamu sallame ka ne kaima, sai a cigaba da yin dressing a gida har nan da kwana biyar da za'a cire ɗinkin."

Dama shi ma ya gaji don kwana biyun da ya yi ji yake kamar ya shekara ne a asibitin.

Wayarta ta ɗauka ta tura email zuwa pharmacy ɗin asibitin na  magungunan da zai yi amfani da shi.

Sannan ta kira Nurse Habeebah a waya bayan ta ɗaga ta ce " Habeebah don Allah ɗan karɓo man wasu magunguna a pharmacy."

" Idan na fito zan karɓa a reception."

Bayan ta gama wayar ta ce "emm zaka iya tafiya da kanka ko na sa Nurse ta kawo wheelchair?."

Girgiza mata kai ya yi ya ce " zan iya tafiya ba sai an kawo ba."

Jinjina kanta ta yi ta ce " Munarh ga makullin motar nan ki taimaka masa kuje cikin mota bari na ɗakko saƙo a office ."

Bayan ta dawo ta tarar da Munarh zaune a passenger seat shi kuma a back seat.

Driver seat ta shiga ta yi reverse ta bar asibitin.