RIGAR ARO

15

by @pherty001

*RIGAR ARO*




©️Fertymerh Xarah💞






15




Washe gari, Nurayyah ba ta fita makaranta ba, tana kwance a saman tsohuwar doguwar sofa din dakin ta, tunani take yanda zata sami kuɗi, tana buqatar kudin sosai kuma ko ta halin qaqa, basu da komai ko wata qaddara da take tunanin zata siyar domin samun kuɗin, sai ta soma tunanin gidan gadon ta da aka bar mata ko zata sace takardun taje ta siyar? Amma ta yaya, ta ina ma zata soma bincike batare da Jaddi ta sani ba, tana cikin tunanin wayar ta ta dauki qara tana dubawa faruq ne, taja guntun tsaki kafin ta ɗauka yace, "Ina jiran ki  a kofar gida, kinsan na fada miki jiya zamu je engagement party na abokina?", Nurayyah ta yi jim cos yau taso kada taje ko ina ta zauna gida ta huta kafin ta amsa masa da "Ina zuwa yanzu", kafin ta kashe wayar.

Wanka tayi ta shirya cikin doguwar riga sophisticated designer long dress, Tayi kyau a jikinta ta fito da irin ta sosai, simple make up tayi, ta dauki bag ɗin ta ta fito, kallon Jaddi tayi tace, "Ina da lectures yanzu Jaddi, sai na dawo", Jaddi ta dube ta tace, "To Allah ya taimaka ya bada sa'a ya kuma tsare mini ke, ki kula da kanki sosai, idan zaki dawo kizo min da abincin kaji."

Nurayyah ta yatsina fuskarta tana kallon Jaddi cikin wani irin yanayi na rashin jin dadi, tana mamakin me yasa har yanzu Jaddi take son aikin ta siyen abincin kaji, she is 19 fa ai ta wuce aiken abincin kaji, ko dan Jaddi bata san matsayin ta a gari ba shiyasa take mata haka, ta karbi kuɗin tana tunzuro baki kafin ta wuce cikin qunquni, tasan idan bata karbi kudin Jaddi ba zata soma tambayoyi ina ta sami kuɗi da sauran su abinda bata shirya bata amsa ba kada ta bata mata lokaci, Jaddi ta bita da kallo tana so ta mata mgnr shigar jikinta bakin ta yayi nauyi, Nurayyah kamar bata san ta girma yanxu ba, duk wata halittar da ke sanya namiji sha'awa a jikin mace ya gama bayyana a jikinta, ga ta da diri kamar na manya mata, bazata jure ganin tana fita da irin wannan shigar ba ko babu bakin mutane akwai aljannu boye, Nurayyah na fitowa ta sami yaron maqoci ta bashi kudin akan ya siyo wa Jaddi abincin kaji ya kai mata, ta shiga motar faruq, ya juyo yana kallonta yace, "Wow Nurayyah, turaren jikin ki yamin dadi it's incredibly mesmerizing and romantic", Nurayyah ta dauke kanta gefe tana faɗin "Muje  kafin Malam Musa fito ya ganni  yaje ya gayawa Jaddi wani zancen daban", Faruq ya tada motar suka bar wurin.

Isar su Hotel 17, suka tarar da harabar gurin ya cika makil da mutane, maza da mata yan gayu irin su faruq, Ango da amaryar basu iso ba da manyan friends na Ango, lokacin tana zaune manyan motoci suka soma shigowa, Mercedes Benz, Range Rover, da Lexus, taga yanda maza suke fitowa da ƴan matan su da irin kalar dressing din su wanda idan tace zata yi shi ta tabbata ko Jaddi bata tsine mata ba unguwar su zaa tsine mata albarka idan ma basu kora ta ba, sun yi matuqar burge ta tana kallon yanda matan suke maqalewa mazan kamar zasu shige jikin su, duka tana zaune tana observing komai faruq kuma yana observing ɗin ta ya dauka abin ya burge ta yaji dadi sosai a ransa, da aka fara biki maza da mata aka soma rawa, faruq ya ja ta suka shiga filin rawa suna takawa kadan duk da tana jin wani iri tana jin nauyin idon mutanen dake kanta, dadin abin ma friends din bana school ɗin su bane da asirin ta ya tonu yau, cikin wayo da dabara faruq ya samu ya shiga jikinsa ya rungumo ta, hannunsa ya sa ya zagayo dashi qugunta wanda nan take yayi loosing control saboda abinda yaji a jikinta da sauri ya kai hancin sa  wuyan ta, yana shaqar qamshin jikinta dake neman gusar da hankalin sa inhaling her scent with deep, romantic intoxication, tana jin haka ta sa hannu da qarfi ta ture shi cikin bacin rai, wurin aka dauki sowa, ya dago yana kallonta qasa qasa cos jikinsa ya gama sanyi, wani kallo tayi masa kafin ta juya ta bar wurin, abokansa suka soma yi masa dariya bai damu ba, ya janyo wata beb ya riqe qungunta suka ci gaba da rawa, Nurayyah ta sami wuri ta zauna tana kallon sa da takaici, tun da suke zuwa club da hotels bai taba yunqurin taba jikinta ba sai yau, sai dai kullum yana tare da wasu mata wanda hakan bai taba damun ta ba tunda ba sonsa take ba, tana zaune gurin har aka yi magrib duka babu wanda yaje allah acikin su, sai shashanci banza suke, sai da aka gama komai sannan faruq yazo yayi mata wani kallon raini ya fice, ta tashi tabi bayan sa suka shiga mota, tana zaune tana huci cike da bacin rai ta kauda kanta gefe tana kallon titi ta cikin glass, Faruq dake driving ya kalleta sannan ya soma magana cikin bacin rai yace, "Gaskiya banji daɗin abin da kika yi min a gaban frnds ɗina ba, you literally embarrassed me in front of my guys, menen aciki dan na rungume ki just to show them ke tawa ce, aikin san ba halina bane tunda ban taba attempting ba amma ji yanda kika wani ture ni kika fice daga fili kina kumburi, kin yi matuqar bata min, baki nuna wayewa ba", Nurayyah ta yi masa wani kallo kafin tace "bana son wannan ko da wasa, respect my dignity in front of your friends, idan har da gaske sona kake aure na zaka yi bazaka min wannan abin a gaban friends da sunan wayewa ba, I hate it namiji ya ɗora hannunsa a jikina". Faruq ya juya yana kallonta ganin yanda take magana cikin bacin rai ya jinjina kansa a ransa yana fadin she hates namiji ya taba jikinta bai gane ba, yace " bakya son namiji ya taba jikin ki kamar ya? Menene aciki idan aka taba jikin ki, dani dake duka daɗi zamu ji and abinda zan miki na rantse sai kin fini jin daɗi dan kullum zaki nemi na dinga miki, Nurayyah idan kina so na da gaske ba zaki nuna bacin rai haka saboda kawai na taba jiki.......Stop please" ta katse sa cike da bacin rai idanun ta sun yi jawur, "park the car na sauka" ta qara fada cikin bacin rai, faruq ya ja numfashi bai tsaya ba kuma bai sake magana ba har suka iso qofar gidan su, ta soma qoqarin bude motar ya rufe ta juyo a fusacce tana kallon sa, murmushi yayi yace "Am sorry, ina son ki da yawa shiyasa na kasa controlling kaina akan ki, kuma ki sani duk namijin da ke son ki da gaske dole yaji sha'awar taba ki Nurayyah ba laifina bane wannan so ne, I promise to control my self akan ki daga yau har sanda zamu mallaki juna". Tace " bude min mota" ba musu ya cire lock ɗin ta fita daga motar a fusacce ya bita da kallon sha'awa ganin yanda qungunta ya fito sosai a rigar, duk yanda ya so haqura da ita bazai iya ba cos yana son ta he want to have a little bit taste of her, da wannan tunanin yaja motar ya fice daga unguwar.

Washe gari da yazo ya kira ta taqi dauka har lokacin tana cikin fushi dashi, ya aika yaro taqi fitowa ya gaji da jira yaja motar ya tafi cikin tunanin hanyar da zai biyo mata.