GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 31

by @nusybee143

Page 31




Kallon Shaheeda Ummeey ta yi, wadda take ta kallonta tunda wayar ta fata ringing,don ta gane abbanta ne ya kira daga yanayin ringing ɗin, Ummeey ta ɗauke idanunta saboda hango damuwa da fargaba da ta yi a idanun ƴar tata,ta ɗaga wayar da sallama a bakinta 

A gaggauce Abba ya amsa,ya kira sunanta "Zainab!"gyara zama tayi tana amsawa "na'am Alhaji"

"Menene gaskiyar maganar da na ji na cewa Fatima ta dawo gida?"

Sai da Ummeey ta kalli sashen da Shaheeda take zaune ta yi tsumu, sannan ta ce "eh haka ne,ga ta a gida"

Abba ya ce "to da kyau"kafin ta yi wani yunƙuri ya kashe wayarshi 

Shiru Shaheeda ta yi tana kallon Ummeey,tashin hankali yana bayyana a kan fuskarta, cikin rawar murya ta ce"Ummeey me ya ce?"

Ummeey ta kalle ta da kulawa ta ce"bai ce komai ba,ki kwantar da hankalinki,babu abin da zai faru sai alkhairi in sha Allah,ke dai ki yi ta addu'a kawai,kin ji?"Shaheeda ta jinjina kai cikin sarewa, sannan ta miƙe don mayar da abincin zuwa kitchen,don gaba ɗaya ya fita a ranta,Ummeey ta kalle ta ta ce"ina za ki je?"

Shaheeda ta ce "na ƙoshi,zan mayar da abincin kitchen"Ummeey ta ce "to dawo ki zauna,idan kin manta bari na tuna miki,a dokokin da aka kafa miki ɗazu har da ta hana zama da yunwa,maza zo ki zauna ki ci"babu musu ta dawo ta samu waje ta zauna,ta cigaba da cusa abincin 

Ummeey tana kula da yadda ta tsangwami kanta tun wayar da suka yi da Abba,don haka ta fara ba ta labarai masu ɗebe kewa,tun Shaheeda bata sakewa har ta fara 

Washe gari da fargaba Shaheeda ta tashi, duk daily activities ɗinta da ta yi a sanyaye,ita kanta a yanzu bata da burin da ya wuce Abba ya dawo ta san makomarta a gidan,ko dukan tsiya zai yi mata bata damu ba muddin zai yafe mata,ya bar komai ya wuce kamar Ummeey 

Haka ta yini zullumi da fargaba har zuwa bayan la'asar,bata juma da idar da sallar la'asar ba ta ji alamun dawowar mahaifin nasu 

Gabanta ya faɗi,ta yi tagumi tana jin yadda zuciyarta take lugude,bata taɓa tsammanin akwai wata rana a duniya da zata zo ta yi fargabar ganawa da mahaifinta ba, saboda irin yadda suka shaƙu, kuma suke tsananin son juna 

Ummeey tana kule da ita, ganin tunanin ba zai ƙare ba sai ta dube ta ta ce"Shaheeda wai lafiyarki kuwa?tun ɗazu kina abu ɗaya? tunanin me kike yi ne haka?"

Hawaye suka cika mata idanu, cikin sanyin murya ta ce "Ummeey ina tsoron gamuwa da Abba ne,ina tsoron hukuncin da zai yanke akaina,don Allah Ummeey ki ba shi haƙuri,na yi nadamar abin da na yi a baya"

Tausayin ƴar tata ya kamata,amma sai ta ɗaure fuska ta ce"ai damuwa kuma kin yi ta gamuwa da ita kina fargaba kenan, tunda kika yiwa kanki tabon da ba zai gogu ba, yanzu bari na je na yi masa barka da zuwa,idan ya buƙaci ganinki sai na kira ki, idan ya ce baya buƙatar ganinki kuma sai zuwa gobe wataƙila"Shaheeda ta jinjina kai ba tare da ta yi magana ba, Ummeey ta saka hijabi ta fice daga sashen 

Kamar yadda aka saba a babban parlourn Alhaji Yusuf iyalan nashi suke haɗuwa da ɗaiɗai da ɗaiɗai don yi masa barka da dawowa daga ƙasar Ghana da ya je wani taron kasuwanci nashi,kamar yadda ya saba yana ta tambayar kowa yadda yake, musamman ƴan makaranta 

Shigowar Ummeey ta rage masa walwala, sannan kuma ta haifar da wani kallo daga sauran matan,amma sai ta yi kamar bata gani ba,ta gaida Alhaji Yusuf,bai amsa ba ya ce"ina Fatima?"

Gaban Ummeey yana dukan uku-uku ta ce"tana sashena "Abba ya ce"to babu laifi,kira min ita"Ummeey ta miƙe ta fice daga parlourn ba tare da ta yi magana ba, kishiyoyinta suka raka ta da kallon banza 

Yadda ta bar Shaheeda haka ta dawo ta same ta,ta ce "Shaheeda taso mu tafi, Alhaji yana nemanki"

Sai da Ummeey ta taimakawa Shaheeda ta tashi,don gaba ɗaya jikinta karkarwa yake yi,har ƙafafun nata suke neman gaza daukarta 

Suna zuwa bakin ƙofar sashen Abba Shaheeda ta coge gabanta yana bugawa, fuskarta ta bayyanar da tsoro, Ummeey ta kalle ta, fuska a daure ta ce"wuce mu je mana, bana son sakarci fa"

"Ummeey tsoro nake ji,ban san me Abbana zai yi min ba, don Allah Ummeey ki ba shi haƙuri kin ji"

Ummeey ta ɗaure fuska ta ce "bana son shirme Shaheeda, wuce mu tafi,idan ba haka ba kuma zan koma na ƙyale ki da shi"tana faɗin haka ta yi gaba ta shiga parlourn,itama Shaheeda bata da wani zaɓi wanda ya wuce ta bi bayan Ummeeyn duk da yadda ƙafarta take rawa

Da sallama suka shiga,kan Shaheeda a ƙasa,da ƙyar take iya controlling kanta saboda yadda jikinta yake rawa

Suna shiga gaba ɗaya idanun mutane ya yo kansu,gaban Ummeey ya faɗi ganin sauran yaran da ba sa wajen ma yanzu duk sun hallara,har da Hassan da Hussaini da Na'ima,ga ƙannen mahaifinta maza, uncle Habib ne kawai babu,ga wasu daga cikin yaransu su ma duk a zazzaune

Sai da ta kusa faɗuwa, Allah ya sa Ummeey tana kule da yanayinta ta riƙe ta,ta taimaka mata ta zauna,ba ita Shaheeda ba,ita kanta Ummeey jinta take yi a muzance,suka samu waje suka zauna, Shaheeda ta rissina bakinta yana rawa tana faɗin"Barka da dawowa Abbana!"

Shiru falon ya ɗauka kowa yana kallonta, ƙasa-ƙasa take jiyo tsaki da maganganu daga wajen mutanen parlourn 

Abba ya gyara zama sosai yana dubanta, kafin ya kira sunanta"Fatima!"a firgice ta ɗago ba tare da ta iya amsawa ba, ƙirjinta sai tsananta bugu yake yi saboda tashin hankali da fargaba da taraddadi, Abba ya sake faɗin "Fatima!

Ki amsa mana!"jikinta yana rawa, bakinta ma yana rawa ta amsa da faɗin "na'am Abbana!"

Abba ya yi wata dariyar takaici ya ce"a baya nake amsa wannan sunan Fatima,amma daga lokacin da kika shaidawa duniya akwai wani mutum da ya fi ni ƙima da daraja a idanunki na san cewa na rasa wannan ƙima da darajar 

Yanzu dai ki faɗa kowa ya ji,ina kika samu ciki?kuma me ya dawo da ke gida bayan tsawon lokacin da kika ɗauka ba tare da kin tuna cewa kina da mu ba?"

Kuka sosai Shaheeda ta fashe da shi mai gunji, kafin ta fara faɗin"don Allah Abba ka yafe min,Abba ka yafe min don girman Allah, wayyo Abbana don Allah......."

"Dakata min!"ya daka mata tsawar da ba ma ita ba,da yawan mutane a ɗakin sai da suka firgita,ita kuma ta dafe cikinta da ta ji ɗan cikin ya yi zillo kamar zai fito duniya, Abba bai kula ba ya cigaba da magana cikin kaushin murya"ki ba ni amsar abin da na tambaye ki, shine abin da ya tara mu anan kawai,me ya faru har kika tuna da mu kika dawo?"cikin kuka da rawar murya Shaheeda ta fara bada labarinta kamar yadda ta ba wa Ummeey, kafin ta gama gaba ɗaya ta fice hayyacinta saboda matsanancin kukan da take yi,ga fargaba da tashin hankali da take ciki 

Tana gamawa kuma Hajiya Atika ta fara da faɗin"ikon Allah!

Dama an ce duk wanda bai ji bari ba ya ji hoho,yawan bariki ai ba shi da daɗi,don wannan maganar dai an samu manya sun yi mata kwaskwarima ne dai kar sunan ƴaƴan ya ɓaci,amma wata maganar mutum yana ji ya san faɗarta kawai aka yi"

Hajiya Sa'adatu ta cafke maganar da faɗin "Ni na rasa ma abin da zan ce,to Allah ya kiyashe mu da damalmalewar zamani,sai a san yadda za'a yi,ko na ce matakin da za'a ɗauka saboda namu ƴaƴan "

Abba ya kalli Shaheeda da ta takure tana kuka sosai,ya kalli Ummeey da kanta yake a ƙasa,babu mai gane yanayin da take ciki,ya fara magana cikin ɗaci da kaushin murya 

"A Tsawon shekarun da kika yi a duniya daidai gwargwadon iyawa babu irin gatan da ban yi miki ba,abu ne sananne a cikin Maliya family gaba ɗaya ke na zaɓa a matsayin wadda na fi ji a raina, kasancewarki ƴata ta fari, sannan kuma ƴa ɗaya a wajen mahaifiyarta,a wancan karon ba zan yi musu ba ba kya son ɓacin raina ko da wasa,don haka nima nake jinki a raina 

Amma kwatsam!kika zaɓi ki zubar da wannan martabar daga gare ni,kika nuna wani kika zaɓe shi a matsayin wanda kike son ki cigaba da rayuwa da shi, wanda na ba ki kika bijire masa,kika zaɓi ki bi wani ki bar ni,ki bar mahaifiyarki ba tare da kin yi tunanin cewa wata rana irin haka zata zo ba,to gashi ta zo,kuma kina kan girbar abin da kika shuka,to madalla,hakan ya yi daidai,dama duk abin da mutum ya shuka a rayuwa shi zai girba,don haka ke ma ki cigaba da girbar naki 

Yanzu abin da na kira ki na sanar da ke shine,a baya ke kika nuna ba kya buƙatarmu,kika tafi kika bar mu, yanzu kuma da duniya ta yi miki juyin kwaɗo sai kika dawo gare mu,to mu ma a yanzu ba ma bukatar ki!!!"a gigice Shaheeda ta ɗaga kai tana kallon Abba idanu a waje,bai damu ba ya cigaba da faɗin"don haka yanzu za ki tattara ya naki ya naki ki koma inda kika fito, sannan da buƙatar ki manta a duniya kina da uba mai suna Yusuf kamar yadda na cire ki a sahun ƴaƴana na bar wa duniyar da kika shiga ke

Na ba ki awanni uku ki tattara ki bar min gida,akasin haka kuma ranki sai ya ɓaci fiye da tunani,sai na sa kin ji a duniya ban taɓa saninki ba"

Kuka mai tayar da hankali Shaheeda take yi yana faɗin"Abba na yi nadama,ka yafe min abbana, don girman Allah, Abba na shiga uku,don Allah Abba ka taimaka min "

Hajiya Sa'adatu da ke gefe tana ɗan murmushi ta ce"a'a Alhaji,tunda dai ta yi nadama,kuma gashi mun gani komai ya ƙare mata,ga tabo ya kamata a duba don Allah "

Hajiya Ruƙayya ta kalle ta da sauri ta ce"ya kamata ki rinƙa duba makomar yaranmu kafin a aiwatar da wani abin 

Idan aka yafe mata nan gaba ma wani daga cikin yara zai yi sha'awar Hakan saboda ya san za'a yafe masa, don haka yana da kyau a hukunta ta"Ummeey dai kasa jurewa ta yi,ta miƙe jikinta a sanyaye ba tare da ta kalli kowa ba ta fice, Shaheeda ta kasa tashi tana gunjin kuka mai tsanani 

Da ɗaiɗai da ɗaiɗai aka fara miƙewa ana ficewa,itama Shaheeda ta miƙe ta fice,sai dai bata koma cikin gidan ba,ta raɓe a jikin bango tana kuka mai sauti 

Uncle Aliyu ne ya dubi Abba fuska a ɗaure ya ce"yaya idan ka yi min izini ina son zan riƙe Shaheeda,ko da ace kana ganin bata horu ba ni zan yi mata wani horon da ba zata sake marmarin yin abin da ta yi ba, ballantana ma duk wanda ya ganta ya san tana cikin nadama mai yawa sosai,ina tsoron kar ta jefa kanta a cikin wata trauma wadda zata yiwa rayuwarta illa "

Alhaji Yusuf cikin ɗaurewar fuska ya ce"ban ba ka izini ba,ko a yau ko a gobe, trauma kuma ta daɗe bata shiga ba,amma ni bana buƙatarta a gidana ko a area da ta shafi gidana,kai ma idan kana buƙata sai na sallama ka kamar yadda na sallama ta,na sallame ku"

Duk maganganun Abba a kunnen Shaheeda,ta yi shiru tana jinginar da kanta a jikin bango, lokaci guda kuma ta ji zuciyarta ta ƙeƙashe,kukan da take yi ma ta daina,a hankali ta ja ƙafafunta ta fice daga gidan,ta cigaba da tafiya a ƙafa har ta fice daga cikin maliya estate,ta hau titi 

Babu ko sisi a jikinta,ga gari ya fara duhu,alamun magriba ta kusa,ga yunwa da take ji saboda ta kasa mayar da hankali ga abinci,a hankali ta ɗago zoben gold ɗin hannunta, wanda ba zata manta ba Abban ne ya bata da hannunsa a wata tafiya Dubai da ya yi,ita kaɗai ya yi wa tsarabar irin zoben,ta shafa kunnenta,ɗan kunnen da Ummeey ta kawo mata ne a wata tafiya Umrah da ta yi,su ne abubuwa na ƙarshe da take da su,a lokacin da tana rayuwa a Spain tare da Arnold su take kalla take tunawa da iyayenta 

Amma a yanzu tana jin cewa lokaci ya yi da zata rabu da su ko da a ce bata son hakan,tana buƙatar ingantacciyar rayuwa ita da abin da yake cikinta,bata da komai,kuma bata da kowa sai wannan zoben da ƴan kunnayen,da su zata gina rayuwarta da na yaron da ya shiga masifar rayuwa da tangarɗa tun kafin ya shaƙi iskar duniya

Ta shafa cikinta a hankali,ta yi ɗan murmushi jin yana motsi,ta ce"kai kaɗai gare ni a duniya yanzu,ina addu'ar Allah ya da ka zame min sanyin idaniya,ka zama duk abin da na rasa, ka share min hawaye, mamanka tana sonka ka ji masoyina, Allah ya kawo min kai lafiya"ta ƙarasa magana yana goge hawaye, zuciyarta tana sake karyewa


(To fa! yanzu labari zai sake sauya salo!)




#Nusy_bee