ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

13

by @gureenjoh

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO


✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN 

(GUREENJOH)


@Gureenjo on Arewapen

@Gureenjih6763 on Wattpad 


ADABI WRITERS ASSOCIATION


TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. 


GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.



*SHAFI NA GOMA SHA UKU*


KAUYEN CHEDIYA

KARAMAR HUKUMAR TSAFE 

ZAMFARA STATE

NIGERIA 


Duƙunkune suke a ƙasan gadon su rai huɗu ƙarar harbe-harbe da ya karade garin shi ya saka suka dunkule tamkar kifin gwangwani wuri guda ko motsin kirki babu mai kataɓus na yi.


"Inna fitsa..."

Da hanzari mahaifinta ya sa hannu ya danne mata baki, da hannu wacce ta kira da Innar tayi mata alama da ta yi a wurin jikinta na rawa ta saki fitsarin haka har gari yayi haske tarrr suna cikin wannan yanayi sai da suka ji motsin mutane kan suka fito jiki duk gajiya.


Hawaye Inna da Baba suke share wa har yaushe wannan fargaba zai bar su? Har yaushe za su kwanta a kan gadajensu su yi bacci cikin salama?


Babu mai iya cewa uhmm ko uhmm inna ta kama yanmmatan da duk suke ɗigar fitsari ta musu wanka, a lokacin Baba yayi alwala ya gabatar da sallah cikin kuka da roƙon ubangiji na ganin karshen musibun da suke fama da shi a kauyen na 'yan bindiga.


Bayan sun yi wanka suka yi sallah inna ta fara kokarin haɗa wutar da za ta dama musu kunu.


Baba kuma wani kullin leda ya saka a gabanshi yana aikin kallo zuciyarshi babu abin da bata raya wa.


"Atika! Yau ne fa muka yi da mutanen nan"


Inna da ta gama ɗora ruwan zafin ta dawo ta zauna kan wani dutse gabanshi idanunta na kan yanmatan guda biyu da babbar bata haura 16 ba karamar ce za ta yi goma sha uku zuwa sha hudu ta ce


"Malam ko za mu mayar musu da tallafinsu, ni dama tun chan hankalina bai kama ba wallahi sai in ga kaman duk wuya duk tsanani gwara a ce suna a gabanmu"


Ya girgiza kai 

"kin san lamarin mu ƙara ta'azzara yake Atika, gomnati babu ruwansu azzaluman nan a kan idon iyaye suke haikewa yara kananun wallahi ba zan iya jurar ganin abin ya zo kan 'ya'yana ba, ko babu komai sun yi alƙawarin saka su makaranta kuma su ma za su samu rayuwa mai kyau ba kaman mu anan ba"


Numfashi ta sauƙe hawaye na zuraro mata, rayuwar da suke ciki ya tsananta, babu sakewar zuwa gona ko kasuwa, makarantu a rufe ana fargabar tura yara, idan kana so ka yi ko noma ne sai ka je ka yi yarjejeniya da su rabi da kwatar abin da za ka shuka nasu ne kwata ne naka shi ma a wulakance za su bar maka.


Rayuwa duk inda suka juya babu daaɗi a kauyen, wani abu da mutanen mu kuwa gani suke nan ne gidansu nan ne marayarsu, nan ɗin ne dolensu duk wuya duk tsanani ba za su iya barin garin ba.


Sallama da aka doka a kyauren gidan ne ya dawo da dukkansu tunanin da suka shiga.


Baba ya amsa wasu mata biyu sanye da hijabai har ƙasa suka shigo cikin fara'a suka shiga gaisawa da jajen abin da suka samu na Shigowar 'yan bindiga jiya kauyen.


"Idan ba matsala za mu wuce yanzu saboda kar su san da zuwanmu"


Hakane ko baƙo ne ya shigo gari akwai awannin da idan ya haura zai iya shiga cikin hatsarin kidnapping don waennan mutane suna da idanu da kunnuwa cikin gari.


"Ma'u, Jidda yehe hose kare mun un dillah, Allah Lamido renu mun wanne mun barka"

(Ku je ku ɗauko kayanku ku zo ku tafi, Allah ya tsare ya kiyayeku duk inda za ku shiga yayi muku albarka)


Miƙewa suka yi jiki a sanyaye zuwa ɗakin su kowacce ta ɗauko 'yan tsommokaranta cikin ɗankwali.


"Inna... Tafiya za mu yi mu bar ku?"

Jidda ta faɗa sai kuka, Innar ma kuka take amma da gaskiyar malam barin kauyen nan shi ya fi musu alkhairi.


Rako su suka yi har jikin wata coaster ashe ba su kadai ba ne 'yan mata sun yi sha biyar kowacce da kayanta a ɗankwali suma suka bi ayari suka hau suka zauna a tare suna rungume juna.


Haka sai da suka haɗu tass kan bayin Allahn nan suka yi musu sallama suka fice da yaran daga garin.


Tafiya iya tafiya suka yi, da suka yi nisa dai an tsaya an ba su pure water da bredi amma daga Ma'u har jiddah kowacce na rike ne da nata.


Ita Jidda ji take a ranta cewa wannan tafiya ba daidai ba ne, duk nan iyayensu sun ba da su ne don su yi rayuwa mai kyau ba kaman na kauyensu ba amma tana jin uneasness akan tafiyar, mutanen sun ce daga wata ƙungiya ne na malamai da suka kafa don taimakon irin yaran garuruwan da zaman lafiya yayi musu karanci, za su yi karatu kuma za'a koya musu sana'ar hannu da har za su iya dogaro da kansu, za su na zuwa gida duk bayan wata uku, har form sun cike.


Jidda ta ɗaga idanunta ta kalli garin da suka shiga da bata sanshi ba, ta dai san akwai tarin mutane kwarai, akwai kasuwanci na ta tafiya, akwai hayaniya sossai anan ma sun tafi sossai kan suka isa wani gidan sama a cikin wani unguwa dake lungu sossai.


"Ku sauƙo"

Matar da ta zago ɓangaren su ta faɗa suka fara fita ɗaya bayan ɗaya har suka kare su goma sha takwas.


"Mu je"

Wasu maza na daga bayansu matan sun shige gaba har kofar gate ɗin suka buga aka buɗe ganinsu ya sa mutanen suka matsa suka shige ciki, Jidda na bin halittar da bata taɓa ganin irin sa ba da ido, sun fi yanayi da yadda ake fasalta samudawa ga tsawo ga kwanji, bouncers ne da ke gadin gidan, gate uku suka wuce da irin waennan mutane kan suka shiga cikin matsatsen gidan, mata ne kusan duka suna ta hada hada, abin da ya fara buga zuciyar su Jiddah ganin yadda yan mata ke ta shaye shaye.


Ma'u ta damke hannun jiddah jikinsu na rawa.


Wani mutum ne ya zo ya lissafa su kan ya raba su gida biyar Allah ya taimaki su Ma'u ba'a raba su ba aka nuna musu inda za su shiga, suna shiga dakunan duk aka bi aka rurrufe da kwado hakan ya sake tsinka su.


Ma'u da ta fi Jidda jin tsoro ta fara kuka, Jidda taje ta na buga kofar amma har suka gaji suka fadi a wurin basu ji motsin komai ko kowa ba, kaman 'yan prison haka suke yashe a ɗakin jiddah maƙale jikin 'yar uwarta.


Sai dare aka kawo musu abinci babu wanda ya motsa har aka ajiye aka fita, Ma'u tace cikin dasashiyar murya.


"Jiddah tashi ki ci abinci, zama da yunwa ba shi ne mafita ba, dole za mu ci ko don mu samu ƙarfin fuskantar abin da zai je ya zo"


"kin san me suka sa a ciki? Ma'u su waye su? Meyasa suka rabo mu da iyayenmu da sunan taimako suka kawo mu nan suka zubar? Me za mu musu? Me ribansu?"

Ta ƙarasa cikin kuka sossai.


Ma'u ta share hawayenta 

"Koma menene za mu rayu jiddah, za mu tsere mu koma wurin su inna, ki ci abinci ba za mu mutu basu san halin da muke ciki ba"


Haka suka tura abincin ba don daaɗi ba, wani irin bala'i ne wannan an fita daga mai an faɗa wuta? Bacci ɓarawo ne kawai ya kwashe su, Washegari da safe aka kawo musu abin kari nan ma sun ci har lokacin kaman kace kule su ce chass tsabar firgita duk sun yi zuru zuru.


Sai da rana tayi kan aka zo aka tattare su suka fito wani parlor mai girma da kujera ɗaya jal, duk a ƙasa aka zubar da su suka tattakure musamman su da suka san junansu waenda suka fito daga chediya, manyan maza majiya ƙarfi ne zagaye da parlorn. Chan wani mutumi ya fito bayanshi mata ne wurin huɗu kowacce da wani irin shiga.


Jiddah ta gane ɗaya daga cikinsu itace ta sa hijabi har ƙasa suka yaudari iyayensu suka kawo su nan ba tare da sun san me za su yi ko me rayuwarsu ke ciki ba.


"Waennan su ne daga ƙauyen chediya J"


Ya kallesu da kyau kan ya zauna, a hankali yake pointing da hannu ana ware mishi har ya gama sorting.


"Waennan su za su mayar mana da kuɗin mu"

ya nuna su Ma'u da aka kaisu gefe.


"Waennan a yanzu su zama 'yan aike kan idanunsu su sake buɗewa, a zaɓi wasu cikin na farko a rabar kaya sun yi karanci irin wannan wurin manya"


"An gama J"


Ya miƙe ya fita, matan nan ne suka sake tarkata su Ma'u zuwa wani daki mai gadaje kaman na boarding, Jidda ta tashi da gudu za ta bi Ma'u wani ya riƙota ya wullar ta bugu da ƙasa ta sake rushe wa da kuka.


"Me muka muku? Gida muke so gida za mu je ku bar mu mu tafi..!"

Ihu take da kuka ganin ba zata yi shiru ba ya gwabeta sai da tayi karamar suma ta farfado, a wuya suka ɗaga ta zuwa wani daki na daban da gadaje irin na boarding, a ciki akwai wata babbar mata ɗaya rike da bulala, ita ta zare mata idanu tayi shiru.


"Ba'a mana taurin kai anan don a take za ki karɓi hukunci, ana cewa ku yi za ku yi ku bari za ku bari, ba'a kananun maganganu ko hira mai yawa idan na kama daya daga cikinku da karya min doka za ku ga abin da zan muku."


Kowacce ta maƙale a bonk da aka ajiye ta, har lokacin Jidda kuka take na rashin mafita.


Da dare aka fitar da su don haduwa ake a ci abinci, a lokacin ne Jidda ta ga Ma'u da sauri taje ta riƙe hannunta.


Ma'u ke duba jikin Jiddan cikin diriricewa take cewa

"Babu abin da suka miki? Basu miki komai ba?"

Girgiza kai Jidda tayi ta riƙe ma'un 

"basu yi mini komai ba ke fa?"


Ma'u ta girgiza kai amma hawaye na zubo mata, a kwakwalwarta take ganin ɗaya daga cikinsu da bayan an shigar da su ɗaki aka zo aka fita da ita kusan awa uku aka dawo da ita aka jefar kan gado jikinta duk jini.


A lokacin sauran 'yan matan suka tsorata don abin da iyayensu suka guda ne yake shirin faruwa a kansu ɗaya bayan ɗaya...


"Ku wuce ku ci abinci"

Ihun da aka yi musu ya sa suka nufi gaban tray ɗin da sauri suka zauna suka shiga ci, kowacce da abinda take tunani.


Suna gamawa aka sake raba su sai da Jidda tayi kuka.


Rayuwa ya zama babu daaɗi, duniya ta ishe su sun gaza sakewa yayinda wasu daga cikinsu har sun fara sakewa, akwai mata a gidan dayawa amma kaman sashe sashe ne, na kusa da su suna da wani buɗewar ido, su suka shiga jikinsu Jidda suka zama ƙawaye.


Suna nuna musu gwara su karɓi rayuwar nan kawai don ba za su taɓa fita ba kila har abada.


"Babu wanda ya taɓa tafiya?"

Tambayar Jidda ya zo musu kaman daga sama 


Ɗayar tace 

"Babu sai dai gawa, sai kuma idan sayar da ke aka yi"


Jidda ta sake cewa 

"Sayarwa? Kaman shanu ko rago?"


Dariya suka yi basu ce komai ba suka fice.


Ma'u ta fashe da kuka.

"Jidda rabon mutuwarmu ne kawai ya rabo mu da chediya, ya zamu yi? Ina za mu sa rayuwarmu?"


Sai da suka ci kuka aka zo aka watsar da su, a daren Ma'u ta ga tashin hankalin da bata taɓa gani ba.


Tana shirin kwanciya aka zo aka ɗauketa wata mata ta mata wanka aka shiryata da kyau kan suka ja ta zuwa wani ɗaki a cikin gidan.


Matar ta zare mata ido fuskarta babu digon fara'a tace 

"Kwanta!"

Kwanciya Ma'u tayi ta buɗata ta yi examining ta tabbatar budurwa ce Dukda fusge fusge da Ma'u ke yi bata kula ta ba sai da ta gama ta bata wani drinks.


"Karɓi ki sha"

A razane tace 

"Me..me? Menene?"

"Kin sha ko sai na tsinka miki mari?"

Ƙin sha tayi kan ta gama girgiza kai ta ji sauƙar marin da ya kusa sumar da ita.

"SHA..."

Hannunta na rawa hawaye na zuba mata ta karɓa ta shiga sha tana gamawa bata yi ko minti ɗaya ba ta fara ganin duniyar na juya mata.


A take ta bugu jikinta ya sake matar ta kama dantsen hannunta ta fito da ita tana layi ta jefawa wani bouncer ya ɗauketa sai mota ya ja ya fice daga gidan.


Ba'a dawo da ita gidan ba sai Washegari, Jidda ta fito karyawa tana ta neman Ma'u bata ganta ba, idanunta ya sauka kan 'yan ɗakinsu da sauri ta nufe su tana tambayar su.


"Ina Ma'u?"


"An fita da ita tun jiya da daddare bata dawo ba"

A firgice Jidda ke cewa 

"Ina aka kaita? Ina aka ce taje?"


Kan su yi magana sai ga Ma'u na shigowa kayan jikinta duk jini ne, tana tafiya tamkar za ta kifa saboda layi sam kallo daya za ka mata ka san bata cikin hayyacinta da gudu Jidda ta isa gareta ta riƙeta...


"Me ya sameki Asma'u? Me aka miki? Ina kika fito? Ji...ni?"

Duk ta firgice sai jero tambayoyin da ma wacce take yi wan ba jinta take ba.


"Innalillahi wainna ilaihi rajiun... Asma'u!!"

Ta fashe da wani irin kukan tashin hankali, wani bouncer ne ya zo ya ja ta...


"Ke kina da hankali? Yi mana shiru anan..."

Kan ya ƙarasa ta dankara masa cizo sai da hannunshi ya fashe ta koma wurin Ma'u da ta faɗi ƙasa ta ɗagota tana kuka da jijjiga ta a haukace tana tambayar me ya faru da ita?


Tsinka mata mari taji an yi ta rarumi flower vase ta jefa mishi a fuska sai ga jini a take wurin ya kacame, bulala ya zaro cikin bacin rai ya rufeta da duka ita kuma tana kare Ma'u tana ihun kuka don abin da take ji a ranta ya fi ƙarfin bulalar da ake yi mata...


Hayaniyarsu shi yayi alerming shuwagabannin gidan.


"Kai Shadow! Menene wannan?"


Wanda aka dakawa tsawar ya tsaya da dukanta.