JODAH

13

by @sadisakhna


 

 

______👑 *JODA* 👑_____ 

 

              

 

 

 

Na  

 

*Sadi-sakhna* 

 

Ƴar mutan Jama'are 

 

 

 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

 

 

 

@sadisakhna on Arewapen 

@SAKHNA03 On Wattpad 

*** on Whatsapp 

 

 

LITTAFI NA 1 

 

 

 

*Harƙa ta (13)*👑 

 

 

 

 

A can yamma da garin Tumbuktu babban birinin daular mali kuma inda fadar Sarki Mansa Fasih take. Tafiyar zira'i dubu daga garin zuwa cikin tsaunuka masu matuƙar duhu da ban tsoro.  

 

Wata matace take taka matakala tana hawa wani dutsi mai matukar duhuwa a gefensa,sunyi tafiya mai nisa kafin suka isa saman dutsen,a bayan wani baƙin bawa ne sanye da kayan bayi yana riƙeda jakar kayan amfaninsu. Shima kansa duk da yakasance namiji mai juriya da jarumta amma alamun gajiya duk ya nuna akan fuskarsa,inaga matar wacce take sanye da kaya na alfarma amma duk ta fita hayyacinta saboda halinda ta shiga na wahala. 

 

Tsugunnawa nayi tana haki da tari kaman kayan ƴan hanjinta zasu fito waje,maganar da bawan yayi ne yasa ta daga ido ta kalli inda ya nuna. 

 

"Ranki ya daɗe inaga mun iso inda zamuzo,domin ga can alamar tafin hannu a jikin wani dutse da alama ya nuna ƙofa ce" 

 

Saurin tashi tayi ta nufi wajen domin ta tabbatar,gabaɗaya ta manta da halin gajiyar da take ciki. 

 

Shashshafa wajen tayi tana nazari,can saita fara dube dube ,idonta ne ya hango abinda take nema. Wani ƙoƙo ne akan wani dutse daga gefe. Wata wuƙa da aka yita da baƙin dutse ta ɗauka ta yanka tafin hannunta. Jini ne ya fito saita mulkeshi a hannunta tamkar fenti ta nufi baƙin ƙofar tasaka hannunta a jikin ƙofar. Girgiza ta farayi babu bata lokaci. Ja tayi da baya saida yagama kana ƙofar ta buɗe. 

 

Bayan hayaƙin daya wanju a wajen ya sheƙe tukunna ta ƙarisa baƙin ƙofar tana lekawa,amma kuma babu abinda take kallo sai duhu kawai. 

 

Ganin idonta babu abinda yake hangota yasa ta tura gangar jikinta zuwa cikin kogon dutsen domin tagane wa kanta abinda ke ciki. Duk da cewar zuciyar ta a tsorace take amma muradin ta nayin doguwar tafiya izuwa wajen bazai taba barinta taja da baya ba. Dole saita cika ƙudurinta tahakanne kaɗai zata kauda duk mahaluƙin da idanuwanta basason gani a wannan doron duniyar. 

 

Babu kowa a cikin kogon sai wasu irin abubuwa masu wuyar fassaruwa a kwakwalwa koda kuwa ido yagani ya aika mata da saƙonsu. 

 

Wata kwalbar idanuwan mutane ne a ciki,wata hannu wani zuciyane an ɗaure ta da wani baƙin zare a cikin ruwa. Abubuwa dai kala kala. Gefe guda kuma bangaren abubuwa masu rai ne,wasu halittun kaman maciji,shanshani da kunama mutum zai iya ganesu amma hadda wasu irin halittu masu saka jiki kyarma idan yayi arba dasu. Wata kwalbar ɗauke da tsutsotsi baƙaƙe suna yawo zululu......abindai babu kyan gani.  Sannan haka bangaren tsirrai suma masu wuyar fassaruwa duk akwaisu. Wata bishiya ta kallah a gefe komai na jikinta baƙine,kama daga ganyenta,bawon jikinta harma da jijiyoyin ta. Sannan ƙasa maimakon kasa gawar mutum ne a jiki tatsaga ta fito. Gawar ta yamutse ta bushe duk jijiyoyin bishiyar baƙaƙe sun shishiga duk wata ƙofa dake jikin gawar suna zuƙe abinda yake jikinta a matsayin taki. 

 

Batakai ga gama kallon abubuwan ba kanta ya juye ta durƙusa a wajen,muryar wani mutum taji wanda hakan yasa ta juya inda take jiyo muryar. 

 

Gajerene sosai da za'a iya ƙiransa da wada,amma kuma bashida siffofi irinna wadannin. 

 

Tsohone yana dogarawa da wata sanda,sannan baƙine yanada cikar farin gemu da tsayi,domin har saida ya kusan taba ƙasa kasancewar bashida tsayi. 

 

Baƙaƙen kayane a jikinsa ko nace tsummokara,domin babu inda bai yage ba a jikin kayan. Bayan ya ƙariso inda take wani shu'umin murmushi yayi kana yace. 

 

"Haƙiƙa ina maraba da wannan baƙunci dana samu daga babbar baƙuwa Denti Shuwara mata ga sarki mansa Fasih. Babban sarki kana hamshaƙi da babu yashi a kaf faɗin wannan nahiya. Zanso sanin mai yake dafe dake da har kika yi wannan doguwar tafiya mai cikeda ƙalubale kikazo fadata ni Sarkin Masu maganin Bori na nahiyar nan. Wato Sarki Duguzah.  

 

Duk da cewar nafara jin labarin abinda kikeso da bakin dan aiken Bararojiya Zarha,wacce itace ta sanar dani zuwanki,kan kina neman wata biyan buƙata daga gareta amma sai ta kalli abin yafi ƙarfinta bazata iya ba. Ina mai sanar miki dole zaifi ƙarfinta,domin a bangaren irin masu maganinmu wanda muka haɗa da bada magani da kuma aiki da baƙaƙen aljanu,bakowane yake iya shiga tsakanin ƙaddara mai ƙarfi ba kamanta Magajin sarki mansa sai irinmu" 

 

Tashi tayi daga tsugunnen da take tana kallon Sarki Duguzah kan ya fayyace mata mai yake nufi da Ƙaddarar Keita hammar tanada karfin da baza'a iya yimasa komai ba? Wannan ai zancene. 

 

"Abinda kike ji hakane mai girma denti shuwarah,Bazaki iya kashe Keita Hammarou ba,domin akwai wata ƙaddararsa mai ƙarfi da har yanzu bai haɗu da ita ba tukunna,ni kaina nakasa gane menene domin tsohuwa Ayyana ce ta bata ruwan Tuffal tasha lokacin da take ƙarama,wannan ruwa shine tsumin magani na ƙarsge da ta haɗa a rayuwarta,kuma ya yi sanadiyyar mafiya yawan shekarunta,saboda abinda uban yarinyar yayi mata yasa ta sadaukar da wannan tsumi ga yarinyar kasancewar tanada matsalark ƙwaƙwalwa. To wannan magani yayi mata magani mai matuƙar tasiri sannan ƙarfinsa yasa ya boyeta daga dukkan hatimin kowanne mai bugun ƙasa. Koya zakayi baxaka iya samota da ƙarfin tsafi ba,har sai idan ta bayyana lokacin da kowa zai ganta sannan muma zata bayyana garemu. . Kuma ina mai sanar miki wannan boyayyar ƙaddara tanada matuƙar haɗarin dazata taka matsayi sama daku ko kunso ko kunƙi,sannan zatazo cikin wannan daula batareda ɗayanku ya iya katange ta ba. Saidai akwai mafita........." 

 

"Menenee sarki Duguzah dan Allah ka sanar dani naji,ni koma menene zaizo batashi nakeyi ba,burina shine wannan yaro da yayi bake bake akan kujerar mulki ya hana ɗana yasamu koda kallo mai darajane daga mahaifinsa. Sannan abin takaici idan naje wajen masu magani saisu ce wai babu abinda zasu iya masa,domin ƙaddararsa ce ya rayu akan mulki,idan suka ja da sai sun kaudashi to su kuma zasu mutu." 

 

"Wannan zance haka yake tabbas,yanada ƙaddara mai ƙarfi da kowa yaja da sai ya hallakashi to kuwa shine zai mutu. To amma maizai hana bazamu kashe gangar jikinsa ba,amma kuma zamu lalata ta ta yanda bazata iya mulkinba. zai zamo gashi akan mulkin amma kuma dole wani ne yake gudanar da mulkin bashi ba." 

 

"Bangane mai kake nufi ba sarki Duguzah" 

 

"Basai kin gane yanzu ba amma sannu a hankali zaki fahimta kuma aikin zai ƙayatar dake sosai. Kedai kice kin yarda dani kuma kin miƙamin ragamar komai" 

 

"Idan da ban yarda dakai ba bazan zo nan wajen ba sarki Duguzah kaidai kayimin aiki wanda bazan ji nayi asarar karfina da lokaci na ba wajen zuwa nan gurin" 

 

"Wannan ɗin baya cikin tsarina, zan fara aikin haɗa magungunan daza'ayi amfani dashi,karki damu maganina ba baki zanyi kije kisaka ba, idan na tashi aika magani zan aiki aljana sanayah taje ta aiwatar aiki kedai kawai saidai kiga sakamako yana wakana." 

 

"Yawwa hakan yayi saboda kar a garin sakawa asirina ya tonu. To yanzu ya zamu dunga haɗuwa domin gaskiya banajin zan sake samun damar fitowa nazo nan wajen. Saboda wannan ma saida nayi dabaru ba kaɗan ba kafin nasamu fitowa" 

 

"Wanann ba matsala bace,zan baki wani Alli a duk lokacin da kikeson zuwa cikin kogonnan ki zanashi a jikin bangon ɗakinki,kofa zata bayyana kawai saiki shigo. Zan fara aikin amma ba nan kusa ba,sai waccar bishiyar tagama zuke jijiyoyin gawar can ta haifi ɗa tukunna,da wannan ɗan zanyi amfani na haɗa maganin. Shekara Ashirin kenan tunda na cirota daga duniyar aljanu ina dakon yin ƴaƴanta,tasha jinin mutane babu adadi kasancewar iskar nan wajen ba irin na inda take rayuwa bane. A jiya hadimina yabani albishir cewar zata fara ƙunsa ɗa a wannan shekarar ko ta gaba" 

 

"Shekara kuma sarki Duguzah,har shekara zan jira" 

 

Haɗe fuska yayi kana ya kalli inda Musso Shuwarah take. 

 

"Nida nayi shekara ashirin ina jira tayi koda aiki ɗaya ne nayi da wannan ɗannata,yazama cewa nine bil'adama na farko da yayi aiki da ita. Saboda itane na tare rayuwata ina zama a wannan wajen saboda tanason cikin tsaunuka da duhuwa. Sai kece bazaki iya haƙurin shekara biyu na zuwa uku domin nayi miki aiki da ita ba. Ki sani wannan aikin dazan miki kuɗi bazai taba biyana ba......." 

 

"To mai kakeso daga gareni kenan idan ba kuɗi ba" 

 

"Idan lokaci yayi zan sanar dake,amma ki sani tabbas cikar burinki ya kusa zuwa,dan saina maidashi fiyeda abin tausayi a cikin da'irar da dubban mutane suka kewayeshi sunayi masa bauta. Sai yazamo tamkar gawa da numfashi,domin sai yayi ta roƙon dama Allah ya ɗauki ransa da wannan rayuwa da zayyi. Kedai ki jinkirin wannan shekaru ƙalilan,zaki samu sakamakon da bakya tsammani daga wannan aiki da zamuyi" 

 

Ganin yanda yake kwaɗaita mata yanda aikin zai kasance,lokaci guda taji dukkan mafarkin ta da cikar burinta ya tafi kan wannan aiki daza'ayi mata. Domin ji take duk duniyar babu wani mahaluƙi daya kaita sa'a. 

 

Ƙara juyawa tayi ta kalli bishiyar,da sauri da ɗauke idonta,domin ji take kaman bishiyar tana janta itama zata zuƙeta.  

 

 

Zagayata takeyi cikeda takama,saida tayi hakan kaman na rabin sa'a kafin ta dawo ta zauna akan kujera tana kallon wacce ke zaunen ta sunkuya kaman zata shige cikin ƙasa. Yarinya ce da budurci yafara kawo mata baƙunta,domin bazata wuce shekara goma sha shida ba. Baƙace amma tanada diri da kuma zatin halitta mai kyau. 

 

Tsareta da ido Musso Lazeerah tayi kafin ta numfasa cikin taƙama da izzah. 

 

"Hazrah inaso ki buɗe kunnenki dakyau kiji duk abinda zan faɗamiki,akwai wani gagarumin aiki danake son kiyimin,sannan kuma aikine mai muhimmanci dayake buƙatar najikina wanda zan iya yadda dashi. Duk da cewar ke ɗin kina daga cikin ƙasƙantattu a dangina amma anan daya kasance kowa barene a gareni ke kaɗaice jinina dazan amince miki da wannan aikin. Amma.......ko kaɗan banason nasamu matsala shin kin yarda zakiyi duk abinda na umarceki bazan samu matsala ba" 

 

Rawa jikinta yafara cikin tsoro da fargaba,tashi tayi daga zaunen da gurfana kaman mai neman gafara tace. 

 

"Ina rayene domin ki umarce ni da abinda kikeso nayi miki ya shugabata,kuma nayi alƙawarin ko menene zaki sakani zan aikata kuma bazan baki kunya ba" 

 

"Yayi kyau naji daɗin jin hakan. Zan sakaki daga cikin jerin matan dazasy shiga gasar zaben gimbiyar Daular mali ta gobe,wato matar keita Hammarou,wanda za'ayi nan da shekara biyu idan yacika shekara ashirin a duniya. Na yimiki wannan bayanine saboda inaso ki fara shirye shirye tun yanzu kafin lokacin yazo. Takun ki ƙasaitarki haɗada Matsayi inaso ya sauya,ta yanda zakiyi zarrah a cikin mata da dama. Sannan akwai wanda na ɗauka zasu koyamiki halayya irin ta ƴaƴan masu mulki,wanda zakiyi amfani dashi ki jawo hankalin sa kiyi nasarar sace zuciyarsa. Wannan shine mataki na farko dazakiyi idan kika shiga gidansa,daganan zaki fara bani duk wani bayanai na sirri akansa,Maganar haihuwa dama bata taso ba,na daɗe da katse mazakutarsa,domin kebawa da mata da zayyi ya haihu wannan shine yake nuna dakatawar samun dama ta,domin ko baiwace ta haifa masa ɗa zai iya yin sarauta idan dai jininsa ne. To yanzu babu wannan damuwar,kawai aiki zamu fara. Daga nan idan muka cimma burinmu muka hankaɗar da gwamnatin sa data Kamarou Zanyi amfani da ƙarfin da nake dashi na samun gwamnoni mafiya rinjaye a Bangarena sai a ɗora Sunjata Akan mulki an ne Alkawarin danayi miki zai kasance,zan aura miki Sunjata kuyi mulkin ƙasar nan kuma na tare duk wata matsala dazata biyo baya. 

 

Lokaci ya ƙure tashi kije akwai wanda sukazo zan gana dasu" 

 

Da sauri cikeda biyayya jiki yana rawa Hazrah tabar bangaren Musso Lazeerah izuwa ga masauƙin da aka bata na alfarma,wanda a lokacin baya a cikin bayi ɗakinta yake saidai ba'a haɗata da bayin ba ɗakinta daban,sannan bata saka kaya irinna bayinba. Yau sati guda kenan da musso Lazeerah ta aika a ɗauko mata ita da daular ghana, mahaifinta ɗan ƙanin baban Musso Lazeerah ne wanda yake kan mulki,soyayya tasakashi auren baiwa kokuma dai ƴar ƙyauye yazo da ita gidan,babu irin wahala ƙyara da hantara da mahaifiyar Hazrah bata sha, Haka Hazrah ta taso bata samun taushi daga wajen kowa sai mahaifanta kaɗai. Ana cikin haka mahaifinnata ya rasu a lokacin tanada shekara Uku, Abin sai ninkuwa dayayi,kullum itada mahaifiyarta in abune na aiki da wahala sune zasuyi,banbancin su da bayi kawai su basuda uniform irinnasu sannan dogarawa da bayi basa hantartarsu saidai ƴan gidan.  

 

Lokacin da wannan ƙudurin yazo kan Musso Lazeerah ta duba dukka dangi babu wata ƴa mai ƙaramin shekaru kuma wacce zatayi mata aiki irin wannan ba sai Hazrah. Hakan yasa ta aika aka kawomata ita,babu tambayar ko tanaso ko bata so haka ta rabata da uwarta wacce ba cikyakykyiyar lafiya ba saboda halin rayuwa da take ciki. 

 

A sashen bayi aka ajiyeta sai yau ɗin aka bata ɗaki lafiyayye daga cikin ɗakunan sashen musso Lazeeran. 

 

Saida ta ƙarewa ɗakin kallo kafin ta zauna akan gadon tana jin laushinsa. Wani murmushi shu'umanci Hazrah tayi kafin tace cikin murya irin ta ƴan duniya. 

 

"Musso Lazeerah kenan haƙiƙa kinyi babban kuskure da har kike tunanin Tsutsar da kuka raineta da kanku saboda tsanin azaba tazama maciji mai dafi kuma zata koma tazame miki wannan tsutsar. Saina sareki a inda baki taba zato ba,inna samu dama ba iya ke zan ruguza ba harda Daular ghana gabaki ɗaya. Ɗan hakin da kuka raina yasamu abinci saura ci ya saura ya girma duk ya tsone muku ido" 

 

Bayan tafita zakadiyarta ce ta kalleta kana tace. 

 

"Ranki ya daɗe ki gafarceni idan nayi miki katsalandan a lamurranki amma zata auri keita Hammarou kuma kixo ki aura mata Ƙaramin shugaba,wanda take sa'arsa a haife,bakya ganin kaman za'a cutar dashi?" 

 

Wani murmushi tayi mai ɗauke da ma'anoni da dama,Shayin Koren ganyen shayin da take sha taƙara kurba a hankali ta ajiye kana tace. 

 

"Hmmm zulaika kenan, Ai ba budurwa ba ko wacce kakanninta basu kasance dukka sarakai bane,sannan ta gaji ɗaukaka,tun tashin ta an killace ta a gida ana shayar da ita ilimin zama sarauniya,duk wanda yakalleta to lallai yasan ta amsa sunan ta sarauniya. To idan ba irin wannan macen ba bazan aurawa ɗana Sunjata mata ba. Inaga kuma wacce ɗan maƙiyita ya buɗeta a  kwali, itama kanta tsatsonta a gurbace yake da bauta,sannan ita kanta ko a baiwar gidan keita Sunjata bazan turata ba ballantana kuma mata .......kawai dai tagama abinda na sakata,in tayi sa'a na samu wani mai matsayi na bata,kuma ta cire uwarta daga halin da take ciki. Wannan idan tayi abinda nasakata mai kyau kenan" 

Tofah......... 

 

Kallon takardar daya miƙa masa yayi cikeda giramamawa yana dubawa. 

 

"Ya mai girma mai nasara ban gane mai wannan ɗin yake nufi ba?" 

 

Keita Hammar ya faɗa yana sake duba fatar dakyau wacce aka jemeta ta zamo tamkar takarda kuma akayi mata ado da zinare. 

 

"Bazaka fahimta ba amma idan kaje da sannu zaka fahimta,wannan itace Jarrabawar ka ta farko kuma mafi girma na zamowarka Sarkin Daular Mali,Banine na zaba ba manyan alƙalai ne suka zaba,ni kaina kasani saida nayi tawa jarrabawar naci tukunna kafin nazamo sarkin wannann nahiya. Dan haka kayi shirin yin wannan jarrabawa daga yau,kuma ina dakon sakamako mai kyau daga gareka nan da shekara Biyu masu zuwa,nasan kanada ilimi da hazaƙa,to amma kasani wannan kaɗai bazai fishsheka ba dole saika haɗa da Juriya,ta hakanne zaka zamo wayayyen sarki kuma wanda yasan halinda jama'arsa suke ciki,ba iya mai faɗin rai ba kaɗai da ɗagawa. Kaje ina jiran isowar nasararka nan da wannan lokaci idan Allah yakai ranmu" 

 

"Ƙarewa takardar kallo yayi,tabbas yafahimci ta mecece,to amma mai yasa sai ta wannan hanyar za'a jarrabashi,anya kuwa abun bayyi tsauri dayawa ba,ya tabbata akwai hannun wani acikin wannan lamari mai wuyar fassaruwa. Inkuwa hakane to yazama dole ya buɗawa idanuwansu ƙasa kaman yanda yasabayi,akan matsayinsa bazai taba yarda wani ya gifta ta gabansa ba,dolene ya nuna cancantarsa kota halin ƙaƙa.  

 

Damƙe takardar yayi kafin ya juya yabar fadar mahaifinnasa. 

  

 

 

Sadi-sakhna ce ✍🏼 

 

Comment  

Like  

Share  

Follow