SAUTIN KARSHE

Chapter 5

by @amanarcool323

Aliyu yana dawowa daga masallaci ya yi wanka, a gaggauce ya canza kaya, hankalinsa na Asibiti. Ya gaza kiran wayarsu balle ya ji yaya a ke ciki, saboda faragaba.
Sai da ya fita ya je ya nemo aron kuɗi, saboda biyan kuɗin gadon da aka ce zai biya, da 'yan sauran buƙatu.
Ya dafa ruwan zafi ya zuba a flask ya nufi Asibiti. A hanya ya tsaya ya saya musu  koko da ƙosai, ya haɗa musu da biredi sannan ya ƙarasa asibitin. Yana shiga a reception ya haɗu da likitan da ya duba su ya fito. Da alama lokacin aikinsa ya fita tafiya gida zai yi. Cikin sakin fuska likitan ya miƙa wa Aliyu hannu suka gaisa, yana faɗin 
"Jiya kuma har aka yi aikin aka gama ba ka dawo ba"

Aliyu ya ce "Na je gida ne, saboda babu kowa kuma mamanta ta taho, ina fatan dai tana lafiya?"
"Yes Alhamdilillah, cikin ikon Ubangiji mun yi nasarar yi mata aiki tun a daren jiyan komai lafiya, Yanzu haka tana nan an dawo da ita ɗakin hutu, an ba ta gado, in sha Allah nan ba da jimawa ba za ta farka". 

Cikin farin ciki Aliyu ya ce "Alhamdulillah, ma sha Allah, sannu da ƙoƙari likita muna ƙara godiya Allah ya saka da alkhairi. Yanzu wane ɗakin aka mayar da su?". 

"Babu komai, godiyar ta isa haka Malam Aliyu, ɗakin da suke yana nan idan ka miƙe corridor nan za ka ga ɗaki mai lamba goma sha uku, suna nan a ciki" godiya sosai Aliyu ya yi masa, sannan suka yi sallama ya nufi ɗakin. Zuciyarsa cike da farin ciki ya tura ƙofar ɗakin ya shiga da sallama. Inna na zaune da carbi a hannunta, idanunta a fure tana gyangyaɗi, tana jin motsin buɗe ƙofar ta buɗe idonta da sauri ta ɗago tana kallon ƙofar. Ganin Aliyu ne ya sa murmushi ya bayyana a fuskarta, "Gadanga kai ne?" Ta yi maganar tana ƙara gyara zamanta. Aliyu ya ce "Eh Inna, barka da safiya, da fatan kun tashi lafiya? Ya mai jikin?". Ya yi maganar yana kallon Ma'u dake kwance kusa da Inna tana bacci. 

Inna ta ce "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, mai jiki gata nan Alhamdulillah an yi aiki lafiya, ɗazu da asuba suka dawo da ita nan ɗakin". Aliyu ya ce "Ma sha Allah, Allah ya saka musu da alkhairi"

Ya ƙarasa gaban gadon da aka kwantar da Abida, jikinta lulluɓe da koren zani na asibiti, fuskarta ta ɗan rame saboda wahalar da ta sha. Ya tsura mata ido yana kallon yanayin fuskarta, haka kawai ya ji jikinsa ya yi sanyi. Ya juya ya kalli Inna, sannan ya sake kallon Abida, ajiyar zuciya ya sauke, ya ce "Allah ya baki lafiya my lovely daughter". Ya yi maganar yana kallon wata ƙaramar ƙofa da yake jin motsin ruwa a ciki, ko bai tambaya ba ya san toilet ne, kuma yana kyautata zaton Halima ce a ciki, barin wajen ya yi ya koma kusa da Inna ya zauna, Inna ta ce "Ai ka kwantar da hankalinka in sha Allah za ta samu lafiya, tunda har an raba ta da wannan mugun ciwon, Allah dai ya biya su da gidan aljanna, har fa magunguna kyauta suka bayar da su". Aliyu ya dubi Inna ya ce "Allah ya sa hayyu ya ƙayyum, ai sun yi taimako sosai" ta amsa da "Amin" tana faɗin "Jiya babu wanda ya rintsa a cikinmu, hankalinmu bai kwanta ba sai da muka ga an yi aikin nan lafiya an fito da ita". Ya ce "Ai dole ne Inna. Ai yanzu na haɗu da likitan ya yi maganar yana kallon Ma'u ya ce "Ya kamata idan yarinyar nan ta tashi ta koma gida ta yi girki, sai ta zo muku da shi". 

Inna ta ce "To shikenan, bari har ta farka sai ta wuce gidan" yana nan zaune Halima ta fito, gaishe shi ta yi, sannan ta nemi guri ta zauna suka ci gaba da hirara sama-sama. Ƙarfe takwas da rabi Ma'u ta bar asibitin, ta tafi gida ta ɗora musu girki.

******

Sudais ne zaune a ɗakin Mammy ya zo gaishe da ita, bayan sun gaisa ne ta dube shi da kyau, fuskarta babu alamar wasa ta ce "Sudais" ya ɗago a hankali ya kalle ta, yanayin fuskarta ya tabbatar masa da magana ce mai muhimmanci take son yi da shi. "Na'am Mammy" ya amsa yana tsare ta da ido. 

Mammy ta ce "Ina son ka bani hankalinka da nutsuwarka, domin magana nake son yi da kai mai muhimmanci". Gyara zamansa ya yi, ya ce "To Mammyna ina jinki". Ta ce "Yawwa, dama magana ce nake so mu yi akan Ilham, Sudais bana jin daɗin abin da kake yi wa yarinyar nan. A tunanina ko da ba ka sonta da aure ai za ka sota a matsayinta na ƴar uwarka, sai dai kai na lura kwata-kwata ba ka wannan tunanin, na rasa me yake damunka, wallahi Sudais na yarda da son da yarinyar nan take yi maka ba ƙarami ba ne, ka duba irin samarin da suke sintirin zuwa wurinta amma ta ƙi kula kowa. Sudais duk zaman da yarinyar nan take zuwa ta yi a gidan nan ni na san saboda kai ne, anya kana ganin Uncle ya cancanci haka daga gare ka?". 

Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ce "Mammy, ba wai bana son Ilham ba ne, ke kanki kin san yadda nake ƙaunar Zahra da Faruk haka nake ƙaunar yaran Uncle, kawai dai yarinyar ta zo mini da wani shirme ne, kuma kin san ni ba biye mata zan yi ba". Mammy ta ce "Cewar da ta yi tana sonka shi ne shirme? Sudais akwai fa aure a tsakanin ka da ita. Kuma dalilin da zai sanya mace ta ajiye ajinta da kunyarta ta iya nuna wa namiji soyayya ai ka san ba ƙarami bane". 

"Please Mammy, don Allah ki bar wannan zancen, taya zan iya auren Ilham? Yarinyar da nake yi mata kallon ƙanwata. Ni dai dan Allah ki yi haƙuri, ni wannan harkar soyayyar ce gaba ɗaya ba ta gabana"
Sudais ya yi maganar yana kawar da kansa gefe. "Na shiga uku ni A'isha, Sudais soyayyar ce ba ta gabanka ko dai Ilham ɗin ce ba ta gabanka?". Mammy ta tambaya tana kallonsa. "Gaba ɗaya matan ne ba sa gabana, Mammy don Allah a bar zancen nan. Idan kin amince mini zan tashi saboda ina da baƙin da zan gana da su da safen nan". Murmushi Mammy ta yi, ta girgiza kai tana faɗin "Shikenan tashi ka je, Ubangiji Allah ya shirya mini kai" tsam ya miƙe, ya yi mata sallama ya fita. Bin bayansa ta yi da kallo. A hankali ta runtse idonta, tunanin mahaifinsu ne ya faɗo mata a rai, ƙara runtse idonta ta yi sai ga ƙwalla ta fara bi ta gefen fuskarta.

Sudais kuwa yana fita ɗakinsa ya koma ya yi kwanciyarsa, ba wasu baƙin da zai gana da su kawai ya faɗi haka ne don ya gudu saboda baya son zancen nan da Mammy ke yi masa. Tunawa ya yi da saƙon da Hanif ya sanar da shi, wayarsa ya ɗauka ya lalubo lambar Alhaji Sardauna ya kira. Duk da kasancewar safiya ce bugu biyu wayar ta yi aka ɗauka, cikin dattako mutumin ya yi sallama. Sudais ya amsa sallamar tare da faɗin "Barka da safiya Alhaji, ina fatan dai ban tashe ka a bacci ba?". Alhaji Sardauna ya ce "Barka dai Adam, ina fatan ka tashi lafiya?". 

"Lafiya ƙalau Alhamdulillah" 

"To ma sha Allah, ina fatan dai ka samu saƙona?" Sardauna ya tambaya. Sudais ya ce "Eh Alhaji, shi ne ma dalilin kiran da na yi maka". 

"To madalla, yanzu to ya za'a yi? Ina son mu zauna da kai in yi maka bayanin komai". Sudais ya ce "To shikenan ba damuwa, anjima zuwa sha biyu na rana idan kana da lokaci sai mu zauna ɗin". Sardauna ya ce "To ya yi, in sha Allah zan zo har kamfani na same ka".

"To ya yi Alhaji sai ka zo" daga haka Sudais ya yi masa sallama ya ajiye wayar, kwanciya ya yi yana tunanin maganar da Mammy ta yi masa, a fili ya ce "Astagafirullah, na aure Ilham na yi yaya da ita? Me zance mata? Shikenan tunda ban da hankali sai dare ya yi sai na je mata da wata guntuwar buƙata ta? Ai daga nan girmana za ta daina gani, sai raini ya biyo baya, ba Ilham ba ni bana jin akwai macen da zan iya wannan zubar da class ɗin a gabanta".

*****

Alhaji Sardauna ne zaune a ofishin Sudais, wani dadaɗan ƙamshi ne yake tashi a cikin ofis ɗin. A hankali ya cire gilas ɗin idonsa. Cikin girmamawa Sudais ya sake yi masa barka da zuwa. Sardauna ya gyara zamansa, sannan ya ce "Adam ya aka ji da jama'a?" Sudais ya ce "Alhamdulillah".

Sardauna ya ce "Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya yi jagora" Ya amsa da "Amin ya hayyu ya ƙayyum". 

"Adam dama ina son mu yi magana ne a kan wasu abokanaina da suke son ƙulla harkar kasuwanci da kai. To duba da yadda kake matsayin ɗa a wurina, kuma kullum ina farin cikin ganin yadda Allah ya ɗaga darajarka da ta wannan kamfani naka ya sa suka biyo ta wurina domin in shige musu gaba. Mutane ne masu mutunci da na daɗe ina hulɗa da su. Sun nuna mini sha'awarsu ta yin haɗin gwiwar kasuwanci da kamfaninka, shi ne na zo domin in ji ta bakinka. Saboda kai ne mai kamfani, kai ne mai yanke hukunci. Ni abin da zan yi shi ne in haɗa ku domin ku tattauna ku fahimci juna".

Sudais ya jinjina kai cike da gamsuwa ya ce "Ma sha Allah, ina godiya sosai Alhaji, Allah ya ƙara girma da sutura, ba damuwa, tunda har ka aminta da su, kuma ka san halinsu, sai ka haɗa ni da su. Allah ya shige mana gaba, ya sa alkhairi a cikin lamarin".

Sardauna ya yi murmushi, sannan ya ce "To ma sha Allah, in sha Allah zan haɗa ka da su, kuma ina da tabbacin za ka ji daɗin mu'amala da su, domin mutane ne masu gaskiya da amana". Sudais ya ce "To shikenan Alhaji, ina ƙara godiya sosai da sosai". Sardauna ya ce "To ya yi, ni zan wuce sai ka jini, Allah ya taimaka ya dafa muku". Sudais ya amsa da Amin. 

Miƙewa ya yi, ya miƙa masa hannu suka sake gaisawa, kafin ya fita daga ofis ɗin. Sudais ya fito domin yi masa rakiya, har bakin motarsa dake harabar kamfanin ya rako shi. Sardauna ya dubi Sudais ya ce "Adam wai ya batun aure ne? Har yanzu ban ji zancen aurenka ba, ka san fa ina bibiyar al'amurranku kai da sauran ƴan uwanka, saboda na ɗauke ku tamkar ƴaƴana. Duba da zaman mutunci da muka yi da mahaifinka Aliyu, mutum mai gaskiya da riƙon amana. Allah ya jiƙan Aliyu ya sa halinsa na gari ya bi shi". Take annurin fuskar Sudais ya sauya, tuno masa da mahaifinsa da aka yi. Cikin damuwa ya kalli Sardauna ya ce "Amin ya hayyu ya ƙayyum". 

Dafa kafaɗarsa Sardauna ya yi, ya ce "Sorry Adam, na tuna maka da mutuwar Abbanka ko? Ka yi haƙuri duk mai rai mamaci ne, in sha Allah Aliyu na aljanna". Ajiyar zuciya Sudais ya sauke yana faɗin "In sha Allah". 

"To ya batun aure ban ji ka ce komai ba?" 

Sosa kai ya yi yana faɗin "Alhaji matar ce ba ta zo ba har yanzu, amma in sha Allah za'a yi idan aka samu yarinyar da ta dace". Sardauna ya ce "To shikenan, Allah ya kawo ta gari, to ko na baka ƴata Zuhura ne ka aura?". 

Murmushi Sudais ya yi yana sunkuyar da kai ƙasa bai ce komai ba. "Kar ka ji kunya, idan ka samu lokaci sai ka zo gidana ka ganta idan ta yi maka shikenan sai a yi ƴar gida". Sudais ya ce "To shikenan Alhaji godiya nake, in sha Allah idan na samu lokaci zan zo". Sallama suka sake yi, sannan Sardauna ya shiga motarsa direbansa ya ja suka bar kamfanin. Sudais kuwa ciki ya koma yana wani murmushin da shi kaɗai ya san ma'anarsa.

****

Sai wajen ƙarfe ɗaya da minti goma Ma'u ta dawo asibitin. Da sallama ta shiga ɗakin fuskarta babu walwala. Ita a dole an saka ta aiki ta gaji, tana zuwa dire kular abincin ta yi ta zauna kusa da Inna tana faɗin "Wshhh Inna na gaji". Inna kuwa na can tana kallon Halima da ta tsura wa ƴarta ido ko ƙiftawa ba ta yi, Aliyu dake zaune bai daɗe da shigowa ba ya yi gyaran murya ya ce "Ai sai ki daina kallonta haka ko, ki nemi wuri ki zauna, tana nan da ranta ba mutuwa ta yi ba balle ki sumar mana a gurin nan" ya ƙarasa maganar kamar ba shi ya yi ba. 

Wata irin kunya ce ta kama ta, ta sunkuyar da kai tana kallon ƙasa, sai a lokacin ta tuna da Inna na cikin ɗakin, ita shaf ta manta tana fitowa daga banɗaki ta tsaya tana kallonta. Cikin jin kunya ta ce "Ma'u yaushe kika shigo?". 

Murmushi Inna ta yi ta ce "Halima daina jin kunyar nan ai kina da gaskiya, rabu da Gadanga shima ai haka ya yi, kin ma fishi jarumta". Da sauri Ma'u ta ce "Inna tuff, tuff, tuff, Allah ya ki yaye wannan tafi Yayana jarumta. Ita da ko a cikin mata irin saluɓaɓɓin nan ne masu....." Ido biyu ta yi da Aliyu, ai babu shiri ta duƙar da kai ƙasa tana mazurai. "Ke dai Ma'u Allah ya shirya mini ke, ni kam ban san ranar da za ki nutsu ki yi hankali ba. Hadda ki tambayi mai jikin ma ba ki yi ba kin bige da yi wa mutane shirme". 

"Allah Sarki Abidatu ɗiyar Asma'u Ma'u, Ubangiji Allah ya ba ki lafiya ya tashi kafaɗunki. Wallahi Inna tana raina fa, kawai dai naga uwarta ta tsura mata ido ne, ita mai ƴa, shi ne na bari idan ta gama ƙare mata kallo sai na yi magana". 

Shiru Inna ta yi ba ta sake bi ta kanta ba, ta ci gaba da hirarta da Halima, Aliyu barin ɗakin ya yi, domin idan ya ci gaba da zama a gurin zai iya dukan Ma'u. Ma'u ganin Aliyu ya fita nan ta fara halin na ta, ta ce Inna "Inna kin san jiya daga Aunty Halima har Yaya ba wanda ya yi bacci a cikinsu, kwanan zaune suka yi, Inna anya akwai tawakali a cikin zukatansu kuwa? Wannan rashin danganar har ina? Yasin ki yi musu nasiha su riƙa tuna cewar su musulmai ne, kuma akwai rai akwai mutuwa". 

"To ke ya aka yi kika san Gadanga bai yi bacci ba? Kodayake bari ya zo sai ki sanar da shi, idan kuma saƙo ne kika ba ni zan gaya masa". Inna ta faɗa tana hararta. 

"Don Allah ki yi haƙuri Inna, ai tsakanina daku ne" cewar Ma'u tana haɗa hannayenta. Inna ta ce "Wallahi kika sake yi mini wata maganar banza a gurin nan sai na sanar da shi abin da kika ce". 

"To na tuba, ba zan sake ba" daga haka Ma'u ta yi gum da bakinta. Don ta san tunda Inna ta rantse to za ta faɗa ɗin. Halima duk kunya ta ishe na abin da ta yi ɗazun, wajen ƙarfe uku Halima ta ce "Inna ina so zan je gida zuwa dare na dawo". Inna ta ce "Me za ki yi a gida Halima? Idan wani abin kike buƙata ki sanar da mijinki ya ɗakko miki mana, ke da kike jinya ina za ki je?" . "A'a Inna ai gaki nan, kuma dama hankalina ne ya kasa kwanciya da na ji zancen za a yi mata aikin nan, tun da an yi aikin lafiya, ina so zan koma gida sai na riƙa zuwa ina duba ta". 

"To Halima, ba zan hana ki tafiya ba, yanzu za ki tafi ne?" "Eh Inna, ina so na yi mana girkin dare ne". 

Inna ta ce "Ba damuwa, sai Ma'u ta bi ki ku tafi tare, idan kuka je ta shirya ta wuce makaranta".

Haushi ne ya kama Ma'u, ta ji kamar ta rufe Halima da duka, ba yadda ta iya dole ta bi Halima suka wuce gida, Inna na ƙara jaddada mata ta je makaranta, kar taga Halima ce ka ɗai a gidan ta ƙi zuwa. Ma'u na turo baki suka yi mata sallama suka tafi.

Amanarcool
***