ALWASHI 2

34

by @rufaidaumar

ALWASHI 

   59

Amarya Kausar tana zaune a tsakiyar gadonta, fuskarta ta sha lulluɓi da tsadaddiyar laffayarta fara ƙal mai adon duwatsu. Babu kowa sai ita ɗaya domin wata Addarsu kaf ta haɗa kan ƴanmatan ta ce ba mai zama wani siyan baki. Haka Kausar na ji na gani duk irin kukan da take yi suka watse suka bar ta.
Zuciyarta sai bugu take da sauri, tsoro take ji. Tsoron abubuwa da dama. Ta sani Laila ita ce zaɓin Areef, ita ɗin zaɓin Maminsa ce, amma kuma ba wai yana wulaƙanta ta ba. Tana tsoron daren nan kamar yadda yake kamar al'ada ga kowace sabuwar amarya da ba ta taɓa sanin mene ne auren ba a aikace. 
Tana ta tunani da saƙe-saƙen zuci, ta ji motsin shigowarsa falon, ƙirjinta sai da ya ba da dam da ta ji an murɗa ƙofar ɗakin ya shigo da sallama hannunsa tiƙr da ledoji. Ta cikin mayafin ta amsa ko sautinta bai fita ba. Shi kuwa ciki ya ƙaraso ya zauna gefen gadon bayan ya ajiye ledojin a gefe sannan ya dube ta da murmushi saman fuskarsa. 

"Barkanki dai."

Shiru ba ta amsa, don haka ya tuna fa ashe shi zai buɗe mayafin, ya sa hannu ya ɗaga mayafin. Ta ƙara sunkuyar da kanta tana wasa da zoben hannunta, zuciyarta sai ƙara ƙarfin gudu take hakan ya ba ƙirjinta damar motsawa ƙasa da sama. Areef ya mata kallon tsanaki ya fahimci kamar a cewa yarinyar arr ta ruga a guje. Faɗaɗa murmushinsa ya yi gami da kai hannu ya riƙo hannunta da suke kaɗawa. Ai sai ta zabura za ta kwace ya kuwa ƙara ƙarfin riƙon. 

"Lafiya?" 

Ta girgiza kai. 

"Bakomai."

Sai da ya tabbatar ta ɗan daina rawar jikin kafin ya saki yatsun nata. Miƙewa ya yi ya ba ta umarnin ta yi alwala su yi nafila daga haka ya fita. Kausar har wata nannauyan ajiyar zuciya ta sauke ganin ya fita. Ta zubawa yatsun da Areef ya kama idanu, ta tuno daddaɗan sautin muryarsa sadda yake mata magana, wata ƴar nutsuwa ta ziyarce ta, ita fa ta ɗauka ko a fuska zai nuna wata alama da za ta ƙara tabbatarwa kanta lallai ita ɗin ba zaɓin zuciyarsa ba ce. Miƙewa ta yi duk da cewar da alwalarta, kawai ta yanke shawarar ƙara yin wata. 

Koda ya shigo darduma kawai ya shimfiɗa ganin haka ta miƙe daga gefen gadon da ta yi zaune ta bi sahunsa suka yi nafila. Ya jima yana musu addu'o'i tana amsawa kafin daga bisani su shafa. 

Kallonta ya yi ta juyar da kai ga barin satar kallonsa da ta ke yi.

"Hey, kunyar ce har haka? Hum, ok. Zan ga zuwa yaushe zan yi nasarar raba ki da ita."

Kausar ta yi murmushi. 

Haka ya jawo ledojin ya buɗe ɗaya ta 
gasasshiyar kaza ya ajiye a gabansu. Tafin hannun da ta ga ya miƙo mata ne ya sa ta ɗago kyawawan idanunta ta dube shi don ba ta san me yake nufi ta miƙo masa ba. Ba kasafai mata suka iya su bi shi da kallo na wasu dogon sakanni ba, balle a yanzun da ta ga kamar sun wani ƙara ƙanƙancewa da ba ta san dalili ba. 

"Uhum?" Ta furta tana kauda kanta gami da duban gefe duk ta daburce. A tunaninta ko wayarsa ke gefen inda take ne, sai ta ga ba haka ba. 

Ba ta yi aune ba ta ji ya matso dab da ita, a hankali kuma ya saka hannu ya fara ware lulluɓin da ta ƙunshe kanta ciki da laffayarnan. 

"Shi mutum ba zai hutar da kansa a ɗakinsa ba. Duk uban lulluɓin nan da ki ka yi ta ina iska za ta ratsa jikinki?" 

Yana zancen amma tuni ya warware. Ya kama ƙullin da ke ƙugunta na laffayar itama zai kunce, ta kuwa yi wuf ta riƙe hannunta ba tare da ta shirya ba. 

"Don Allah Hamma ka yi haƙuri zan cire da kaina."

Mutmushi ya yi ya sake ta, ta jima tana ta ƙoƙarin kuncewa ba don ba zai kuntun ba, sai don kunyar hakan da ta ke ji. Shi kuwa maida hankali ya yi ga wayarsa da yake duba saƙonnin da suka shigo masa a whatsapp. Na Fareed ne ya ɗau hankalinsa da ke tambayar ko tafiyarsu Yobe tana nan nan da kwanaki ukun? Saboda akwai uzurin da yake son matsar da ranarsa idan har tafiyar na nan. Ya ba shi amsa yana satar kallon Kausar da ke faman kame-kame. 

Malam Bahaushe ya ce duk wayon Amarya sai an sha man ta, hakan ce ta faru a wannan dare. Duk yanda Kausar ta ke kakkaucewa Areef, sai da ya bi da ita ta hanyoyi da ya samu lagonta har ya kai ga cimma gaci. 

Shi ya rarrashi abarsa ya lallaɓa ta, ta yi ta kanainayewa a jikinsa don ba ta son su haɗa idanu. Haka dai har ya taimaka mata ta gyara jikinta kafin shi ma ya wuce nasa ɗakin dake a ɓangarenta. 

Bacci mai dadi suka yi tana manne a jikinsa a wannan dare.

***
Washegari su Afrah suka zo gidan ita da wasu sa'anninsu da wata aminiyar Kausar din dake zaune a Adamawa mai suna Haulatu. Areef na ɓangarensa, nan suka yada zango daga kawo abinci suna yi wa Kausar shaƙiyanci don kaf ba yaro, sun kuma fahimci akwai abin da ya wakana daga ma yanayin Kausar din da ba ta son motsa jiki sosai. 

"Ke sai fa kin kama kanki, kin san ba ke ɗaya ba ce a wurinsa ba ko? Toh kar ki sake ki nuna masa ke raguwa ce a fannin shimfiɗa. Duk sadda ya buƙaci wani abu ki ba sa." 
Faɗin Haulatu, ai kuwa suka ɗau shewa ita kuwa Kausar ta harari Haulat din. Kalmar 'ba ke ɗaya ba ce a wurinsa ba' ya ɗan sosa mata rai. Babu matar da ba ta kishin abin da take so. Ta sani kishi halitta ce, kuma tabbas tana jin kishin kasancewar Laila matar da Areef ke so fiye da ita. Takan tuna darensu na jiya, kalamansa da ma yanda ya dinga sumbatu, sai take aunowa to idan ita da ba wani shahararren so yake mata ba, ya ba ta kulawa har haka, ina ga kuma zaɓinsa? 

"Tab! Wallahi Adda Kausar kina da aiki. Yanzu maganar da Haulatu ta yi ne ya jefa ki tunani haka? To gaskiya ina ba ki shawara kar ki yarda ki saka kishi a ranki tun kan a je ko'ina."

Cewar Afrah da ta kula hankalin Kausar din ba ya kansu. Kausar ta dubi Afrah, ta sani dama can mace ce mai saurin tsinƙaye da lamura. Wani bin takan cewa Afrah kamar fannin halayyar dan adam take karanta (Psychology) ba fannin asibiti (Medicine) ba saboda kafin ma kowa ya ankara tana kaunar Areef to fa ita ce ta soma fahimta. 

Nan dai sauran suka hau fadin aikuwa hakane, yayin da Haulatu ke faɗin aa ita sam ba ta ga laifin ƙawarta ba saboda ai kishi halitta ce. Kuma mai son mijinta dole ta yi kishinsa. 

Suna cikin wannan musun ne suka ji sallamar Areef, ba shiri duk suka shiga taitayinsu suka hau gaida shi. Kausar ta saci kallonsa, ya yi tsaf cikin farar tshirt da jeans. Ya ɗora baƙin agogo. Ƙamshin turarukansu sun mamaye falon kai ka ce shi kaɗai ya fesa cikinsu. Bai ko tsinci zantukansu ba. Su din ma ganinsa suka miƙe suka yi musu sallama, haka suka fice suka bar su. Kausar ta gaishe shi tana sunne kai, ya ƙarasa ya jawo ta jikinsa gami da sumbatar goshinta. 

"Hope babu wani abu da ke damunki?" 

Ta girgiza kai ba tare da ta kalle shi, uwa uba rashin sukuni sakamakon ɗan murza yatsunta da yake.

"Yunwa nake ji. Zan samu ko ruwan tea?" 

Ta miƙe tsaye. 

"Bari na haɗamaka, ga abin kari nan ma Mami ta aiko."

Ya jinjina kalmar Mami ta aiko din, ya ƙara tabbatarwa fa dagaske dai Mami ta fi son nata. Yana jinjina yanayin zamantakewar musamman idan Mamin suka gano sam ba Sameera ba ce, ƴar uwarta ce Laila. 
Ajiyar zuciya ya sauke sadda Lausar ta ɓacewa ganinsa zuwa kicin. Har ga Allah koda ba zai ce yana son Kausar irin sosai sosai ba, to fa ya yaba da yanda ya same ta, ya san cewa muddin za su gina rayuwarsu a haka, kyautatawa da ganin girman juna, to tabbas zamansu da ita zai yi daɗi. Daga daren jiya zuwa yau, ta samu muhalli a zuciyarsa da bai taɓa hasashen za ta samu ba. Ya dinga aunawa yanzu idan ace har haka ya yi farin ciki da samun Kausar a cikakkiyar budurwa, ya Sameera ta kasance idan misali ta yi aure amma mijinta bai risƙe ta haka ba? Ina Sameera? 

Ya lumshe idanu gami da kwantar da kai jikin kujera. Duk sadda ya tuna Sameera ba ta kusa, kwakwalwarsa na shiga wani yanayi, idan ya ji kamar ya tambayi Laila sai wata zuciyar ta hane shi, ta tunasar da shi ba yanzu ba Areef, akwai sauran lokaci. Uwa uba kuma yana tsoron abin da za'a faɗamasa a kan Sameera. 

"Hamma! Hamma!!" Ya ji sautin muryar Kausar murya kamar daga wata duniya saboda zurfin da ya yi a tunani, ya buɗe idanunsa da sauri wanda suka ɗan tsorata Kausar ganin yanda suka kaɗa hakanan fuska a ɗaure kamar Hamma Areef din da ta sani a shekarun baya da yake matuƙar ba su tsoro da sanya su shiga taitayinsu idan ya shigo wuri. Ta kasa magana don fargaba sai ta yi shiru kawai tana motsa baki amma murya ta ƙi fita. Ya ɗan shafi fuskarsa da tafukan hannaye yana ambaton sunayen Ubangiji har dai wata ƴar nutsuwa ta ziyarce shi. 

"Sorry, kina magana ban ji ba."

Daga yanayin sanyin muryarsa ya sa ta samu ɗan nutsuwa. 

"Dama abin karin ne na hadamaka."

Ta yi masa nuni da gefensa inda ta shimfiɗa masa darduma kamar yanda ta kula ko wurin Mami ya fi ƙaunar cin abinci a ƙasa madadin saman kujera ko dinning table. Ganin kofi ɗaya da kuma wani bowl na soup da faranti dauke da soyayyen dankali da agada da ƙwai sai sauce a gefe ya sanya shi dubanta. 

"And you, have you eaten?"

Turancinta ba sosai ba, tana fahimta kwarai sai dai ba da amsa ne ba ta fiye yi ba. Nauyin ka yi ɓarna a maka dariya ya sa ta koma baya a fannin harshen. Kawai ta girgiza kai. 

"To haɗo tea ki zo mu ci."

A dolenta ta bi umarnin yin hakan. 

***
Ɓangaren Mami kuwa tun da ta tsinci hirar da ƴanmatan ke yi ta fahimci tabbas Areef ya karɓi auren da ta yi masa da Kausar da daraja, ranta ya yi ƙal. Kaso saba'in na haushinsa da take ji ya ragu. 

***
Misalin ƙarfe sha biyu na rana, Laila ta jima da kammala kimtsa gida, shiru ya yi mata yawa tun tana tunane-tunane har dai bacci ya yi awon gaba da ita a saman kujera three-sitter dake a falon. 

Haka ya shigo ya risƙe ta, da ya yi sallama ya fahimci ta yi nisa a bacci. Ya ƙaraso ciki ya nemi wuri ya zauna yana kallonta. Baccinta take bilhaƙƙi, doguwar riga ce ta material mai laushi a jikinta. Hular da ta rufe gashinta da shi ya zame, hakan ya ba sa damar ƙarewa gashin nata kallo, sam ba ta da sanƙo don gashinta har gaban goshi. Ya kai duba ga ƙafafunta da rigar ta fallasa sakamakon ɗagewar da ta yi har gwuiwarta. Murmushi ya yi, ya sani tabbas da ace idanunta biyu da ya sha harara. 
Idanu ya zuba mata sosai, so yake ya ga ta inda suka bambanta da Sameera, zai so ya ƙara ganin Sameera su jeru ya gani wai suna mugun kama ne da har ya kasance Laila ta samu ƙarfin gwuiwar ta shigo rayuwarsu matsayin Sameera? Shi dai ya san ba wai ya yi wa Sameera mugun sani ba, kawai dai yana ɗan tuna kaɗan daga cikin kamanninta wanda ya ke gani a fuskar Laila. 

Ita ko muskutawa ta yi da zummar gyara kwanciya, ta ɗan bude idanu, ganin mutum zaune ya sanya bayan tafukan hannayensa a ƙasan haɓa kawai yana kallonta kai ka ce tv ya samu yasa ba shiri ta miƙe zaune tana kallon ko'ina na jikinta. Da sauri kuma ta miƙe tsaye ta gyara zaman rigarta kafin a fusace ta ce. 

"Tsakani da Allah hakan ya dace? Mutum na bacci ka shigo kawai ka zuba masa ido? Me hakan ke nufi?" 

Yanayin muryarta ya sa ya gano tsantsar haushinsa da ta ji. Bai ankara ba ya ji muryarta ta ja tsaki gami da nufar hanyar ɗaki. Bai taɓa jin zafin wannan tsaki da take masa ba sai a yau. Don haka a gaggauce ya karasa sai ji ta yi an fisgo hannunta baya, ƙirjinsu ya gogu juna ba su shiryawa hakan ba. Ita sai ta kasa magana ban da idanunta da ta ƙara zarewa dama ga su a zare saboda baccin da ta sha. Za ta ja baya ya riƙe ƙugunta gam ta kasa motsi. Ba kuma ta so ta buɗe baki ta yi magana da zai ji bakin na tashi irin na mai bacci. 


©Rufaida Umar