ALWASHI 2

35

by @rufaidaumar

ALWASHI 

    60


"Don't try me Laila, ina girmama ki. Amma ki sani ba na son tsaki. Please stop it."

Ta janye jikinta ganin ya saki riƙon da ya yi mata, ganin tana murza hannun da ya riƙe. Ya sanya da sanyin muryarsa ya ce. 

"I'm sorry. Na ji maki ciwo ne?"

Ta watsa masa harara, har ta turo bakin da zummar tsaki sai kawai ta fasa gami da juyawa cikin ɗaki tana ƙunƙuni. Ya bi ta da kallo yana murmushi. 

"Ba ki gaishe ni ba." 

Ko juyowa ba ta yi ba balle ta tanka. Ya girgiza kai kawai ya fice fuskarsa a sake kamar ba shi ne ya gama haɗe rai ba.

***

YOBE

Inna ta dubi Adam wanda ya kawo musu ziyara na farko bayan dacewar da ya yi na samun aiki a Abuja ta hannun abokinsa Nagoda. Ya je an masa interview kuma har an ba sa muhallin zama a Abujan. 

"Adamu." Jin ta kira sunansa a yanayin da ta saba muddin za ta furta abu mai muhimmanci ya sa shi dubanta shi ma a nutse. 

"Na'am Inna."

"Adamu domin Allah zan roƙe ka wani arziƙi, na sani mu masu tarin laifuka ne a wurinka wanda har gobe muna cike da dana sanin yanda lamura suka wakana. Ji nake inama na dawo da hannun agogo baya na shafe abin da muka aikata, sai dai kuma ƙaddara ta riga fita. Komai tsarin Allah ne, na kuma yi imanin shi ne ya tsara faruwar hakan. Ina kuma ƙara neman afuwarka bisa son zuciyar da muka yi maka."

Ya sauke ajiyar zuciya. 

"Inna komai ya wuce, na sha faɗamaku bana son zancen, don Allah komai ya wuce. Ni musulmi ne, na rungumi ƙaddarata."

Ta yi murmushin jin daɗin kalamansa, ta jinjina kai. 

"Masha Allahu, Allah ya bayyana mana su duk inda suka shiga. Sai arziƙin da zan roƙe ka Adamu, bai wuce na ka yi aure ba. Na sani ba ya daga ra'ayinka, amma kuma auren shi ne cikar kamalarka. Ina so na ƙara gani daga zuri'arka, rayuwar tafiya take. Tsufa na ƙara cimma ni, koyaushe ji nake ƙiris ya yimin saura na tarar da mahaifinku nima."

"Ki daina faɗin haka Inna, in sha Allahu har auren jikokin jikokinki sai kin gani."

Ta yi dariya jin abin da ya ce mai kama da almara, shi ma ƴar dariyar ya yi. Kafin shiru ya ɗan biyo, ya gyara murya ya ce. 

"Inna na amince, na kuma bar maki zaɓi. Duk wacce ki ka zaɓa min ina mai tabbatar maki zan zauna da ita. Koda kin ce na zaɓa da kaina Inna, ban san wa zan zaɓa ba. Amma ke na bar maki ki zaɓa min duk wacce kike ganin za ta yi haƙurin zama da tsoho irina. "

Inna ta yi ƴar dariya can ƙasan ranta cike da tausayinsa. 

"To idan hakane ka kuma amince zan sa a daura maka aure da Shatu a goben nan in sha Allahu."

Ya kasa tuna wace ce hakan, sai da ta tunasar da shi, ƴar ƙanwarta ce da mijinta ya rasu bayan gajeruwar jinya, haihuwarta ɗaya, yaron ma yanzu haka yana karantar fannin soja a can Kaduna. Shatu ba ta da matsala, ta yi karatu tana aikin asibiti matsayin Nurse. Ya ji ba shi da matsala da aurenta saboda kyawawan yabon da take samu a bakin ƴan uwa don haka a take ya amince. Ya sani auren nasa a yanzu shi ne kawai mafita, ko ba komai da lafiyarsa, ba zai ce ba ya buƙatar mace ba. Haka kuma abu mafi ɗaukar hankalinsa shi ne, yin auren ƙila ya sa Affan kautar da hankali a kan rayuwarsa. Hakan zai shiriritar da Affan din daga barin bibiyarsa har dai ya soma binciken da ya sa a gaba domin yanzu haka da niyyar zuwa Maiduguri a ransa kawai dai yana taraddadin ta ina zai fara bai zamewa Kubra matsala ba?

Aikuwa hakan ce ta faru, a washegari ƴan uwa da makwaftan arziƙi suka shaida auren Shatu da Adam bayan an idar da sallar azhar. Inna tun a ranar da suka yi magana da Adam ta kira mahaifin Shatu don yar uwarta ta jima da rasuwa. Mahaifin Shatu ya yi na'am da batun, ya kuma aminta da kawai a daura auren yadda Innar ta buƙata. Inna ta ce sam sai ya ji ɓangaren Shatu ko ta amince, aikuwa yana tambayar Shatu itama ta ce ta ba sa zaɓi. Da wannan aka ɗaura auren kan sadaki dubu ɗari wanda ya fito daga aljihun Yayansa Ahmad Kibiya. 

Wannan Kenan!

***
ABUJA

Tun bayan tariyar Laila Daddy Affan da iyalansa suka tattara suka dawo Abuja ganin Nihla ta tashi hankalinta, sai dai Mahaifin nata ya yi ƙoƙarin kwantar mata da hankali da kuma yi mata wasu alƙawura muddin ta kwantar da hankalinta. Da haka suka shawo kanta ta ɗan saki jiki ta kuma fara fita yawo da abokanta na nan waɗanda dama can an san juna, wasu ta media aka haɗu, wasu ko a nan ɗin ta san su. 

  A wani yammaci, Daddy Affan ne zaune ya ƙurawa video da Sunday ya turomasa idanu, sai da ya kalla har ƙarshe kafin ya ajiye ya yi shiru yana tunani. Kada dai ace wannan mutumin ajiyar banza suka yi masa babu wani labari da zasu ji na Kubra a ɓangarensa? Da ace har yanzu Kubra na nan, da zuwa lokacin ta bayyana, to bai ga alamarta ba duk da a binciken Sunday ya ce masa tsohuwar matarsa sunanta Kubra kuma ta ɓata ɓat da twins din da ta haifa, ba a ma san duniyar da suka shiga ba. Ko dai Adam Kibiya ya bar batun saboda tunanin sun mutu? 

Kasa cankar komai ya yi har zuwa sadda ya ji muryar Nihla na yi wa Maigadinsu ihu da faɗan don me bai buɗe mata gate da wuri ba. Ya miƙe da sauri daga barandar da yake zaune yana dubansu, haƙuri Maigadin ya ke ba ta ta ƙara dakamasa tsawa. 

"Nihla Please!"

Daddy Affan ya furta murya a ɗage yanda za ta ji. Gaba ɗaya suka dube shi, ita turo baki ta yi tana kokarin yi masa bayani, ya dakatar da ita ta hanyar ɗagamata yatsu.

"Is ok, ya ba ki haƙuri. Wannan ne first time da ya yi irin wannan kuskuren, so let it slide."

Ta ƙara duban Maigadin ta harare shi ta ja tsaki gami da furta "Stupid!" daga nan ta nufo wurin mahaifin nata. Shi dai Maigadi ya juya ya wuce zuciyarsa ba daɗi ganin cin kashin da yarinya ƴar cikinsa ke masa. 

Daddy Affan ko murmushi ya yi ya koma mazauninsa, ta ƙaraso ta zauna gefensa tana shan mur. 

"Saki fuskar mana ƴar Daddynta, Amaryar Areef Sada."

Aikuwa ta yi dariya, shi ma ya taya ta. 

"Daddy bana so fa."

"Au, kin haƙura da shi?"

Da sauri ta girgiza kai.

"No, ba haka nake nufi ba. I mean ka bar tsokanata."

Ya yi dariya sannan ya gyara murya. 

"Yanzu ko ke fa, kin ɗan dawo hayyacinki. Na tabbata sababbin friends da ki ka yi making suka ɗauke maki hankali ko? To haka nake so na ga kina rayuwa kamar babu wata matsala. Ki cigaba da dauriya har nan da wata ɗayan da na maki alƙawari. Ni kuma zuwa lokacin zan share maki kukanki. Kin dai ce za ki aure shi ko mata nawa ya aura ko?"

"Yes Daddy!"

"Then ki shiryawa zama matarsa ta uku."

Ta yi dariya sannan ta tsuke fuska. 

"How I wish ni ɗaya ce zan zama mallakinsa."

Murmushi Daddy ya yi,

"Da sannu za ki zama ke ɗayar."

Ta kuwa yi murmushin itama. Momi Inayah wacce tun ihun farko da Nihla ta yiwa Maigadin ya sauka kunnenta, tana tsaye jikin window duk hirar da suka yi ya shiga kunnenta. Sauke labule ta yi zuciyarta cike da baƙin ciki. Ta gaji kwarai da ganin irin rayuwar da ɗiyarta ke gudanarwa, ta yi shigar banza ta kuma taka wanda duk ta so. Ta yi abota da kowane kare da biri. Ta sani tun ran gini tun ran zane, ba ta yadda za ta iya tanƙwarata a yanzu don gaba ɗaya ta fi ƙarfinta. Ba ma ta isa ba a kan Nihla koda ace babu idanun Affan a wurin. Share hawayen da suka gangaro mata ta yi, meyasa ta yi wasa da damarta ta Uwa? Babu abin da ya ƙara burgeta irin yanayin tarbiyyar yaran makwaftansu, makaranta yini suke zuwa, boko da arabi. Ga larabci tas a bakunan yaran, ta taɓa tarar da su sun dawo daga makaranta suna ta zabga musu da harshen larabci, uwar ta amshe ta shiga rabon da nata larabcin da bai kai na yara  fita ba. Ta yaba kwarai da tarbiyyar gidan, duk da rayuwar Abuja babu ruwan wani da wani, amma su kam suna ɗan leƙawa juna ita da makwafciyarta. Ta ba ta shawara kan ta ja ɗiyarta a jiki ta kuma ɗaukar mata malamin addini da zai dinga koyar da ita, sai dai koda ta yi maganar daukar malamin a gaban Nihla da Daddy Affan, dariya suka sheƙe da shi. Har Nihla na shaƙiyancin wai Daddyn ya ya hangota a gaban Ustaz ta saka hijabi har ƙasa da nikaf? Suka ƙara darawa, lamarin da har yanzu Momi Inayah bai sake ta ba. Ta kuma ji har ranta ita kam sai ta yi iyakar yin ta wajen  gyara tarbiyyar ɗiyarta koda kuwa hakan zai zama silar rabuwarsu da mijin nata da a yanzu ta tsane shi ainun. Ga baƙin cikin irin tarbiyyar da ya ja Nihla ta samu, gefe guda kuma ga rashin barinta da bai yi ta ziyarci ƙasarsu ba. Tsakaninta da yan uwanta sai magana ta waya. Ta kuma kasa furzar musu da damuwarta. 

***
KATSINA

Duk yanda Areef suka so tafiya Yobe a ranar litinin kamar yanda suka tsara hakan bai yiwu ba sakamakon aikin da ya taso gadan-gadan na batun kayansu da ke New-York da har lokacin ba su kammala haɗuwa ba balle su taso. Dole aka ajiye komai gefe Fareed ya bi sahu, Areef ya so zuwa amma Abba ya dakatar da shi ganin duka duka bai jima da tarewa ba. 

Wannan ta sanya shi shafe sati a gidan Kausar suna cin amarcinsu. Ya yi mamakin yanda Mami ta sassauto masa, ya dai fahimci ba ƙaramin ƙauna ta ke nunawa Kausar ba. Ƴan biki duka an watse. 

  Ranar da zai komai ɓangaren Laila ne ya yanke shawarar haɗa su ya yi musu nasiha tare.  Don haka ya yi wa Laila text cewa ta zama cikin shiri bayan isha'i zai zo tare da Kausar domin su gaisa. 

Laila ta buɗe saƙon ta karanta, tsaki ta ja. Ita duk abin da zai shiga rayuwarta fa ba ƙaunarsa take ba, mene ne kuma na zuwa da wata Kausar? Shi bai san su biyun duka ba sa gabansa ba? Ta dai yi girki kamar yanda Zakiyya ta ba ta shawara, ta nusar da ita lallai wasu abubuwan sai ta kwantar da kai matuƙar ba wai ta ba shi kanta ba ne, ta hakan ne kaɗai zasu samu damar cimma wasu manufofin nasu. To kamar haɗin baki itama Hajja Zayha haka ta nusar da ita. Ita dai ta ɗan yaba da kirkin yaran Hajja din domin kaf dinsu daga Zahra, Fadila har ma da Nasreen babu wacce ta nuna mata wata ƙyama, sosai suka mutunta ta da suka shigo, kuma ta ɗan sake da su. Duk da zuciyarta na kwaɓarta cewa kul! yaran Hajja Zayha ne jinin Sada Bilyaminu, amma hakanan ta sakar musu. To su ɗinma kowacce ta koma gidan aurenta. 

A yaran Mami idan za ta tuna ko, Benazir kaɗai ta gani sun shigo tare da Adda Mardiyya, amma ba ta ga ƙeyar Afrah da Maryama ba. Tsaf tana kula da takun kowa, tana jiran ganin ta inda za ta fara ne kawai. 

Jin da Kausar zai shigo ne ya sa ta yi kwalliya mai rai da lafiya ta kuma saka wani lallausan maroon lace  ɗinta mai kwalliyar furanni yellow. Medium metallic yellow veil ta yafa a kafaɗa. Wani irin yafe na ƴan birni na gefe guda. Ta saka humrarta mai bala'in ƙamshi na musamman na mutan Borno. Sai da ta kalli kanta sosai a madubi, karon farko da ta yi wani ado a gidan Areef da ya burgeta har ya sanya ta murmushi. Duka wannan domin haɗuwa da ƴar gaban goshin Mami ne. 


©Rufaida Umar