MAƘOFTAKA DA ALJANU

CHAPTER 9

by @deejasmah

Kamar wacce aka tsikara da sauri ta isa gaban gawar wacce har lokacin idanun ta buɗe ta kafa su kan Nana tana bin ta da wani irin kallo, hannun matar kusa da ita ta kama tana cewa '' ba fa ta mutu ba, ku bar kuka wallahi ba ta mutu ba ga idanun ta nan buɗe''.

Cak suka tsaya suna duban ta da mamaki ganin ba su san daga ina ta faɗo ba, tana musu surkullen wai bata mutu ba. Sake cewa tayi '' Wallahi ba ta mutu ba, ga shi nan tana kallona''.

Nurse ɗin da ke gaban gawar ne ta dubi fuskar wanda mayafin da aka rufe shi ne ya kwaye amma idanun mamaciyar a rufe suke ruf. Ta karɓi zancen da cewa '' wani irin tana kallon ki? Da wani idanun ta kalle ki bayan a rufe suke''.


''Wallahi a buɗe suke, magana ma take son yi. Don Allah kar ku binne ta wallahi da ran ta''.


Tsaki babbar yayan mamaciyar ta saki tana share hawayen ta tace '' baiwar Allah daga ina?  Lafiyan ki kuwa zaki saka mu a gaba da zancen bata mutu ba? Aina kika taɓa ganin an mutu an dawo? Ko kin fi mu son ƴar uwar mu ne? Don Allah ku mu wuce su Hashimu na jiran mu a waje da mota''.


Buɗe baki tayi da niyyar bayar da amsa Inna Yabi da dawowar ta kenan zata shiga ɗaki ta tarar da wannan tirka-tirka tayi saurin cewa '' Nana me kike yi a nan? Bayin Allah lafiya?".


Wancan matar ne ta yiwa Inna bayanin abinda ya faru, sallallami Inna ta fara tana tafa hannaye zuciyar ta na rawa kan abinda ake gaya mata, cike da damuwa tace ''Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Nana me nake ji haka? ''. Kafin ta kai ga bayar da amsa matar ta kuma cewa '' mu dai mun yi nan, baiwar Allah Allah ya baki lafiya'' suka raɓe ta gefen ta suka wuce aka bar su ita da Inna tsaye a wurin. Duban ta tayi cike da damuwa tace '' wai Nana anya ƙalau kike? Wainnan abubuwan na ki fa ba lafiya cikin su. Me ya fito da ke?".


''Allah Inna lafiya ta ƙalau, kuma da gaske nake matar can bata mutu ba. Idanun ta a buɗe suke tana kallo na, ki bar ni in je waje in gaya musu kar su binne ta da ran ta''.


''Babu inda zaki je Nana, shige mu tafi'' ta ƙare tana jan ta cikin ɗakin, duk yanda ta so tayi mata bayani bata saurare ta ba. Sai da ta dangana ta da gado kafin ta tsaya kan ta tana cewa '' Ni dai ba zan zauna ina ganin mara lafiya in yi shiru ba, lamarin nan naki akwai jinnu a ciki nayi magana Yayar ki ta taso. Allah ya kai mu gobe da kaina zan gayawa Umman ki idan ta zo''.


Kallon ta tayi tana cewa '' Ni dai Inna babu wani aljanu, na san me na gani. Matar can ba ta mutu ba'' tsaki Inna ta saki ta koma kan tabarmarta ta zauna tana cigaba da mita, a haka har aka kira sallar magriba. Ko da dare da Khaleed ya dawo da abincin dare sai da ya fuskanci kamar akwai damuwa tsakanin Innan da Nana sai dai ko da ya tambaya babu wata amsa mai ƙarfi, bai ja zancen da tsayi ba a zuciyar shi yana ayyana ko Innan ta gaji da zaman asibitin ne shiyasa. Hakan ya sanya yau tafi da wuri ba sai da ya jira likitan dare ya shigo an gama round ya bi shi yana tambayar yanayin jikin nata, cewa yayi '' Babu wani matsala, gobe allurar ta zata ƙare da safe In Shaa Allah zuwa rana za mu sallame ta''.


Godiya yayi masa ya koma ɗakin, bai ko zauna ba yayi musu bayanin da likita yayi masa kana ya musu sallama ya wuce gida. Ɗakin ya kuma yin shiru daga Inna har Nana ba wanda ya cewa wani uffan kowa da lissafin da yake yi  a zuciyar sa, ita Nana tayi nisa a tunanin wancan gawar da wani hali take ciki ba ta san me ya sa abun ya tsaya mata a rai ba. Yacce ka san ta san wacce ta mutun ko kuma akwai wani alaƙa tsananin su, haka ta yi bacci cike da jimami tana jin ran ta babu daɗi ko kaɗan.


''Nana, Nana, ki tashi'' da ake faɗi tare da bubbuga pillown da ta ɗaura kan ta ne ya sanya ta buɗe idanu don ganin ko waye, a nata zaton ta san bai wuce Inna amma dalilin tashin ne bata sani ba. Ko dai ta makara ne? Hasken fitilar da ya dalle mata idanu ne ya sanya ta runtse su tana kawar da kan ta gefe, ji tayi an kuma kiran sunan ta. Buɗewa tayi a hankali yanzu kam fitilar bai kallon ta shi yasa ta iya ganin gaban ta, Khaleed ne sanye da jallabiya yana duban idanun ta kana ya saki murmushin da ke ƙara masa kyau a idanun ta yace '' ba ki yi farin cikin gani na bane?".

Yawu ta haɗiye tana cewa '' me ya dawo da kai?".


''Ganin matata mana'' ya amsa yana kai hannun shi cikin nata ya riƙe, wani kalar sanyi ƙalau ya ji hannun ya mata ta dube shi tana cewa '' me ya samu hannun ka?".

''Iska ne, na fito a cikin sanyi''.

Zata yi magana yayi saurin cewa ''shhh, kar ki tada Inna daga bacci zo mu je''.

Bai ko jira amsar ta ba ya fara jan ta suka fita daga ɗakin, harabar asibitin tarwai da haske haka suka dinga tafiya cikin shiru har suka iso wani ɗaki daga can ƙarshen ɗakunan. Buɗewa yayi ya tura ta ciki ya mara mata baya, wani kalar sanyi ne ya fara mata barka da isowa cikin ɗakin. Juyawa tayi ta dube shi tana cewa '' Yaya me muke yi a nan........''

Tambayar tata katsewa tayi sakamakon ganin ya isa gaban wata ƙofa yayi shigewar shi ciki, yawu ta haɗiye a tsorace ta bi bayan shi. Tana shiga cikin ɗakin ƙofar ta rufe kan ta har ƙarar sakata sai da ta ji amma ba ta wannan take ba, ƙarasa shiga tayi. Abinda ta gani ne ya sanya ta tsayawa cak ƙafafun ta sun yi mata nauyi, gawarwaki ne kwance wurin sun kai guda goma. Kowacce lulluɓe da ƙyalle bulu, ga sanyin masifa da ya fi na wanda ta ji a farkon shigowar ta sai warin chemical da ke tashi. Ba sai an gaya mata ba ɗakin ajiyar gawa ta shigo, amma miyasa Khaleed ya kawo ta ciki? Wannan tambaya ce da bata da mai bata amsa.


Amsar tambayar tata ta samu ne a daidai sanda lulluɓin gadon gabanta ya zame tayi arba da idanun gawar ɗazu tana kallon ta tace ''Nana, ki taimake ni kar su binne ni. Ban mutu ba'' cikin karaji tayi maganar tana duban ta. Ja da baya ta fara yi tana girgiza kan ta, sai ji tayi duka gadajen suna motsi lokaci guda. Muryar Khaleed ta kuma ji yana cewa ''Nana'' ɗagowar da zata yi tayi arba da abinda ya kuma tsoratar da ita, duka gawarwakin sun miƙe zaune kuma in ka ɗauke ta farko duk suna ɗauke da fuskar mutanen da ta sani ne. Na farko Abbanta sai Umma sai Yaya Adama, ga Khaleed a ƙarshe ga Umman su ita ma, akwai Inna Yabi sai Iyami sai kuma yarinyar nan da ta fara zuwar mata a asibitin na ƙarshen kuma fuskar ta gare ta a tare suka haɗa baki suna faɗin ''Nana ki taimake mu, bamu mutu ba. Ki gaya musu!!!".


Toshe kunnen ta tayi tana runtse idanun ta, tana jin ƙarar saukan su daga kan gadon har zuwan da suka yi gaban ta suna jan mata hijabi har lokacin ba su daina maimaita ''Ki taimake mu!! Ba mu mutu ba!!!! Kar a binne mu!!!!" ba. Wani kuka mai ban tausayi ta fashe da shi tana jin ɗaci kan harshen ta da ƙarfi tace ''Ku ƙyale Ni!!!! Na shiga uku!! Ku ƙyale niiiiii..............''