Chapter 22
Qarfe goma saura ʼyan mintuna ta yi musu a cikin airport ɗin Abuja.
Suna sauka Zannur ya yi musu order bolt.
Kai tsaye gidan Mamy suka wuce.
A parlour ƙasa suka sameta tana yi wa masu aikinta bayanin abinda zasu dafa.
Bayan sun gaisa Mamy ta ce " yanzu nake shirin kiran ku naji yaushe za ku taho?"
Zannur ne ya ce " dama saboda kar su jira me ne , kinga ai ba mu san lokacin da zasu zo ba."
Jinjina Kai ta yi ta ce " haka ne kam."
" Na san baku yi breakfast ba, bari a kawo maku abinci ku fara ci sai muyi magana daga baya."
Da kanta ta shiga kitchen ta haɗa musu kayan breakfast ɗin a cikin tray ta fito.
Zannur ne ya tashi ya karɓi tray ɗin daga hannun Mamy.
Haka a gidan su Jay tun bayan da aka yi sallar asuba Mom da su aunty Naja suka shiga kitchen suna ta aikin snacks da abincin karɓar baƙi.
Wuraren ƙarfe goma na safiya Mom ta fito ta bar su su ƙarasa sauran aikin da ya rage.
Ta tafi ta yi wanka.
Bayan ta yi wanka ta shirya ta koma kitchen ɗin don ganin abinda suke yi.
Tana shiga ta tarar suna juye abincin da suka gama cikin flask.
Karima ta kira ta ce ta je ta ƙara gyara parlourn baƙi ta kuma sa mashi turaren wuta.
Bayan ta gama da kitchen ɗin ta fito zata koma ɗaki sai ga Jay riƙe da waya ta ƙaraso inda take.
" Mom wai dama Sadeeq ne yace a faɗa ma su Dad wai iyayen na shi sun taho."
" Har sun taho kenan bari naje na sanar da su."
ɗaki ta koma ta saka mayafi sannan ta fito ta wuce part ɗin Dad.
Bayan su HAYDAR sun gama breakfast
Suka wuce parlourn sama,a zaune suka tarar da Mamy da ɗan ƙaramin littafin Adhkar a hannunta.
Wurin zama ta nuna musu tana ajiye littafin da ke hannunta.
Bayan sun zauna ta kalle su ta ce " ALIYU tambayar ka nake son na yi."
Ɗagowa ya yi ya kalleta ya ce " toh Mamy Allah ya sa na sani."
" Ina son ka faɗa min gaskiya, kun sami wata matsala ce tsakanin ka da matarka?."
" Mamy tun jiya kike yi min wannan tambayar, kuma ina da tabbacin kin fi kowa sanin cewa matata ta rasu."
Zannur ta kalla suka haɗa ido,ta ce " Usman anya ɗan uwanka bai fara shaye shaye ba kuwa?"
Zannur da yake ta kallon HAYDAR ya ce " Mamy jiya nima da muka yi maganar nan da shi ta daɗe tana min yawo a kaina."
" Amma ni kuma ina tunanin ruwan addu'oin da ya fara amfani da su ne."
Mamy ta jinjina kai ta ce " nima na yi tunanin hakan amma ta ya za'a yi yaga yarinya ya ce yana so, ya aureta sannan yanzu ya ce bai san zancen ba ."
"Anya babu wani abu kuwa.?"
Zannur da ya rasa abinda zai ce, sai kawai ya ce " mu jira su zo muji abinda zasu ce shine kawai mafita."
Knocking ta yi bayan an bata izini ta tura ƙofar ta shiga.
Dad ne zaune ya saka wata cream colour shadda an yi masa ɗinkin babbar riga, shaddar sai maiƙo take yi.
Kana ganin shaddar nan ko ba'a faɗa ba kasan manyan kuɗaɗe ne suka siye ta.
Akan kujerun dake gefen shi kuwa, biyu daga cikin manyan abokan shi ne sai cousins ɗin shi guda biyu.
Suma duk sun yi shiga irin ta alfarma.
Suna jiran iyayen Sadeeq su zo.
Gaishe da su Mom ta yi suma suka mayar mata da gaisuwar.
Ɗaya daga cikin cousins ɗin dad ne ya ce " ni kam Hajiya mama na gidan nan ko?"
Dad ne ya bashi da " tana nan mana baka shiga kun gaisa ba?"
Girgiza kai ya yi ya ce ban shiga ba amma bari mu gama da baƙin sai na shiga.
Ita dai Mom murmushi ta yi ta ce " nikam ba ruwa na kun fi kusa ai."
Dariya ya yi ya ce " aikam dai hajiyar mu rigima."
" Emm ranka ya daɗe dama iyayen yaron nan Sadeeq ne suka a faɗa maku sun kusa ƙarasowa."
Abokin Dad ne ya ce " Masha Allah dama su muke ta jira ai, Allah ya kawo su lafiya."
Gaba ɗaya suka amsa da ameen.
Mom ita ma ta juya ta koma part ɗin ta.
Ƙarfe sha ɗaya da rabi motoci guda biyu suka shigo cikin compound ɗin gidan Mamy.
Bayan sun yi parking suka fara fitowa motar farko Momma ce a ciki sai Safiyyah.
Ɗayar motar kuma Hamma khaleel ne tare da Addah Fatimah.
A bakin entrance ɗin suka tsaya Addah Fatimah ta danna bell.
Mintuna kaɗan sai ga mai aikin Mamy ta buɗe musu.
Tana ganin Safiyyah ta yi murmushi ta ce " aunty sannun ku da zuwa."
Murmushin ƙarfin hali safiyyah ta yi don tunda motar su ta tsaya ƙirjinta ke dukan tara tara ta ce " yawwa Barakah."
Matsa musu ta yi suka shigo, bayan sun shigo ta ce " Mamyn na parlourn sama bari na sanar da ita."
Jinjina mata kai kawai ta yi, don ba zata iya yin magana ba.
Sama ta wuce wurin su Mamy.
Tana zuwa ta ce " Mamy ga aunty Safiyyah nan da wasu mata biyu sai namiji ɗaya a parlourn ƙasa suna jiranki."
Jinjina mata kai ta yi ta ce " toh Barakah jeki ki ƙaraso dasu nan."
" Sannan ki kawo musu ruwa da ɗan abin motsa baki."
" Toh" ta ce sannan ta koma ƙasa.
Safiyyar dai da ta sani ita ta ƙara kalla ta ce " aunty Mamyn ta ce wai ku shigo."
Sai a lokacin ta ƙara jin gabanta na faɗuwa fiye da lokacin da suka zo gidan.
Addah Fatimah ce ta kalli inda Barakah take ta tabbatar ko ta yi magana ba zata ji ba ta ce " ni wallahi Momma banda kin takura da bazan zo ba."
" Tun kafin mu shiga wallahi kunyar kaina nake ji akan abinda ban aikata ba."
Ta faɗa tana hararar inda Safiyyah take a tsaye ta kasa gaba ta kasa baya.
Momma ce ta kalli Addah Fatima ta ce " Fatimah zan saɓa maki kiyi man shiru."
Momma ce ta kalli Safiyyah ta ce " muje."
Tafiya take yi amma ƙafafunta sai karkarwa suke yi kamar wadda zata faɗi.
Tafiya take yi kamar wacce ke koyan tafiya.
Tana tafiya tana jin kamar duk zunuban da ta aikata ne aka ɗora mata a kanta take tafiya da su.
Lokacin da ta taka step na ƙarashe taji kanta ya sara mata,baya ta yi luuuuu zata faɗi Hamma Khaleel dake bayanta ya riƙe ta.
Bayan ta dawo hayyacinta ya ce " ki kula."
Jinjina masa kai ta yi ta aro jarumta ta yi sallama ta shiga,Momma da Addah Fatimah a bayanta sai Hamma Khaleel ya shigo daga ƙarshe.
Mamy dake zaune akan kujera me zaman mutum biyu ta tashi ta ƙaraso inda Momma take ta miƙa mata hannu suka yi musabaha ta ce " barkan ku da zuwa Hajiya."
Momma da sai sadda fuska ƙasa take saboda kunya ta ce " yawwa,mun same ku lafiya?"
" Lafiya ƙalau"
Kujerar da ta taso ta nuna mata ta ce " muje ki zauna."
Bayan sun zauna ta kalli Safiyyah da ke ta raɓe raɓe ta ce " Safiyyah kamar wata baƙuwa ki zauna mana ."
Ƙin zama ta yi a kujera ta nemi gefen kujarar da Mamy take zaune ta zauna.
Addah Fatimah da Hamma Khaleel ta kalla ta ce " ga wurin zama nan kuma ku zauna."
Gaishe da ita suka yi ta amsa Addah Fatimah ta zauna.
Hamma Khaleel ya miƙa ma HAYDAR da Zannur hannu suka yi musabaha kafin shima ya zauna.
Mamy da taga duk sun yi shiru basu ce komai ba sai ta ce " Allah ya sa ba wani abu shi ALIYUN ya yi wa Safiyyah ba?."
Jin abinda Mamy ta faɗa yasa Momma ta ji kunya duk ta ƙara rufeta ta kasa cewa komai.
Hamma Khaleel ne ya yi gyaran murya ya ce " babu abinda ALIYU ya yi wa Safiyyah."
" Hasali ma,mune muka zo bada haƙuri akan abinda Safiyyah ta aikata.
Shi dai HAYDAR kallon su kawai yake yi saboda ya kasa tuna inda ya san fuskokinsu.
Ɗan murmushin manya ta yi ta ce " haba babu komai, ni iya zaman da muka yi da ita bata taɓa yi man wani abu da naji ban ji daɗin shi ba."
Sai a yanzu ne Momma ta sami bakin magana ta ce " kayya Hajiya ba dai ki san irin ta'asar da ta aikata ba shiyasa."
Momma ce ta kalli Safiyyah da tunda suka zo kanta yake a ƙasa taƙi yarda ta haɗa ido da kowa ta ce " sai kiyi musu bayani ai."
Tun kafin ma ta fara magana hawayen baƙin ciki da nadama suka wanke mata fuska.
Shiru ta yi ta kasa cewa komai sai da Addah Fatimah ta daka mata tsawa ta ce " zaki yi magana ko sai na zo nan na bibbige ki?"
Mamy ce ta ce " haba ke kuwa ai sai ki ƙara firgita ta."
Hannunta Mamy ta riƙe ta ce " yi magana kinji Safiyyah babu wanda zai iya miki wani abu,ai ina nan."