KARFE DÜKKA KARFE NE

BABI NA TARA

by @maidambu41

KARFE DUKKA KARFE NE...!!!

{Zanen ƙaddarar Falilah}

BABI NA TARA

   

Page din na Group din MIJIN Mariah ne da fıtıklar Hikayar Mai_Dambu🥰

Gatan da na samu kaf yaran gıdanmu babu wanda ya samu. Wannan dalilin yasa na taso Ina yadda nazo, Ya Man da yayuna suka rike min kan maciji nake wasa da shi. Kusan da Yaran Ya Nafi’u da sauran Yaran muka taso a cikin gidanmu inda muka fara karatu tun daga primary school,  Allah ya min baiwar farın jini tun ban kai haka ba, domin wannan farın jinin yasa dük inda na shiga sai nayi saurayi.

     Bani mantawa ina aji uku a secondary school na fara haduwa da Ahmad Lamido, Ahmad Lamido bautar kasa ya zo Yobe aka turo shi makarantar mu, wanda yayı daidai da yiwa Asad Transfer daga lagos zuwa yobe shi, Ajiyar zuciya na sauke Ina kallonsu da suka zuba min idanu hatta su Ya Man da suka shigo dakin, hawaye ne ya zubo min na saka bayan hannuna, na goge sannan na kalli Mubarak da ya zuba min idanunsa  sun yi jajjur.  Sannan na dafe cikina da yake wani irin juyawa na bude bakina. “Dük aure aure bakwai da nayi ban dauke su a matsayin abinda zai saka na faka hujja ba Akwai so da fahimta cikinsa, Ahamdi yaso ni a lokacin da iyayena suka gaza fahimtar sauyi dağa gare ni.

       Tunda Asad ya sauka makarantarmu shi kenan kome ya tsaya, domin irin İdol din nan ne Yara masu burin waka, abinda na sani shine ya zo mana da wata irin sauyi domin yan mata sun yi ta fada da dambe, dük wannan abinda nake Teacher Ahmad yana kallon mu, amma ni asad bai taba burge ni ba kasancewar bana son na ga namiji da wasu Dabi’u irin na son harka da mata da sauransu Infact im jealousy type, ba kome da mutane suke so yake burge ni ba, haka kuma muna Jss 3 lokaci.

       Yaron dan manya ne, domin a lokacin yadda ake kawo shi makaranta da yadda ake kulawa da shi yasa na kara gane ba dan karamın gıda bane, sai dai kamar yadda muke gani a fina-finai Yaran masu kudi suna bullied din wasu Yaran haka ce ta faru a makarantarmu,  amma a lokaci ganin yadda Teacher Ahmad yake tsaye a kan yan class dinmu yasa Makarantar suka Kara rike shi, kaddara ba ruwanta da waye kai, idan ta zaneka cikin da,iranta ka shiga kenan.

   Lokacin da muka yi hutu na gama jss 3 zamu tafi ss1 a ranar Malam Ahmad ya fara min magana inda ya sa aka kira ni, da yake da yarinta. Ya kura min idanu kafin ya ce min. “Aishatou!” D’ago kai nayi ina kallonshi kafin nayi kasa da kaina Ina wasa da yatsuna. “You are so pretty.” Wannan shine abinda ya fito bakinsa sannan ya ce min. “Zaki iya tafiya.”

         Ni dai nasan jikina yayi sanyi,  lokacin da na koma class kawata, Hanny taso ta ji me ya saka na fita amma naki gaya mata. Inda na cutar da kaina kenan Ina da zurfin ciki, waahe garı Teacher Ahmad da muke kiranshi Uncle Bobby, ya mana sallama bayan ya ajiye min wasu cards masu kyau da chocolate, aka da cookies, aka yi ta min ihu a class, bayan tafiya mu ma muka watse a makatantar.

          Akwai wani abu da na fahimta ya shigo rayuwata shine girman da na fara, domin muna dawowa gıda, muka tafi gidan AuntyÜmmî muka dawo sai ga bakin maza sun zo ba fa Yara ba manya, abin ya bawa kowa mamaki,  Ya Man yayı ta basu hakuri da gaya musu ni Yarinyar ce yanzu zan shiga 1ss,  dakyar Mutanen nan suka yarda suka kyale ni,sati daya a yobe muka gudu kaduna gidan Aunty Zahra, rayuwa a kaduna akwai dadi,

   Satinmu biyu ranar mun fita da Aunty Zahra, inda ta kwashe mu zuwa gidan governor kaduna, bayan mun gama abinda da zamu yi, muka fito  mun rigata shiga mota ta tsaya tana magana da Matar governor, Hanny tana wasa da wani bralacet da aka bamu, kamar an ce na d’ago kai na hango Mr aljanil, ni dai ban san me ya faru ba, ma farka na ganni a jikin Ya Nafi’u Ina sauke ajiyar zuciya. “Daddy ka kai ni wurin Ya Man, ya biyo ni.” “In sha Allah mun kusan Ita gida!” Lumshe idanuna nayi, barci ya kara gaba da ni. Wurin karfe shida ya taba fuskana. “Falilah!” Bude ido nayi, “Ga Ya Man nan” da sauri na tashi a jikinsa na fita da gudu,  Ina ganin Ya Man da gaske ma fashe da kuka, kuka irin sosai din nan. Zuwa nayi na kwantar da kaina a jikinshi. “Ya isa haka. Ba aljanin da zai kuma damunki in sha Allah.” Haka Hajja warisa ta girgiza kai tana fadin. “Jaira kewan iyayenki kika shi yasa kike wani kukan banza wuce ki barshi ya tafi sallah.” Ai kuwa na fashe da kuka Ya Bana ya ce mata, “haba Hajja yarınya bata da lafiya amma kına kara mata ciwo,” dakuwa ta masa tana fadin. “Ungo naka!” Haka na wuce Ina kuka ko da na shiga parlorn mu, wata Uwar harara da Hajja Mama tayı min tuni na nime kukan na rasa, ai wargi wuri ya samu,asalima Ina sallah na koma barci Ya Man da kanshi ya zo ya duba ni, ya bani ruwan addua na sha tun daga ranar na samu nutsuwa.

      Kasancewar makarantarmu Bodin school ne, amma akwai day da muka gama hutu, ni na zabi bodin yayinda Hanny ta zabi Day, wanda yayi daidai da saukar kur’aninmu, shima sai da Ya Man yayi da gaske domin manema na tara, a haka ya sallame su ya ce ya min miji.  Haka muka koma makaranta, watanmu biyu sai ga Teacher Ahmad, wanda zuwansa ya sauya abubuwa dayawa, na farko fallin balaga, da yazo min da wani irin reni, na biyu shine yadda Asad yake bibiyata, haka muka shirya zuwa Yankari na jahar Bauchi wani Hutu, a lokacin kamar ba zan je ba, amma Hanny ta saka ni zuwa, da nasan abinda zai faru shine silar lalacewar alakata da dangina ba zan je ba.

   Haka muka tafi an dibi malamai goma, maza biyar mata biyar,  haka muka iso Bauchi, Teacher Ahmad shi yayi ta mana bayani, duk inda muka shiga ko muke son sani.

     Bayan mun huta da dare muka fito aka fara games da sauran su, tashi nayi na nufi can dakin da muka sauka, a hallway na cikin yankarin na hango Asad da wasu Yan ss3, mata biyu su kuma maza uku, Ashe tun tashina Teacher Ahmad yana biye da ni,  Ina zuwa zan wuce kawai na ga Asad ya wani taso zai rungume ni, ai kuwa na kifa mishi mari, wanda yayi daidai da zuwan Teacher Ahmad ya ce min. “Good Girl!” Haka yasa Asad ya sake bakin yana kallona, wuce shi nayi Teacher ya ce mishi. “Ka gama lalacewarka kazo inda ake gyara tarbiyya, kul ka Kara kuskuren da kayı domin gidan su baa koya mata haka ba” ya kore su zuwa waje, sannan ya tsaya na fito yayı gaba Ina abin bayansa.

     Tun daga ranar ban kara shiga wani wuri ni daya ba, domin Teacher Ahmad ya samu labarin abinda ake shirin yi min, Wanda yayi report har makarantarmu,  muna dawowa aka kori Asad, amma mahaifinsa ya zo har gıda ya bawa Ya Man hakuri, domin abin ya shafi iyayen Yaran makatanta, dole aka kafa mishi sharadi, sannan ya cigaba da makarantar, ni dai ya bani hakuri kuma yayı alkawarin shiryuwa, da gaske yake nufi domin ya daina dük abinda yake har islamiyyar makaranta yake zuwa, wani lokaci ya tafi wurin Ya Man.

     A hankali Asad aya sauya ko nace ya shirya shirin da yake, a saura watanin shidan da ya rage ya bar makarantarmu,” shiru nayi Ina kallon kasa, kafin na cigaba da labarin. “Ya shiga jikina, ta hanyar nutsuwa da fitar da kyakyawar halinsa, tare da wasu abubuwa da Yarinya irina zata fada mishi. Haka kuwa aka yi dare daya na fadawa soyayyar Asad, wani irin mahaukaciyar soyayya, haka yasa nayi nisa a lokacin na ga tashin hankalin a idanun Ahmadi, domin yaso dakatar da ni amma nayi nisa, wanda a janyo nayi ta mishi rashin kunya da reni kala kala, hakura yayı ya zuba mana idanu.

       Ni dai nasan na haukace akan Asad, wanda ya fara bude min idanu, na daina tsoro ko shakkar ya min wani abu, dük da ban yarda nayi wani Abu ba, amma Asad yayı nasarar bude min ido sosai.” Na fashe da kuka, Aunty Zahra ta rungume ni, tana shafa bayana. “A ranar da suka gama

Makaranta, a ranar shaidan da tsautsayi suka shiga tsakaninmu, zaka iya auren mazinaciya?” Na tambayi Mubarak, “koda yake ban yarda har haka yayı nisa ba, domin Ina Jin abinda zai fara na kai mishi ciwo a wuyarshi, haka yasa shi rabuwa da ni, ya kuma fashe da darıya ya nufi wani wuri da ya saka camera na recording ya dauko, ya ce min. “Na gama dake dük da ban samu damar cika burina ba, zan dawo gare ki Falilah,” tashi nayi na fisge cameran na buga da kasa Ina kuka. “In sha Allah sai Allah ya nuna maka akan Yarka! Na barka da Allah” nayi maza na gyara kayana, shigowr Teacher Ahmad scenes din ya kwace kome na shi, sannan ya Zane shi kafin ya kuma mishi gargadin ya bar makarantar idan suka yi ido

Hudu sai ya kashe shi, daga nan ya raka ni hostel dinmu, na sauya kaya ya ce na same shi a wajen makarantarmu, ban San me

Ya gayawa Asad ba amma naji ance ya bar makatantar cikin mugun Yanayi, daga nan kuma ya kai ni wani asibiti aka duba ni tare da min dinki da wanke min mara, sai dai daga lokacin na ji shima Malam Ahmad din ba a bin yarda ba ne, na roke shi ya tafi bbq son ganinsa, idan ya kuma zuwa nasan shima ya zo kwasar rabonshi ne, sai da yayı darıya ya ce mim, “Zan dawo in sha Allah!” Ya juya ya tafi, haka na tako da kafa har gida, kamar yadda likitan ta bani shawara na kula da jikina, haka na saka a raina,  Hajja Mama taso ta fahimci halin da nake çıkı

Nace mata alada nake, haka ta Kayle abin, amma idan na tuna kuka nake.

    N rayuwa da wannan firgicin, har na gama secondary school, na tafi School of nursing, a lokacin hankali ya shige ni, na manta da wani Asad, na fuskanci rayuwata amma na kasa sake nayi koda saurayi ne.

    Haka na cigaba da rayuwa, Ya Man ba yadda bai yi ba na fitar da MIJIN aure amma na kasa, saboda tsoro haka na yi ta mishi aljanun karya daga karshe Daddy ya dauke ni na koma wurinsa a kano, a can na hadu da Muyyasir, dük yadda naso kin maza sai dai gayen nan ya saka ni Jin cewa nima mace ce, domin ya fitar min da abinda nake adanawa na soyayya, ya sani fadawa soyayyarshi.

    Wanda dole na gabatar da shi a lokacin, Ya Bana zai yi aure zai auri Abida, bana sonta domin ta cika nuna isa wata ce, amma haka muka hakura tasan bana sonta dük da muna da dangantaka da Ita,  ita tana Jin haushina wai na shiga rayuwar Yayuna akan idan Ina gida tare da muke zuwa hira gidansu da Ya Bana, wani bin muna zauna zan ce na gaji haka zai hakura mu dawo gida, Kai karshe har nuna mata yayı bai da biyu na a kannensa wannan shine silar da ta tsane ni.

            Ban taba kawo kome a raina ba, domin tunda na gabatar da Muyyasir aka fara turo min sakon ban isa nayi aure ba, har lokacin ban San waye ba, sai da aka saka Rana aka gama kome ya rage biki ne Asad ya bayyana a gare ni, ya min barazana sosai, amma ban yarda na biye shi ba. A lokacin da ya bada sako aka kawo min wata faifen video ne ba shiga dakin Hajja Mama na rufe kofar na saka a laptop dina, a ranar na fahimc na rasa Muyyasir, sai da nayi kwanaki uku Ina kwance ba lafiya, haka aka yi ta samin ruwa, har bıkın ya tumkaro.

   Ina firgice gashi na kasa fadawa kowa halin da nake ciki, ana saura kwanaki biyu Asad ya kara turo min sako, a ranar a kaina aka kwana, washe gari na ji sauki aka yi walima don Ya Man ya ce walima zamu yi,

        Ranar da ba zan manta ba, a kundin tarihin rayuwata, shine ranar daurin Aurenmu, kowa ya shirya tun safe Ina kwance ga baki yan daurin Aure dağa kano, ga Manyan mutane ta ko Ina, wannan abun ya saka ni shiga tashin hankalin yau asirina zai tonu yau duniya  zata juya min baya, babu wanda ya fahimci tsorona ko wani halin da nake ciki, sai da aka fara daura auren Ya Bana da Abida, Hannatu da Saifullah, an zo daurin Aurena, waliyin Muyyasir ya ce a dakatar yana son magana da Ya Man, haka suka fita da Yayuna maza suka shiga çıkın gıda dağa masallacin, waliyin yayi shiru kafin

Ya ce musu.

“Malam kayi hakuri mun kaunaci hada zuria da kai Wallahi, amma wani sako da muka samu ya tabbatar da cewa Yarka bata Jin magana har da zubar da ciki kasan yaran yau mun haife su bamu haifi halinsu ba, Kayi hakuri mun janye wannan auren!” Ba Ya Man ba hatta Ya Nafi’u tsuma yake, zuciyar da ta kwashe Ya Man ya fito filin masallacin ya ce. “An Fasa auren Falilah amma idan akwai wanda yake bukatar sadaka ce zan bashi aurenta.” “Ya Man!” Yayuna maza suka fada lokaci guda, yana juyawa ya kifawa Ya Nafi’u Mari, sai da ya zube a kasa.

  “Akwai me bukata ko babu?”

“Ya Man kada ka yi gaggawa!” Inji Ya Bana, nuna shi yayı da yatsa. “Malam Ina da bukatar Kari, ga sadakina nan ba zan amshi sadaka ba” inji Alhaji Salisu.

    “Ka rike sadakinka sadaka zan baka ita.” Ya nufi masallaci, a wulakance aka bada aurena, sannan ya kira shi har parlor ya gaya mishi abinda ya faru.

         Sannan ya shigo cikin gidan ya wuce daki, da wata itacce, ya Man ya rufe ni da duka. Kun san me? Ina son Ya Man” na fada hawaye na zuba min, na goge na sake murmushin. Shi yake dukana shi yake kuka, ya ce min “Aishatou idan har namiji ne gaki gasu, su cika miki kome da kike shaawa kika kasa hakuri da lokacin aurenki, jamaa ku shaida na zare Falilah a cikin zuria na, idan na ganta cikin gıdana sai na sake Uwarta! A yanzu ma ku fitar min da ita a gıdana na bada sadakarta “ yayuna kuwa ya ce musu. “Allah ya isa dük wanda ya kara kira min sunan Falilah çıkın gidana, kuma ban yafewa dük wnada ya taka ya je inda take ba, ya hada ki da bakin cikin da kika!” “Mustapha Kenan!” Wannan kalmar da Hajja Mama tayi yasa Ya Man ya fasa furucinsa, daga wannan ranar Ya Man ya gina katangar karfe me girma da tsawo a tsakanina da zuriarmu, ana kai Amarya da yan rakiya. Ni haka aka bawa mijina babu kowa sai shi.

   Ya kawo ni fataskum a can ma wani kauye ne………