ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

14

by @gureenjoh

 ball yayi da ita sai da ta faɗi ta sake tashi ya shiga duka, sai da ta fita hayyacinta ya barta a wurin ya yi ficewarsa.


Duk sauran yaran an kora su sun koma an kukkule su ita ce kawai yashe a wurin tana kukan fitan hayyaci.

Sanyin wurin ne ke ratsa ta don daɓe ne na siminti, a hankali ta shiga Miƙewa har lokacin hawayen idanunta basu tsaya ba ganin ba zata iya tashi ba ta shiga rarrafe har ɗakin da Ma'u take, yadda ta ganta babu sutura ya ƙarasa karyata tana kuka sossai ta nufeta ta ɗauketa ta ɗora kan kafafunta.


"Allah ya isa! Allah ya saka mana!"

Ta faɗa tana kuka, kalle kalle take a ɗakin da babu komai ciki ta hangi wani kofa, da kyar ta miƙe taje ta buɗe ta ga bayi ne, ruwa ta tare babu na zafi sai dai bai da sanyi sossai ta zo ta kama 'yar uwarta zuwa ciki ta dinga zuba mata ruwan Ma'u ta sauƙe ajiyar zuciya tana jin ruwan na ƙara mata raɗaɗin da take ciki.


Wanka kawai ta mata suka fito bata san wani taimako zata bata ba, a nan ɗakin suka zauna bayan ta mayar mata da kayan da wanchan azzalumin ya cire ta ɗora kanta kan kafafunta tana cigaba da hawaye me ciwo.


Buɗe kofar aka yi, Uwa ce wacce ke kula da ɗakinsu Jidda ɗin haka ta ji ana ce mata.


"Sannu me 'yar uwa fitsararra ni Shadow bai burgeni ba ma da bai ɓallaki biyu ba, ki wuce ki koma ɗaki"


"Babu inda zan je in bar Ma'u, bakya ganin halin da take ciki? Me muka muku ne kam?"


J da yake kallonsu ta cctv ya gyaɗa kai ya kalli na gefenshi 

"Wannan yarinya akwai abin da ya kamata a mata amma ba yanzu ba, ka ce Uwa ta barta da yayartata a basu abinci kar ayi mana asara..."


"An gama J"

"sannan yaran da za mu tura kasashen waje...Visa's ɗinsu sun fita ina so a fara shirye shiryen tafiyar su"


"Hakan za'a yi"

Yana kai nan ya tashi ya fice daga gidan gabaɗaya shi kuma mataimakinsa Ya fice don faɗawa uwa sakon shugaban nasu.


****


Miƙewa zaune Diva tayi tana kallon Mazan da suke tsaye a kanta saboda haske da suka kunna mata, ta ɗan cije lip tana mutsutsuke ido kan ta sake kallonsu ta tabbatar NDLEA ne.


"Me hakan? Ya za ku shigo mata har ɗaki tana bacci? Idan kuka sameta cikin wani yanayi fa?"

Biggy da shi ne me kula da komai na Jagaban ya faɗa yana shigowa saboda kiranshi da aka yi.


"No! Barsu su yi aikinsu, Big"

Ta gyara zama tana kallonsu, a fuskarta za ka karanci ranta a ɓace yake, su kuma sun zuba mata ido daga ita sai wani long silk gown me hannun vest amma ya sauka har ƙasa kawai ya bi jikinta ne gashinta a ɗaure da Ribbon sakwa-sakwa.


Ta sake cewa 

"Idan kun gama sai ku shirya shari'a da ni don sai na yi sueing ɗinku kun gayamin a wani doka ne aka baku izinin shigowa inda nake cikin kowani yanayi... Me kuka kamani da shi? Ko me aka ce na yi...!"


Ogansu ne ya yayi musu hannu akan su fita.


"Ba ke muka zo nema ba kuma muna da warrant na kama Jagaban don haka ko bincikenmu ya bi ta ɗakin da kike a cikin gidan Jagaban ba matsala ba ce"


Ta sauƙo ta nufeshi tana kallonshi cikin rashin tsoro ta zubawa tag ɗin gaban rigar shi ido.


"Ado Alkali! Wow"

Tana kai nan ta zagaye shi ta fita a ɗakin zuwa parlor sun wargaza komai amma basu sani ba shi Jagaban da taku yake komai, babu abin da suka samu a gidan har ma jikin matasan, karshe suka gaji suka tafi.


"Diva"

Ta waigo tana kallon Biggy


"Baba ya san da zuwansu?"


"Tun kan su zo aka sanar da shi"

Ta gyaɗa kai.


"Waye ne kuma wannan karon?"


"Wani ne Alhj Buba a cikin Layin nan danshi dan sanda ne, su suka shigar da ƙara akan an ishesu da shaye shaye a Layin nan"


Tayi murmushi tana nufar ɗakinta take cewa 

"Gidanshi ne ko haya?"


"Nashi ne!"


"Ka ba ni kudin da zai sayi gidan"

Tana kai nan ta shige ɗakinta.


Ba'a jima ba ta fito sanye da wasu riga da wando kanta facing cap ne, da alama kuma ta sha wani abin wukarta na riƙe a hannunta tana kokarin sakawa cikin wandon jikinta.


Wani karamin jaka Biggy ya bata don bata da shamaki da duk kudin Jagaban, haka kuma Jagaban bai yarda wani ko wata yayi defying ɗin abinda zata aikata ba shiyasa Biggy be ce komai ba, ta saba magance kananun abubuwan nan.


Su Shaly ne suka tare ta a waje suka karɓi jakar, Ta kalli Zubash 

"Muje gidan Alhj Buba mai yaro ɗan sanda"


Zubash ta fi su sanin kowani gida a Layin kuma ta fahimci jagora Diva ke so zuwa gidan don bata sani ba.

Tuni suka yi gidan su takwas, babu sallama ko knock suka faɗa ciki kawai.


Iyalan sun shiga cikin tashin hankalin ganin su haka a kansu 

"Ina me gidan?"

Fitowa yayi 

"Bayin Allah lafiya?"

"Tambaya kake? Ku ne munafukan da kuke shisshigi a abinda ba'a saka ku ba ko?"

Skipo ya shaƙo shi tare da haɗa shi da gini.


"Innalillahi wainna ilaihi rajiun...don Allah ku yi haƙuri ku yi haƙuri"

Matanshi da wasu daga cikin yaran suna kuka suna basu haƙuri, Obafiya ya zaro Adda ya buga kyauren gidan da ƙarfi suka sake firgita a ruɗe suke ta ba da haƙuri.


"Me za'a yi Diva?"


Tana zaune kan wani dakali haka daga tsakar gidan ta harɗe kafa tana kaɗawa bata ce komai ba.

Ta ɗan kallesu sun yi zuru zuru matan da yaran suna kuka.

"Ya kawo takardun gidan duka"


"Ki yi haƙuri wallahi sai da na gargadi yaron nan ashe bai ji ba ya zagaye ya janyo min jafa'i..."


"Mu ne ma jafa'in?"

Shaly ta faɗa tana kai mishi duka Zubash ta tare.


"Shaye shaye ne baka so kuma baka isa ka hana ba, kaje ka tattare komatsanka a yanzu ba sai anjima ba ku bar unguwar nan masu shiryayyun yara"

Zubash ɗin ne ta faɗa.


Pabloo da bai ce komai ba tun fara abin ya daka mishi tsawa

"Kana zaune har yanzu?"


Ba arziki suka cigaba da basu haƙuri amma sun ƙi dole dolen suka shiga ya fito musu da takardun ganin suna kokarin illata shi, haka Diva ta jefa mishi jakan bayan ta karɓi takardun, sai sannan ta sake magana.


"Ka je ka sayi gida a unguwar shiryayyu ka cigaba da zama Na rantse da Allah ko agwagwar gidanka aka ce min an gani a Layin nan sai na sassara duka mutanen gidan nan....idan kana zaton magana nake ku gwada bi ko ta cikin Layin nan ne"


"Ku fice!"

Obafiya ya faɗa da ƙarfi, ba shiri suka fita mutane sun ɗan tattaru a gefe amma babu wanda ya iya yi musu magana saboda tsoro, a haka Alhj Buba suka bar unguwar bayan kayan sawansu sai kudin da ta bayar, su kuma suka garkame gidan da manyan sarkoki suka fice.


Tana zuwa gida ta samu Jagaban ya dawo.

Kirari yayi ta mata tana murmushi saboda tayi ƙoƙari a wurinshi a haka ɗin ta tayashi magance kananun ƙwarin unguwa.


A waje suka zauna ana ta hira sai ga Pascal ya shigo nan aka shiga mishi ya jiki ita dai tana kallonsu kawai da wani yanayi, har lokacin maganganun Shehi basu bar kanta ba tun daga na farko zuwa na ɗazu amma ta ƙi bari ya shiga zuciyarta har yayi tasiri, kawai ta yanke cewa za ta fitar da duk abin da ya shafe shi daga kanta ta haƙura kuma ba zata bari wani abu ya sake haɗa su ba don baya gabanta.


****


"Barka da yammaci mama"

Ta kalli matashin da ke ta fitar da kamshi tayi murmushi 

"Barka dai ɗan saurayi"

"Sunana Khalil, za ki ga na zo ba shawara ko sanarwa, Zubaida ce na gani kuma na ji hankalina ya kwanta ƙwarai da ita idan babu damuwa ina so zan nemi aurenta"


Ta ɗan kama fuska kaɗan kan tace 

"Masha Allah, Khalil shine sunan?"

Ya amsa da eh yana murmushi 

"Baka faɗa min sunan babanka ba kuma kai ma'aikaci ne?"


Ya ɗan kalleta

"Ni ma'aikaci federal government ne Babana retired Navy ne duk 'yan asalin Kano ne mu amma Abuja nake aiki"


Ta gyaɗa kai tana sake kallonshi da kyau

"Ba damuwa zan yi magana da babanta in ya so duk yadda ake ciki za ka ji daga gareni, saka min layinka anan"


Mamaki ya ɗan kamashi amma bai uzzura ba ya saka ɗin ya miƙe ya fice bayan ya ajiye mata dubu ashirin. Baba ya zo gani amma da ya tura a masa iso aka ce baya nan jin da mota ya zo ya sa tace a ce ya shigo, ta dauka tana juyawa a hannunta cikin wani tunani.


"Mama don Allah wannan karon ki bar Yaya Zubaida tayi aure matukar har kun bincika kun ga kyaun halinsa"


"Sannu 'yar iya! Ni zaki gayawa abin da zan yi? Ko aka ce miki 'yar tawa na kananun mutane ne da zan dauka in ba ma'aikaci ga manyan 'yan kasuwa da sunansu yayi shura suna murza kuɗi? Har yanzu ban ga namijin da zan iya bari ya auri Zubaida ba ke har ke! Bana son shashanci..."


Nana hawaye ya cika idanunta tana kallon Maman wani lokacin ta kan tambayi kanta anya matar nan ita ta haife mu? Anya ba sato mu tayi ba? 

"Mama me kike nema ne?"

"Ubanki nake nema...baki san duniya ba yarinya irin waennan masu kyautar dubu ashirin dubu hamsin ana aure ko biyar ba za ki gani ba, gwara ki kama kanki ki san rayuwa"

Takaici ne ya sake zuwa ma Nana har wuya ta tattari takardun karatun ta ta shige daki tana hawaye.


Sai tsakar dare Zubash ta dawo Nana bata yi bacci ba don damuwar 'yar uwarta na hanata sukuni.

"Yaya Zubaida"


"Nana! Baki yi bacci ba?"

"Ban yi ba ke nake jira"

"Lafiya kam? Akwai wanda ya taɓa ki ne? Ke ba zan je makarantarkun nan in ja wa duka ma'aikata da daliban kunne ba kuwa akan taɓaki?"


"A'a yaya Zubaida kar ki sa a koreni don Allah ina tsaka da paper, ba ma makaranta ba ne ina so mu yi magana ne Yaya"

Zubaida ta zauna tana kallonta.


"Ina jinki"

"Ɗazu wani ya zo neman izinin iso gidan nan"

Murmushi me kyau da ba kasafai ake gani ba a fuskar Zubaidar ta saki.


"Alhamdulillah zan aurar da ke hankalina sai ya fi kwanciya Nana"

Nana ta girgiza kai tana jin zuciyarta babu daaɗi.

"Ba a kaina ba ne akan ki ne. Sunanshi Khalil yana da kyaun hali da natsuwa gashi kyakyawa mai rufin asiri, Don Allah yaya Zubaida ki aureshi"

Miƙewa tayi tsaye ranta na ɓaci 

"Khalil ya zo gidan nan?"

Ta gyaɗa kai tana fitar da wayanta don kiran Ghali ta san babu mai kawoshi gidansu sai Ghali za ta mishi rashin mutunci kan ta isa ga shi Khalil ɗin a gobe ba sai jibi ba.


"Yaya Zubaidah Don Allah"

Nana ta riƙe hannunta.


"Ya suka yi da Mama?"

Bayani ta mata Zubaida ta sauƙe wayan tare da wani numfashin baƙin ciki.


"Ko na yi niyya ba zata bari ba shiyasa ma ba zan yi ba Nana, da dai ke ce zan tsaya kai da fata wurin ganin kin samu ingantaccen rayuwa ta hanyar aure da hayayyafa amma waennan kalaman ba sa cikin rayuwar Zubaida! Mama ba zata taɓa bari ba Dukda a yanzu ba don tsoronta ba ne zai hanani kawai ba zan yin ba ne. Ki yi bacci kina da paper gobe"

Tana kai nan ta kwanta tare da juyawa Nanar baya don ɗaki ɗaya suke.


Shi dai Khalil Allah yana jin son Zubaida har jininshi, kuma abin da ya gani na Red flags daga mahaifiyarta ba shi zai sa ya ji ya fasa aurenta ba.


*****


Yana zaune gaban Maamah yana shan Kunun gyaɗa da farar Safiyar don Dutse za shi, a natse yake sha har ya gama yayi hamdala Maamah ta saki murmushi.


"Da ma ina son Magana da kai Shehi"

Ya gyara zama yana bata dukkanin natsuwarsa.


"Ammie ta kawo min ƙararka"


Ya san kwanan zancen, idanunsa na zube kan bandage na hannunshi da yake nan fresh ta ce 


"Maamah na so zuwa amma ban samu lokaci ba ne"


"Ya kamata ka samu ka je ɗin Shehi, kai ne babba duk ƙannenka mazan har Ammar ka tare musu hanya, Ammie kullum tana cikin damuwar rashin auren nan naka don mata dayawa an kawo ka ce ba haka ba kai ka ƙi fitar da naka har yaushe za mu cigaba da zuba ido uhmm?"


Ya sauƙe numfashi kaɗan yana ɗan cizan labbanshi.

"Ku yi haƙuri zan je"


Maamah da ta sanshi sarai ta ce 

"Ba ni rana, muddin ka bani ranar zuwa na yarda zaka je ɗin amma kalaman zan je basu da tabbas a wurinka"


Ya ɗan murmusa kadan 

"Ko sunday ne sai mu je da Ammar"


Kai ta gyaɗ