...BASHI!

Page 8

by @sanazty

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

                   Page 8

__________🖌️Tun daga nesa ya hango yadda Doctor ke faɗa, da kuma yadda Umma ke ta zubar da hawaye.
   Yana ƙarasa gurin a dai-dai lokacin Doctor ya juya ya tare tare da nurses ɗin dake biye dashi.

Jikinsa a sanyaye yake kallon mararsa lafiyar dake ɗakin kafin ya mayar da idanunsa ga Sadiya wadda ke kwance kamar gawa, hannunta yana kan cikinta. Fatar jikinta gaba ɗaya tayi duhu yayinda idanunta sun kumbura, kuma zageyen idanun sun yi baƙi. Ciwon dake goshinta an cire bandejin sai dai an liƙa auduga da alamun ciwon bai gama warkewa ba.
   Sam bai san cewa haka ya ɗauko ta jiya ba, bai taɓa tunanin har haka take jin jiki ba, domin ya san duk wanda za a sakawa oxygen to numfashin sa ne ya samu matsala. Ga kuma zagayen idanunta da ya yi baƙi sai kuma fatun idanun sun kumbura, sam bai fahimci hakan ba a jiya sai yau.

Har zai tsaya gurinsu sai kuma yabi bayan Doctor da sauri.
  "Doctor..." Ya tare shi a waje.
   Kallon shi ya yi sannan ya ce "Ni?"
 "Eh... Ina son nayi magana da akai a kan patient ɗin da ka duba yanzu."
  "Sadiya?"
"Eh...! Ina so nayi magana akan abinda yake damunta"
   "Okay, ko zamu ƙarasa office?"
 "Okay babu damuwa muje"
 
Doctor na gaba yayinsa Habib ke bin bayansa har suka ƙarasa office ɗin. Sai daya sallami nurses sannan ya mayar da kallonshi ga Habib.
  "Ya kake da waɗan can mutanen?"
   "Am.... Ita ɗin ƙanwata ce"
   "Okay... But kamar ma na san face ɗin nan, Habib right?"
  "Ni ne!" Ya furta a taƙaice.
   "Amma Habib ya aka yi ƙanwarka suna cikin wannan matsin amma ka kasa yin wani abu akai"
   "She's my Cousin Sister sannan ban san cewa suna cikin wannan halin ba sai yanzu"
  "Eh to da yake yanzu zumunci ya yi ƙaranci, kuma ma naji sun ce ba a gari suke ba, amma raina ya ɓaci a kansu, suna wasa da rayuwar yarinya"
   "Doctor! Please go straight to the point, ina son sanin meye matsaya yanzu?"
    "Ƙodar dake jikinta fa gaba ɗaya biyun sun samu matsala, idan har ta ƙara kwana uku ba batare da an yi mata aiki ba to zata iya rasa rayuwarta, amma abin mamaki sun kasa samo kuɗin da za a yi yarinyar aiki, ga shi a ɗayan ɓangaren ta kamu da cutar paraplegia"
  "What...?" Ya furta da mamaki, sannan ya dafe kai.
   Ƙara ɗago kai ya yi sannan ya ce "Nawa ne kuɗin aikin?"
   "7M"
"What? Are you serious?"
  Ɗan murmushi  Doctor ya yi sannan ya ce "Ai da private hospital kaje, abinda zasu cajeka sai ya fi haka"
  "Nayi tunanin abinda za a kashe ba zai wuce 1M ba"
  "Dashen ƙoda fa za ayi mata"

Tashi ya yi, jikinsa gaba ɗaya ya yi sanyi. "Yaushe zaku kawo dan gaskiya tana jin jiki sosai wallahi, a cikinta take ji, sai dai wani ciwon ya danneta shiyasa ma ko motsi bata yi sai numfashi"
  "We will think about it, dan naji kuɗin suna da yawa"
  "Okay ba matsala." 

Ɗakin ya koma har lokacin Umma na hawaye yayinda Inna ke ta mata nasiha.
  A jikin gadon ya tsaya sannan ya gaidasu. Inna ce ta amsa ita kuwa Umma sam ta kasa tsayar da hawayenta.
  "Ya mai jiki?"
"Gata nan da sauƙi za a ce"
  "Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne"
  "Amin ya rabbi" 

"Am...Inna sun faɗa maku abinda ke damunta ko?"
"Eh sun ce ƙoda ce, kuma ana buƙatar kuɗaɗe wanda mu kanmu bamu taɓa ganin kqatankwacinsu ba"
"Hakane! Amma irin wannan dagewa ake a nema, a tuntuɓi ko ƴan uwane a samu a haɗa"
Sai lokacin Umma ta kalleshi ta ce "Ka ga dan Allah mun gode, amma surutan nan naka sun ishemu"
"Haba Lami, wanda ya nuna ya damu da kai ai kaima ya kamata ka gode masa ba irin wannan kalaman ba"
"Inna to ina ruwansa? Mene zai zo ya tasamu a gaba yana irin wannan magnganun, ya fimu sonta ne? Ai muma muna ƙaunarta, Inna shin ko gidan mahaifinta da suka ci gado da aka saka kasuwa nawa akace? Gaba ɗaya Miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu, ko kwatan kuɗin da aka ɓuƙata basu kai ba. Mahaifinta daya cutar da ita gashi ya bar duniyar itama kuma zata bishi, waye zai bamu kuɗin da zamu biyu, a cikin dangina ko danginsa duk rufin asiri kawai damu. Shi kuma yazo ya tsaremu da surutan banza" Ta ƙarasa maganar tare da miƙewa ta bar gurin.

"Kayi haƙuri yaro, tana cikin damuwa ne, saboda su biyu kaɗai ke gareta. Dole zata shiga damuwa"
  "Ba matsala, nima na lura da hakan. Na san baku gane ni ba ko?"
  Inna ta sake dubansa sannan ta ce "Eh gaskiya dai ban shaidaka ba"
  "Nine wanda ya kawoku asibitin nan jiya, to na tafi na barku a damuwa shiyasa nazo in ƙara duba jikinta"
    "Allah sarki, ai bamu ganeka ba, muna godiya sosai, Allah ya saka da alkhairi."
   "Amin Hajiya" 

Inna tuni tayi masa nuni da gurin zama, ai kuma sai hira ta ɓarke tsakaninsu, anan ne take faɗa masa ai Sadiya lafiyarta tana rayuwarta amma a cikin wata guda wannan ibtila'i ya sameta, har ya yi sanadiyyar tsayawar karatunta, daga nan kuma sai Babanta ya ɗauketa ya kuma ƙi faɗa masu inda ya kaita, sai kawai kiransu aka yi aka ce gata anan Aminu Kano, haka suka taho daga Gaya hankali tashe.
  Ya tausaya sosai, har ya ƙara jajanta masu. Kusan mintuna talatin ya ɗauka kafin ya yi mata sallama ya tafi, tare da dubu goma daya ajje masu ya ce su ɗan rage wani abin.

Godiya sosai tayi masa, har ya tafi Umma bata dawo ba.

                ***** ***** *****
Murmushi tayi lokacin data zauna akan gadon da Fa'iza ke kwance, ƙafa tasha naɗi na karaya da aka mata.
  "Ƴammata masu tsoron mutuwa" Aziza ta furta tana faɗaɗa murmushinta.

Fa'iza ta kalli Daddy ta ce "Daddy kana ganin tana tsokanata ko?"
  "Aziza idan kika cigaba da tsokanarta ranki fa zai ɓaci"
   "Afuwan Sister" Ta faɗa tana murmushi.

"Meyasa Yaya bai zo ba?" Fa'iza tayi maganar tana kallon Aziza.
   "Ya ce ya daina yawo, na manta ya ce idan nazo in kirashi a waya ya dubaki"
  "Allah sarki Yayana"
Sai a sannan Daddy ya ce "Ina ita mai jinyar taki ta tafi?"
  "Wasu baƙi ne suka zo shi ne taje ta kaisu ɗakin da Mommy take su dubata"
  "Okay"
"Daddy amma dai ka dawo kenan ko?"
 Murmushi ya yi bai kai ga bata amsa ba aka turo ƙofar.

"Kawu ashe ka shigo, barka da zuwa"
   "Yauwa Farida ya mai jiki kema kuma ya ɗawainiya"  
  "Alhamdulillah jiki ai ya warware"
  "Allah ya saka ya kuma bar zumunci"
  "Amin Kawu"

Miƙewa ya yi tare da faɗin "Bara na ƙarasa gun Rukayya idanunta biyu ko?"
  "Eh ta farka, ai itama naga jikin nata Alhamdulillah"
  "Ma sha Allah"

Yana fita Fa'iza ta kalli Aziza ta ce "Wallahi daɗi nake ji da Daddy ya dawo"
  "Nima haka, ai baki ga hirar da muka sha jiya ba."
  "Ayya anyi babu ni kenan"
  "Ai yau ya ce min a gurinki zai yini.

                      *****
"Zuwa kayi ka ƙarasani?"  Ta faɗa tana kallonsu.
"Haba Rukayya kar kice haka mana, in ban yi fafutukar neman lafiyarki ba, ai ba zan so na ƙarata ba"
"Rashin lafiyar tawa ai kaina sila" Ta faɗa tana kallonshi.

Naja'atu wadda ta kasance ƙanwa ce itama a gurinsa ta ce "To bari na baku guri ku tattauna" Bata ko jira abinda zasu ce ba ta fice.
"Kin san in ban da aiki ya yi min yawa acan, da babu abinda zai saka na tafi na barku"
  "Amma tun kana nan Muhasin ke fama da matsala, kuma zuwa lokacin da ka tafi abin ma ƙaruwa ya yi, amma ka kasa zuwa kaga halin da yake ciki, idan kuma da ya mutu fa? Ban taɓa tsammanin baka son 'ya'yanka ba sai yanzu"
  "Kina bani mamaki Rukayya, tun ina can kike faɗin bana son su, idan har bana son su zan bari ki haifa min su? Ko kuma zan kula da rayuwarsu tun daga ƙuruciya har girma"
  "Kenan ni ce baka so? Tun kafin in haifi Muhasin na fara fuskantar wulaƙanci na rashin ƙaunar da danginka ke min, duk da cewar ni nayi faɗa da nawa ahalin saboda kai, amma sai ka riƙa tsallakewa ka tafi ƙasashe ka barni, har gashi na tara 'ya'ya amma halinka bai sauya ba, wane irin arziƙi kake so ka tara, kai kanka a yanzu bana jin ka san adadin kuɗinka, amma a haka ka kasa bayarda just 10M"

Ɗan murmushi ya yi sannan ya ce "Rukayya kenan, 10M kike cewa just saboda kina zauna ake turo miki, amma ni da nake nemowa na san muhimmancin su, dan haka ba zan iya ɗaukar zunzurutum kuɗi na bayar kawai dan wata buƙatarki ta iska, wai 'yar aiki just imagine"

"To ai ta rasa rayuwarta kaji daɗi ko?"
  "Ni rayuwarta ba a hannuna take ba, sannan bani na ɗaura mata ciwo ba, haka nan bani zan cire mata ba"
   "Na gani ai, ba sai ka ƙara tabbatarwa ba, to ɗanka ma ka kasa bare na wani"
  "Rukayya kiji tsoron Allah. Akan rashin lafiyar Muhasin nawa na kashe ina nan? Sannan bayan tafiyata nawa na kashe, nine kawai baku gani, amma duk wata ɗawainiya na ɗauke muku fa, me kuka rasa?"
  "Kai...! Mu ganinka a kusa damu yafi mana wani abu da zamu kashe ko wasu maƙudan kuɗaɗe da kake saka mana a ccount. Yanzu kamar Fa'iza kuɗin da kake tura mata sun yi yawa ina zata kaisu?"
  "Gashi nan tayi hankali kuwa tunda Aziza ta faɗa min cewar ta buɗe makeup shop da botique ta kuma sayi mota kin ga kuwa at least ta yiwa kanta tanadi ai"
   "Botique ɗin da Makeup shop na bada kuɗi an ɗebi ma'aikata, amma mota kuma na ƙwace, SS3 fa zata shiga meye na dogon buri tun a yanzu"
  "Ah gaskiya bai kamata ba, taya sauran 'yan uwanta na da motoci ita kuma ki tauye mata"
  "Ba zan bawa Fa'iza mota ba har sai ta gama makaranta wannan shi ne hukuncin dana yanke. Su 'Yan uwan nata ai ma'aikata ne kum sun kai su hau"
  "Ita ma haka, nawane 'ya'yan masu kuɗi da zaki ga ƙanana ne amma suna murza sitiyari, ai idan kana dashi asan kana dashi"
  "Ni ban yarda a kan Fa'iza ba"
  Murmushi ya yi yana faɗin "Na ga dai rigima kike ji bari na ƙyaleki"
  Harara ta watsa masa sannan ta ce "Ai wannan rigimar tun kafin na haifi Muhasin, lokacin ina amarya kana kula dani"
   "Oh na shiga uku ni dai na tarowa kaina." Ya ƙarasa faɗa yana saka hannu a baki yana rufe fuska.

          ***** ***** *****

Wasu mutane daya hango akan benci ya ƙarasa gurinsu, ya gaisa dasu cikin mutantawa.
  "Sunana Kamal Alqali daga CID, nazo nan ne domin ganawa da wata Lami Mahmud kuma na tarar da gidan a kulle"
  
"Ai sun daɗe da tashi gaskiya, dan a ƙalla zasu ɗauki sati biyu ba"
  "Ko kun san inda suka koma?"
  "Gaskiya ni dai ban sani ba."

Ɗayan ne ya ce "Eh to kamar fa naji ance suna Kano, ita tana aaibiti an kwantar da ɗiyar tasu.
   "To ai muma binciken namu tun daga can ne, ka ga kenan faɗuwa tazo dai-dai da zama"
   "To gaskiya bamu da masaniya akan hakan, amma dai ka shiga nan sune maƙotansu, dan na san suna mu'amala dasu"
   "Okay na gode." Ya furta yana barin gurin.

        ***** ****** ******

"Ashe ma hakanan kake zaune ba aiki kake ba" Najwa ta furta tare da zama.
  
Kallonta ya yi yana murmushi kafin ya ce "Najwa sarkin rigima, kin huce dani kenan?"

"Sanin da kayi bana iya fushi da kai, shiyasa kake min abinda ka ga dama"
  Murmushi ya yi, sannan ya ɗan juya yana kallon ƙofa.

"Ya dai?" Ta faɗa tana kallonsa.
  "Wai ina dubawa ne in gani ko baki taho min da Sojanki ba"
  "Ka ganka ko? Ka kiyaye ni"
  Murmushi ya sake tare da faɗin "Kin san ni matsoraci ne, musamman idan aka ce soja"
   "Ni fa babu wani doja da zan aura gara ma ka sani"
  "Ba dai kin canza sheƙa ba, to wallahi ki bi a hankali kin san dai ba a wasa da soja"
   "Kai ka sani." Ta faɗa tana ɗan harararsa.

"Wai kin san mene?"
  "A'a sai ka faɗa"
"Ina wannan yarinyar da muka kai asibiti jiya?"
  Jin haka ya saka Najwa ɓata fuska.
  "Kwantar da hankalinki ba fa wani abu bane, kawai dai ina son na faɗa miki ne abin ya tsaya min"
  "Me kenan"
"Ashe wai Kidney ɗinta gaba ɗaya biyun sun lalace, dole sai an mata dashe"
  "To ko taka zaka bata?" Ta faɗa rai a ɓace.

Ɗan zaro ido ya yi, tare da faɗin "Ni da ko allura bana so, taya zan yarda har an farkeni in kuma bayar da ƙoda"
  "To ai na ɗauka ma bata zakayi"
  "Kuɗin da za ayi mata aiki yana da yawa amma ba dan haka ba dana taimaka musu"
  "Lallai, sannu sheik" Ta furta tana kallonsa.

"Wai mene haka? Na ga tun da muka ɗauketa ranki a ɓace, har gabar kwana biyu kikayi dani"
  "Saboda kishinka nake. Naga baka gane ba har yanzu, to zan faɗa maka a yanzu, kai nake so Habib kuma kai nake so na aura" Ta furta tare da miƙewa tsaye.