Page 9
by @sanazty
*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
Page 9
__________🖌️Da ido yake bita ita kuma ta kama ƙugu kamar wadda ke shirin yin dabe.
Fashewa da dariya ya yi, ta kalleshi rai a ɓace "Oh dariya ma kake kenan?"
"No ba haka bane, kawai dai maganar taki ce kina yi kamar irin wani serious issue"
"Au wai da wasa ka ɗauka?"
"Ai bana na ɗauka ba, hakan take ma"
"To ba easa nake ba, ka saka a ranka Najwa t Habib ce"
"Kin ga ni karki kashe ni da dariyarki, kin san mene?"
"Sai ka faɗa"
"So nake na fitar da wani album amma wannam karon ke nake so kiyi min amshi"
"Baka da damuwa indai nice"
"Kin san kwana biyu ban fitar da waƙa da voice na mace ba, dan tunda kika faɗa soyayya kika daina samun lokacina"
Harara ta watsa masa kafin ta ce "Ka ga ka ƙyaleni da maganar soyayya in dai ba so kake muyi faɗa na biyu ba"
"Season 2 kenan, an gama 1 ai"
"You are on your own"
Dariya yi sannan ya ɗauko book ɗin daya rubuta mata waƙar yana rerawa ita kuma ta kafeshi da ido.
Sam ya kasa gane tsananin son da take masa, duk da ta kan faɗa masa, amma shi a sigar wasa yake ɗaukar abin.
"Habib...!" Bata san lokacin da ta ambaci sunan nashi da sigar shauƙi ba"
"Ya dai 'yammata waƙar har ta tafi dake ne kike faɗi sunana da shauƙi haka."
Murmushi tayi sannan ta ce "Wato a duk sanda kake rera min waƙar da za kayi, sai inji muryarka a haka ma tafi daɗi da amsa amo"
"Ehen naji wannan kafcen"
"Dagaske fa nake, muryarka kamar sarewa akwai daɗi, shiyasa shegun 'yammata sai su riƙ nace maka, ka san da ina da hali wallahi fasa wayarka zan yi in hana ko wace 'yar iska kiranka"
"Oh a taƙaice so kike ki kori fans ɗina"
"Eh mana, ai ni kaɗai nake son raɓarka, Habib ga kyau ga iya waƙa ga iya wanka ba dole mata su yi rushing ba"
"Ya isa haka, wannan yabon soja ya kamata ayi wa ba Habib ba"
"Kai fa ana maganar arziƙi kuma kana son ɓata ran ko?"
"Am sorry" Ya furta yana ajje book ɗin akan table ɗin dake gabansa.
Sun ɗan taɓa hira kafin daga bisani ta tafi, tare da alƙawarin zasu haɗu gobe dan ƙara tattaunawa akan album ɗin.
****** ****** *******
A gaban gadon ya tsaya, su kuma suka gaidashi cikin mutunci, dan tunaninsu Doctor ne.
"Kune wanda kuka zo daga Gaya?"
"Eh mune"
"Wacece Lami matar Malam Halliru?"
"Ni ce" Umma ta faɗa cikim damuwa.
Fito da katinsa ya yi ya nuna mata tare da faɗin "Muna gayyatarki zuwa ofishinmu domin amsa wasu tambayoyi"
"Wane tambayoyi? Malam baka ga 'yata ce a kwance ba lafiya ba?"
"Kiyi haƙuri muje, domin tambayar tana da nasaba da rasuwar mijinki"
"Ba zan iya zuwa ko ina ba a wannan hali da Sadiya ke ciki, gara ta rasu a gaban idanuna"
"Dole muje dake, domin umarni ne daga sama" Ya furta yana kallonta.
Ta daɗe tana cijewa har ma sai da abin ya so ya zama hayaniya, kafin daga bisani ta bisu dolenta ba wai dan ta so ba.
"Shikenan! Sadiya haka muna ji muna gani zaki rasu, bamu da wani wanda zai tallafemu, ga itama Lami an tafi da ita." Inna ta faɗa tana fashewa da kuka. 'Yan ɗakin sune suke bata haƙuri.
Ladi wadda a lokacin tazo tare da Ibrahim ta kalli Sadiya da ke kwance ko motsi bata yi, gashi sai ƙara rama take, ƙasusuwan jikinta sun bayyana.
"Inna karki fidda ran ganin Sadiya ta tashi, cuta ai ba mutuwa bace"
"Kina gani kullum ba ruwa kawai ake saka mata, ko abinci sai ta hanci ake ɗura mata koko, shi ma sau ɗaya a rana, ga duhun da take saboda lalatattun ƙodojin dake jikinta, gaba ɗaya dangina dana mahaifinku bamu da arziƙin da zamu iya haɗa kuɗin da aka nema, dama dai dangi ba wani yi maka suke ba, kina dai gani ko dubiya ba kowa ne yazo ba, bare har suce zasu bayar da wani abu. Ga ita kuma Lami sun tafi da ita."
"Babu komai ai Allah baya bacci, kuma shi ne zai kawo mana mafita. Inn ina ganin yau kije ki kwana a can Burget tare da Ibrahim ni zan kwana da Sadiya"
"A'a ba zan iya tafiya in barta ba"
"Inna kema kina buƙatar hutu, sati guda ai kin yi ƙoƙari, nima yanzu dana zo sai in yi sati guda kafin nan kin samu kin huta. Naga Baffa ma anan yake yini ashe, na baro shi acan waje ya ce shi ɗinma sai dare yake komawa Burget ɗin, idan kuma ya ga abu ya yi tsamari anan waje yake kwana"
"To ya zamuyi, dole ai mu zauna muga yadda Allah zai yi damu, hukuncinsa shi ne dai-dai"
"Inna duk da haka kuna buƙatar ku huta, saboda jikin tsufa, dan Allah yau ke da Mallam ku tafi ku ɗan samu ku huta, ni zan zauna anan da ita, sai ku tafi da Ibrahim"
"Ni dai ina tare da Adda" Shi ma Ibrahim ɗin ya furta kamar zai yi kuka.
"Gobe da safe ai zaku zo, ka ga ba'a barin yara su kwana anan" Ta faɗa da sigar rarrashi.
"Wane hutu kike tunanin zan samu Ladi? Kina ganin dai Sadiya a kwance, Halliru ya rasu ga kuma Lami a hannun hukuma"
Ajiyar zuciya Ladi ta sauke bata sake cewa komai ba.
*2 weeks later*
Yana kwance a kan gadonsa yaji knocking. Ɗan lumshe ido ya yi tare da sauke ajiyar zuciya sannan ya ɗauko rigarsa a zura.
"Come in" Ya furta yana kai dubansa ga ƙofar.
"Mama ashe kece" Ya furta yana kallonta, ita kuma bata bashi amsa ba har ta zauna.
"Habib...! Ka faɗa min gaskiyar mene ke damunka?"
"Babu komai Mama, kawai dai zazzaɓi ne na kwana biyu" Ya furta yana ɗsn cije leɓe.
Miƙewa tayi ta nufu side drawer. Ji ya yi gabansa ya faɗi, ya kawar da kansa gefe lokacin data fito da ledar magunguna.
"Wannan uban magungunan duk na mene?"
"Naje an rubuta min a asibiti"
"Ba inda kaje nake tambaya ba, na mene?"
Ɗan ɓata rai ya yi, kafin ya ce "Na zazzaɓi ne"
"To ai ko bana aikin asibiti na san yanda magungunan zazzaɓi suke saboda nima ina amfani dasu"
Shiru ya yi, bai ce komai ba, sai data ƙara ce masa "Ka faɗa min meke damunka? Domin naga kwana biyu baka da kuzari, ko studio baka zuwa ga kuma baka son cin abinci sosai"
"Mama dan Allah karki tsananta bincike, kin dai san bana miki ƙarya dai"
"Idan ma baka yi to a yanzu ka fara, domin wannan magunguna basu yi kama dana zazzaɓi ba, tunda kaƙi faɗa min gaskiya zan kira Najwa ta duba ai ita aikinta ne na san zata san na mene"
Miƙewa tayi ta fita daga ɗakin shi kuma ya dafe goshi da hannu tare da lumshe ido.
Tunda ta fita yake kiran Najwa amma taƙi ɗagawa da yaga dai haka sai kawai ya tura mata text, sannan ya kwanta yana sauke nufashi.
***** ****** *****
"Gani nazo" Ya ji maganar kamar a mafarki. Da sairi ya buɗe ido, sai kuma ya ga mace zaune a gefensa.
"Wacece ke? Mene ya kawoki har cikin ɗakina?" Ya faɗa lokacin daya miƙe, tare da ɗaukar rigarsa da sauri ya zura dan singlet ce kaɗai jikinsa.
Taɓe baki tayi sannan ta ce "Ko baka gane ni ba?"
"Kin ga koma dai na ganeki ko ban ganeki ba, ina so ki fita parlour mu yi magana"
"Anan nake si mu yi duƙ maganar da zamuti da kai Muhasin" Tayi maganar cikin faɗa.
"Wacece ke? Sannan taya kika samu gots ɗin shigowa har cikin bedroom ɗina.
"Bilkisu Abdulrahim, wadda ta baka complement card ɗinta."
Kallon mamaki yake bin ta dashi, har ya ɗaga baki zai yi magana tayi saurin tarar numfashinsa da faɗin "Naso kazo inda nace kazo, domin in ɗauki fansa, amma sai kaƙi zuwa shiyasa na biyoka har gida"
"Fansa kuma?"
"Eh"
"Tame?"
"Baka buƙatar tuni, amma ka sani nazo ne in kasheka, yaau zaka biya bashin daka ɗauka...hahahahhh" Dariyarta ce ta karaɗe ko ina.
Jin an taɓa shi ya farka a hargitse.
"Lafiya kuwa?" Daddy ya faɗa yana kallonsa.
Aziza ta zauna gefensa tare da faɗin "Shigowarmu kenan muka jiyo ihunka"
Zufar data karyo masa ya saka hannu ya goge tare da faɗin "Wani mugun mafarki nayi, kuma a mafarkinma tashina aka yi shiyasa ban ɗauka mafarki bane."
"Kayi addu'a kafin ka kwanta?"
"Ai ban ma san bacci ya ɗaukeni ba"
"Ya kamata ka kasance cikin addu'a koda yaushe" Cewar Aziza.
Shi kuma Daddy ya ƙara da faɗin "Ya kuma kamata ƙa fara shirin tafiya tun yanzu, saboda Rukayya da Fa'iza gaba ɗaya sun samu lafiya"
Jin haka ya saka Aziza ɓata rai. "Ni gaskiya ban son ya tafi shi kaɗai, domin akwai haɗari"
"To su nawa kike so su tafi"
"Ni dashi"
"Ba zai yuwu ba"
"Amma Daddy kana ganin larurarsa fa, kuma kaƙi faɗa masa garin da zai je bare in muka ji shiru nu bi sahu"
"Babu wanda zai sni sai shi kaɗai" Yana gama faɗa ya miƙe ya fita.
"Ina son samun lafiya Aziza, dan haka koma ina ne dole zanje"
"Amms ya kamat ai mu san ina ne, dole sai nayi convincing Daddy ya faɗa min" Ta furta tare da miƙewa ta fita.
A hankali ya miƙe, ya ƙarasa jikim mirrow sannan ya janyo drawer ta biyu.
Complement card ɗin ya kalla.
"Rigacikum" Ya furta a fili sannan ya sauje ajiyar zuciya tare da manna bayansa da bango.
Zuciyoyinsa ne suka fara masa wasa, domin wannan na cewa yaje, yayinda ɗayan ɓangaren na gargaɗinsa da kar ya je.
A ƙarshe dai ɗaya ta rinjayi ɗaya, dan haka ya faɗa wanka a gurguje ya yi wanka ya gama.
Bai tarar da kowa a parlour va, dam haka ya wuce farfajiyar gidan tare da shiga motarsa.
Aziza sai jin ƙarar buɗe gate tayi, ta windown ɗakinta taga fitar motarsa da sauri ta fito amma tuni ya yi nisa.
Komawa tayi ta ɗauki waya ta kirashi, sai dai kuma bai samu damar ɗagawa ba. Ta kira yafi sau uku amma bai ɗaga ba.
A wannan complementary card ɗin ya riƙa bin address ɗin har ya kaishi ƙofar katafaren farin gate.
Maigadi ya buɗe ƙofa ya fito. Shi kuma ya sauke glass.
"Barka da zuwa"
"Barkanka dai. Am....nan ne gidansu Bilsu Abdurahim"
"Eh nan ne, ko kaine Muhasin?"
"Eh amma ya aki ka sani?"
Murmushi ya yi tare da faɗin "Ai kullum sai ta ce min wani baƙo mai suna Muhasin zai zo nemanta, sannan ta fasalta min yadda kamaninka suke shiyasa na gane."
"Allah sarki" Ya furta, shi kuma mai gadi ya koma tare da wangale masa gate.
Yana zaune a babban falon da yaji kayan alatu, kallon falon kawai yake ya ƙayatu sosai, white parlour mai ratsin black.
Yana nan 'yan aiki sai sunturi suke suna kawo kayan ciye-ciye.
Shi dai bai taɓa komai ba, saboda hankalinsa ma ba a kwance yake ba.
"Muhasin ashe dai zaka zo" Ta furta tana murmushi tare da zama kan kujerar dake kusa dashi.
Murmushi na yaƙe ya yi. Tana sante da wani baƙin lace, da ratsin ash a jikinsa, fitted gown dan da ƙyar take tafiya ma da ƙyar take saboda yadda kayan suka kama jikinta sosai.
Ɗan murmushin yaƙe ya cigaba dayi kafin ya ce "Gashi dai na cika alƙawari"
"Ko dai saboda mafarkin da kai ne?"
Kallonta ya yi a tsorace, ita kuma dariya kawai tayi sannan ta ce "Abin ya baka mamaki ko?"
"Ƙwarai ma kuwa domin taya akai kika san mafarkina"
"Kana son ka sani?"
"Gaskiya, domin na shiga tantama"
Miƙewa tayi ta dawo daf dashi tare da hura masa iskar bakinta.
***** ***** *****
Kallonta ya yi yana ɗan girgiza kai. Ita kuma ta nuna kamar ma bata san yana yi, bakinta sake take ƙara duba magungunan.
"Habib!" Ta ambata da mamaki tana kallonsa kafin ta mayar da kallonta ga Mama.
"Rabu dashi ki faɗa min na mene?"
"Mama wannan magungunan sun tabbatar dana ƙarin jini ne da kuma sugery ɗin da aka masa dan ya samu sauƙi sosai.
"Ban gane ba?" Mama ta faɗa tana kallonsa.
"Kenan ka bayar da ƙodarka wa yarinyar da baka san asalinta ba?" Najwa ta faɗa tana kallonsa da sigar tuhuma.
"Ni ban bawa kowa ƙoda ba, kawai dan nayi maganar yarinyar nan shikenan sai kice na bayar."
"To idan kana so mu tabbatar ka cire sigarka mu gani" Cewar Mama.
Shiru ya yi bai cire ba, kuma bai ce komai ba.
"Mama daga kai yarinya asibiti kawai shikenan ance ƙodarta ta lalace shi kuma ya bayar da tashi."
"Yanzu Habib har za a iya cirar wani abu a jikinka baka faɗa mana ba, muna matsayin iyayenka?"
"Mama ni fa taimako nayi, saboda nag...." Bai ƙarasa ba yaji saukar mari a kuncinsa.
Dafe gurin ya yi,ita kuma cikin faɗa ta ce "Kaf family ɗin su a rasa wanda zai bayar sai kai. Kenan yanzu dai ƙoda ɗaya ce ta rage a jikinka" Ta faɗa cikin takaici.
Bai ce komai ba, kawai dai ya sauke hannun daga kuncinta, ya kuma sauke kai ƙasa.
"Yanzu idan kai taka ta samu matsala fa? Wane irin hauka ne wannan?"
Shiru babu wanda ya ce komai.
Sai da Najwa taji shirun ya yi yawa sannan ta ce "Mama ba a sayar da ƙoda ƙasa da miliyan biyar, amma shi yaje ya bayar da tasa a kyauta ga mutanen da bai taɓa saninsu ba"
"To waye ya sani koma kuɗin suka bashi"
"Ni babu wanda ya bani kuɗi, nayi ne domin Allah kawai"
"Mama basu da kuɗin da zasu iya bashi" Cewar Najwa.
Cikin ɓacin rai Mama ta ce "To idan baka koma sun baka ƙodar da suka cire ba, Allah ya isa"
Ido ya zaro yana kallonta.
Sannan ya mayar da ksllonsa ga Najwa, ita kuma ta taɓe baki cikin ɓacin rai.
***** ***** *****
Kallonsu kawai yake, kafin ya miƙe daga gadon da yake.
"Sannu Yaya" Aziza ta faɗa.
Sai a lokacin ya gane cewa a gadon asibiti yake. Yana shirin dira daga gadon Daddy ya yi saurin riƙeshi. "Muhasin ka zauna baka da ƙwari fa"
Aziza kai ta dafe, tare da faɗin "Yaya wai ina kaje ma?"
"Ya aki nazo asibiti?" Shi ma ya mayar mata da tambaya.
"Yaya a bola fa aka tsinto ka. Wanda suka ganka sunce dai a zaune suka tarar da kai kana ta magan kai kaɗai, kafin daga bisani suka ga ka faɗi a gurin. Sai ma da suka je kanka sannan suka ga key ɗin mota anan suka gane wannan motar da aka parker gefe taka ce, to anan ne ma suka buɗe motar suka ɗauki wayarka, ni kuma ina ta faman kiranka dama tun bayan dana ga fitarka"
"Bola fa kika ce Aziza"
"Ƙwarai kuwa, ni fa ina tunanin gaskiya aljanune suka fara buɗe maka ido"
Wani jiri ya fara ji, dan haka ya dafe kai.
"Aziza ki daina faɗ masa haka." Cewar Daddy. Sannan ya taimaka masa ya kwanta tare da faɗin "Kana buƙatar hutu dan haka ka ɗan samu ka huta" Ya furta ya ɗan shafa masa baya.