...BASHI!

Page 10

by @sanazty

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

*'Yan facebook wannan shafin naku ne, tukwuici gareku, ina matuƙar godiya ga yadda kuke nuna ƙaunarku ga book ɗin nan.*

                   Page 10

__________🖌️Miƙewa tayi ta fita waje, dan zata iya yi masa kuka a yadda take ganin yanayin nasa.
  Akan É—aya daga kujerun Ć™arfe dake gefen É—akin, anan ta samu ta zauna, kuma a daidai lokacin ne wayarta ta fara ruri.
  Kalla tayi ta ga sunan _Lifeline_ yana yawo kan screen É—in, kamar ba zata É—aga ba sai kuma ta É—aga.
 "Kaina bisa Ć™asa"
"Hmmm!" Shi ne abinda ta faɗa ba tare da ta iya ce masa komai ba.. "Kiyi haƙuri sweetheart na san na ɓata miki rai amma wallahi nima na ɗanyi jinya ne"
 "Baka da abinda zaka wanke kanka Hafeez, nayi tunanin ko baka zo dan ni ba, zaka zo dan Yaya, amma ga mamakina sai kawai naga su Mommy su kaÉ—ai babu kai."
"Wallahi ba haka bane, kin san dai ba zan iya tahowa Kaduna in ganki in koma ba a ranar, shiyasa nayi deciding tahowa yau, yanzu haka gani a hanya"

Miƙewa tayi cikin farin ciki ta ce "Ka wanke lafinka, sai kazo"
"Sai nazo, ki duba min Mommy kafin na ƙaraso"
"Za taji insha Allahu."

*_Few Hours Later_*

Yana tsaye jikin gadon da Muhasin ke kwance. "To ai Aziza bata faÉ—a min shi ma Muhasin É—in kwance yake ba" Hafeez ya faÉ—a yana kallon Daddy.
"Shi Muhasin ai ciwon nashi daga jiya ne, kuma da yake ka riga ka san ciwon ai"
"Daddy to ko dai alkanune suka shafeshi?"
"To ba ace a'a ba, tunda mutum da zai je bola ya yi ta surutai in ba shafar aljanu ba menene?"
"Magana ta na gab da zama gaskiya, duk yanda aka yi Muhasin aljanace ta aure shi"

Ajiyar zuciya Aziza tayi tare da faÉ—in "Insha Allah mutuwa zatayi wannan aljanar" 
"Allah ya sa, amma gaskiya Muhasin na shan wuya" Cewar Hafeez.
  
"Ki kai shi gida ya ci abinci ya huta ko?"

Daddy ya faɗa yana miƙa mata key saboda a mota ɗaya suka zo.
  "Daddy ai da mota nazo, ba flight na biyo ba"
  "Okay"

Tun a hanya ake taɓata ita kuma ta shiga shauƙi ta kasa hanashi.

"Hafeez wai yaushe za ai aurenmu ne dai mu huta" Ta faÉ—a a lokacin daya parker motar a farfajiyar gidansu.
"Da zarar komai ya zama normal, kin ga yanzu ga rashin lafiyar Mommy da Fa'iza da kuma Muhasin" Ya faÉ—a yana É—an lumshe ido.
"Allah ya kaimu" Ta faɗa tare da kama murfin mota, kawai sai ji tayi ya riƙo hannunta.
  "Ina sonki Aziza" Ya furta tamkar wani bugagge.
  "Na san kana sona Hafeez"Ta faÉ—a tana kallonsa.

"Ya kamata mu ƙarasa ciki"

Ita ta buɗe ta fita, sannan da ƙyar ya iya fita ya rufe motar yabi bayanta.
Tana shiga bedroom ɗinta shima ya shiga tare da sawa ƙofar lock.

"Yau kuma nan kayo" Ta faÉ—a tana ajje gyalenta akan sofa.

Shi kuma gado ya faÉ—a tare da baza hannayensa. "Kewarki naki taho Babe"
  Kallon shi tayi ta É—an É“ata rai ta ce "Gaskiya Hafeez tsoro nake" 
Tashi ya yi zaune, tare da faÉ—in "Tsoro kuma, name? Ni ne fa mijin da zaki aura"
  "Hafeez ba zan iya ba, ka haĆ™ura zuwa lokacin da zamuyi aure, a baya ma da nayi wallahi har yanzu dana sani nake"
  "Kasancewa dani ne kikewa dana sani?"
  "Sex É—in da nsyi da kai. Domin ko romance É—in da mukeyi ka sani haramun ne, ni gaskiya ina tsoro, kayi haĆ™uri tunda Daddy ya dawo ana sallamo su Mommy a saka bikinmu ko sati biyu ne."
"Dama kin san ba zaki cigaba da yarda dani ba shi ne kika yarda a farko"
"Wancan ma dana yarda ai kai ne kayi ta lallaɓani kuma cewa ksyi daga shi babu ƙari"

Duk yadda Hafeez yaso ya mata dubara su sheƙe aya amma sam taƙi yarda, a ƙarshe ma dai cewa ya yi zai koma parlour ya huta.
  Hafeez kwana yaso ya yi, amma ganin bai samu abinda yake so haka ya tafi, tare da sanar mata da zarar su Mommy sun warke zai turo.

             **** **** ****

Kallonta ya yi sannan ya ce "Mene ribarki akan abinda kikayi?"
  "Haba Habib" Ta furta tare da zama gefen gado.
  "Yanzu kawai sai inje ince su ba ni Ć™oda? Najwa idan kece a situation É—inta zaki so haka?"
   "Ni bama zan kasance a haka ba, domin na san koda bamu da arziĆ™in da za a sayi Ć™odar da za a yi min dashi, to tabbas akwai wanda zai bani"

"Gorin arziƙi kike min ko kuma kina so kice gorin dangi zaki min?"
  "Babu É—aya, domin ka san kafi Ć™arfin gori a gurina"
   "Yanzu duk da kina da dangin, sai in baki tawa Ć™odar, Najwa ba zaki ji daÉ—i ba?"

Miƙewa tayi, dan dama a hasale take. "Ka daina haɗani da wancan mutanen da ban ma san asalinsu ba. Ni na faɗawa Mama ne kawai saboda na sani ka sani abinda kayi ba dai-dai bane, tunda ba saninsu kayi ba"
    "Kenan sai ka san mutum zaka taimakeshi?"
   "To mene haÉ—inka dasu?"
  "Musulunci! Dan haka ni zan taimaki mutum ko da ban san shi ba"
   "Haka kace?
 "Eh"
"Shikenan" Ta furta rai ɓace sannan ta fita.

           ******* ******* 

"Ki faÉ—a mana gaskiya" Ya furta idanunsa cikin nata.
  "Ni bani da wata gaskiya da zan faÉ—a muku wadda ta wuce wannan"

Kallon wanda ke tsaye ya yi sannan ya masa alama da ido.
Shi kuma ya bar gurin. Da leda fara ya dawo wadda ake saka abubuwan da ake suspecting.

Sai daya ajje sannan ya juya ya fita. Shi kuma Mahmud ya fito da hanky sannan ya É—aga ledar.
  "Na san kin gane meke ciki ko?"  
 "Eh naga wuĆ™a"
"To da ita aka yi amfani aka kashe mijinki, kuma da aka bincika shatin yatsunki sun fito a jiki" Baki sake take kallon ledar.

"Ki faɗa mana mene ya yi miki kika kashe shi, domin mun ji labarin ya sakeki, kuma ya karɓe 'ya'yanshi daga hannunki, kenan wannan dalilin ne ya saka kika raba shi da rayuwarsa?"

Kuka Umma ta fashe dashi, sannan ta kalleshi cikin kuka ta ce "Ba zan taɓa iya kashe mutum ba. Ko bayan daya sakeni ban sake zuwa gidanshi ba, sai ranar dana karɓo ɗana"
  "Kuma a washe garin ranar kika kashe shi ko?"
   "Tun daga ranar wallahi ban Ć™ara zuwa gidanshi ba"
  "Taya zamu yarda, bayan ga sahun hannayenki an gani, kawai dai ina so ki faÉ—a mana abinda yasa kika kai shi har lahira"

Sun danbaru amma sam sun kasa gano gaskiya dan haka suka bayar da umarnin a mayar da ita É—akin da ake tsaronta. Kuka sosai take, domin bata san halin da Sadiya take ba, ko ta mutu ko kuma tana raye.

_Bayan Wata ĆŠaya_

"Wallahi a matsayina na mahaufiyarsa ban yarda ba, kawai yaje ya bawa wasu wanda basu san ciwonsa ba ƙoda, haba Alhaji ka duba wannan lamari fa"
   Murmushi wanda aka kira da Alhaji ya yi sannan ya ce "Ni sam ban ga laifin Habib akan haka ba, domin idan kin duba haka nan wani lokacin ake bayar da jini a asibiti, baka ma ga waye za a sakawa ba, kawai ka bayar ne domin Allah"
   "To ai jini da ban, amma Ć™oda fa, haba!"
   "Sai maimaita Ć™oda kike, kada ki manta, ita Ć™oda ana rayuwa da guda É—aya shi kuwa jini idan babu shi babu rayuwa" 
   "To amma tsakani da Allah kawai babu dangin iya bana Baba, to ni dai ban lamunta ba, cikin biyu ayi É—aya, ko dai a bashi kuÉ—in Ć™odar da aka cire ko kuma a bashi Ć™odar shi wallahi" Tana gama faÉ—a ta tashi ta bar parlourn.

Murmushi Abba ya yi sannan ya kalli Habib wanda duk ya shiga damuwa. "Ka kwantar da hankalinka Habib, abinda kayi daidai ne, kuma Allah ne zai biyaka"
   "Abba wallahi tun ranar da abin nan ya faru, har yau faÉ—a take min, bata ko zama muyi hira"
    "Ka rabu da ita, zata sauko, ni na san yadda zan yi mata"
   "Allah yasa"
"Amin zan yi magana da ita karka damu"
   "Nagode Abba"
"Yanzu naga kamar fita zakayi?"
 "Eh zan je studio ne" 
 "Okay to Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a"
  "Amin ya rabbi"

Ya daÉ—e a mota kafin ya yi mata key. Kai tsaye asibiti ya nufa.
   Tun daya hango gadon da aka É—auketa babu kowa ya ji gabansa ya yi mummunar faÉ—uwa. Ya Ć™arasa gurin wanda ke kusa da nasu gadon, bayan sun gaisa ya tambayesu wannan masu jikin.
  "Ai tun jiya da wajen magriba aka sallamesu"
 Shiru ya yi na É—an wani lokacin kafin ya ce "Ta samu sauĆ™i ne?"
 "Eh da sauĆ™i, dan har tana tashi zaune ma. To sai kuma jiya aka sallamesu"
   "To shikenan nagode" Ya furta sannan ya cire dubu biyu ya basu, sukayi godiya shi kuma ya tafi.

Ya rasa dalilin da yasa kawai yake son ya taimakesu, dan ji yake zuciyarsa na turasa burget, dan ba zai manta inda yaje ya É—auko su ba.
   Amma sam ya kasa zuwa, kawai sai ya koma studio, amma kuma bai yi wani aiki cikin kuzari ba, saboda yana ta tunanin ta yadda zai shawo kan Mama.

Bai wani daÉ—e a studio ba, saboda mutanen da suke shigowa, shi kuma gaba É—aya jinsa yake wani iri.

Fita ya yi ya nufi Burget dan hankalin sa ya kasa kwanciya kan ya zauna É—in.

Ya daɗe a cikin mota a ƙofar gidan, domin ya kasa yanke hukuncin da zai zama daidai a abinda yake shirin aikatawa, samarwa da wasu farin ciki ko kuwa mahaifiyarsa.
  A Ć™arshe dai ya yanke hukunci fita, tare da samun yaro ya aika domin ayi masa sallama.

Baffa ne ya fito, kuma yana fitowa ya gane shi, dan haka cikin mutuntawa suka gaisa. "Tun jiya da aka sallamemu nake son in ganka dan mu ƙara maka godiya, to kuma sai ya kasance bamu san a ina zamu ganka ba, ina ta tunanin kar mu bar Kano bamu ganka ba"
   "Eh da yake na san nan É—in shiyasa nace bari nazo"
  "To bismilla mu shiga daga ciki"

Sai nan-nan suke dashi, Inna ma kuwa ta saka masa albarka sosai, sai dai bai ga Sadiya ba, domin ko daya dubata kawai sun amsa masa ne. Haka kawai yaji gabansa yana faÉ—uwa.

"Ai ta samu lafiya sosai, dan da gobe muke shirin tafiya, to sai kuma Baffanta ya ce a bari ta ƙara warwarewa. Tana ɗaki ko zaka shiga ka dubata?"
  "To bara na dubata" Ya faÉ—a tare da miĆ™ewa, ita kuma ta masa jagora.

Ɗakin a tsabtace yake, dan har ƙamshin turaren wuta irin masu arhar nan yake. Sai dai ɗakin ba wani babba bane, sannan ko ledar tsakar ɗaki babu, sai dai katifa madaidaiciya, sai kuma tabarma a shimfiɗe a gefen katifar.

Sadiya tana zaune a kan katifar da littafin ahlari a hannunta. Tunda sukayi sallama ta ɗago tare da amsawa, sai ido da ta bishi. Shi ɗinma ita yake kallo, dan bai taɓa ganinta a zaune kuma ido biyu ba.

Tana da manyan ido, wanda wahala ta saka suka ƙara fitowa, dogayen hannunta ne riƙe da wannan littafin ibada, dogayen ƙafafunta kuma ta miƙar dasu. Bata da ƙiba ko kaɗan, sai ma rama da ta ƙara yi, laɓɓanta round ne yayinda hancinta yayi daidai da fuskar, baya da wani sayi sosai haka faɗi ma. Sannan tana da kwantaccen gashi a goshinta da kuma ɗan saje kaɗan.

Kan tabarmar ya zauna, Inna tayi saurin cewa "Da ka bari an saka maka abin sallah a ƙasa kafin ka zauna"
"Babu komai, nan É—in ma ya yi"

Sadiya dai Inna tabi da ido lokacin da take faɗin "Wannan shi ne wanda ya bayar da ƙoda aka saka miki"
  Kallon shi tayi, cikin siririyar muryarta ta ce "Nagode"
"Karki damu, ni ai yayanki ne"
Inna dai murmushi tayi sannan ta fita.

Ita kuwa Sadiya ta kafeshi da ido tana son tayi masa tambaya amma ta kasa.
  "Ko dai akwai abinda kike buĆ™ata?"
  "A'a kawai ina mamaki ne da aka ciro Ć™odarka aka saka min, dama in aka cire abu a ciki mutum baya mutuwa?" 
Murmushi ya yi sannan ya ce "Shekararki nawa?"

Yatsarta ta É—an ciza sannan ta kalleshi ta ce "Kamar fa sha biyar"
 Dariya ya yi dan yadda ta faÉ—a abin ya bashi dariya.

"To ana iya rayuwa da ƙoda guda ɗaya, amma ita kaɗaice ake iya rayuwa da ƙwaya ɗaya"
"Kenan yanzu kaima guda É—aya gareka tunda ka bani taka?"
"Eh kuma gani lafiya lau kina gani ai"
Murmushi tayi sannan ta ce "Nagode sosai, da baka bani ba da yanzu na mutu fa"
"Ba zaki mutu ba sai lokacinki ya yi"
  "Kuma kaima É—an uwanmu ne?"
  "Ehmana baki sani ba?"
  "Eh gaskiya, ai da yake bamu zuwa ko ina"
  
Shiru ne ya É—an biyo baya kafin ta ce "Tunda naga wata aljana tayi min duka shikenan fa ban Ć™ara gane komai ba sai tashi nayi na ganni a asibiti wai an Inna ta ce wani ne ya bayar da Ć™oda aka saka min, kuma ma bazan Ć™ara tafiya ba" 
  Kallon Ć™afafuwanta ya yi da mamaki, kafin ya yi magana Iya ta shigo.
  "Sadiya ba dai surutu ba, to waye ya tambayeki"

Ɗan turo baki tayi tana kallonta, ita kuma ta ajje lemo da ruwa a gabanshi. "Sai kayi haƙuri da surutunta"
  "Babu komai" Ya furta yana murmushi.

Tana fita ya mayar da kallonsa ga Sadiya, yaga har lokacin tana ta zunɓurar baki, abin birgeshi ya yi, ya sake yin murmushi. "To mene na ɓata rai.

Kallon shi tayi sannan ta ce "Sune fa suka min wai za a saya min keken guragu, ni wallahi ba zan hau keke ba, ni dai sai dai a kaini a warkar da ƙafafuna" Sai kuma ta fashe da kuka a fili.

Ya rasa yadda zai yi, har sai da Baffa dasu Inna gaba É—aya suka shigo.
  "Lafiya kuwa?"
"Muna hira kawai ta fara kuka"

"Sadiya mene ne?" Cewar Inna.
  "Ba kune kuka ce zaku sayo min keken guragu ba, ni wallahi ba zan hau keke ba" 
Jin haka ya saka Inna fashewa da kuka.
  "Haba ke kuwa, to waye zai rarrashi wani?" Cewar Baffa 
Iya ce ta zauna a kusa da Sadiya ta ce.
  "Sadiya kiyi haĆ™uri kin yo, kin ga ai kowa da nashi Ć™addarar"
  "Ni dai sai dai in tafi da Ć™afafuna, ga Ć™afafuna amma kuma ace sai na hau keke"

"Mun ji ba zaki hau keke ba" Baffa ya faÉ—a.
  "To ai cewa kukayi zaku saya min, ni bana so"
  "An fasa saya miki"
  "To yaushe zan iya tafiya da Ć™afafuna?"
  "Da kin Ć™arasa warkewa"

Shi dai Habib gaba É—aya sun saka shi a duhu.

Baffa ne ya jashi suka fita, aka bar Inna da Iya suna sake rarradhunta.
  "Amma naga kamar Ć™afafuwanta lafiyarsu Ć™alau"  
"Likita ya tabbatar mana da ba zata sake takasu ba"
  "Amma wane ciwo ne wannan?"
  "Ya ce ta samu matsala ne a lakarta, zata iya motsa su, amma ba zasu taÉ“a takuwa ba"
   "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Baba accident suka yi ne?"
  "Ko É—aya, wallahi mu dai haka aka kawo mana ita, mahaifinta ne da suka samu matsala da mahaifiyar sai ya karÉ“e 'ya'yan to ita sai ya dauketa ya kaita can wani garin. Bayan ta samu lafiya ta ce mana aikatau ya kaita wai acan Kaduna kuma aljana ce ta zaneta a gidan har ta suma iya abinda ta faÉ—a mana kenan"
   "Ya ilahi"
"Gashi mahaifin ya rasu, mahaifiyar na gurin hukuma, kukan nan da kaga tana yi kullum sai tayi, ta tambayi uwar ta tambayi uban da kuma kuman ƙafar, to har gara iyayen mukan ce idan mun koma Gaya za a kaita amma na ƙafar mun rasa yada zamuyi"
   "LallaÉ“ata za ayi, insha Allah zata amince"
   "Wallahi da ka ganta a haka komai sai anyi mata"

Ji ya yi har ƙwalla ta taho masa, ya ɗan ɗaga idanunsa sama dan kar ta fito.
  "Insha Allah zan dawo zuwa gobe."
  "Allah ya kaimu"
"Amin ya rabbi"  

            ******* *******

_Jihar Katsina ƙarƙashin ƙaramar hukumar Mani, akwai wani ƙauye dake da nisa daga nan amma a ƙarƙashin mani yake sunan ƙauyen Murna, a ƙarƙashin ƙauyen akwai wata rugar fulani mai suna Baye, a wannan rugar akwai wani ƙaton dutse a ƙarshen garin, ta dutsen aƙe hawa a gangara tafiya msi nisa zata kai ka wata rugsr fulani mai suna Unguwar Bello to anan zaka samo maganin ciwonka gurin shahararren Malamin dake garin._ Ajiyar zuciya ya sauke tare da akje takardar da Daddy ya ba shi.

Ji ya yi kan shi yana juyawa, amma ya daure ya riƙe kan gam. Sannan ya mike da niyyar nufar parlour, amma ji ya yi kamar an riƙeshi gam, dan haka ya kasa motsawa daga inda yake.

Tana zaune a É—aki tana jera kayan da aka kawo mata guga, dan bata fiya son masu aiki su jera mata kaya ba, idan ita ta jera tafi ganin kyaun su.

_Aziza_ Taji an ambaci sunanta kamar cikin raɗa. A ɗsn tsorace ta kalli ƙofar closet ɗin ta dake a buɗe, wanda daga nan take jiyo kiran.
  Sharewa kawai tayi ta cigaba da abinda take. Sai kawai ji tayi ruwa ya É—igo goshinta, hannu ta saka ta taÉ“a, sannan ta kalla, sai ganin jini tayi.
 A tsorace ta É—aga ido sama sai ganin mummunar hallita tayi tayo kanta, kafin ta goce tuni ta cafko mata fuska.