14
by @sadisakhna
______👑 *JODA* 👑_____
Na
*Sadi-sakhna*
Ƴar mutan Jama'are
THE TRIO OF TALES
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)
@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp
LITTAFI NA 1
*Warƙa ta (14)*👑
*Jodah*
A zaune nake nayi zugum na rasa mai yakeyimin daɗi,tun dukan da wannan bijimar tayimin ta tozartani a bainan nasi ga tafiyar Abokina hamad, wanda nakejin ba lallai mu sake haɗuwa ba har abada,sannan ga zoben daya bani wanda inna kalleshi zan dunga tunawa dashi, waccar azzalumar da kwace saikace batada su Dayawa a akwatin kayan adonta.
Gabaɗaya na zama wata shuru shuru,shin abinda yafaru ne kokuma baƙom lamarin dana tsinci kaina a ciki kwanannan ne kai ni bansani ba. Rafin dayake gabana na tsirawa ido ina kallon yanda igiyar ruwan take sauya siffa lokaci bayan lokaci,a zahiri shi nake kallo amma cikin kaina cike yake tabb da tunani. Jiya naje wajen horon yaƙi inda nayi shigar maza saboda kada a ganeni,duka ɗaya akayi min na faɗi,saida aka kuzamin ruwa tukunna na tashi. Ban faɗawa kowaba na kama hanya na dawo. Inaa wannan ma ba mafita bace,domin ƙarfinnawa a iya kaina yake banda dantsena kenan. To ya zanyi mutane su kalleni kana su gane baiwata harna taka matsayin danake muradi,sannan na bada kariya ga mutanen da suke nawa. Gashi kuma gargaɗin Baba yakub na ƙarshe a garenin shine kada na kuskura na nunawa wanda sukeda ƙarfi baiwar danake da ita,idan hakan ya fara zasu mori baiwata ne kawai,a duk lokacin da nagaza basu abinda suke so,to zasu jefar da ganga ne bayan sun gama cin moriyarta. Kuma zancensa tabbas hakane,domin ba'a kai ga ko inaba nafara ganin hakan. Tunda abin yafaru bansake fita daga sansaninmu,domin har yanzu bandawo da shirya kallon mutanen danake mallaki a garesu ba. Gabaɗaya sun sakamin tsoronsu a raina,na yarda duk lokacin dana gaza basu abinda sukeso tofah zan zama tsohuwar gangane a wajensu.
"Wai meyake damunki ne Joda gabaɗaya kwanannan tunda wannan abun yafaru kika sauya,babu yawan magana saidai ki kebe gefe ke kaɗai kiyi ta tunani?"
Juyawa nayi a hankali na kalleta da tulelen ciki a jikinta tanata gwigwiyar goruba,kaman Allah ya haɗata da ita. Ɗan murmushi nayi na ɗauki ƙaramin dutse na jefa a ruwa kafin na sake kallonta.
"Tunani"
Shine amsar dana bata a taƙaice,bata sareba ta sake jefamin wata tambayar a karo na biyu.
"Tunani wanne iri?"
"Wanda nasaba fadamiki inayi a kullum Addah Rahilah,jinake kaman ba anan yakamata na kasance ba,inason duniya ne wacce zata kasance inada ƴan cin zuwa inda naga dama,gani nake kaman an katange kifin cikin kaina a ruwan rijiya,yayinda shikuma ruwan kogi yakeso. Inason samun ilimi mai yawa Addah Rahilah sannan inaso nafita naje wajen ummata wacce ita kaɗai ta ragemin matsayin ahalina wannan rayuwar bayan ku dana sameku a wajennan"
Jefar da ƙwallon gorubar tayi kafin ta kaikaita da dabara ta zauna,hannuna ta kama ta riƙe a nata kana tace.
"Bazan hanaki wannan mafarkin ba Joda,amma ki sani a rayuwa ka rungumi abinda yake zahiri a gareka,ki dunga rage waɗannan tunane tunanennaki wanda ke kanki bakida masaniyar zasu ƙare ko ahah. Sannan wajennan ma ai yana ɗauke da ɗumbin ilimin wanda ko farcensa baki sani ba tukunna,mai zai hana ki fara da gamashi kafin kije ga wani..... Ɗazu naji lukman yana cewa za'a fara ɗaukar wanda zasu shiga gasar "Ƙiraan" a cikin bayi,idan aka tantance za'a zabi bayi guda biyu mace da namiji wanda sukayi nasara,za'a basu kaya irinna sauran ɗalibai dazasu fafata na tsawon shekara biyu,idan kikayi nasara a dukka gabaɗaya hukuncin ki shine ƴanci,daga nan kinada damar dazaki iya yin makaranta naki na kanki ko ki zama Malamar jinya mai zaman kanta,sannan zaki iya rubuce rubuce idan idan kin so........."
Jijjiga ta nayi batareda nabari naji mai zatace ba nace zanyi.
"Daɗina dake Joda mazari,ki tsaya kiji inda zancena zai ƙare mana,wannan gasa tanada matuƙar haɗari da wuya,domin manyan ƴaƴan sarakuna zasu shiga wannan gasa,saboda idan kikayi nasara za'a baki wani hatimi dazai iya ɗaga darajarki sosai a gabaɗaya wannan nahiya. Saidai a wannan shekara biyun zaki yi karatu matuƙa,kama dagan na Qur'anin,hadith,shari'ah dakuma Kimiyya da fasaha da kasuwanci,akwai bangare kala kala a ciki, za'a kasafta dukka lokacinki akan neman ilimine kawai,sannan za'a baku abinci ayi muku komai iya karatu kawai zaku dunga yi"
Farin cikine fal a fuskata jin bayanin da addah Rahilah takeyi,kuma Inada damar shiga gasar farko ta bayin tunda ina daga cikin bayin da aka basu damar rubutu.
Tashi nayi da gudu nayi hanyar zuwa sashen ummu hajar,wanda rabona da ita tun ranar da Hamad yatafi ƙasarsu. Addah Rahilah ce take ƙwalomin ƙira kam cewar ina zanje,ban bata amsa ba sai guduna dana cigaba ina dariya.
Razana tayi ta ɗaga ido ta kalleni ganin na shigo da gudu kanta kaman zan bugeta,lomar abincin dazata kai bakinta tayi saurin ajiyewa tana min kallon mamaki. Nima ganin hakan yasa nasha jinin jikina tareda komawa gefe ina sussune kai.
"Lafiya Joda waye ya biyoki?"
"Ahah babu kowa"
"Uhmm naga alama,wai tukunnama ina kike shiga kwana biyu,an cemin bakida lafiya yasa bakya fito aiki,amma banga alamun hakan ba domin marar lafiya bazayyi abinda kikayi ba"
"Uhmm banida lafiya amma na warke yanzu da sauƙi"
"To haka akeso mai yafaru to kika shigo da gudu?"
"Labarine ya iskeni yanzu kan cewar an bada dama ga bayi su shiga gasar ƙiraan shine nazo nafaɗamiki inaso zan shiga nima"
"Kin makara ai,domin jiyyannan na bada jaddawalin sunayen wanda zasu shiga gasar,ke kuma bakya nan ance bakida lafiya,sannan na wanda suke shiga ajine ke kina shiga ajine,baki iya haɗa baki ba taya zaki shiga gasa"
"Wlh na iya Ranki yadaɗe,dan Allah kisakani zanyi,nayi miki alƙawarin zan dage bazan baki kunya ba na iya karatu zan iya "
Kallona take da yanayin dana gagara fassarawa,na tagane na iya karatu kenan tun ba yanzu ba,domin banga alamar mamaki ba a fuskarta dana faɗamata.
"Hmmm Joda kenan duk da kinada wayo amma shekarunki da saura,a zatonki bansan wannan yaron ya koya miki karatu bane,sau nawa zanyi rubutu na ajiye na yanda ake haɗa magani,kawai saidai nasameki kin iya haɗawa batareda na faɗamiki ba. Tsawon lokaci bakisan dama ni nake ajiyemiki ba,a zatonki wato na ajiyene bansani ba kekuma sa'arki ta haska kika gani kika karanta koh?"
Ƙasa nayi dakaina,kuttt kenan tasan na iya karatu da rubutu,cije bakina nayi sai a lokacin na tuna da sunan magunguna danake rubutawa ajikin kwalba idan nagama aiki,ashe fah duk tana gani.
"Karki damu na riga na saka sunanki,domin dama ke kaɗaice wacce shekarunta sukayi daidai da gasar,dan haka bakida abokin karawa,wannan karon bamuda bayi masu matsakaicin shekaru dayawa,dukka mun gwadasu k ke kadaice wacce ta iya karatu da rubutu a ciki ,wanda aka kawo waccar shekarar su shekarunsu basu kai na shiga gasar"
Alhamdulillah wani daɗine mai matuƙar tsuma zuciya ya ziyarci ƙirjina,kenan ni bansani bama ashe har an sakani a ciki Mashaallah.
Durƙusawa nayi hawaye suna zirara daga idanuna,tabbas ummu hajar mai sona ce in ba mai kaunarka ba wazai yi maka haka.
"Nagode Ummu hajar Allah yasaka miki da alkhairi Allah yacika miki burinki duniya da lahira"
Murmushi tayi ta amsa da ameen kafin tacigaba tacewa.
"To amma fah tsugunne bata ƙare miki ba,jiya maza sunyi gasarsu kuma an cire zakara daga cikinsu wanda shima zai jona gasar,dan haka a goben za'a kaiku bangaren tsakiya anan ne zaku dunga karatu dakuma ɗaukar darasi. Akwai ɗalibai dayawa masu muradin shiga gasar,wanda yawancinsu ƴaƴan sarakuna ne na sauran nahiyoyi,shigar bawa cikinsu ke kanki kinsan ba abune mai sauƙi ba ya iya jurewa,abinda yasa kika kalla bayi basacin gasar bawai dan basuda ilimi bane ko kuma ba sa zuwa, illah dai Baƙar wahala,hantara,da kuma ƙasƙantarwa daga wajen Ɗalibai ƴayan masu matsayi shine yakesaka su gudo suce sun haƙura,wasu ma kashesu akeyi a wajen kokuma ayi musu illah,sanin kanki ne babu wanda zai hukunta ɗa mai ƴan ci akan bawa,sannan su kuma zasuyi iya ƙoƙarinsu wajen ganin baki kai labari ba,domin samun nasararki tamkar zagine ga dukkan ɗaukacin masu mulki. Abinda yasa na faɗamiki haka saboda nasan kinada fikira da basirar dazaki iyayin nasara,amma kuma ke macece kuma mai rauni,kinga dai abinda yafaru dake a lokacin da kikayi abota da wanda ba matsayinku ɗaya ba,dan haka kiyi tunani. Zan baki nan da gobe kiyi shawara idan zaki iya shiga garken Zakuna kin a matsayin akuya ko kuma zaki haƙura.
Ga takardar Shiga gasa idan kin amince to ki saka hannu,abi mafi nasara da gasar shine idan kika shiga kinada damar sanin duk wani ilimi dayake cikin wannan makaranta,domin ta hakanne kaɗai zaki iya cin gasar,nasan kuma wannan shine babban muradinki to gashi kije zabi yarage gareki"
Tana gama faɗin hakan ta miƙamin wata farar fata ƙarama mai laushi an rubuta sunana a jiki,a gefe kuma an bada filin saka hannu. Numfasawa nayi na karba daga bisani natashi nabar turakar tata. Raina cikeda zullumin na abinda ta sanar dani.
Tunda na koma zuciyata take cikeda zullumi, ta ƙarfin jiki na nufi Umma hajar ɗin amma sai gashi na dawo da sanyin jiki saboda abubuwan data faɗamin,ko kaɗan gwiwata bata sare ba da ƙudurin shiga wajen,saidai ina so ne nasamo mafita na bayanin danaji daga garetan. Idan har garken zakuna zan shiga to a ganina bai kamata nashiga a matsayin akuya ba,idan banshiga a matsayin Gurege ba,karami mai wayo da tsallake haɗari to kuwa yakamata na shiga a matsayin ciyawa ko tunku, da yanda zan zamo bansan mai nake ba ballantana harsu saka ran nashigane domin nayi gasa dasu.
Kwana nayi ina tunani yanda zanyi,da safe bayan na tashi nayi sallah Fatar na ɗauko wacce take ɗauke da saka hannun Shehu Azhar a jiki, babu bata lokaci ta dangwali tawada na danna babban yatsana a gaban inda aka rubuta Joda da larabci,murmushi nayi kafin nace.
Rigima wata kashe,sannan ba'a taka mataki sai an haɗu da kalubale,shima duk yana cikin ilimi na wannan duniyar da muke ciki.
Fitowa nayi harabar sansaninmu rikeda ƴan kayana,da addah Aneesa muka fara haɗa ido tashigo da akushin Koko a hannunta,ganina da ƙullin kaya yasa tace.
"Kina nufin kin saka hannun Joda,duk maganar da Umma hajar ta faɗamiki,da kuma wanda ni na faɗamiki cewar baiwa ta ƙarshe data shiga gasar wani ne a cikin ƴaƴan manya ya turasata yayi mata ciki,dayaga asirinsa zai tonu ya kasheta,amma shine ke zaki kai kanki kawai don kwadayin ki sami ilimi,idan kin samu ilimin dayafi ƙarfin matsayinki mai zakiyi dashine,bazaki zauna a wajen ummu hajar ba kina ɗan koyon aikin jinyarki ba,muma kina taimaka mana,dahaka harki ƙware tabaki matsayi na mai taimaka mata,idan kin samu wani bawa mai nutsuwa kiyi aurenki ki gadar da ilimi ga ahalinki haka baifi miki ba Joda. Idan dan mahaifiyarki ne na tabbata in akai wasu shekaru zasu barki kije ki dubota,mu dukkanmu babu wanda bai rabuda danginsa ba shima. Sannan Rahilah tana buƙatarki,dake ta dogara akan idan tazo haihuwa zaki tsaya a tareda ita,to idan kika tafi taya hakan zai kasance"
Saurin jijjiga mata kai nayi idona cikeda hawaye, Fasihmman dana kalli Addah Rahilah itama tashigo tana rikeda cikinta,fuskarta ɗauke da damuwa.....hawayenne ya gangaromin wannan karon banyi ƙoƙarin tareshi ba. Nasan duk maganganun Addah Aneesa gaskiya ne,amma......zuciyata cike take da wata ƙishirwa da har yanxu bansha ruwan kasheta ba,zancenta gaskiya ne inda zan shiga yanada matuƙar haɗari,amma zaman nan ɗin ma jinake tamkar a cikin keji nake. Ji nake kaman an halicceni domin yin wata gwagwarmaya da har yanzu ban ma fara taba ballantana na ƙarisa. Duk bayanin dazanyi musu bazasu fahimta ba dan haka bazan tsaya bata yawun bakina ba. Ƙarisawa nayi inda addah Aneesa da Rahilah suke.
"Kuyi haƙuri ƴan uwana,haƙiƙa ina ji banida tamkarku,amma wannan hanya dazan ɗauka banajin zan iya dakatawa ban cimma ba,sannan kada ku damu ba kai tsaye zan shiga wajen ba dole saina shirya tukunna. Sannan ina cikin wajen ai ban tafi ba,idan kinzo haihuwa addah Rahilah nayi alƙawarin zanxo na kasance a tareda ke"
Nasan basu gamsu da bayani na ba,sannan idonsu ya bayyana ƙarara kan cewar basason tafiyar tawa,amma kuma dasuka ga hakan shine muradina sai sukayimin fatan alkhairi kawai.
Bayan na fito daga sansaninmu kai tsaye sashen ummu hajar na shiga,domin yaune nayi alƙawarin faɗamata amsata.
Ban sameta a sashenta ba dan haka kai tsaye Ɗakin haɗa magani na nufa,wayam na hango kujerarta inda tasaba zama bata nan,leƙawa nayi ko akwai abinda tafara bata gama ba,amma na tarar babu aiki a wajen,dan haka saina yanke shawarar kaiwa Baba Almahdi ziyara,tunda ya dawo daga masar bamu haɗu ba.
Ɗakin karatunsa na shiga,yana zaune ya rufe idonsa a gabansa akwai wani zomo wanda yake fitar da numfashi ɗaɗɗaya kaman zai mutu,Hannunsa a ɗora akan zomon ɗata hannun kuma ya ɗora a gadon bayan zomon. Cikeda mamaki nake kallonsa amma kuma banyi magana ba,sanɗa nayi na zauna a gabansa,ina kallon zomon kana kuma ina kallon Baba almahdi,sai can bayan wani lokaci naji yace.
"Ya kika tsareni da ido haka kodai nayi miki kyau ne kin ƙyasa kinga saurayi"
Saurin kauda kaina nayi ina murmushi,idonsa a rufe yake kota ya yaganni oho,nayiwa kaina tambaya.
"Ko ɗaya kawai dai naga kana gudanar da wani nau'in karatune daban taba gani kayi ba sai yau,shiyasa abin yabani mamaki nake kallonka kaida zomon. Mai ya sameshi haka?"
"Sarkin tambaya a iya nan tambayar taki kawai ta tsaya,bazaki tambayi mai nakeyi masa ba sai iya mai ya sameshi kaɗai?"
"Dukka nakeson tambaya,amma ina tsoron tambayoyinnawa suyi yawa ne Baba Almahdi"
Ɗaga hannunsa yayi daga kan zomon wanda hakan yasakata ƙare masa kallo,ganin duk da an sakeshi bai motsaba yasa ta ɗagashi tana duddubashi,kallo ɗaya zakayi masa ka tabbatar bashida lafiya.
"Jeki a can akwai wani akwati da zomo a ciki ki ɗaukomin"
Tashi nayi da rawar jikina domin nasan abune na ƙaruwa da zan samu ,wanda yasabamin hakan idan yaso koyamin wani sabon abu.
Dawowa nayi gabansa na ajiye bayan na ɗauko,buɗewa yayi amma wannan karon zomon mai lafiyane domin daya ɗaukoshi yana ta motsi zai ƙwace,ajiyeshi yayi yana shafashi saida ya nutsu kafin yacemin na saka hannuna akansa kana na rufe ido.
Bayan na aikata yanda ya umarceni shuru nayi ina kallon duhun dayake cikin idanuna,kana daga baya najiyo sautin dattijuwar muryarsa a cikin dodon kunnena.
"Akwai abinda nakeso ki jiyo daga jikin wannan dabbar wanda ake ƙira Ruhush-shifah,wani tsarine na magani dayake buƙatar kaifin ƙwaƙwalwa,nutsuwa lura da kuma zuciya,kiyi amfani da jijiyoyin tafukan hannunki wajen jonasu da kwakwalwar wannan dabba domin ki gano mai yake damunta,wacce jijiyace take aiki wacce batayi,sannan wacce batada lafiyar ina ta nufa sannan wanne irin ciwo rashin yin aikinta ya haifar."
Duhun dayake cikin idona na tsurawa ido,sannan wani sashen na idon zuciyata yana jikin tafin hannuna da zummar san karbar saƙo daga kwakwalwar zomon ta cikin motsin da gudun jini yakeyi a cikin jijiyoyiinsa,har na sare akan bazan ji ba sai naji wata jijiya daga cikin jikinsa tana motsawa a hankali,bibiyarta nafara yi harta kaini ga idanuwansa,da alama bata aiki mai kyau kenan. Buɗe idona nayi na ɗagashi ina kallon idonsa,sai a sannan kula ƙwayar idonsa tayi fari alamar bata aiki ko kuma baya gani sosai.
Kallon baba Almahdi nayi wanda ashe shima niya ke kallo,tun kafin nayi magana ya katse hanzarina tareda cewa.
"Lale da wannan sabuwar ƙwaƙwalwa mai matukar fasaha,ko bakiyi magana ba nasan kin rigada kin gano mai wannan karatu namu na yau yake nufi. Naji Umma hajar tace zaki shiga gasar ƙiraan,bazan hanaki ba domin inada tabbacin zaki iya yin nasara,to amma sai kinyi taka tsantsan da kalubalen dake cikinta. Idan har kin samu lokaci kizo nayi miki alƙawarin zan sanar dake yanda ake warkar da ciwo na jijiya da kuma ruhin ɗan adama idan yakamu da cuta ko kuma baya aiki da kyau.
Sannan ina mai gargaɗarki da kada ki sanar dakowa wannan magana,domin sabon ilimine kuma mai matuƙar hatsari da iya manyan malamai ne suka san dashi tukunna ba'a fara sanar dashi ga ɗalibai ba,idan kikace kiyi amfani da damarki wajen yin bincike mai yawa sannan ki koyi ilimi badan gasar kaɗai ba sai domin yanada muhimmanci Fasihmman ga rayuwa irin taki"
"Naji daɗin yanda kake sanar dani ilimi Baba Almahdi kuma nayi maka alƙawarin zanbi dukkan shawararka wajen ganin na tara sani mai amfani"
Muna cikin hira kamar ta jika da kaka Ummu hajar ta dawo,Abin yake hannunta ta ajiye tana kallon zomayen dasuke gaban Baba Almahdi.
"Baba wannan ilimin kake sanar da ita, amma baifi ƙarfin shekarunta ba kuwa naga nima......."
"Ai har tayi nasarar haɗa ruhinsu waje guda,kuma ta karbi saƙon dayake nasa ruhin kuma tayi nasarar gane matsalar dayake tattare dashi"
Zaro ido ummu hajar tayi tareda zama tana kallona,nikuwa ganin hakan yasa na sunkuyar dakai,ni abinda ya nunamin ɗin ban ganshi ko kaɗan a wani abu mai wahalarwa,ashe abune da wani tun yana saurayi zai fara koya amma har tsufa ya tareshi ba zai iya ganewa ba, Ummu hajar tunda yadawo yake nuna mata amma ta gagara tsallake matakin farko har yau,kuma ilimine da in ta iya zai taimaka har wajen warware sihirin da akayiwa ruhi ba iya gangar jiki kaɗai ba. Hakanne yasa basu tsallaka mataki na biyu ba na haɗa maganin,domin bakasan inane yake ciwo ba taya zaka iya bada magani.
"Baba ka koya mata haɗa maganin kawai,tabbas yanzu na gamsu da dalilin dayasaka kake janta jikinka fiyeda mu dakuma ƴayanmu,ga gano cewar Allah bai bamu irin baiwarka bane,saidai Allah mai yadda yaso gashi yabada ita ga baiwa wanda ake gani a matsayin ƙasƙantacciya"
Jinsu kawai nake har suka gama hirar su kafin tafito nabi bayanta zamuje Sashen da masu gasar zasu zauna.
Muna hanya take sanar dani cewar duk ranar juma'a idan anyi sallah ba'a cigaba da karatu ranar hutuce to na dunga zuwa wajen baba almahdi ina ɗaukar darasi gameda ilimin ruhush-shifah dama sauran wasu manyan darrussan. Amsa mata nayi da toh ina mata godiya,murmushi tayi ta amsa dan yanxu na kula ko kaɗan batayimin kallon baiwa marar daraja,face matsayin ƴar adam wacce Allah ya azurta da wata baiwa.
Babban gini muka dosa wanda yafi kowanne gini tsawo a wajen,kana gani kasan ana bawa wannan gasa muhimmanci sosai,gabana ne yafara bugawa fatt fattt lokacin da muka shiga wajen,jikina sanye da Doguwar riga Fara sol na farin saƙi mai kyau,na ɗaura ɗan kwali akaina shikuma Shuɗi mai duhu,sannan na ɗaura wani ƙyallen a kunkumina shima mai duhu. Alama ta ni baiwa ce,amma kuma ina cikin rukunin masu shiga gasa,sannan babu wanda zai sakani aikace aikace na bayi,kuma inada damar shiga kowanne ɗakin karatu nayi karatu,kuma na ɗauki kowanne littafi danaga dama.
Muna saka ƙafa a babban ɗakin taron wajen wanda yake cikeda mutane kamar 100 nayi saurin wargaza ɗaurin ɗankwalina,sannan na washe maganina ina rarraba ido kamar wawiya,a taƙaice dai na koma tamkar joda mai shanyewar ƙwaƙwalwa.......... Ance akuya bazata iya rayuwa a cikin garken Zakuna ba,to amma ciyawa fah. To kuma karnaje na haɗuda wacce take ciyawar,ita kuma zata iya cinyeni in su zakuna basu cinyeni ba..........tu muje zuwa dai.
Kucigaba da bibiyar littafin Joda,salon na dabanne kuma ba'a fara ba.
Sadi-sakhna ce ✍🏼
Comment
Like
Share
Follow