...BASHI!

Page 11

by @sanazty

Version:1.0 StartHTML:100 EndHTML:118856 StartFragment:413 EndFragment:118848

*...BASHI!* 

   _Wattpad@SaNaz_deeyah_ 

 

*K.W.A* 

 

_Sadiya S. Adam🌸✍️_ 

 

                   Page 11 

 

__________🖌️"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shi ne abinda ta furta cikin tsananin tashin hankali. 

Miƙewa tayi zaune, gaba ɗaya a jiƙe ta jita tamkar wadda ta zug fitsarin kwance, sai dai tashin da tayi ne ya saka ta ɗan fara jin sanyin AC na ratsa sassan jikinta. 

Sai dai kuma abinda ya ƙara ɗaga hankalinta shi ne rashin gani, domin ta dai ta buɗe ido amma kuma duhu dumɗum take gani, a tunaninta, dare ne. Amma data lalubi side lump ta kunna taga babu abinda ya ragu daga duhun da take gani sai hankalinta ya sake tashi. 

 

A lalube ta isa parlourn gidan, anci   sa'a kuwa Mommy na zaune a parlour tana kallo. 

"Lafiyarki kuwa? Ya naga kina tafiya kamar wadda bata gani?" 

"Mommy ya naga ko ina duhu? Bayan ina jin ƙarar tv?" 

Miƙewa Mommy tayi tana kallonta kafin ta ce "Ban gane abinda kike nufi ba?" 

"Bana gani" Ta furta da muryar kuka. 

 

Mommy da sauri ta ƙarasa ta ruƙota tare da zaunar da ita kan ɗaya daga cikin kujerun parlourn. "Ban fahimta ba, baki gani kamar ya?" 

"Shikenan nima abin yazo kaina Mommy"  Sai kuma ta fashe da kuka, wanda hakan ya ɗaga hankalin Mommy. 

"Ina zuwa bari na kira Daddynki" Ta furta tare da ɗaukar wayarta. 

 

Ta ɓangaren Muhasin kuwa, ji ya yi kamar ƙarfi yazo masa dan haka ya ɗaga ƙafar ya fita zuwa parlour a lokacin kuma Mommy na waya da Daddy. "Mommy mene ke faruwa?" Ya furta bayan ta gama. 

Aziza ta ɗaga hannu tana lalubensa ya zauna kusa da ita. "Mene ke faruwa?" 

"Wai ta daina gani gaba ɗaya" Cewar Mommy. 

"Kamarya kin daina gani, kina nufin baki ganinmu?" 

"Bana gani ɗan uwa, ko ina duhu kawai nake gani, na ɗauka ma dare ne ya yi" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Muhasin ya furta yana kallon Aziza wadda idanunta suke a buɗe amma sun kalli sama, kuma ga dai idanun lafiya lau babu alamar suna tare da wani ciwo. 

 

"Shi ne matsalar gidan nan amma yaƙi barin gidan" Kawai suka ji muryar Daddy ta furta hakan lokacin kuma ya ƙaraso cikin parlourn. 

"Me kake faɗa haka, haba Alhaji" Cewar Mommy. Gaba ɗaya sun miƙe tsaye hatta ita Aziza. 

"Da nayi shiru dan kar aga ina aibata ɗana amma abin is getting much" 

"Daddy wai me kake son faɗa ne, wallahi Yaya ba shi bane" 

"Wallahi ko ku yarda ko karku yarda akwai maita ko kuma wani tsafin a tare da wannan yaron, shiyasa na turashi can garin dana san ba lallai ya iya dawowa ba, amma tsabar mugunta so yake sai ya gama halaka kowa na gidan nan kafin ya tafi" 

 

Tuni hawaye sun ɓalle a idanun Muhasin. Mommy cikin ɓacin rai ta ce "To ahir ɗinka, kar ka ƙara jifan ɗana da wannan mugun kalamin, domin ba zamu kwasheta da daɗi ba ni da kai" 

"Ai dama ke in dai akan yaran nan ne sam baki son gaskiya, amma yaro gashi sai kisan ɓoye yake kin kasa fahimtar shi ne nakasun ku, da ya bar gidan nan da komai ya lafa, amma da yake shi ne ɗanki namiji guda ɗaya tilo ko, shiyasa sai kika kasa ganin illar dake tattare dashi. To ki bari sai ya gama lalata komai ta yadda ba zai gyaru ba sannan anan zaki gane gaskiyar abinda nake faɗa." 

"A'ah Daddy, wallahi ni na san Yaya baya da laifi, sannan kuma ba shi ne matsalar mu ba, akwai dai dole abinda ke faruwa" Aziza ta furta itama tana hawayen. 

"Ke da ya lalata idanunki, amma har yanzu kina ganin haskensa, da yake baki da hankali ko? To ni dai na faɗa maku, muddin Muhasin bai bar mu ba to matsala ba zata barmu ba har abada" Kallon Mommy ya sake yi sannan ya ce "Ku fito da Aziza ni ina mota" Har ya juya sai kuma ya sake juyowa. "Ina Fa'iza?" Babu wanda ya iya amsa masa. Taɓe baki ya yi sannan ya ce "Kar dai ku barta a gidan nan ita dashi don na san zai iya cinye nata idon." Jin haka ya saka Muhasin ƙarasawa gaban Daddy kamar wani zaki. Hannu ya saka ya shaƙo wuyan Daddy, jijiyoyin goshinsa gaba ɗaya sun fito. 

"Anya kaine asalin mahaifina? Anya kaine ka kawo ni duniya? To koma kaine ka sani ba zan taɓa yafe wannan ƙazafin ba, sannan idan ni maye ne to kai ya kamata na fara cinyewa saboda ka muzgunawa mahaifiyata, sannan ka sani yau zan bar garin nan bama gidan nan ba, kuma har abada ba zaka sake ganina ba" 

 

Mommy kuka kawai take, kuma a lokacin ta ƙarasa gaban Muhasin tana roƙarshi daya saki mahaifin nasa. Sakinshi ya yi, idanunsa gaba ɗaya sun zama red ya kalli Mommy "Wannan dalilin ne ya saka lokacin da ake faɗa masa matsalata bai damu daya dawo ba har sai da kuka samu accident ke da Fa'iza" "Yaya please kayi shiru ka rabu dashi mu muna ƙaunarka" Aziza ta faɗa cikin kuka. 

 

Murza wuya Daddy ya yi sannan ya kalleshi ya ce "Ai ni ba zaka taɓa iya cin naman jikina ba, domin dubunka ma sun yi sun gama" Yana gama faɗa ya juya ya fita. 

"Muhasin dan Allah kayi haƙuri, ka riga ka san halinsa, kuma ni na san kai ɗana ne, kuma babu maye a ahalinmu, ka rabu dashi, inda na san ko ya dawo abinda zai faɗa kenan da ban bari ya dawo ba, amma dan Allah kar ka biyewa maganarsa sannan kar kaje ko ina mu muna ƙaunarka, kuma muna son ganinka a tare damu" 

"Yaya ni dai da kai zamuje asibitin" Aziza ta faɗa cikin kuka. 

"Ba zanje ba" Ya furta cikin ɓacin rai tare da zama kan kujera ya kama kanshi da yaji yana barazanar tarwatsewa. 

 

Mommy ta ƙarasa inda yake sannan ta zauna tare da kallonshi. "Dan Allah kayi min alƙawarin ba zaka je ko ina ba, kana nan har muje asibiti mu dawo" Kai kawai ya gyaɗa ko kallonta bai yi ba. 

 

Da ƙyar Azima ta yarda suka tafi asibiti dan gani take kamar in sun dawo ba zata ganshi ba. 

 

              ***** ***** ***** 

 

Har ƙasa ya durƙusa ya gaida Inna da Iya lokacin da suka shigo gidan tare da Baffa. 

  "Sadiya tana ɗaki sallah take" Inna ta faɗa tana kallon Habib. Shi kuma murmurshi kawai ya yi. 

 

"Ya sayo mata keken yana cikin motarsa" Cewar Baffa. 

  "Allah sarki, irin wannan ɗawainiya haka, ai abin ya yi yawa" 

  "Haba babu komai Inna ai yiwa kaine."  

  "To Allah ya sa a mizani, sai dai kuma ban san ya zamuyi da ita wajen hawa keken ba, dan da anyi magana kuka take ta ce an mayar da ita gurguwa."  

  "Cikin hikima za a lallaɓata ai" Cewar Baffa. 

  "Habib ka ƙarasa ku gaisa da ita ɗin."  

   "To Baffa" Ya furta tare da miƙewa ya nufi ɗakin daya sameta wancan karon. 

 

Yana yin sallama a dai-dai lokacin ta shafa addu'a. Ta juyo tare da amsa masa sallama. 

  "Sannu da zuwa" Ta furta a sanyaye. 

 

Kan tabarmar ya ƙarasa ya zauna, tare da faɗin "Fatan dai kin haɗa dani a cikin addu'arki ko?" 

  "Nayi maka addu'a sosai, saboda ba zan manta da kai ba" 

  "Wow kice haka na ciri tuta" 

  Murmushi ta yi tana cire hijabin jikinta, sannan ta kunce ɗankwalin kanta ta yafa, dama da hula akan nata. 

  "Yanzu dai ya jikin naki?" 

  "Bana jin komai, na samu sauƙi, sai dai ƙafafuna bana iya komai dasu hatta wanka da tsarki sai anyi min, sannan sallah ma a zaune nake yi" Sai kuma ƙwalla ya cika kurmin idanunta. 

  "Sarkin kuka, to mene na yin kukan?" 

  "Shikenan idan na zama gurguwa ba zan yi karatu ba?" 

  "Waya faɗa miki?" 

"Ina ganin guragu sai dai su riƙa bara a bakin titi da cikin kasuwanni" 

  "Sadiya...!" Ya kira sunanta a sanyaye. Da ido ta kalleshi a lokacin kuma ta saka hannu tana goge hawayen daya zubo mata. 

 

"Ki daina kuka ki share hawayenki, ba dai karatu kike so ba?"  

  Kai ta gyaɗa tana kallon shi. 

  "To za kiyi karatu har zuwa matakin da kike so, nayi miki alƙawari" 

  "Baba ya bani kuɗi zan je nayi thumb print na WEAC kuma kawayena suna ta yi min dariya shiyasa naƙi yi, yanzu na san ƙawayena sun kusa gama WAEC" 

  Shiru ya yi na ɗan wani lokaci kafin ya ce "Ka da dariyar mutane ta saka kiji kin karaya a rayuwa Sadiya! Haƙorin da ya yi miki dariya wata rana shi zai je yana yayata nasararki tare da mamakin yadda aka yi kikayi making a rayuwa, kin san me nake so dake?" 

  Kai ta gyaɗa alamar a'a "Ina so ki yadda da ƙaddarar data zo miki, kin ga kamar yanda kikayi jinya kika warke, to haka suma ƙafafunki zasu samu lafiya" 

  "Dagaske?" Ta faɗa cikin mamaki. 

"Eh, amma sai kin yi haƙuri kin hau keke"  

   

Haɗe rai tayi tana kallonsa kafin ya ce "Haƙuri zakiyi kin ji, wata rana ai ba zaki hau ba, daga zarar kin warke shikenan" 

   "Ni bana son ace min gurguwa" Ta faɗa cikin yanayi na shagwaɓa. Shi kuma ya sake yin murmushi, dan yadda take abu kamar wata ƙaramar yarinya, sai  a lokacin yake ji ashe dama haka masu ƙanne suke, tabbas zai masheta ƙanwarsa kuma zai mata duk abinda ya dace gwargwadon iyawarsa. 

 

"Waye zai ce maki gurguwa bayan ina nan, ai kuwa da nayiwa mutum duka. Ni fa ina son ki hau keke don in baki hau ba to ba zaki warke ba" 

  Murmushi tayi wanda ya ƙara bayyanar da kyawunta kafin ta ce "Na yarda zan hau" 

  "Yauwa my beautiful sister, yanzu zanje mota a fito dashi" 

  Kai ta gyaɗa alamar to. 

 

Yana fita tsakar gidan ya sanarwa dasu Inna cewar Sadiya ta amince za ta hau keken. 

  "Yauwa har ta riƙa fitowa, amma kayi ta zaman ɗaki babu gajiya." 

 

Kamar dai da wasa a haka Sadiya ta shaƙu da Habib sosai, sai dai basu wani daɗe tare ba Inna da Baffa suka fara shirye-shiryen komawa Gaya, saboda Umma anƙi yarda a sakota, ga kuma Sadiya bata san da rasuwar mahaifinta ba, so suke sai sun je can su sanar mata. 

   Ranar kuwa daya zo yaji labarin kasa bacci ya yi, yana ganin ya samu wadda zata maye masa gurbin ƙanwa da baya da ita gashi kuma suna ƙoƙarin tafiya, duk da har lokacin Mama da Najwa basu san yana zuwa wurin Sadiya ba. 

 

        ***** ***** ***** 

 

Tana saka glass ɗin ta ga komai washar tana gani. 

  "Mommy ina ganinku yanzu" Ta faɗa cikin farin ciki. 

 

Doctor ya yi murmushi ya ce "To yanzu cire glass ɗin. 

  Hannu ta saka ta cire, ta fara kallonsu. 

  "Ina ganinku amma dai dishi-dishi kun yi blur." 

   

"Kenan yanzu sai da glass zata riƙa gani? Na ɗauka tunda snyi wankin ido shikenan" Cewar Mommy. 

"Eh to! Nima nayi tunanin haka amma kuma ga dai yadda abin ya kasance" 

 

"Tunda da glass ɗin zata ga komai ai Alhamdulillah, da ace ya lalace gaba ɗaya" Daddy ya faɗa yana ɗaukar glass ɗin tare da sakawa Aziza. 

 

"Kuma zamu ɗorata akan magunguna, idan aka yi sa'a tana gama sha zata samu lafiya, idan ta samu sauƙi sai ta ajje glass ɗin" 

 

Mommy dai bata so haka ba, amma babu yadda ta iya da ƙaddara, haka dai suka baro asibiti cikin jimami. 

   "Yanzu ai na san shi wanda yaso ya cinye idon nata idan ya ga ta samu lafiya abin ba zai masa daɗi ba" 

 

Jin haka ya ƙara hargitsa Mommy, ranta ya kai ƙololuwar ɓaci, ta kalleshi ta ce "Idan ka sake aibata Muhasin shari'a ce zata rabamu, domin ka san yanda shari'ar maita take" 

  "Ai naga baki son gaskiya, shikenan na ƙyaleku" 

  "Ka ƙyalemu ɗin, ni wallahi dawowarka bata min amfani ba" Ta ƙara faɗa a harzuƙe. 

  

Aziza kuwa ji take da ba dan shi ɗin mahaifinta bane, da sai ta faɗa masa maganganun da har mutu yana dana sanin aibata Muhasin da yayi. 

  Gidan ma gani tayi ya yi mat nisa sosai, sai taji kamar ta karɓi key ɗin ta tuƙa da kanta. 

 

Ana yin parking kuwa ita ta fara ficewa daga motar. 

  "Ita kuma waccan ya naga yanayinta ya canza, na ganta a fusace ta fita?" Daddy ya yi tambayar yana kallon Mommy. 

  "Ai cikin gidan ta shiga, za ka iya tambayarta in mun shiga" 

  "Ikon Allah, da alamu na taɓo ɗan so" Bata ko kulashi ba kawai ta fice. 

 

Fa'iza na kallo a parlour taji shigowar Aziza. Juyawa ta yi ta kalleta sannan ta ce "Ya na ganki da glass yaushe kika sayi irin wannan ban sani ba"  

   "Ina Yaya?" Shi ne abinda Aziza ta faɗa ba tare data amsa waccan tambayar ba. 

 

"Anya Yaya yana gidan nan kuwa? Dan koda na tashi daga bacci ban ganshi ba, amma indai motarsa na waje to maybe ko yana ɗakinsa" Fa'iza ta furta tana cigaba da shan Apple. 

   "Ni ban kula da motocin dake waje ba, amma dai bari na duba ɗakin nashi." Ta furta tare da wucewa da sauri. 

 

Tana murɗa handle taji a buɗe, dan haka ta kutsa kai cikin ɗakin. Gabanta ya yi mummunan faɗuwa saboda abinda idanunta suka gane mata...!