Page 12
by @sanazty
*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
Page 12
__________🖌️Wardrobe ɗin sa a buɗe take, duk da da kaya a ciki ta san tabbas yadda ta ga ɗakin nashi sam ba lafiya ba.
Drawer ta madubi duk ya buɗe wasu ya barsu a buɗe bai rufe ba.
Idanunta suka kai saman wardrobe ɗin sai ta hango babu akwati na tsakiya a cikin akwatuna uku da yake dasu.
Jikinta taji ya fara rawa, dan haka ta zauna a gefen gadon tare da fashewa da kuka mara sauti. Hannunta ne ya sauka akan takardar daya ajje masu.
Da ido take bin takardar kafin ta saka hannu ta ɗauka, a daidai lokacin Fa'iza da Mommy suka shigo ɗakin.
"Shikenan!" Aziza ta faɗa tare da fashewa da sabon kuka.
"Ban gane shikenan ba" Mommy ta furta hankali a tashe.
"Mommy Yaya ya tafi, ya bar gidan nan, gashi ya bar takarda." Ta faɗa tana miƙa mata takardar, Fa'iza tayi sauri karɓa tare da warwarewa.
_Kuyi haƙuri!_ Ta karanta abu na farko daya rubuta a wasiƙar sannan ta kallesu.
Dukkansu babu wanda ya iya cewa komai, ita Aziza hannu ma ta saka ta dafe goshinta. Fa'iza ta cigaba da karanto wadiƙar.
_Na san gaba ɗaya zaku ji babu daɗi a lokacin da kuka ga wannan wasiƙar tawa, amma babu yadda na iya dole na barku ko hakan ya saka ku samu sassauci da raɗaɗin abinda ke damummu, sannan na san hakan zai saka ku samu raguwar fargaba._
_A lokacin da Aziza ta samu makanta hankalina ya tashi, kuma ba zan iya jurar ganinta a haka ba, bana so ace matsalar da take jikina tazo kuma ta shafe ku, ba wai furucin Daddy ne ya saka na tafi ba, a'a nima dama ina da wannan tunanin, domin abubuwan sun fara yawa, rasuwar mai aiki da kuma Safiyya wanda basu ji ba basu gani ba har yanzu abin ya tsaya min arai, dan haka dole na ɗan nisanta daku kuma zan cigaba da neman magani, sannan ina fatan Allah ya bawa Aziza lafiya, sannan bana fidda ran wata rana zan sake haɗuwa daku idan kuwa na mutu ku yafe min, nima na yafe muku._
Daga Fa'iza dake karantawa har Mommy kuka suke, talkless of Aziza da take jin kamar zata amayo zuciyarta.
A fusace Mommy ta fuzgi takardar ta fita. Sai lokacin Aziza ta cire glass ɗin fuskarta tare da rushewa da kuka. Blanket ɗin shi ta damƙa ta rungumeta tana kuka mai tsuma rai, saboda shaƙuwar da tayi da Muhasin ko gurin aiki lokacin yana zuwa ba dan tana so ba. Fa'iza ta rungumeta suka cigaba da rera kuka.
"Burinka ya cika sai ka zuba ruwa a ƙasa kasha" Mommy ta faɗa tana miƙawa Daddy takarda. Yana danna waya ya ɗago ba tare daya karɓi takardar ba.
"Ka karɓa ka duba mana. Muhasin ɗin da baka son gani ya tafi ya bar maka gida."
"Ni fa kawai gata nayi muku, domin kuke zaune dashi, ni tafiya zan yi na barku"
"Bamu san gatan naka, tunda tun can muna zaune dashi a hakan ai. Wallahi nadamar aurenka nake, kuma na san da wannan nadamar zan mutu"
Murmushi Daddy ya yi sannan ya ce "Ni kuma na san a gaba sai kin gode min abisa gatan da nayi miki" Yana gama faɗa ya miƙe ya bar mata parlour.
**** **** ****
Kallon zhi tayi sannan tayi dariya ta ce "Wai ya kake ta ɓata rai?"
"Ba dole na ɓata rai ba, tunda gobe war haka baki tare dani"
"Sosai tayi dariya kafin ta ce "Ni kuma ka ga murna nake da ɗokin komawa can"
"Kina nufin Kano ba daɗi?"
Ɗan yatsina fuska tayi, sannan ta ce "To ku san haka ne"
"Baki taɓa fita kin ga yadda Kano take ba shiyasa"
"Eh to kuma fa hakane"
"Da ace da wata 'yar budurwa kamarke, kin ga da sai mu fita"
"Akwai wata jikar Iya mai suna Salma, tana boarding school itama Waec take, ka ga da tana nan da sai mu tafi tare tunda ni gurguwa ce ko mota yanzu sai an saka ni"
"Ni dai ban faɗa ba, kuma ban so na ƙara jin kin faɗi haka"
"To shikenan na daina, amma Yayana yaushe zaka zo idan mun koma?"
"Ranar monday saboda ina so muje ayi miki thumb print na neco"
"Shikenan Allah ya kaimu"
"Amin"
Sallamar Baffa ce ta hana Habib sake yin wata magana, sai miƙewa da ya yi ya ƙarasa gaban Baffa ya gaidashi.
"Habib ka shigo kenan"
"Eh Baffa"
"Dama so nake sai kazo mu haɗu muyi mata magana, ƙarasa muje"
Jin haka ya saka Sadiya ɓata rai.
Baffa ya kasa cewa komai, ita kuma tayi tsammanin faɗa za a mata shiyasa ta haɗe rai dan bata son faɗa ko kaɗan.
"Sadiya..! Na san yanzu haka kina nan kina ɗaukin idan muka koma Gaya zaki ga Babanki da kuma Ummanki ko?"
"Ni fa ba zan koma gidan Baba ba, saboda cewa ya yi karatu za a kaini amma tun a mota suka fara zagina da turanci wai ai ni 'yar aiki ce, gani 'yar kauye, gaskiya ni kam ba zan koma ba Baffa, gurin Ummana zan zauna"
Shiru Baffa ya yi, jin haka ya saka ya kasa faɗa mata.
"To naji shikenan" Ya faɗa sannan ya miƙe ya fita.
Kallon Habib tayi sannan ta ce "Ya naga kaima ka ɓata rai"
"Sadiya ban son kina faɗar maganganu haka akan mahaifinki, kin dai san yana ƙaunarki kuma ba zai taɓa yin abinda zai cutar dake ba"
"Hmmm! Yayana kenan, lokacin da baƙar ƙaddara ta gicco ciikin rayuwata hantara ya fara min ya..." Sai kuma tayi shiru tare da sauke ajiyar zuciya.
"Ka san me? Kawai abar maganar"
Ta saka hannu tana murza zoben da take gani a matsayin abu na farko daya fara tarwatsa rayuwarta.
"Naga wannan shi ne kaɗai zoben ki, sai ki bani shi kin ga zan riƙa tunawa dake"
Kallon zoben tayi sannan ta kalleshi.
"Wannan fa zoben akwai dalilin da ya sa nake riƙonta a hannuna amma nima ba dan ina so ba, ko maƙiyina ba zan zo na bawa wannan shegiyar zoben ba"
"Tofa, meyasa?"
"Mamallakin wannan zoben shi ne wanda ya fara tarwatsa rayuwata kuma nemansa nake ruwa a jallo"
"Kin min magana a baibai, ban fahimceki ba"
"Yayana ka bari a hankali zaka san komai"
"Wato 'yar ƙarama dake amma sai manyance"
Murmushi kawai tayi, wanda iyakarsa laɓɓanta.
**** ****
Tana daga kan kujerarta tana ganin yadda Inna take ta aikace-aikace a tsakar gidan. Can dai ta kalli Inna lokacin da take ta fama hura itace sai hayaƙi suke, gaba ɗaya madafar da tsakar gidan sun turniƙe da hayaƙi.
"Inna sannu" Ta faɗa tana ɗan turo baki.
"Sannu Sadiya"
"Inna wai ni yaushe zan fara takawa da ƙafafuna gaskiya ni wallahi na gaji kullum daga zama sai kwanciya"
"To aikuwa yanzu da kin fara mitar nan sai na kira Baffanki ya kira Habibu ya sanar masa"
"Kai Inna ni fa ba mita nayi ba, kawai na gaji takawa ne, jifa har ƙoƙarin tashi nake amma sai naga na kasa"
Fitowa daga madafa tayi tana tafa hannu. "Oh abinda kikeyi kenan? To ai gara da Allah ya sa kika faɗa tun wuri. To bari kiji, wallahi in har baki daina gigin miƙewa tsaye ba,za ki karya ƙugunki a banza,kuma keda tashi har abada, ke zaman ma sai ya gagareki sai dai kwanciya."
Hannu ta saka ta dafe kai. "Na shiga uku, aikuwa ban sakewa"
"Ah to gara ma dai ki sani"
Shiru ya ɗan biyo baya, Inna ta ce "Wai ina Ibrahim yake?"
"Ya fita, keda kika san halinsa da shegen yawo"
"Ibrahim akwai son wasa"
Shigowar Ibrahim ɗin ce ta saka suka kalleshi gaba ɗaya.
"Yaro kaci sa'a akan keke nake da sai na maka duka, ban hanaka fita idan yamma tayi ba? Wato dan ka ga Umma bata nan kuma ba a gun Baba kake ba." Ta kalli Inna ta ce "Allah Inna sai kin riƙa zane shi"
"Ai Inna bata duka na" Ya faɗa yana murguɗa baki.
"Ni kake murguɗawa baki ko? Hmmm zaka shigo hannuna yaro"
Ta kalli Inna ta sake cewa.
"Yauwa Inna wai yaushe Umma za ta dawo? Kuma naga tun da muka dawo yau kwana biyu amma Baba bai zo ya dubani ba"
"Baba ya mutu fa, a gida aka yanka shi" Ibrahim ya ɓaro maganar kai tsaye.
Duk da akan kujera take sai da ta zabura. Sai kuma tayi saurin kallon Inna.
"Kai kul na ƙara jin ka faɗi haka, waye ya faɗa maka, Babanku yana nan, duk sanda zai zo kina bacci ne"
"Inna wallahi Baba ya mutu, ance kashe shi akayi a gida, kuma nima har gawar Baba na gani"
Kuka Sadiya ta fashe dashi, ganin Inna ta kasa ƙaryata Ibrahim.
"Sadiya ya isa haka, addu'a za kiyi, mun so faɗa miki tun a Kano amma mun rasa ta ina zamu fara"
Ai kamar ana ƙara hura wutar kukan haka ta cigaba da rerawa, shi ma Ibrahim ya yi joining ɗin ta suka cigaba da yi.
*_1 Hour Later_*
Da sallama Baffa ya shigo gidan, ganin Inna a zaune a tsakar gidan tayi tagumi ya san ba lafiya ba.
Kusa da ita ya ƙarasa ya zauna tare da ajje ledar hannunsa "Wai ya naga kin zauna kin yi tagumi lafiya kuwa?"
"Daga nan inda kake baka jiyo shashsheƙar kukan Sadiya?"
"Eh ina ji yanzu da kika faɗa amma a farko ban kula ba"
"To abinda dai muka daɗe muna ɓoye mata yau ta sani, ta san mahaifinta ya rasu, wannan kukan da take tafi awa guda tana yi. Anan ta fara ita dashi, to daga baya sai kuma tsyi shiru ta ce in kaita ta kwanta. Ina kwantar da ita ta dasa daga inda ta tsaya."
"Ya akai kika faɗa mata?"
"Ya za ai na faɗa mata, ɗan uwanta ne ya faɗa mata, tare suka fara kuka shi daya gama nashi ya ware ya fice wasa ita kuma har yanzu taƙi yin shiru, nayi rarrashin nayi nasihar amma kamar ƙara cewa nake tayi kuka"
"Bari naje na sameta"Ya faɗa tare da tashi ya shiga ɗakin.
A kwance ya ganta kanta na kallon sama ta rufe fuskarta da hannu tana kuka.
"Mene ya faru?"
Jin magana ya saka ta janye hannun. Dafa hannayen tayi kan katifa sannan ta miƙe zaune.
"Kukan me kike haka?"
Cikin sheshsheƙa ta ce "Baba ya mutu ba a faɗa min ba, kuma ban nemeshi gafara ba" Ta ƙara rushewa da sabon kuka.
Cikin siga ta rarrashi ya ce "Ki kwantar da hankalinki, saboda bamu san halin da zaki shiga ba shiyasa muka kasa faɗa miki, amma Baban ki ya yafe miki, kuma kukan nan da kike yi kamar raɗaɗi kike ƙara saka masa, baki san yana jin zafi ba a duk lokacin da hawayenki ya ɗiga? Ki daina kuka a yanzu addu'a yake buƙata"
Hannu ta saka tana goge hawaye duk da wani na ƙara fitowa daga idanunta.
"Shikenan ba zan sake ganin Baba ba?" Tana ƙoƙarin fito da kukan shi kuma Baffa ya cigaba da mata nasiha tare da faɗa mata illar yiwa mamaci kuka.
Kwananta biyu sam bata da sukuni, abinci ma da ƙyar sai sn dage mata take ci, shi ma baya fin loma guda. Cikin ƙanƙanin lokaci gaba ɗaya ta faɗa ta rame sosai,ga idanunta sun ƙi komawa kalarsu kullum cikin kuka take shiyasa ko da yaushe idanunta sun yi ja ko sun fara.
***** ****** *****
"Baffa ina jin gobe zan shigo insha Allah" Ya faɗa wayar na kunnensa a kuma lokacin Mama ta shigo ɗakin.
"Eh ai takura mata za ai ko ya ya idan ya shiga ai yafi ace bata ci komai ba."
"To shikenan Baffa zan kiraka anjima insha Allah"
Yana gama wayar ya yi murmushi "Mama"
"Da alama dai baka da gaskiya"
"Ina da gaskiya me kika gani?"
"Yanzu dai ba wannan ba, mahaifinka na kira, idan ya gama nima zan yi magana da kai, dan ban manta da batun ƙoda ba"
"Kai Mama" Ya faɗa yana miƙewa ita kuma tsaki kawai taja.
Suna zaune a parlour, dukkansu babu wanda ya ce komai.
"Habib"
"Na'am Abba"
"Mene tsakaninka da wannan yarinyar Najwa?"
"Babu komai Abba, kawai dai course mate ɗina ce a lokacin da nayi jami'a"
"Kana nufin babu alaqar soyayya a tsakaninku?"
"Eh Abba"
"Idan ma kai baka sonta ita tana sonka, dan ni naga hakan a idanunta"
"Mama wallahi ni dai na san tana da wanda iyayenta suka zaɓa mata."
"To kai yaushe za kayi aure? Ka girma kuma naga ka kammala gininka, to ya kamata kuma a nemo abokiyar zama ko?"
Ɗan sosa kai ya yi cikin jin kunya ya ce "Abba ai ina nema, kawai har yanzu Allah bai kawo ba"
"To ka nemo kafin ni na saka maka lokaci"
Murmushi kawai ya yi.
"To ai kamata ya yi yaje ya ga Ilham su fahimci juna tunda baya son Najwa, amma ga na kusa sai ace sai ya tafi waje"
"Bana son in yi masa dole, shi kaɗai fa garemu, amma.." Ya kalli Habib ya ce "To Habib kaje ka duba Ilham ɗin idan tayi maka sai a daidaita ko"
Shiru ya yi bai ce komai ba.
"Idan kaga dama kaje da yamma, zan kira Yaya in faɗa mata" Mama ta faɗa sannan ta miƙe ta bar gurin.
Murmushi Abba ya yi sannan ya ce "Kaje ɗin Habib, ka san Mamanta ka sai haƙuri"
"To Abba" Ya faɗa yana murmushi.
**** ***** ****
Tun daga nesa ya fara ganin kamar yanayin gurin ba lafiya, gashi dama daji ne yake ta ratsawa.
Wata dalleliyar fitila an dalle masa motar wanda har baya ganin gabansa ya saka yaci burki.
A hargitse ya fito, tare da janyo jakarshi da takardunsa masu muhimmanci ke ciki. Ya ciro ƙaramar trolley ɗin kenan ya ga suna neman cimmasa, dan haka anan ya saketa ya kuma ruga su kuma suka rufa masa baya.
Gudu yake tun ƙarfinsa amma ina har ya fara gajiya, dan haka ya samu guri ya ɓoye a cikin ciyayi.
"Ku duba ko ina ba zai yi nesa da nan ba" Yaji ɗaya daga cikinsu na faɗa.
"Oga ina ganin tunda an samu ya bar motar kawai mu ware, domin kaga asuba ta ƙarato komai ka iya faruwa.
"To ai ya tafi da mukullin yana hannunsa gara mu kamo ɗan banza"
"Ai muna da na bogi mai tada ko wace mota, kawai muje"
Yana ji suka bar gurin gaba ɗaya a tsorace yake.
Ƙananun ƙwari da sauro babu wanda baya cizonsa amma sam bai fito ba har sai daya ga gari ya fara haske, anan ya tabbatar har anyi asuba an idar.
Fita ya yi yana sauke ajiyar zuciya, sannan ya ƙarasa inda motarsa take, amma gurin wayam, sai trolley ɗinsa da take a yashe a ƙasa.
Trolley ɗin ya ɗauka, yana kallon ko ina, bai ma san ta ina zai fara ba.
Inda ya masa kawai ya yanka ya fara tafiya.
Taji kawai yake yanka yana tafiya amma bai ga alamun zai samu gari a hanya ba.
Allah ya bashi ikon fitowa da wayarsa dan haka ya ɗaga yana dubawa sai dai babu network ko tsinke ɗaya a ciki.
"Ya salam" Ya furta a jigace, sannan ya zauna a ƙasa dan ji yake ba zai iya cigaba da tafiya ba idan bai saka koda ruwa ne a bakinsa ba.
"Dalla ka tafi a hankali mana so kake muyi asara" Jin muryar mace ya yi da yaren fulatanci. Da sauri ya miƙe tsaye gami da kallon inda suke.
Budurwa ce da ba zata wuce kimamin shekaru 20 a duniya ba, tare da wani yaro da ba zai gaza shekaru 13 ba, tare da shanunsu masu yawan gaske, da baza sun kai guda 12.
Fara ce sol, mai ɗauke da manyan idanu masu haske, sai dai kalar idanun nata blue, doguwa ce mai diri, komai na jikinta ya yi kyau daidai tsarin da ko wace mace take burin samu. Kayan fulani ne a jikinta riga da zane farare, sai sarƙoƙi da abin goshi na fulani da tasha. hancinta dogo ne sosai laɓɓanta pink ne masu matuƙar kyau, suna da ɗan tudu kaɗan.
Sai kuma gashi da take dashi wanda aka kisa mata kalaba guda biyu ta zuro su gaba.
Ya ƙura mata ido tun daga dogayen yatsun ƙafarta har zuwa fuskarta.
Ji ya yi kamar an tsikareshi sai kuma ya yi sauri ya juya.
Wata mummunar halitta ya gani, haƙoran nan zaƙo-zaƙo, gashinta wani yalolo fari handa ya wuce ƙugunta, idanunta jajir.
Zaro idanu ya yi yana kallonta tare da matsawa baya. Gani ya yi ta wanƙale haƙoranta zaƙo-zaƙo wanda cikinsu kuwa baƙaƙe ƙirin, da wani harshe kamar na maciji.
Tana zilalo harshe kuwa ya faɗi ƙasa tim..!