Page 13
by @sanazty
*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
Page 13
__________🖌️Jin an taɓa shi ya saka ya buɗe ido a hankali. "Tashi mana" Ta faɗa cikin hausarta wadda kana ji ka san fulani ce usul.
A hankali ya miƙe zaune, ya ƙara juyawa baya, ta sake saka sanda ta taɓo shi. "Ni zaka kalla fa ba bayanka ba"
Kallonta ya yi, itama ta kafeshi da manyan idanunta.
Ƙaninta tayiwa magana da fulatanci, shi ma ya mayar mata da amsa.
Ƙurawa Muhasin ido tayi taƙi ɗaukewa har sai da yaron ya kawo mata nono a ƙwarya.
"Na san kana shin yunwa ga kindurmo kasha ko kaji cikinka ya ɗago"
Murmushi ya yi sannan ya ce "Nagode sosai"
Kurɓa ɗaya ya yi, sai kuma ya ajje.
"Hala baka jin yunwa, kuma gashi dai da alamun yunwa a tare da kai"
Idanunsa ya ɗan lumshe dan yadda yake jin su suna masa zafi, ga kuma fargabar take tare dashi..
Sunkuyar da kai ya yi, ta ƙara saka sanda ta ɗan buge shi.
"Muma fa a lokacin rani muna shiga binni mun san 'yan binne kuma mana jin yarenku ka saki jikinka kayi min magana yadda zan gane kar ka shume min anan"
Kallonta kawai ya ke, ita kuma ta kira kaninta.
"Kai Rabilu ka kula da shannun mu zan je da baƙon nan gurin Arɗo ya duba shi"
Kai ya gyaɗa ita kuma ta miƙe tare da miƙa masa hannu. Har zai riƙe sai kuma ya fasa kawai ya dafa ƙasa ya mike.
Ita ta dauki trolley ɗin shi aka. Mamaki kawai yake, a gajiya yake tafiya dan haka ba wani sauri suke ba.
**** **** ****
"Anya ƙanwar nan tawa jaruma ce kuwa" Cikin kuka ta rufe fuska ta ce "Ni ba jaruma bace"
Ajiyar zuciya Habib ya sauke sannan ya ce "To ai so nake ki zama jarumar."
Ɗagowa tayi ta kalleshi.
"Dan Allah ki goge hawayen idanunki Sadiya"
"Yayana...!" Ta furta a sanyaye, sannan ta zare zoben hannunta ta ce "Tun ranar dana fara ganin zoben nan a hannuna ban ƙara ganin farin ciki ko haske a rayuwata ba, daga wannan tashin hankalin sai wancan."
"Bani zoben" Girgiza kai tayi sannan ta cigaba da faɗin "Mai wannan zoben shi ne azzalumin daya rabani da farin cikin rayuwata kuma ya hanani morar ƙuruciyata gashi a ƙarshe na zama gurguwa" Ta saka hannu tana goge hawaye.
"Bana son ki riƙa kiran kanki da wannan sunan"
"To ai haka ne, ba gashi ba, komai sai dai ayi min fa, ni ban san waye ba, ban san mene nayi masa da hat ya tarwatsa rayuwata, naso nemosa amma a ƙarye ga inda rayuwata ta kasa, babu Baba Umma na hannun hukuma ji nake ina ma na mutu"
"Sadiya ki daina faɗar haka"
"Dole na faɗa, yanzu su Inna ke kula dani daga zarar sun ƙara tsufa wa zai kula dani? Na rasa inda zan saka kaina, zuciyata zafi take, dama na rasa ƙafafu shikenan ba zan sake taka ƙasa ba"
Sabon kuka ta rushe dashi, wanda har sai da Inna ta shigo, anan suka hadu suna ta rarrashinta amma sam taƙi haƙura.
"Habibu ka ƙyaleta idan ta gaji zata daina, muje waje"
Ji ya yi kamar ya cewa Inna a'a zai tsaya ya rarrasheta amma kuma ba zai iya hakan ba, ran shi bai so ba suka fita. Baffa daya shigo yake tambaya, Inna ta faɗa masa komai, shi ma bai shiga ɗakin ba, yaja Habib suka fita.
"Habib babu abinda zamu ce maka sai dai Allah ya saka da alkhairi, a farko ka bayar da ƙoda dan Sadiya ta rayu duk da baka san mu su waye ba, numfashin da Sadiya ke yi a yanzu a dalilinka ne. Sannan kuma yanzu kana yi mata da ƙarfinka, bamu san mene ya shigo da kai rayuwarmu ba, amma tabbas kai alheri ina jin haka a raina, daga ni har kakarta da ita kanta Sadiya da kuma mahaifiyarta, ba zamu taɓa mantawa da kai ba"
Murmushi ya yi, sannan ya ce "Babu komai Baffa ai duk yiwa kaine, ni Sadiya ina kallonta a natsayin ƙanwa, kuma duk abinda zan yiwa ƙanwata zan yiwa Sadiya"
"Mun gode mun gode"
Murmushi kawai ya yi.
***** *****
"To ina yaje? Ni fa mukayi magana dashi ya ce min daga nan zai wuce gidan Yayata, kenan bai je ba, tunda gashi na kira bai ɗaga ba"
"Mama ko dai asibiti yaje?"
"Haba shi ya isa ya fara ai ya san halina ya kuma san abinda zan yi da wanda ba zan yi ba"
"Kuma ina ta kiran wayarsa bata shiga, to amma Mama ko dai yaje location?"
"To ba ace a'a ba."
Shiru ne ya biyu baya kafin Mama ta ce "Najwa ni kam in tambayeki mana?"
"Mama ina jinki, Allah yasa na sani"
"Wai yaushe zakiyi aure? Kin ga dai shekaru na ƙara ja, shi ma Habib nayi masa maganar yake ce min baya da kowa ni a tunani na tare kuke ai"
Shiru Najwa tayi gami da sauke kai ƙasa, ji tayi gaba ɗaya kunya ta rufeta.
"Baki ce komai ba"
"Mama shi ne baya so, a lokuta da dama nuna wa yake kamar ma bai damu ba"
"Amma shi ne ya ce min babu komai tsakaninku?"
"Hmmm!" Najwa tayi ajiyar zuciya.
"Yanzu dai faɗa min, kina son Habib ko kuwa?"
Murmushi tayi tana ɗan jan gyalenta.
"Na gane ma, to karki damu zan yi magana da Habib da kuma mahaifinsa gara ayi komai cikin gaggawa. Zan zo har gida in yi magana da maman taki"
Najwa dai bata ce komai ba, amma har cikin ranta tayi matuƙar farin cikin jin wannan furuci na Mama.
Miƙewa tayi tare da faɗin "Mama ni zan wuce gida"
"To Najwa, ki gaida min da Mommyn taki"
"Za taji insha Allahu"
**** **** ****
Matsalarka babbar matsala ce, amma akwai wani Malami a wani ƙauye kusa damu, wataƙila shi yake nufi, yanzu ka huta anan zuwa gobe sai muje na rakaka can, wataƙila idan ya yi maka magani za a dace"
Godiya Muhasin ya yi shi kuma mutumin ya kalli budurwar ya ce "Zaliha a share masa wancan ɗaki na baya sai a shimfiɗa kaba ya huta" Cikin muryar fulatanci yake maganar. Ita kuma ta miƙe domin gabatar da abinda aka sakata.
Kallon ɗakin ya riƙ yi yana kuma tariyo rayuwarsa ta baya sam ya kasa cin tuwon masara da miyar kuka da aka kawo masa, domin bai ma san su ba ba kuma cimarsa bace.
Yana nan zaune ya yi shiru sai ga sallamar Zaliha daga ƙofar ɗakin. Ya amsa mata sannan ta shiga ta zauna a gabansa.
"Da alama wannan ba cimar ka bace ko?"
"A'a na dai ƙoshi ne" Ya furta yana dariyar yaƙi.
"Ni na san baka saba da wannan bane, amma Arɗo ya tafi neman fura a dama maka na tabbatar za ka iya shanta ko ya yane" Shiru babu abinda ya biyo baya.
"Yanzu dai na tambayeka"
"Ina jinki"
"Wane ciwo ne yake damunka?" Ta faɗa tare da yi masa ƙyar da ido.
"Nima ban sani ba, amma dai na san duk macen da nace ina so ka ta ce tana sona sai ta mutu"
Ɗan zaro ido tayi "Mutuwa kuma? Kashe ta ake ko ita take kashe kanta ko kuma kai kake kashesu?"
"Kasheta ake, amma ko bani ne mai kisan ba dole a sanadina ne"
"To ni ina sonka, bari na gani zan mutu daga nan zuwa ranar da zaka bar garin nan"
Ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin wucewa ya dakatar da ita.
"Dan Allah ki janye kalamanki."
Dawowa tayi ta ɗan tsugunna ta ce "Tunda har na cire kunya ta fulani nace ina sonka ka san dole akwai dalili, za muyi soyayya kuma zan gani idan ni za a kasheni." Tana gama faɗa ta tashi ta wuce ta bar ɗakin.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil? Ya Allah mene ke shirin faruwa dani?"
Ji ya yi zuciyar shi ya faɗa masa ya gudu kawai, sai kuma ya tuna ai ya samu masauki anan idan ya tafi bai san ina zai faɗa ba, musamman yadda 'yan fashi suka so yin raga-raga da rayuwarsa.
Kan tabarmar kabar ya kwanta. Aziza ce ta fara faɗo masa a rai, a take yaji wasu hawaye masu zafi sun sauka a kuncinsa.
*** *** ***
A ruɗe Inna ta fito ƙofar gidan tana salati. Baffa da Habib a ruɗe suka miƙe ysaye.
"Malam ina shiga naga yarinyar tana ƙoƙarin daɓawa kanta wuƙa"
"Wuƙa?" Baffa ya faɗa a tsorace, shi kuma Habib ya ma rasa mene zai ce.
Gaba ɗaya suka ɗunguma zuwa ɗakin. Suna shiga suka tarar tana kuka.
"To ki sani muddin kika kashe kanki wuta zaki shiga, ke baki da hankali ne? Dan kin rasa wani ɓangare na halittarki kin rasa lafiyarki ne gaba ɗaya? Wani ma numfashunsa baya tafiya daidai wani abinci ma baya iya ci wani gaba ɗaya ya babbake sai kece ba zaki riƙe taki ƙaddarar ba? Idan kuma mahaifin ki da aka faɗa ya rasu ne abinda muke maki kin rasa gata ne a yanzu. Dashi mahaifin naki da ƙafafun naki ai duk mallakin Allah ne, shin dan ya rabaki dasu ba zaki rungumi ƙaddara ba, haba tun jiya ake abu ɗaya shekararki 16 kin isa a aurar dake ki zauna amma shi ne kike abu wanda ko Ibrahim ba zai yi ba. To ki kashe kan naki ki gani in lahirar daɗi ce ga wanda ya yi sanadin mutuwarsa yana sane" Yana gama faɗa ya wuce rai a bace.
Inna ma bata iya cewa komai ba kawai wucewa tayi.
Habib dake tsaye sai a lokacin ya sauke sjiyar zuciya. Ta ɗago manyan idanunta da suka zama kamar gauta ta kalleshi sai kuma ta saukesu ta saka yatsa tana goge hawayenta.
"Meyasa kika yi haka?"
Bata xe komai ba kuma bata ƙara ɗago ido ba.
Gari ya samu ya zauna sannan ya ce "Sadiya kin ga abinda kika yi ya ɓata ran Baffa ina so idan ya shigo ki bashi haƙuri"
"Kowa ya tsaneni, wallahi da ina da ƙafafu godiya zan yi" Ta furta cikin matsanancin kuka.
"Wallahi duk muna sonki. Kin san su Baffa ba zasu taɓa ƙinki ba,ransa ne ya ɓaci shiyasa har ya yi miki faɗa. Nima kuma ina sonki, domin jinki nake tamkar ƙanwar da muka fito ciki ɗaya"
Bata ce komai ba sai dai ta tsagauta kukan nata.
"Dan Allah kiyi haƙuri Sadiya ki bar wannan kukan ki fawwala Allah, domin ba dan baya son ki ba, jaraba imaninki yake, ya kamata ki karɓi ƙaddararki ki kuma rungumta da hannu bibbiyu ta hanyar godewa Allah" Haka Habib ya yi tayi mata nasiha kafin ta yi shiru ta tsagaita kukan nata.
Ranar kuwa bai bar Gaya ba har sau daya karɓi takardunta ya kuma cewa Baffa za suyi waya domin yana son da neco da private Waec gaba ɗaya tayi a kano dan ta samu admission da wuri. Baffa godiya sosai ya yi.
****** ******
Kallon shi Malamin ya yi sannan ya ce "Gaskiya akwai wani babban ibtila'i a cikin rayuwarka. Kuma abu ne mai matuƙar wahala wanda za a iya rasa rayuka wajen maganinsa.
Cikin tsananin tashin hankali Muhasin ya ce "Malam rayuwaka kuma? Nawa kenan?"
"Wasu daga cikin mahaifinka ko mahaifiyarka ko kuma ƙannenka dole a ciki za a rasa mutum biyu"
"Ban fahimta ba?"
"Sune za a bayar a matsayin fansa kafin ka warke, ko kuma matar da kake aure"
Cikin tsananin tashin hankali ya miƙe tsaye. Zaliha da ido ta bishi tana murmushi. Arɗo ya zaunar dashi.
"Ni ban taɓa aure ba, hasalima duk macen da ta ce tana son ko ni nace ina sonta mutuwa take kamar yadda na faɗa maka. Sannan ni ban yarda a halaka kowa nawa ba domin ni ban yarda da wannan hanyar maganin ba, dan haka gara na zauna da ciwo na har zuwa ranar da zan mutu"
Malamin ya yi murmushi ya ce "To tunda baka yarda kana da mata ba, a bayar da ita a matsayin fansa?"
Cikin ɓacin rai Muhasin ya miƙe "Ni ban yarda a bayar da kowa koda kiyashi ne a matsayin samun lafiyata ba" Ya fusace yake maganar yana ta haki. Arɗo ya miƙe tare da riƙeshi.
"Ka keantar da hankalinka yaro. Haki yake tayi kuma a fusace yake har zuwa lokacin da Arɗo ya zaunar dashi.
"Ni dai dana duba naga mace a cikin rayuwarka, amma kuma kai ka ƙaryata hakan, sannan ni dai wannan hanyar maganin ita kaɗai na sani, amma dai kuje nan da kwana biyu ku dawo kafin nan nayi tunani akan wata mafitar."
"Baka faɗa min mene yake damuna ba, Asiri ne ko aljana ce?"
"Ni kaina har yanzu ban gani ba, amma dai kuje nan da kwana biyun ku dawo"
"Baka gani ba amma kuma ka iya gano maganin,anya kuwa kai Malami ne?"
"Ka ga muje kawai" Arɗo yajashi suka fita.
Aikuwa ya fara yi masa faɗa tare da faɗa masa in har baya kwantar da zuciyarshi to ba zai samu lafiyar da yake nema ba, domin irin wannan Malamai da suke da mutane basu son ana masu hayaniya aka.
"Ni ba zan sake dawowa wurinsa ba, domin na fahimci boka ne ba Malami ba, ni kuma ba zanyi shirka ba"
"Kin ga Zaliha kuyi gaba, ku wuce gida, ni zan yiwa Malam magana"
"To Arɗo" Juyawa ya yi ya wuce. Ita kuma ta kalli Muhasin ta ce "Muje ko" Ranshi a ɓace ya wuce ita kuma ta girgiza kai tana murmushi.
Suna ta tafiya a cikin gonaki, domin daga garin dasu Zaliha suke nai suna Marke zuwa garin da Malamin nan yake akwai tafiya sosai.
Ganin shirun ya yi yawa ta ce "Wai dama haka kake da zafi kamar barkono? Matarka ta bonu"
Bai kulata ba, sai da ta ce "Ni fa ban ga laifin Malamin nan ba"
Kallonta ya yi sannan ya ce "Kenan kina so a kashe ahalina?"
"Ba ina nufin haka ba, Muhasin ko jiya nayi mafarki kuma a mafarkina wannan wadda ke kashe-kashen tazo sannan ni bata ci galaba a kaina ba, dan haka zan cogaba da sonka har sai lokacin dana gane gaskiya."
"Hmm! Soyayyarki gareni ai ta ƙarya ce, haka mafarkin ki ma ƙarya ne, domin kuwa kin saka a ranki ne shiyasa har kikayi mafarkin"
"Kaine kake ganin haka, amma ni na san mafarkina gaskiya ne, domin kuwa naga wani abu a cikinsa"
"Me ki ka gani?"
"Ba zan faɗa maka abinda zai ɗaga maka hankali ba"
"Ki faɗa min dan Allah"
"A cikin mafarkina naga an kashe wannan Malamin da muka je gurinsa, ka san nene na gani?" A tsorace ya girgiza kai.
"Duk irin maganganun da kukayi da Malam da kuma irin faɗan da ka riƙa yi sak haka na gani a mafarki, sai dai bayan Malam ya ce mu komo nan da kwana biyu, mun fito Arɗo na maka faɗa, zai ce muje gida zai gana da Malam yana shiga zai tarar an yankawa Malam..." Bata ƙarasa ba tayi shiru domiɓ jin yanda Arɗo ke kwaɗa mata kira.
Juyawa tayi tana kallonsa, daga nesa ya baza riga sai gudu yake duk da cewar ya manyanta . Sai daya ƙaraso inda suke sannan ya tsaya yana haki. "Arɗo lafiya?"
"Na san kin ga haka a mafarkinki meyasa baki faɗa min ba?"
"Arɗo ban ga komai ba"
"Aradun Allah ƙarya kike"
"To naji, shikenan kuma Arɗo sai na faɗa maka cewa wannan Malamin zai mutu?"
"Amma ai sai kice min kar na koma ciki tunda kin ga ka in na koma zan ganshi a mace"
"To ai ina son tabbatar da mafarkina shiyasa na kasa fada maka"
"Mtswww" Yayi tsaki sannan ya wuce.
"Muje ko?" Ta furta tana kallon Muhasin da ya yi mutuwar tsaye.
"Na san ka shiga shakku da tunani, amma karka damu, zan faɗa maka duk abinda kake son sani idan muka ƙarasa gida."
Shi dai Muhasin har suka ƙarasa gidan amma jin sa yake kamar ba shi ba.
Bayan an dama masa fura yasha kaɗan, dan dama tun a jiyan daya zo ita kawai yake sha. Ya zauna a ɗakinsa ya yi zugum sai ga Arɗo ya shigo.
"Sannu yaro" Ɗagowa ya yi ya kalleshi.
Shi kuma ya samu guri ya zauna. "Na san ta faɗa maka tayi mafarki shiyasa ka shiga damuwa ko?"
Kai ya gyaɗa yana kallon Arɗo. "To ka kwantar da hankalinka Zaliha mutum ce kamar kai. Kawai dai tana da wata baiwace wadda mu kanmu bamu sonta, kuma muna alaƙanta abin da shafar aljanu saboda tun tana ƙarama hatsabibiya ce" Ya yi shiru sannan ya cigaba da cewa "Taya yin irin wannan mafarkan kuma wani lokacin sai kaga sun tabbata amma dai bata taɓa yin mafarkin yawancin mafarkan da take da suke zama gaskiya tana yi ne a iya mutanen da take ƙauna, ko kuma inda za aje da ita, babu wanda ya san ranar da wani zai mutu sai Allah haka itama Zaliha a mafarkinta bawai tana mafarki bane kafin ya mutum ya mutu, idan tayi mafarki an kashe mutum ya mutu, to tayi mafarkin ne bayan mutumin ya rasu babu wanda ya sani ka gane? Wannan shi ne karo na uku da tayi mafarkin mutum zai mutu kafin ya mutu. Da har ta fara bayar da magani sai na hanata domin ita macece kuma aure za tayi, idan nace Zaliha ta fara bayar da magani to fa har abada ba zatayi aure ba bare naga zuri'arta, amma sai gashi har yanzu taƙi auren domin ko saurayin yazo korarshi take da kanta, ita tafi son ta fara bayar da magani ni kuma na hana zan ga ni da ita wanda zai ci galaba akan wani" Ɗan lumshe ido Muhasin ya yi sannan ya buɗe yana kallon Arɗo.
"Nima ban bayar da goyon bayan haka ba, ita macece, aure ya dace da ita"
"Arɗo! Arɗo" Yaji muryar Zaliha na kwaɗa masa kira. Kallon Muhasin ya yi sannan ya tashi ya fita.
Wasu ganyayyaki ya gani a hannunta. "Wannan fa"
"Arɗo ina so kayi min izni nayi masa magani da kaina"
"Me zaki iya? Kina ganin Malam Hadi ya rasu ko a dalilin haka"
"Ni na san sai lokacina ya yi zan rasu Arɗo, kuma a mafalkina na gano cewa zan iya warkar dashi Arɗo"
"Ban amince ba" Ya faɗa tare da fuzge ganyayyakin dake hannunta ya fita a fusace.
Muhasin daya fito daga ɗakin da aka bashi ya zauna ita ya tsaya kallo. Itama shi take kallo kafin ta juya ta ƙara kallon hsnyar da Arɗo ya bi.
"Ke macece, hakan bai dace dake ba"
A hankali ta taka zuwa gabansa.
"Ni ina ganin wataƙila ina da baiwar da zan bayar da magani, amma Arɗo ya hana"
"Yana da gaskiya domin ko wane uba indai yana da budurwa kamar ke, to zai so ya aurar dake"
"Tun lokacin daka bamu labarinka na tausaya maka, kuma naji ina son na taimakeka, kuma naji a jikina zan iya taimakonka, har yanzu a mafarkina ba a nuna min taƙamaimai abinda ke damunka ba, amma kuma ni a jikina ina ji wata rana zan gani"
"Zaliha nima bana so ki mutu, nazo na sameku kuna zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin gidanku keda ahalinki bana son na zama silar tarwatsa farin cikinku"
"Ko ma mene a cikin rayuwarka ba zai iya cutar dani ba, domin kuwa da zai iya daya cutar dani tun a jiya dana furta ina sonka"
"Saboda ba soyayyar gaskiya bace, kin faɗa ne dan ki gani ko zaki mutun"
"Da gaske ina sonka Muhasin tun ranar dana fara ganinka, soyayyar da nake maka bata ƙarya bace, anan nake jinka" Ta furta tana nuna saitin zuciyarta.
SaNaz Ce🌸🤘