...BASHI!

Page 14

by @sanazty

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

                   Page 14

__________🖌️ *****
 Yamma liƙis ta mayar da Habib Kano. Bayan ya parker motarsa ya shiga gidan kai tsaye. Alla-allah yake ya shiga kar ya yi katari da Mama domin ya ga missed calls ɗinta da kuma na Najwa barkatai. Amma kuma yana shiga ya tarar da ita zaune tana cin tuwan buski miyar taushe. Zama ya yi kusa da ita sannan ya ɗauki spoon ɗin ya kai loma ɗaya bakinsa "Yummy! Kai Mama abincinki ya yi daɗi sosai, kamar ba a ƙasar nan ba" Harara ta watsa masa tare da faɗin "Ban son rainin hankalinka fa, sakarai kawai shin ma daga ina kake? Kuma meya hanaka ɗaga wayata?"
"Mama ina studio fa, aiki muke so wayata tana silent shiyasa"
"Okay tun daga safe har dare wato duk kana studio ko sallah baka yi kenan sai waƙa?"
"A'a Mama ba haka bane fa, kawai dai dana tashi sallah ban bi ta kan wayar ba, am sorry"
"Sorry for yourself, Najwa fa ta faɗa min cewa taje baka studio ɗin"
"Najwa? Kai she's lying gaskiya ina can kin dai san ba zan miki ƙarya ba Mama"
"Na nawa kuma? Ƙarya sau nawa kike min? Ai sai dai kuma kar a kuma"

"Ni dai afuwan Mama wallahi I don't mean to hurt you" "Hmmm kai ka sani, sai kaje kayi wanka kaci abinci ko"
"Okay sweetheart" Ya furta yana kai mata peck a kumatu. Kai kawai ta girgiza tana kallonsa. Tana matuƙar ƙaunarsa har cikin ranta saboda shi kaɗai suka haifa kuma sannan ya san zafin nema, domin ya yi aiki tuƙuri har ya buɗe nashi studio ɗin ya kuma riƙa tallafa musu.

Yana shiga ya rage kayan jikinsa tare da faɗawa wanka. Ya daɗe a toilet yana wanka kafin ya fito ya shirya. Jallabiya kawai ya saka dan babu inda zai fita in ba masallaci tare da Abba ba. Zama ya yi shiru akan gadonsa kawai tunanin Sadiya ne ya tsaya mishi a rai. A yanzu kam ya fara tunani da tantamar anya zuciyarshi bata kamu da son Sadiya ba, a yadda yake zaune baya cikakken mintuna 10 ba tare daya ga hoton kyakykyawar fuskarta a cikin idanunshi. 

_Haba Yarinya ki dubeni fa, handsome guy dani kice in auri musaka god forbid._ Ya tuna irin zantuttukan da suke yi da Najwa, amma kuma yanzu ga Sadiya lokacin da take kukan rashin ƙafa ji yake ina ma muharramarsa ce ya ɗauketa ya cigaba da kula da ita. "Sonta nake kenan?" Ya tambayi kan shi sai kuma ya yi murmushi. "Maybe izgilancin da nake yi ne ya saka Allah ya jarrabeni da matsanancin son Sadiya. Ya salam" Ya dafe goshinsa. "Ba zan yi gigin faɗa ba har sai tayi nisa a karatunta, sai na bari ta shaƙu dani dan ina tsoron na furta mata a yanzu tayi tunanin ko dan na bata ƙoda ta ne." Ya faɗa tare da tashi ya nufi parlour dan lokacin ana kiran sallar magrib.

Bayan sun dawo daga masallaci suka ci abincin dare tare da Abba anan ne Mama ta sanarwa da Abba yadda suka yi da Najwa. "Alhamdulillahi, to abu ya yi kyau dama ai naga shaƙuwar tasu tafi ƙarfin ace ba soyayya bace" Habib kallon Mama yake da mamaki ɗauke a fuskarta, "Mama ni sam babu soyayya tsakanina da ita" 
"Ita kuma tana sonka dan haka na lamunce mata, domin bata da wani aibun da zaka ce bata maka ba" 
"Ni dai na san Najwa an bayar da ita ga wani Soja"
"Yarinyar fa ta faɗa min wasa take maka kai kuma ka kasa fahimta."
Shiru ya yi bai ce komai ba, dan baya son ya riƙa musu da iyayensa.

"Habib ba zan takuraka akan dole sai ka so ita Najwa ba, amma ka zauna kayi tunani tunda har ita tana sonka, sai ka kuma bincika ka gani in ba a bata wani ba, sannan ka faɗa min, domin ba zan so ka karya zuciyar mace ba"
"To Abba insha zan yi yadda kace"
"Ni kuma kar kayi ta tawan, ai gobe zanje gidan su Najwa muyi magana da uwarta. Ga kamilar yarinya tazo amma kai saboda ba auren ne a gabanka ba. Kuma dan nayi shiru akan batun ƙoda ko? To wallahi kar ka yarda na sake ɗaga maganar domin kai ka san mai laifi ne a gurina" Abba dai kallon ta ya yi kawai yana murmushi yanda ya ga tana faɗan gaira babu dalili. Habib kuwa ji ya yi gaba ɗaya kamar ma ba shi ba.

Miƙewa ya yi ya koma ɗakinsa ya haye gado.
  _Sadiya...!_ Kawai yaji zuciyarsa ta ambaci sunan.
"Gaskiya ba zai yuwu ba, ni ba zan yi aure inda ba za a ga darajar iyayena ba" Ya furta a fili gami da lumshe ido tare da sakin nannauyar ajiyar zuciya.

            **** **** **** ****

Daga inda take zaune ta miƙe tsaye cikin tsananin tashin hankali. Fa'iza dake shan custard ta riƙe spoon ta kasa kaiwa baki kawai ta tsaya kallon Aziza.

"Na shiga uku, wayyo Allahna" Aziza ta furta tare da sakin wayar hannunta, Fa'iza na shirin yi mata magana kawai sai gani tayi ta sulale a gurin ta suma.

"Mommy..! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta a lokacin data ƙarasa kan Aziza tana jijjigata. Mommy a firgice ta fito daga kitchen ta ƙarasa da gurin sauri. "Mene ya sameta?"
"Muna zaune kawai ta miƙe da waya a hannu, kafin ma na kai ga yi mata magana ta faɗi."
"Maza ɗauko min key ɗin motana a kan dressing mirrow" Da sauri Fa'iza ta wuce side ɗin Mommy.

*30 minutes later*

"Doctor baka ce mana komai game da Aziza ba?"
Shiru ya yi na wani lokacin kafin ya ce "Na rasa ta ina zan faro maganar"
"Ka faɗa ko taya ya ne zan gane"
"To a gwaje-gwajen da muka yi mata mun gano tana..." Sai kuma ya yi shiru. 
"Doctor just go straight to the point."
"Hajiya na san dai babu wanda ya yi aure a cikin 'ya'yanki amma kuma da aka mata gwajin mun gode tana ɗauke da ciki har na tsawon wata huɗu da sati biyu, sannan kuma abinda ya sakata suma an faɗa mata abinda ya ɗaga hankalinta wanda har jininta ya yi mugun hawa"

Ba Aziza da abin ya faru a kanta ba, hatta Mommy da kuma Fa'iza sai da suka girgiza da jin furucin Doctor. Aziza kuka kawai ta saki a gurin, Mommy ta kasa cewa komai, har Doctor kasa ce masa komai tayi, ji tayi wata kunya ta rufeta gaba ɗaya.

A mota an rasa mai magana. Duk da Mommy bata bawa Fa'iza mota, amma a ranar ita tayi driving nasu zuwa gida, saboda ji tayi gaba ɗaya jikinta na rawa ba zata iya tuƙi ba. Tun daga asibiti har gida Aziza na kuka, glass ɗin ma ɗora shi tayi a cinya sai da taga Fa'iza tayi parking sannan ta saka ta fita da gudu.

A kan gado ta kwanta ta cire glass ɗin ta ajje gefen side drawer. 

"Waya miki ciki?" Maganar da kuma shigar bulala jikinta gaba ɗaya lokaci guda taji su. Tsabar tashin hankalin da take ciki ashe ma a buɗe tabar ƙofar bedroom ɗin ta shiyasa bata san shigowar Mommy ba.

Cable na waya da tayi amfani dashi shi ta ƙara tsula mata a karo na biyu, a gigice ta zabura tare da laluben glass ɗinta dan bata iya ganin Mommy sosai, sai dai kuma tana taɓoshi ya zame ya faɗi ƙasa dan haka bata samu damar ɗauka ba sai neman ceton kanta daga dukan da Mommy ke mata.
Kuka sosai take itama Mommy na kuka tana dukanta gami da tambayarta akan waye ya yi mata ciki. A haka Fa'iza ta shigo ɗakin da sauri kuma ta riƙe Mommy, "Mommy please dan Allah ki ƙyaleta" Fa'iza tayi maganar cikin kuka.

Mommy kuwa anan ta saki wayar sannan ta fita tana goge hawaye, Aziza kuka kawai take a fili, duka uku. Na farko abinda ta gani a waya, na biyu cikin da aka ce tana dashi wanda har ya kai wannan watannin bata taɓa jun ko alamunsa ba, abu na uku kuma dukan da Mommy tayi mata. Fa'iza ta saka hannu tana goge mata hawaye sannan ta ɗauki glass ɗinta ta saka mata a fuska. Kallon Fa'iza ta yi sannan ta ce "Shikenan tawa ta ƙare" Aziza ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka.
"Bata ƙare ba Sister ki kwantar da hankalinki insha Allah za a warware komai" 
A haka dai ta lallaɓata sannan ta fita daga ɗakin.

"Yaya Muhasin kana ina? Ina ka shiga Yaya? Kazo ka gani yanda abokinka yaci amanata. Hafeez ya cuceni shi ne namiji kaɗai daya sanni a mace, amma kuma gashi yanzu an saka bikinsa zai yi aure ya bar ni da tashin hankali, Hafeez Allah ya isa tsakanina da kai, daka ruɗi zuciyata da kalaman ƙarya ka yaudareni ka lalata rayuwata sannan za kayi aure" Sai kuma ta goge hawaye ta ce "Nayi alƙawarin sai dai muyi mutuwar kasko amma yadda ka tona asirina ka tozartani wallahi sai ka gwammace kiɗa da karatu. Sai na tozartaka sai na ɗaiɗaita rayuwarka" Ta share hawaye tare da maka uban tagumi.

Fa'iza kuma tana fita daga ɗakin Aziza kai tsaye na Mommy ta wuce. A zaune kan sofa ta tarar da ita da Hanky tana goge hawaye. Zama tayi tare da riƙo hannayen Mommy "Mommy dan Allah kar ki bari damuwa ta saka miki wani ciwon" Kallonta tayi sannan ta ce "Fa'iza dole na damu, dole na kuma zubar da hawaye. Bayan tashin hankalin da muke ciki, aka zo Muhasin ya gudu bamu san ina ya tafi ba, yanzu kuma ga wannan abin da Aziza tayi, ji nake na karaya na kasa cinye wannan jarabawar" Ta furta tana goge hawaye kafin ta cigaba da cewa "Duk yanda nake ganin a cikin 'ya'yana Aziza ce mai addini da tsananin tsoron mahaliccinta amma kuma sai gashi itace ta watsa min ƙasa a ido. Mahaifinku kina gani ya kaɗa Muhasin kuma shi ma ya tafi, da wanne zan ji?"
"Ke uwa ce Mommy, you have to control your anger" sai kuma tayi shiru. "Am...I mean na san it hurts you alot, but, but Mommy dole sai kin danne zuciyarki please" Ita kan ta Fa'iza tana jin hawaye amma dai ta rasa su, domin sun kasa zubowa bare taji sauƙi a ranta.

Yinin ranar haka gidan ya kasance tamkar na makoki, kowa na ɗakinsa ko parlour babu wanda ya shiga, hatta 'yan aikin gidan sai da suka gane akwai matsala, musamman Aziza da ko abinci da suka kai ɗakin nata da sukayi knocking basu samu damar shiga ba.

_Washe Gari_
*11:30am*

Gaba ɗaya fargaba ta cika zuciyarta, amma haka tayi dakiyar murɗa handle na ɗakin Mommy ta shiga. "Eh ba matsala hakan ma ya yi zamu zo anjima" Shi ne abinda taji Mommy ta faɗa a lokacin da ta shiga ɗakin, kuma shi ne last abinda ta faɗa ta ajje wayarta.

Har ƙasa ta tsugunna ta ce "Mommy good Morning" Bata samu amsa daga gurinta ba kuma dama tayi tsammanin hakan zata faru. "Am...am..so..sorry for what i did, but actually shar..." Bata ƙarasa ba taji saukar mari a kuncinta. "Actually..? Kin zo ki min lakca ne ko me?"
"No Mommy i just come to apologize"  
"Aziza baki da wasu kalamai da zaki iya min magana dasu na gaskata muddin baki faɗa min wanda ya miki ciki ba"
Hannu ta saka ta goge hawayen da suka mata kaca-kaca a fuska sannan ta sake kallon Mommy sai kuma ta sauke kai. "Hafeez ne Mom..."
"What? Hafeez?" Kai kawai Aziza ta gyaɗa tana hawaye.

"Yanzu dama duk tarayyarku da Hafeez bata tsakani da Allah bace. "Mommy nayi ƙoƙarin na nusar dashi amma ya ce ai ni zai aura, ya yaudareni da kalamansa ya saka nayi... Kuma wallahi sau ɗaya ne Mom...." Hannu Mommy ta saka ta kwaɗe bakinta, wanda har sai da jini ya fito. "Ki tashi ki ɓace min da gani, kuma mintuna talatin na baki ki shirya zamuje asibiti.

Bata iya cewa komai ba kawai ta tashi ta fita. A zaune ta tarar da Fa'iza akan gadonta tayi tagumi. Sai da ta fara shiga toilet ta fito sannan ta zauna gefen Fa'iza "I just want to die"
"Haba Sister sai kace baki san ƙaddara ba, kece fa kike tausasa zuciyar Yaya yau kuma kema kina kirawo wa kanki mutuwa"
"Fa'iza ni na san irin zafin da nake ji, i regret knowing Hafeez in my whole life, ya yi convincing ɗina na aikata zina and na samu ciki, sau ɗaya tal a rayuwata na aikata sex Fa'iza skin love kawai na san muna yi da Hafeez sai ranar da naje Abuja karɓar transfer letter ɗina anan ya ruɗeni mukayi sex kuma i swear to god ko a karo na biyu daya nemi muyi naƙi yarda dashi ne, domin na farkon ma abin ya daɗe a raina ban mata ba, ina ta dana sani, and yanzu ga pregnant sannan in the next coming 2 weeks bikin Hafeez I don't even now about it naga kawai yana yawo a social media ne, sai na tambayi wata friend ɗina ta gaskata min Asiya tayi min sending I.V ɗin, and na gani a wani group ban kawo shi Hafeez ɗin ba" Sai kuma ta sake fashe wa da kuka.

"Dama How would he inform you about his wedding bayan he betrayed you, shiyasa fa ni I don't trust men, they are all wicked, hmmm dor ni ban taɓa soyayya ba, am still young and i don't think zan tsinci kaina at that situation of loving someone that much da har zan iya bashi ko tafin hannuna ya taɓa a matsayin soyayya i can't do that i swear. But to be honest Aziza you made a mistake, you read alot of novel both English and hausa, fiction and true life stories and you watch alot of movie and bakiyi experiencing komai ba akan soyayya, you are matured fa, wallahi Aziza kin sani na sani duk namijin daya rike koda hannunki ne da sunan feelings to daga wannan lokacin darajarki ta ragu a idanunsa. Kuma dama ai daga nan suke farawa yana taɓa jikinki kin ƙyaleshi dole wata rana ya nemeki kuma gashi ya nemeki ke daɗi soyayya kin bashi jikinki at the end zai yi aurensa. Shi fa iskanci a gurin namiji ado ne amma a gurin mace babbar musiba ce, kece zaki zama uwa wata rana dole ba zaki so wannan image ɗin naki a bayyanawa 'ya'yanki ba, Aziza wallahi ko da kin auri Hafeez ba zaki taɓa daraja a idonsa ba, sannan zargi dole sai ya shiga kuma kin san duk auren da yake da zargi cikinsa to babu wannan auren, sannan a kanshi ba zai ga darajarki ba saboda kin ɓarar masa da ita tun a waje. Kuma shi namiji ɗan iska ba a ganeshi, sai dai kawai ni na san jijiya naso take kuma ita zina BASHI CE, abinda ya yi miki sai anyi masa sai ya yi dana sani a gaba kamar yadda kikayi a yanzu ko fiye da haka"

Mommy dake tsaye bakin ƙofa tana jin tattaunawar tasu, runtse ido tayi jin furucin Aziza na ƙarshe “ZINA BASHI CE” ji tayi jikinta har ya fara karkarwa a take ta fara ganin rayuwarta ta baya ta fara dawo mata kamar a lokacin abin ke faruwa.

*WAIWAYE*