...BASHI!

Page 15

by @sanazty

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

                   Page 15

__________🖌️ *Waiwaye*

Adamawa Yola shine asalin garin su Hajiya Rukayya Mu'azzam(Mommy) talakawa ne liƙis wanda a wasu lokutan ma sukan tsinci kan su a halin neman abincin da za su saka a bakin salati. Gidansu gini ne nada wanda akayi da jar ƙasa, sai dai akwai guraren da suka zagwanye wanda aka mayar da langa-langa saboda halin talauci basu da ko kuɗin da za a mayar da jar ƙasar. Babban gidane mai a ƙalla yanki goma sha a ciki, domin daga iyaye har kakanni anan suka rayu hakan ya saka a unguwar ake kiran gidan da gidan gado, wato tun iyaye da kakanni duk a zaune suke anan, ko 'ya'ya idan za suyi sure anan suke yankar guri kasamcewar gidan gidane babba, matan ne kaɗai aure ke fitar da wasu amma wasu a ciki tsakaninsu suke aure(Cousins). Gida ne mai matuƙar aƙida kuma ahaline masu matuƙar haɗin kai.

Saifullahi wanda ya kasance ɗan Yayan Mommy ya taso da so da kuma ƙaunar Mommy, tun daga yarinta har girma. Mutum ne da yake da ƙoƙarin neman na kansa domin shi Malam Mu'azza baya da wata sana'a data wuce gyaran radio, wanda yau idan ya samu gobe ba samu yake ba, sai kuma Maman Mommy ita tana sana'ar surfe. Su biyu kawai iyayensu suka haifa daga ita sai Yayanta Naziru wanda baya da wani buri a rayuwarsa daya wuce karatu. Ya kan ɓata lokaci akan karatu tun daga safiya har dare, sai dai kuma baya da wani ƙoƙari. Itama Rukayya ta kan je makaranta ta dawo duk da mahaifinsu nason suyi karatu amma ita kuma sam abu ne da baya cikin tsari na rayuwarta. Sai dai kuma Saifullahi ya tsaya tsayin daka dan ganin tayi karatun. Kamar yanda yake son ta haka itama tana matuƙar ƙaunarsa, tun ahalin gidan basu fuskanta ba har suka zo suka gane hakan. Hakane ya saka iyaye maza suka zauna kamar yadda suka saba zama domin a tsayar da ranar aure, sai dai shi Saifullahi da mahaifinsa ya tuntuɓeshi da maganar sai ya roƙi alfarmar a barta ta ƙarasa karatu domin kuwa yana da burin ko a gidansa Rukayya ta cigaba da karatu.

Sai dai kuma tana aji huɗu na sakandire anan ne Muhammad(Daddy) Ya shigo cikin rayuwarta, lokacin ya zo service anan Yola. Tun bata son shi ba kuma ta kulashi har ta kai ta kawo ta fara son shi saboda manyan kuɗaɗe da yake kashe mata, a lokacin kuma tuni anyi baikonta da Saifullahi.

Gidansu babu wanda ya iya gane meke faruwa domin kuwa komai a ɓoye suke yin shi, har waya ya saya mata sai da kuma sabbin suturu wanda a gidan ƙawarta mai suna Aliya anan take ɓoye su. Soyayya ce mai ƙarfi ta shiga tsakanin Daddy da Mommy, wanda har ta kai ta kawo su kan yini tare sai dai tayi ƙaryar cewa a makaranta yanzu suna daɗewa saboda ana masu bita ta musamman. Daga nan kuma idan ya ɗauketa zasu fita yawon shaƙatawa daga nan ya wuce da ita gidan shi. Ƙarfin son da sukewa juna da kuma ruɗin shaiɗan ne ya haddasa masu kasancewa tare kusan ko wace rana ba tare da sun yi aure ba. A haka kuma har ciki ya shiga, sai dai inda Allah ya taimaketa ta gane tun kafin a gida a ranfota ta shiga tashin hankalo ainun, domin a lokacin ma tuni ya gama service ɗinsa sai dai ya nemi aiki anan Yola kawai saboda ita. Shi dama ɗan msu hannu da shuni ne ɗan gata kuma ɗan so, ko me yake so shi ake masa hakan ce ta saka ko daya nemo ya cigaba da zama a Yola ba a hana shi ba. 

Ya nemi da a zubar da cikin sai kuma taƙi yarda saboda tsoro da kuma fargabar kar ta rasa rayuwarta, amma daga ƙarshe sai ta amince dan gudun kar asirinta ya toni. An zubar da ciki kuma har tayi jinya ta gama bata bari iyayenta sun ranfo ta da yake ta haɗu da iyaye mararsa kula. Daga nan kuma sai ya nemi da suyi aure kawai su huta da wannan rayuwar barikin. Tayi murna sosai da kuma farin ciki, sai dai tashin farko tana faɗawa iyayenta suka ƙi yarda sai dai wan ta Naziru shi kaɗai ne ya goya mata baya.

Ita kuwa tayi ruwa tayi tsaki ta ce ita sai Muhammad babu kuma wanda ya isa ya hanata aurenshi. “Idan har Muhammad kika zaɓa to na yafe ko cikin ahalina” Malam Mamman wanda ya kasance kaka a gareta shi ne ya furta hakan amm tayi tsalle ta dire ta kuma ce taji ta gani. Saifullahi a wannan lokacin babu irin magiya da roƙo da bai yi kan karta gujeshi. Amma haka ta sakawa idanunta kwalli ta ce ita ga arziqi ba zata raɓi tsiya ba. Jin wannan furucin ya saka mhaifinta Malam Mu'azzam ya yi mata dukka wanda har tayi zazzaɓi na kwana biyu, domin sai daya farfasa mata jiki, kuma ya ce a talaucin da aka haifeta bata isa tayi gori da asalinta ba, dan haka ko mutuwa za tayi ba zai aura mata wani bayan Saifullahi ba. Ita kuma tana gama jiyar ta sameshi ta ce dashi muddin ya aureta sai ta kashw shi. 

Haka ta samu mahaifiyarta a ɗaki ta ce da ita “Mama ni dama asali na tsani talauci na kuma tsani talaka, ƙaddara ce ta saka aka haifoni anan, amma kina ganin kyawuna da dirina kin san nafi ƙarfin talaka da gidan hutu na dace dan haka wallahi ba zam taɓa auren Saifullahi ba” Mamanta kuwa kuka sosai tayi tare da faɗin ba dan a gida ta haifi Rukayya ba da zata iya cewa musanya mata akayi domin su ahalinsu suna da kunya da kuma kara.

“Ni ba zan yi kara in kuma cuci kaina ba wallahi” Shi ne abinda ta faɗa. Ƙarshe dai daga iyayenta har sauran 'yan gidan babu wanda bata yiwa rashin kunya ba, aka yi baram-baram. Mahaifinta ya ce shi bai mata baki ba amma kuma ya zame hannunsa a kanta saboda bata g mutuncin shi shi da uwar data haifeta da kuma Saifullahi da ya riƙa ɗawainiya da ita, da kuma kakanninta haka take ta gasawa kowa magana. 

Zaman da akayi da ita aka ce ta zaɓa ko dai ta bar ahalinsu idan ta auri Muhammad ko kuma ta haƙura ta auri Saifullahi sai ta buɗe baki ta ce dama ai a gidan aure sabuwar rayuwa ake buɗewa dan haka ita ta zaɓi Muhammad, ta kuma yarda da furucinsu na ta rasu dasu ɗin. Sannan ta ƙara da cewa ai nan gaba sune zasu nemeta domin kuwa kaf ahalin nasu babu wanda ya auri mai ko kwatan ƙuɗin Muhammad duka talakawa suka aura, dan haka ita kam tana buƙatar hutu.

Sati ɗaya aka saka bikinta, har akayi auren Muhammad ya tafi da ita amma Saifullahi na kwance yana jinyar zuciyarsa domin tsananin son da yake mata bana wasa bane. A ranar kuma da zata tafin sai da suka ƙara jaddada mata basu san ƙara ganinta a cikin rayuwarsu ta ce hakan ma ya yi.
Gidan da aka kaita Abuja danƙareren gida ne, ko a mafarki bata taɓa tunanin samun irinshi ba. Sannan ya saya mata mota kuma da kanshi ya koya mata, ya kuma kaita makaranta ta ƙarasa secondary school ɗinta. Gata so da kuma ƙauna babu wanda bata gani ba saboda ya san irin ƙalubalen data fuskanta a kanshi kuma shi ɗinma Allsh ya dasa masa tsananin ƙaunarsa. Sai dai kuma tana shiga aji ɗaya a jami'ar Base University komai ya fara canzawa a lokacin ta samu cikin Muhasin sai ya fara zargin cikin ba shi ne bane ganin yadda take jami'a kuma dole sai anyi cuɗanya da maza. Duk yadda ta so ta nusar dashi amma ya kasa fahimta kuma wannan kuskuren bashi jikinta a farko da tayi shi ne ya jawo hakan.

Tayi kuka tayi dana sani domin ya juya mata baya sosai, sai ya tafi wata ƙasar ya barta wata ɗaya wata biyu har uku, idan kuma ya dawo maganarsa ɗaya ce jikinsa yana basa idan baya nan tana kawo masa maza,zantuka dai kala-kala. A haka ta samu dai ta haifi Muhasin ba tare da kulawarsa ba sai ma baƙin ciki data fara ƙunsa. Har aka yi suna bai dawo ba bata ma san wace ƙasa ya tafi ba. Sai dai yana dawowa ko hutu kirki bai samu ba ya ce dole sai sunje anyi DNA. Haka suka tafi asibiti kuma suna zuwa aka yi gwajin tare da tabbatar masa da ƙwayoyin halittarsu iri ɗaya sai a sannan ya bata haƙuri tare da yi mata aƙawarin ya daina zarginta. Sai a sannan hankalinta ya koma Yola, domin kuwa Daddy sati biyu kacal ya yi ya tafi.

Zama na minti ɗaya bssu yarda tayi ba, domin cewa suka yi gidan ma ba dan basu san zata zo ba da ba zasu bari ta shiga ba, abin mamaki hatta Mamanta ta juya mata baya.

Anan ne bayan ta fito Naziru ya sulalo ya biyota shi ne ya haɗata da Malam Yakubu tunda yana Kano da zama shima, ya ce duk abinda take so ta tuntuɓeshi tunda Baba da Mama sun ce middin ta ƙara zuwa sai sun tsine mata kuma sun saka yara sun mata korar kare har bakin gari.

To bayan ta koma ne ta haɗa kuɗi ta aikawa Naziru kan yaje ya nemi admission, shi kuma sai ya yi amfani da damar ya tafi ƙasar uganda yana kasuwanci.

Daddy kuwa baya bata kulawa kuka da dana sani a duk lokacin data tuna abinda tayisa ahalinta dominsa sai tayi amma kullum haƙuri yake bata kan yanayi ne na aiki kuma yana nema masu abinci ne. A cewatsa idan ƴa dawo ya zauna to wata rana kuɗin daya tara ƙarewa za suyi shi kuma ya tsani talauci. A sannan ƙuncin a haka ta haifi Aziza da Fa'iza daga nan ne kuma haihuwa ta tsaya mata. Kuma tun zuwan da tayi lokacin tana goyon Muhasin bata ƙara ko maganar Yola ba, domin sun ce sun tiga sun fitar da ita a cikinsu.

_Wannan shi ne taƙaitaccen labatin Mommy_

Hannu ta saka tana goge hawaye. _Kenan abinda na aikata a baya shi ne yanzu ya shafi 'yar cikina. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un._ Ta furta lokacin da taji jikinta yana kyarma. Aikuwa da sauri ta euce ɗakinta da sassarfa.

"Kenan abinda na aikata shi ne ke bibiyar 'ya'yana? Rashin biyayya da kuma butulcin da nayiwa Yaya Saifullahi wanda ban san a yanzu yana wane hali ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta hankalinta a matuƙar tashe.

       ***** ***** *****

"Ba kallona za ka tsaya yi ba, ka faɗa min kawai shin zaka aure ni?" Ta faɗa tana ƙarasowa gabanshi tare da tokara sandar dake hannunta. 

"Ba yanzu ne lokacin daya kamata kayi aure ba, har sai ka warke" Shi ne abinda Mommyna ke faɗa min a koda yaushe.
"Waye kuma haka?" Ta furta idanunta a kansa. "Mahaifiyata" "Oho na gane, amma kuma ni ina so ka aure saboda in taimaka maka" "Idan har kika mutu a sanadina ba zan iya yafewa kaina ba, bana son in cigaba da cutar da kowa ina son kawai in samu lafiya amma ba ta wannan hanyar ba"
"Babu abinda zai faru dani Muhasin, da akwai da tun ɗanar da kazo zan mutu kamar yadda duk wanda kuke soyayya suke yi, domin tun lokacin dana fara ganinka naji duk duniya bani da wani wanda nake so face kai"

Shiru ya yi, domin a wannan karon bai kalleta ba. "Ko zaka ce baka sona? Ko zaka ce ban maka ba kamar yadda sauran 'yan kauye ke fada" Bai bata amsa ba, ta tsugunna gabansa ta ce "Tun lokacin da nayi wannan mafarki naji tsanankn tausayinka ya kamani, har naji ina so na taimakeka, dan haka ka bani wannan damar." Ta furta a sanyaye.

"Shikenan na amince, Allah ya shige mana gaba" Ya furta yana jin gabansa na tsananta faɗuwa. Murmushi tayi sannan ta ce "Idan Arɗo ya dawo zaka sanar masa kana sona kuma so kake a ɗaura aurenmu" Kallonta ya yi. "Ni mace ce ba zan ce nice nake sonka ba" Ta bashi amsar a taƙaice kafin ta tashi ta bar gurin.

*2 hours later* 

Jin kamar maganar Arɗo a tsakar gidan ya saka ya yi saurin fita, amma bai samu ya ƙarasa ba saboda maganar da yaji suna yi da matarsa Yafindo. "To kana ganin idan muka tsafe ta zamu iya yin nasara?"

Arɗo ya yi dariya ya ce "Ai naji daɗin yanda Zaliha ta ce tana son shi, domin dama, dama nake nema dan ganin na cimm burina a kanta, ta yadda zan cire idanunta in kuma yi amfani dasu wajen cimma burina, kin ga idan an tashi za a ce shi wannan baƙon shi ne ya cire mata idanun domin shi ne baƙo a cikinmu."

_Anya wannan shi ne mahaifin Zaliha?_ Ya furta a ransa, a kuma tsorace ya juya kawai sai ji ya yi yaci karo da mutum, a kiɗeme ya ɗago ya kalleta.

Hannu ta saka kan leɓenta sannan ta juya ta shiga ɗakinsa, shima bin ta ya yi, gaba ɗaya a tsorace yake.
A tsaye ya sameta tayi shiru tana riƙe da sandarta. Murmushi tayi sannan ta ce "Sune iyayen Rabilu amma ni ba sune suka haifeni ba, na san kana mamaki ace iyayena ne zasu nemi hallaka min rayuwa. Na san da haka tuntuni shiyasa na zaɓi dana aureka domin koda na mutu to zan yi farin ciki na matu da aurena."

Fkrgigit ya farka daga nannauyan bacci da yake, hankalinsa a tashe yake ƙarewa bukkr da yake kwance kallo. "Ko ban faɗa ba na san kayi mummunan mafarki ne. Kallonta yake kafin ta samu guri ta zauna tana kallonsa. "Da alama mafarkin da kayi ya yi bala'in ɗaga maka hankali ko? Dan naga ka haɗa zuffa" "Ina so na tambayeki" 
"Ina jinka" "Wanda kuka tare dasu iyayenki ne ko ƙuwa?"
"Amma meyasa kayi wannan tambayar?" 
"Ina so na sani ne kawai" Shiru tayi na wani lokacin kafin ta ce "Arɗo ƙanine ga Baffana, kuma a hannun Arɗo na tashi tun kafin nayi wayo har na girma, shi ne Baffana a yanzu" Ji ya yi zuciyarshi ta cigaba da harbawa da sauri.

"Tabbas Arɗo mutumin kirki ne domin ya yi min ruƙo na kirki da kyau" Ta faɗa tana ƙara jaddadawa. Shi kuwa Muhasin kallo yake bin ta dashi dan ya rasa bakin magana.
"Tabbas naso na taimakeka Muhasin kuma a yanzu ma zan yi iya ƙoƙarina, sai dai na san idan ka aureni Arɗo zai yarda in maka magani saɓanin anan da yake ganin bamu da alaqa ko ta kusa kota nesa. Amma na san ba zaka iya auren 'yar fillo da suke da ruga a dokar daji, kuna da ƙyanƙyami 'yan binni na sani"

"Zan aureki, amma da sharaɗi guda?"
"Wane sharaɗi?" 
"Zan ɗaukeki mu koma garinmu?"
"Nima ina da nasa sharaɗin"
"Faɗi naji"
"Zan bika garinku amma har sai bayan ka samu lafiya"
Shiru ya yi ita kuma ta ƙara faɗin "Arɗo na zuwa ka sanar masa don Allah"
Kai kawai ya gyaɗa.

          **** **** *****

Kallon Doctor tayi sannan ta kalli Mommy, tare da girgiza kai. "Ba zan iya ba" Ta faɗa tana fashewa da kuka.
Cikin kwantar da murya da kuma rarrashi Doctor Isma'il ya ce "Ki kwantar da hankalinki, na san kina tsoron mutuwa ne, to ba zaki mutu ba, lafiya ƙalau za a cire cikin, bama zaki wani sha wahala ba" 
Kallon shi tayi hawaye sun mata bibbiyu ta ce "Bana tsoron in mutu a yanzu domin na san mutuwa tana kan kowa, amma ni ba kaina nake tausayawa ina tausayin ɗan dake cikina, domin har na fara jin motsinsa dan haka ba zan yarda a zubar min dashi ba" Ta ƙarasa maganar tare da kai hannu tana riƙeshi.

Cikin ɓacin rai Mommy ta ce "Kinsan abinda kike faɗa kuwa? Ko kin haukace ne? To wallahi sai an zubar da cikin ba zaki saka muyi abin kunya ba. Da wane idon zan kalli dangin babanki, sannan ke kanki sai kin haifi shegen kin rasa kuma wanda zai aureki sannan zaki ce dama kin zubar. Ko kuma idan yaron ya girma ya fara tambayar mahaifinsa"

"Mommy wallahi ba zan zubar ba, zan haifa in kaiwa su Hafeez, amma ni ba zan kashe rai ba, bayan ban sani ba ko shi ne kaɗai abinda zan haifa a doron ƙasa" Tana gama faɗa ta wuce tana goge hawayenta. Su kuma da ido suka bi ƙofar.

Ɗan lumshe ido Mommy tayi yadda taji kanta na sara mata. "Hajiya a hankali za a bita idan aka ce za a mata da ƙarfi to ba za ta amince ba, amma ki samu ki lallaɓata.
"Lallaɓawa? Aziza zan tsaya ina lallaɓa akan laifin data aikata min"
"Take it easy, dole sai an bi a hankali, ki daure kiyi controlling anger ɗinki a kanta"

"Shikenan, bari naje, idan na lallaɓata zan dawo sai a cire"
"To shikenan Hajiya"
"Yauwa Doctor nagode"

Tana fita ta nemi Aziza ta rasa kuma tana ta kiran numberta amma taƙi ɗagawa dan haka ta shiga motarta ta wuce gidan ƙawarta Hajiya Sailuba.

Ta ɓangaren Aziza kuwa tana ganin kiran Mommy amma taƙi ɗagawa saboda kukan daya ci ƙarfinta, kuma tana cikin napep ɗin ma babu abinda take ban da kuka, da kuma dana sani kala-kala.
Tana ƙarasawa ta miƙa masa 2k ta wuce, ya girgiza kai tare da faɗin "Allsh ya yaye miki ko mene ke damunki" Lokacin ma tuni ta kai gate.

Tana shiga parlour Fa'iza ta tareta "Aziza lafiya" Rungume Fa'izar tayi tana ƙara volume ɗin hawayenta, a lokacin kuma Fa'iza itama ta fashe da kuka duk da bata san mene ba. Sun sha kuka sosai kafin daga bisani su haƙura. Suka zauna a parlourn sama anan Aziza ke faɗa mata yadda sukayi da Mommy da kuma Doctor.

"Nima ban goyi bayan ki cire ciki ba, tunda dai kin san wanda ya miki ai kawai a shirya a tafi Abuja wallahi sai dai ya aureki" "Ba zan auri Hafeez ba, Fa'iza Hafeez gaba ɗaya ya fitar min a rai, na tsane shi, ji nake ina ma ina da halin da zan kashe Hafeez sai dai na san duk wanda ya kashe wani to ya rataya a kansa ne, zan barshi da zunuban daya ɗauka da kuma alhakina." Ta ɗaga idanunta sama tare da hannayenta "Allah na tuba, Allah ka yafe min, ban taɓa bin maza ba sai Hafeez shima kuma sau ɗaya amma kuma sai gani da ciki, na san ka nuna ishararka ne a kaina, Allah ka yafe min" Fa'iza na hawaye ta janyota a jikinta tare da goge mata hawaye.

Ɗaya daga cikin masu aikince tayi sallama. Fa'iza ta juya tana kallonta dan ita Aziza bata ko ɗago kai ba.
"Dama baƙuwa ce aka yi tana parlourn ƙasa sai hayaniya take" Jin haka ya saka Aziza tashi ta goge hawayen fuskarta sosai duk da idanunta sun canza kala.

"Ina ganinku na san jinin Muhammad ne ku" Ta faɗa tana kallonsu lokacin da suka sauko. "Baiwar Allah lafiya? Wacece ke?"
"Kishiyar uwarku" Jin haka ya saka gaba ɗaya suka kalli juna.

"Sai dai mu kuma mun san cewa mahaifinmu matarsa ɗaya kuma koda zai ƙara ba zai auri kucaka kamarki ba" Cewar Fa'iza
Cikin faɗa ta zaburo "Ke ki kiyayeni, ni ba sa'ar yinki bace, da uwarki zanyi ba dake ba"

"Baiwar Allah mu fa bamu sanki ba, kawai kin shigo mana gida kina ta zagi, idan ma ke matar Daddy ce to ai sai ki kirashi bamu ba" Aziza ta faɗa da dasasshiyar muryarta. "Aziza dalla kyaleta ta samu daidai da ita"
"Ke ki kiyaye ni ki turo min uwarki da ita zan yi"
Har za ta cakumo ta, Aziza tayi saurin riƙeta "Ki rabu da ita"
"Ai da kin ƙyaƙeta nayi mata duka"

Aziza dai jan Fa'iza tayi suka yi upstairs.