...BASHI!

Page 16

by @sanazty

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

                   Page 16

__________🖌️Ajiyar zuciya ta sauke, gaba ɗaya ji take zuciyarta na zafi da kuma raɗaɗi. "Wannan fa ba wani abu ne da zai ɗaga miki hankali ba" 
"Haba Hajiya Sailuba, ke kanki kin san irin matsalolin da suke faruwa damu, yanzu haka maganar da nake miki Muhasin ya bar gidan nan bamu san inda ya nufa ba, ga kuma Aziza. Wannan wane irin iftila'i ne"
"Matsalar Aziza ƙarama ce fa, da kanki zaki saka mata ƙwaya tasha ko ki bata a matsayin wani magani, daga zarar tasha ko minti goma ba za ai ba cikin jikinta zai zube"

"Amma kina ganin ita ba zata samu matsala ba?"
"Babu abinda zai sameta cikin jikinta ne kawai zai zube"
"To shikenan, zan yi ƙoƙarin yin hakan, zan karɓi maganin daga gurin Doctor, yanzu ma zan koma asibitin kafin na wuce gida"
"To shikenan Allah ya kiyaye gaba, amma Rukayya ki riƙa sassautawa zuciyarki, gaba ɗaya fa kin fita hayyacinki"
Murmushi kawai tayi.

       ***** ***** *****

"Kin san Allah zan yi rashin mutunci fa, naga matar nan har yanzu bata bar gidan nan tana parlour sai rashin mutunci take"
"Ina ruwanki da ita, ki rabu da ita kawai abokin faɗa take nema idan muka shareta ta gaji ta tafi"
"Hmm! Ai ni da kin ƙyaleni na mata rashin mutuncin da sai tayi dana sanin shigowa cikin gidan..." Jin horn ɗin mota ya saka Fa'iza yin shiru, ta kuma miƙe gami da buɗe labule ta hango motar Mommy ta shigo.
"Yauwa Mommy is back" Jin haka ya saka gaban Aziza faɗuwa ta dafe ƙirjinta cikin tashin hankali. "Taso muje" Fa'iza ta faɗa tana kallonta. "Kije kawai" Aziza ta faɗa jikinta a sanyaye. 

"Sannu da zuwa baƙar annoba mai baƙin hali" Matar ta faɗa lokacin da Mommy ta shigo. "Baƙar annoba?" Ta furta da mamaki sannan ta wuce, kawai sai gani tayi matar ta tare ta a daidai lokacin da take ƙoƙarin wucewa.
"Bakiyi attending baƙuwarki ba, kuma kike shirin wucewa"
"Babu amfanin nayi attending ɗinki domin abinda kika ga dama shi kike a koda yaushe idan kika zo gidanmu na nan ko kuma na Abuja" 

"Mommy kenan kin santa?" Fa'iza ta faɗa da mamaki tana kallon Mommy da kuma matar da take ta harare harare. "Matar babanku ce" Ta faɗa tana kallonta, ita kuma da kalli Fa'izar kafin ta ce "Wannan ashe 'yarku ce, daga gani jinin Muhammad ce, waccan ɗayar itace saliha kamarke." 

Murmushi kawai Mommy tayi. "Hmmm! Ai da yake na daɗe bani ƙasar ban ma sansu ba, domin ko zuwa mukayi ni bana ƙarasowa"
"Mommy ni fa kin sakani a duhu, a yaushe Daddy har ya yi aure?"

Murmushi kawai tayi ba tare da ta bawa Fa'iza amsa ba. "To uban naki kin ɗauka da mace ɗaya zai zauna, to bari kiji, bayanni akwai wata, domin yanzu amarya ya yi shiyasa ni kuma ya dawo dani nan in zauna"
"Zama anan?"
"Ƙwarai da gaske dan baki da 'yancin hanani zama"
"Amma daya dawo dake ɗin meyasa bai sama miki gida ba, wai meyasa Daddy ke haka ne ya rasa da wacce zai haɗa kishi dake Mommy sai wannan?"
"Ke....! Ki kiyayeni wallahi, da uwarki zanyi ba dake ba"

Zata ƙara magana Mommy tayi saurin dakatar da ita.
"Matar ubanki ce dole ki bata girmanta, kuje kije ki saka a gyara mata duk inda take so ta zauna."
"Kuma dai" Ta faɗa tana ƙara tuge ɗankwali.

Aziza dake zaune a ɗaki tana jin duk abubuwan dake wakana, jikinta gaba ɗaya ya gama yin sanyi, ta ƙara sarewa da lamuran mahaifinsu, yanzu shikenan Mommy bata da 'yanci sannan kuma akwai abubuwa da yawa da take ɓoye masu, wanda bata san dalilin Mommy na ɓoyewa ba.

             **** **** ****

A yatsine ta fito kuma tabi Mama da kallo kafin ta kalli 'yar aikin "Ba ko wane baƙi zaku bari su riƙa shigo min parlour ba, ban ce ku riƙa barinsu a can lobby na samesu ba" "Ai ranki ya daɗe naji ta ce ita ce mahaifiyar Habib kuma na san Habib abokin Najwa ne" 
"Shikenan jeki ki cigaba da aikinki" Mameey ta faɗa gami da zama.

Jikin Mama gaba ɗaya ya yi sanyi amma ta tattaro ƙwarin gwiwarta suka gaisa da Mama. Sai kuma ta ɗora da cewa "Dama nazo ne akan yaran nan" 
"Wane yara? Ya kamata ki taƙaita magana saboda ina da abin yi a ciki muna aiki a kitchen saboda akwai baƙi da zamuyi" Duk da Mama taji babu daɗi amma ta cigaba da cewa "Naga Najwa da Habib sun fahimci junansu to shine n..." "Hold on Malama" Mameey ta takadar da ita gami da faɗin "Na fahimci inda kika nufa" Sai kuma tayi dariya.
"Yanzu ban da abinki ina Najwa ina Habib, haba ai ba ajinta bane, a gaskiya ni ba zan iya kai Najwa inda zata sha wuya ba, dan haka Habib yaje ya samu wata, na barshi da Najwa a farko ne dan kawai naga sun shaƙu amma ba wai dan suyi aure ba. Dan haka ni ina da abinyi ki gaida gida" Ta shi ta bar Mama zaune a gun tana jin kamar ta mutu saboda takaici.

Ranar yini Mama tayi ba tare da ta samu wani sukuni ba. Abba na dawowa ta magriba ta sanar dashi, ya yi dariya sannan ya ce dama ya ƙyaleta ne ya ga gudun ruwanta.

Bayan Habib ya gama cin abinci ya zauna kusa da ita tare da faɗin "Mama tunda na dawo na ganki baki cikin walwala Allah yasa ba fushin kike dani har yanzu."
"Ban fushi da kai a yanzu Habib, kuma naganar daka faɗa gaskiya ce" Labari ta bashi duk abinda ya faru a gidansu Najwa, shi kuma ya ce sai yaje ya mata rashin mutunci ta hana shi ta ce kuma kar ya nunawa Najwa komai domin bata da laifi.

"Mama uwa ba fin uwa tayi ba, zan iya faɗa da kowa a kanki"
"Na sani amma ni dai ina so ka ƙyalesu kawai"
"Amma dole in ja baya da Najwa domin ina ƙaunar kimar ahalina"
Shiru tayi kafin ta ce "Habib..." Kallonta ya yi sai dai bai ce komai ba.
"Ina so ka auri duk wacce kaga ta kwanta maka a rai, amma ba zan ƙara takurarka ba"
"Mama kin tabbatar duk wadda nake so kuma na kawo miki zaki amince na aureta?"
"Ƙwarai kuwa indai tana da ɗabi'a mai kyau"
Murmushi ya yi tare da faɗin "Akwai wacce nake so Mama, sai dai kuma..." Sai ya yi shiru.
"Ka faɗa mana"
"Mama yarinyar dana bawa ƙoda"
Murmushi tayi sannan ta ce "Dama na san ba banza ba"
Ɗan sosa kai ya yi sannan ya ce "Mama ni a lokacin dana bata sam banji haka ba"
"To shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi, amma 'yar wace unguwa ce?"
"Mama ba a garin nan take ba, su 'yan gaya ne, kuma..." Shiru ya sake yi a karo na biyu.
"Kuma me?"
"Mama bata tafiya sai akan keke, amma ba dashi aka haifeta ba, bama akwai wata uku da samun matsalar ba"
"Gurguwa"

Shiru ya yi yana karantar fuskar Mama.
"Ban yarda ka auri gurguwa ba wallahi, kai a wahale ita a wahale sannan shikenan ba zan ga 'ya'yanka"
"Mam..." "Habib ban amince ba, ni dai na baka zaɓi kan mace amma banda gurguwa" 
Duk yanda yaso ta fahimta amma sam taƙi hakan ba ƙaramin saka shi a ruɗani ya yi ba.

                   ****** ******

"Mommy a gaskiya kin saka mu a duhu, Mommy kina rufe mana abubuwa da yawa matsayinmu na 'ya'yan cikinki. Hakan bai kamata ba Mommy, ya kamata ki faɗa mana wacece ke, ina ahalinki suke? Sannan ya akai Daddy har ya yi aure bamu sani ba"

"Fa'iza mahaifinku yana yin aure ne ba tare dani kaina na sani ba, sai anyi auren daga baya nake sani" "Amma meyasa? Shin ke da Daddy ba auren soyayya kuka yi ba? Mommy wai su waye ahalinki ma?"
"Fa'iza ya isa haka, nagaji da wannan tambayoyin, idan lokacin ki san komai daga gareni ya yi zaki sani, amma ba yanzu ba"

"Mommy amma fisabilillahi sai ki bar wannan matar da bata da kunya ta zauna mana a gida"
"Itama gidan mijinta ne, Fa'iza da Allah fita, i need privacy" Ta furta tana ningina kanta da fuskar gado.

Fa'iza ranta a ɓace ta tashi ta fita ta bar ɗakin.

*Bayan Isha'i*

Suna zaune ita da Fa'iza Mommy ta turo ƙofar ta shigo, sai da taji gabanta ya faɗi.
Zama tayi kan sofa su kuma gaba ɗaya suna daga gado. Aziza ta sauke kanta ƙasa. "Aziza kin ci abinci?" Kallon Mommy tayi sannan tace "Eh" "Yauwa, to ga magani an bani na baki saboda kina da ciki dole ki kula da lafiyarki, Fa'iza ɗauki ruwa a fridge"
Miƙewa Fa'iza tayi, ita kuma Aziza idonta gaba ɗaya ya ciko, dan ta saka a ranta maganin abortion ne."

Mommy da kanta ta ɓalla ta miƙa mata, ita kuma ta saka maganin a baki Mommy tana kwallo tasha ruwa sannan ta miƙe ta ce "Sai da safenku"
"Wannan wace irin rayuwa ce" Fa'iza ta furta ita kuma Aziza da sauri ta miƙe ta nufi toilet.

A ƙasan harshe ta maƙale maganin, t zubar dashi sannan ta kuskure bakinta sosai. Jikinta a sanyaye ta fito bata ga Fa'iza ba dan haka ta cire kaya ta zura na barci tare da fashewa da kuka.

01:50am

Kamar daga sama taji ana bugun ƙofar ɗakinta, dan haka da sauri ta miƙe zaune tana kallon ƙofar a matuƙar tsorace take.

Jin dai bugun yaƙi ƙarewa ya saka ta miƙe a hankali ta kai bakin ƙofar "Waye" Ta furta lokacin da taji bugun zuciyarta ya ƙaru. "Aziza buɗe" Jin muryar Mommy ya saka Aziza buɗe ƙofar. Da sauri Mommy ta mayar da ƙofar ta rufe, gaba ɗaya jikinta ya haɗa zuffa. Hannu Aziza ta kai ta kunna wutar ɗakin, kawai sai taga an kashe.
"Aziza rayuwarmu na cikin haɗari na san wanda yake wannan kashe-kashe Aziz..." Sai kuma tayi shaƙuwa sai jin faɗuwarta tayi. "Mommy, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, to ina Fa'iza?"
Sai ji tayi an buga ƙofar, tare da shigowa a furgice. "Aziza a tsorace nake gidan nan babu lafiya?" Fa'iza ta furta tana sakin numfashi, Aziza ta ƙara kai hannunta ta kunna wutar ɗakin. "Ya ilahi? Mene ya samu Mommy?" Ta furta tare da zama a ƙasa tana ɗago Mommy.

Kuka Aziza ta saki tare da faɗin "Wa meke faruwa damu ne?"
"Mommy, Mommy ki tashi" ta faɗa hankalinta a matuƙarta tashe. "Ya ilahi, Aziza Mommy fa ta suma"
"Bari na ɗauko mota mu kaita asibiti" Ta furta jikinta sam babu ƙwari ta fita.

*Asibiti*

Hawaye sharkaf a idanunta ta kalli Doctor.
"Kana nufin faɗuwar da Mommy tayi har ta samu matsala?"
"Bugun zuciyarta ne ya ƙaru sosai, amma karku damu insha Allah zata samu lafiya zamu bata duk wata kulawa data dace." Hannu ta saka tana goge hawaye.

Fa'iza kallon Aziza tayi tace "To ke ki tafi gida ni zan yi jinyar Mommy anan" 
"A'a ba zan iya barin Mommy cikin wannan yanayin ba, kawai kije Fa'iza"
"Aziza na san a yanzu ba cikin nutsuwa kike ba, ya kamata ki samu kije ki huta, sai ki ɗauko mana kaya sannan kuma ki saka ayi girki"

"To shikenan. Bara naje" Kallon Mommy tayi sa take kwance tana numfashi ɗai-ɗai. Sannan ta juya ta bar gurin.

Tun a ƙofar gida taga mutane a gurin da kuma 'yan sanda. "Meke faruwa?" Ta ƙarasa maganar tana kallon maigadi. "Wannan ɗin wacece?"
"Itama 'yar gidan ce ranka shi daɗe"
"Imrana wai mene ke faruwa?"
"Hajiya yau ma dai anyi kisa a gidan" "Waye ya rasu?" Ta furta cikin tashin hankali tare da ƙarasawa ciki.

A shimfiɗe taga gawar an rufeta har ka, jikinta gaba ɗaya karkarwa yake, ta saka a ranta ma wannan ɗaya daga cikin 'yan aikinsu ce. A ɗan tsorace ta buɗe zanen da aka rufe gawar. Aikuwa cikin tsananin tashin hankali ta yi baya.