Page 18
by @sanazty
*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
Page 18
__________🖌️"Babu wani abu da yake a rayuwata wanda ba dai-dai ba, ban ce ni bana laifi ba, amma ni na san ban aikata laifin da zan samu irin wannan mummunan hukuncin ba, sai dai ban sani ba wataƙila jarabawar rayuwa ce kawai." Muhasin ya faɗa yana kallon Zaliha. "Muhasin dan Allah kada ka ɓoye min komai domin ina tunanin ko wata ce ka taɓa soyayya da ita ka yaudareta baka san aljana bace shi ne take ɗaukar fansa"
Murmushi ya yi sannan ya ce "Ban yi karatu a ƙasar nan ba, ban yi rayuwar ƙasar nan ba, ban san wannan yaudarar da kike faɗa ba, bani da lokacin tsayawa nayi ta, amma na san akwai 'yammata da yawa da suka nuna suna sona, sai dai ni ban basu dama ba saboda basu gabana, macen dana fara soyayya da ita itace wadda aka fara kashewa bayan an yi baikon mu."
"Akwai al'ajabi a labarinka, to waye yake maka wannan abun?" Ta faɗa tana miƙa masa maganin. Karɓa ya yi ya kafa kai ya shanye tas duk da cewar baya jindaɗinsu bai ma taɓa shan irinsu ba amma haka ta daure ya sha kusan rabi sannan ya ajje.
"Nafi tunanin aljana ce a jikina kuma ita take kashe duk wadda ta ce tana sona."
"Ni kuma bana tunanin haka, akwai dai wani abu na musamman, amma a hankali zan gano shi"
***** ****** ******
"Mommy! Alhamdulillah kin farka kenan" Aziza ta faɗa lokacin data tattaro ɗan sauran kuzarin daya rage mata.
"Wai ina kika tsaya ne?" Fa'iza ta tambaya tana kallonta.
"Na ɗan biya gidan wata ƙawata ne Babanta baya da lafiya shi ne naje nayi dubiya"
"Ayya to Allah ya bashi lafiya"
Gefen Mommy ta zauna tare da faɗin "Mommy ya jikin naki?"
"Da sauƙi Aziza ji nake kamar ma babu abinda ya sameni"
"Amma Mommy wacece?" Ta tambaya tana kallonta. "Wacece me?"
"Mommy ba jiya kin shigo ɗakina kina faɗa min cewa kin san wanda yake kisa"
"Ni kuma?" Ta tambaya.
Aziza baki ta saki tana kallon Fa'iza, kafin Fa'iza ta ce "Amma Mommy a ɗakin Aziza kika suma fa"
"Ni dai na san na kwanta bacci amma daga nan ban sake sanin ina nake ba, sai tashi nayi na ganni anan tare da Fa'iza"
Mamaki gabaɗaya ya cikasu, sai dai dukkansu sun kasa cewa komai.
_Kenan an gusar mata da tunani? Wannan wace irin rayuwa ce._ Aziza ta faɗa cike da mamaki.
_Wai mene ke shirin faruwa damu ne? Yaya baya nan amma kuma matsaloli sun ƙi rabuwa damu, ya rabbi ka dubemu._ Cewa Fa'iza tana msi dafe goshinta da hannu.
Har akayi sallama gaba ɗayansu basu da sukuni, Aziza tayi driving ɗinsu zuwa gida dukkansu basu da kuzari a jikinsu.
Bayan Mommy tayi wanka ta shirya a parlour ta iske Fa'iza da Al-qur'ani a hannu. Zama tayi sannan ta ce "Ina Aziza?" "Tana ɗakinta" "Kirawo min ita" Ta faɗa tana gyara zama ita kuma Fa'iza ta miƙe zuwa ɗakin Aziza.
A zaune ta tarar da ita tana ta kuka, ita kuma ta zauna a gefenta tare da faɗin "Kuka fa ba shi ne maganin matsalarki ba Aziza, kuma wallahi kin san zaki iya samun matsala a zuciyarki ko kuma idanunki da basu da cikakkiyar lafiya"
"Fa'iza tsoro nake, rayuwata bata da wani amfani, Hafeez ya cuceni, na kasa samun sukuni"
"Hafeez ba zai tsayr da rayuwarki ba, ya kamata ki tsaya ki fuskanci alqiblarki"
"Wace alqibla nake da ita bayan rayuwata ta ruguje, gaba ɗaya Hafeez ya ruguza ta" Ta furta tana goge hawayen da bai bar zuba ba.
"Kin ga Aziza ya kamata ki nutsu, you are matured bai kamata wannan abin ya riƙa ɗaga hankalinki ba" Kallonta tayi sannan "Fa'iza ke kike faɗar haka? Ko dan cikin ba a jikinki yake ba shiyasa kike ɗaukar matsalata ƙarama"
"A'a amma dai kawai na san shi Hafeez yanzu yana can yana rayuwarsa ya manta dake, amma ke kin kasa fitar dashi"
"Kina tunanin zai fita a rayuwata bayan shi ne ya ɗai-ɗaita min ita?"
"Yanzu dai ba wannan ba, Mommy na kiranki a parlour" Tana gama faɗa kawai ta fita ta bar ɗakin.
Jikinta a sanyaye ta ƙarasa cikin parlourn musamman da taga yadda Mommy ta haɗe rai.
A kan rug ta zauna tare da sauke kanta ƙasa. "Kuka kike ko?" Mommy ta jefa mata tambayar ita kuma bata ko ɗago ta kalleta ba, sai gabanta da taji ya tsananta faɗuwa.
"Idan har baki yarda an cire cikin jikinki ba, to ina mai tabbatar miki da cewa kuka ma yanzu kika fara"
Shiru babu wanda ya yi magana, har ita Fa'iza ɗin.
"Fa'iza je ki kirawo min Hadiza" Mommy ta furta tana kallon Fa'iza. Sai da Fa'iza ta fita sannan ta mayar da kallonta ga Aziza. "Sati ɗaya na baki kiyi tunani akan zubar da cikin jikinki, in kuma ba haka ba, wallahi ni dake ne. Ki tashi ki bani guri" Jikinta sam babu ƙwari haka ta miƙe ta koma ɗakinta ta cibada da kuka daga inda ta tsaya.
**** **** ****
Cikin jindaɗi ta ƙarasa ta kan katifar da take ta kuma rungumeta, dukkansu suka fashe da kuka. Inna dai murmushi kawai take, har sai da suka yi kuka suka gama sannan suka share hawayenki.
"Umma ashe Baba ya rasu, Umma tun lokacin daya turani Kaduna ban sake ganinshi ba, kuma aka ɗaura miki sharrin ke kika kashe shi"
"Kar ki damu Sadiya, shi Allah ba azzalumin tsarki bane, domin kuwa gashi yanzu na fito daga hannunsu cikin hikima ta ubangiji" "Umma kuma na zama gurguwa" Sai kuma ta fashe da kuka.
"Kiyi haƙuri Sadiya, insha Allah zaki samu lafiya" Jin sallamar Habib da Baffa ne ya saka Sadiya tayi shiru, ta kuma ƙurawa ƙofa ido dan ganin shigowarsa.
"Umma tare da Habib kike?"
"Eh shi ne ma ya yi ciku-ciku har aka fito dani" Jin haka ya saka Sadiya goge hawaye, tana ƙara kallon ƙofa amma shiru basu shigo ba.
Habib da Baffa kuwa suna tsakar gida dan akan tabarma suka zauna suna ƙara tattauna batun bikin shi Habib da Sadiya.
"Muna ƙara godiya a gareka da shigowa cikin rayuwarmu a lokacin da muke buƙatar hakan, tabbas kai namiji ne kuma jajirtacce, da ba dan kai ba, da yanzu babu Sadiya" Cewar Baffa, Habib kuwa bai ce komai ba, kan shi na ƙasa ya kasa magana dan Baffa shi ne yake ma kallon suruki"
"Mu yanzu a shirye muke duk ranar daka turo magabata to zamu ɗaura aurenka da ita Sadiya"
"Dama Baffa bana son abin ya ɗauki lokaci saboda ina so ta fara karatu daga zarar sakamakon jarabawa ya fito"
"To ka turo su, sai a tsayar da ranar biki."
"Insha Allah dana koma zan yi magana da mahaifina"
"Babu damuwa, ka shiga ku gaisa da Sadiya ko, bara nayi musu magana" Baffa ya ƙarasa maganar yana miƙewa.
"To ke kullum baki da aiki sai na kuka, Lami ta dawo itama da kukan kika tareta" Baffa ya faɗa lokacin daya shiga ɗakin. "Ai bata gajiya, shiyasa nske ƙyaleta tayi ta gama"
"Yanzu dai ku ɗan bada guri yaron nan zai shigo su gaisa. Ke kuma sai ki goge hawayen ko?" Ya faɗa tare da juyawa a lokacin Umma da Inna ma suka fita.
Har ƙasa Habib ya duƙa ya gaida Inna. "Muna godiya sosai a bisa ƙoƙari da kake yi a kanmu, Allah ya biyaka da 'ya'ya nagari wanda kaima zasu maka fin haka" Inna ta furta yayinda shi kuma ya kasa magana.
"Habib ka shiga ku gaisa da ita"
"To" Ya furta sannan ya wuce ɗakin da Sadiya take.
"Sarkin kuka" ya furta bayan ya yi sallama ya zauna.
"Sadiya wai yaushe za ki daina wannan kukan"
"Sai ranar dana miƙe nake tafiya da ƙafafuna"
Murmushi ya yi tare da faɗin "To ai kuwa ki shirya dan kin kusa fara biyana kuɗin wannan hawayen nawa da kike ɓatawa"
"'Yar harara ta aika masa tare da cewa "Na san ai wasa kake"
"Oh haka kika ɗauka? To da gaske nake"
Murmushi tayi tare da faɗin "Ya gida, ya kuma aiki"
"Lafiya lau, aiki muna ta fama, kin ƙi zuwa ki tayani"
"Zan tayaka, ai kaima ka san da ace..." "Ya isa ni bance ki ƙarasa ba"
"Oh har ma ka san mene zan faɗa"
"Eh mana ai na san dai mitarki ɗaya ce"
"To naji na kuma yarda kuma zan daina insha Allah"
"Dole ki daina tunda kinji batun biya" 'Yar dariya tayi wadda har ta bayyana haƙoranta masu kyau.
"To ina jinki faɗa min"
"Me zan faɗa maka?"
"Abinda kika ce sai nazo nan za ki faɗa"
Idanunta ta ɗan juya sannan ta ce "Ni ban tuna ba"
"Ai kam sai kin tuna"
"Ka san mene? Dama ina tunanin idan mun yi aure yadda danginka za su karɓeni, kana ganin za su soni?" Ta jefa tambayar wadda har ta tsayar masa da murmishi.
"Meyasa kika min wannan tambayar?"
"Saboda ina da nakasa a jikina, na san wasu zasu iya ganin kamar in ka aureni ka cutu"
"Nakasa ba kasawa bace, kuma ki saka a ranki dangina za su soki fiye ma da yadda ni make sonki"
"Ina fatan haka"
"Insha Allah"
Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin ya ce "Ya kika yi shiru?"
"Ina tsoro ne"
"Tsoro" Ya maimaita kalmar. "Eh tsoro nake kar a rabamu, saboda ko Kano ka tafi jina nake wani iri, bare ace an rabamu na har abada, na...na..na kamu da sonka Yaya Habib bana son na rabu da kai, ko wane bugun zuciyata sunanka ne yake fidda wa, a yanzu ina ji a jikina cewa ina numfashi ne dominka"
"Ki daina tunanin za a rabamu, ni dake muna tare har abada, ina mai tabbatar miki da mutuwa ce kaɗai zata raba tsakaninmu" "Ina fatan haka" Ta furta a sanyaye sannan ta sauke ƙwayar idanunta ƙasa.
"Bana so ki shiga damuwa akan wannan abin"
"Ina jin faɗuwar gaba ne, sosai kuma"
"Babu abinda zai faru da iznin Allah, kawai kina jun faɗuwar gabane saboda aure, kuma ko wace mace tana jin haka idan bikinta ya ƙarato sai dai hakan ba yana nufin wani mummunan abu zai faru ba"
Kallon shi kawai take bata ce komai ba, amma ita kawai dai yau ɗin ta riski kanta a fargaba."Sai kuma magana akan wannan zoben" Ya faɗa yana nuna zoben da hannunsa, wanda hakan ba ƙaramin tashin hankali ya watsata ciki ba.
"Ki cire ki adana a wani gurin gaskiya ina kishi, bana som ganinki sa ita" Ya jaɗe rai sosai. Ita kuma ta zare zoben ta ajhe a gefe.
"Na ajje"
Bai ce komai ba. "Na ajje ba, to kayi murmushi mana"
"Bana son ki ƙata sakata ne" Kai ta gyaɗa shi kuma ya yi murmushi.
Sun ɗsn taɓa hira kafin ya tafi kuma da alƙawarin a satin zai turo manyansa.
*Abuja*
Sam bata da ƙwari ko kaɗan a lokacin da ta dira garin Abuja, gabaɗaya ji take kamar dukkan wanda ke ciki maƙiyanta ne. Kai tsaye Wuse ta nufa kuma bata dire a ko ina ba sai a ƙofar gidan su Hafeez, inda ta danna horn tana jira a buɗe mata.
Sai da gateman ɗin ya tabbatar da wanda yazo sannan ya wangale makeken gate ɗin ita kuma ta kunna kan motarta ciki, tana ƙara tsara yadda zata yi rashin mutunci a gidan. "Lah Aunty Aziza kece a gidan barka da zuwa" Ƙanwar Hafeez ɗin ce tayi magana, kamar ma irin tana ƙaunarta yadda take nuna jindaɗin ganinta, takaici ya saka Aziza ƙin mayar mata da amsa dan ji take kamar ta kifeta da mari dan takaici.
Kayan ciye-ciye aka ajje mata haɗi da drinks, da ido take bin kayan kafin ta taɓe baki, a bayanta taji sautin muryar Hafeez "Aziza muna shirin zuwa sai kuma gaki kinzo" Juyawa tayi ta kalleta sai kuma ta sauke gwiwoyinta ƙasa ta gaida ta.
"Ya kike ya aiki yasu Mamanku" "Komai lafiya" Aziza ta mayarda amsa a taƙaice kafin ta koma kan kujera ta zauna a lokacin taji Momman Hafeez na faɗin "Tun kafin bikin Hafeez naso muje sai Allah baiyi ba, amma tunda an gama biki lafiya insha Allah zamu ce, saboda an kwana biyu ba a gaisa ba"
Aziza ta tsinci kanta a yanayi wanda ba zata iya duban idanun mahaifiyar Hafeez ta faɗa mata maganganu ba, domin gani take hakan zai zama rashin tarbiyya da kuma rashin girmama na gaba.
"Kin ganshi ma ɗan halak ya shigo" Jin haka ya saka Aziza ɗaga ido ta kai dubanta gareshi. Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya. Ya ƙara kyau, sai sheƙi yake, ya yi wani ɗan jiki, kana ganin Hafeez ka san cikin nutsuwa yake da kuma kwanciyar hankali yayinda ita ya barta da tashin hankali da kuma neman mafita. Tana wannan tunanin bata san har ya zauna ba, sai ji tayi yana gaida Momma. Ɗagowa tayi tana dubansa, bata iya magana ba har sai da Momma ta ce "To bara na ɗan shiga ciki, Aziza na san yanzu 'yan uwan naki zasu shigo tunda sun ji zuwanki" Murmushi kawai tayi wanda iyakarsa leɓe.
"Mene ya kawo ki gidanmu?" Taji Hafeez ya wurgo mata wannan tambayar lokacin da Momma ta bar gurin. "Dole zaka tambaya ai tunda ka san abinda ka aikata a gareni"
"Ni fa sam ban miki rashin daidai ba Aziza, domin ina tsoron yadda mutane suke mutuwa akanku"
"Mutuwa a kanmu? Hafeez bakinka ne ke faɗar haka?"
"Kin ga Aziza don't take it gor granded, ni ba wani abu nake nufi ba, amma kawai ina da future a gaba shiyasa na haƙura dake, kin san duk yadda nake sonki ko kuma shi Muhasin ba kamar yadda nake son rayuwata ba"
Wasu hawaye masu zafi taji sun sauka kan kuncinta. "Lallai Hafeez na yarda ɗan adam butulu, yanzu Hafeez har kake faɗar haka, ka manta irin samarin da nayi a baya ka riƙa korar min su, baka son ko wane namiji ya raɓeni, ka ɓata min lokaci almost 7 years muna tare, ina zama jiranka Hafeez ina ta dakun soyayyarka, amma yau ni ka juyawa baya tare da wata hujjarka marar inganci"
"Aziza mata takwas suka mutu a dalilin Muhasin anan Abuja, a Kaduna biyu, to taya zan iya auren ahalin da suke da wani ɓoyayyen al'smari irin wannan, aurenki haɗari kuma barazanace ga nawa ahalin, domin zai iya shafarsu"
"Amma kuma shi ne a hakan ka iya sex dani? Ba zaka iya aurena ba amma kuma zaka iya lalata rayuwata? Ashe dama yaudarata kake?"
"Ni ban yaudareki ba, 'yan uwana da kuma iyayena sun zauna sun kuma yi duba cikin lamarin ganin kamar aurenki ka iya zama haɗari ya saka aka ce na nemi wata"
Miƙewa tsaye tayi ta saka yatsa ta goge hawaye tare da dafa cikinta "Akwai ajiyarka anan, ita ɗin ai jininka ce dan haka dole zaka riƙa, dan haka ina mai maka albishir cikin jikina ya kai wata biyar, ka faɗawa matarka nan da watanni huɗu masu zuwa zata fara reno, dan ba zan riƙe maka ɗa ba"
Jin haka ya saka Hafeez miƙewa ya yi saurin shan gabanta dan lokacin har ta fara tafiya.
"Sau ɗaya a rayuwa na san na kusance ki, dan haka ba zaki zo min da rainin wayo ba, sai dai in wani ya yi miki bani ba"
"Ba zan tsaya ina maka jayayya akan abinda bai zo duniya ba, dama ai ku haka kuke, da zarar kun samu abinda kuke nema sai kuma ku fara wuƙaƙanta mace, to ka sani nayi dana sani kuma na koyi darasi akan ɗa namiji, amma ina mai tabbatar maka da zan kawo maka ɗanka, in yaso su magabatan naka da suka hana aurenmu zamu garzaya ayi DNA test shi ai baya ƙarya ko?" Ta ƙarasa maganar tana kallonshi.
"Amma..." Sai kuma ya yi shiru.
Har zata wuce ya ƙara shan gabanta. "Ka bani hanya kafin in kurma ihu, kuma ana taruwa zan sanar masu da batun cikin"
Matsa mata ya yi tare da faɗin "Aziza yau sati biyu kacal da bikina, kenan ta nan kina ɓullo" Tsaki kawai taja tare da ficewa.
shi kuma zama ga yi kan kujera ya dafe kai tare da faɗawa duniyar tunani.
*40 minutes later*
Yana fitiwa daga main part ya hango motar Aziza, gabansa ya faɗi, dan a tunaninsa ta daɗe da tafiya.
Ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ya kwaɗawa kira, ya ƙaraso ada sauri.
"Aziza dama bata tafi ba"
"Eh to naga shigowarta amma da yake ina ta aiki ban ma lura ba, amma ai kamar da waccan motar tazo" Ya ƙarasa yana pointing motar, aikuwa da sauri ya wuce part ɗin sa dan gaba ɗaya tunaninsa ya yi can. Tsoro da fargaba ne ƙarara a fuskarshi.
Yana shiga ya ganta zaune tana shan lemo, Jalila amaryarsa tana daga gefenta. Shigowarshi ya saka dukkaninsu suma ɗaga kai suka kalleshi. Kallon daya ga Jalila nayi masa ya saka shi shiga wani sabon tashin hankali.
"Aziza kin ganshi kuwa ya shigo da fargaba a fuskarshi"
"Ai zai yi fiye da haka ma"
"Ka kyauta Hafeez, kai kana ganin abinda kayi daidai ne?" Jin haka ya saka wata zuffa ta karyo a goshinsa, duk da sanyin AC dake cikin parlour, tunda suka fara soyayya da Jalila bata taɓa kiran sunanshi haka ba, in ba a gaban Momma ko wani babba ba, shikenan ya san yau kam kashinsa ya bushe.
"Kayi wani tsaye, ka zauna mana" Aziza ta faɗa tana kallonsa.
"Ai ba zai zauna ba, tunda ya san abinda ya aikata" Jalila ta faɗa tana ƙara haɗe rai.
"Habibty kiyi haƙuri wallahi sharrin shaiɗan ne, amma ni ban yi haka da nufi ba, kuma..." "Kuma me? Okay wanke kanka kake so kayi bayan a side ɗin Momma kayi min wulaƙanci" Aziza tayi saurin katse shi. Jalila ta ɗora da faɗin "Ai da alama baya son kawo min ke ɗin mu gaisa tunda gashi anan ma kamar bai so hakan ba"
"Ki rabu dashi kawai,shi gani yake dan mun yi soyayya a baya shiyasa, to amma mene a ciki tuɓda nima dai nayi aurena ko, shima ya yi aurensa to kuma za a fasa zumunci ne? Ai dama ba soyayya bace ta haɗa zumuncinmu, amma shi ne ko I.V ban gani ba, kuma yanzu nazo ana min riwar ganinki, daɗin abun nima fa ina da ƙafafu" Ta furta tana dariya.
_Kenan ta ɓoyewa Jalila komai._ Ya furta a ransa.
"Ka zauna mana" Cewar Jalila.
"Kin ga wannan mijin naki fa, ba sakewa zai yi ba in ban tafi ba, gara in lallaɓa"
"Haba dan Allah muna hira kuma zaki tafi"
"Ai gara na tafi, Kaduna ba nan bace"
"To jira ni dan Allah" Ta miƙe da sauri ta nufi ciki.
Kallon banza Aziza ta watsa masa tare da faɗin "Dubeka sai kace na Allah"
"Aziza duk meye haka?"
"Kai kana tunanin cikin sauƙi zan tona asirinka..." Fitowar Jalila ya saka ta datse maganar tare da sake yin murmushin yaƙe" Ta miƙe tsaye lokacin kuma Jalila ta miƙa mata leda.
Har mota ta rakata sannan ta dawo.
"Tana da kirki sosai wallahi" Jalila ta faɗa tana zama kujerar da Hafeez yake tare da ɗora kanta a kafaɗarsa.
"Zaki ce haka mana, tunda ta saka kin kirani da Hafeez"
"Au dan ka tsure ne kayi tunanin fushi nake da kai"
"Wato kin tsurar da mijinki ba"
Murmushi kawai tayi.
****** ****** *******
"Sannu da zuwa Malam maraba" Umma ta faɗa tana shimfiɗa masa tabarma a madaidaicin tsakar gidan.
Yana zama Inna ta fito daga kewaye tana faɗin "Yau Malam Yakubu ne a gidan namu"
"Ni ne ina wuni"
"Lafiya lau, ya kuma muka ji da ƙarin haƙuri, ashe Safiyya lokaci ya yi"
"Wallahi kuwa"
"To Allah ya bada haƙurin rashi, muma muna nan cikin tashin hankali shiyasa bamu samu mun nutsu ba"
"Hakane, ai da yake kusan lokaci ɗaya suka rasu da Malam"
"Wallahi kuwa"
"To Allah ya gafarta musu"
"Amin ya rahamanu" Ɗakin Sadiya ta wuce, tana shiga ta tarar da ita tana cin abinci.
"Ke sai abinci ya gama yin sanyi kike ci ko?"
"Wai ni kam Inna meyasa gabaɗaya kin saka min ido, ko dan kin ga bani tafiya, to yasin da sauran bakina"
"Iyeee! Eh lallai kin warke, dole ki ɗora daga inda kika tsaya"
Dariya tayi tare da faɗin "Inna kisha kuruminki nan da sati biyu na bar miki gidanki, kin ga sai kici karanki ba babbaka"
"Ke kika sani dai 'yar bani na iya kawai" Ta faɗa tana zama.
"A'a ya haka kuma, ni gaskiya karki takura min, waya fa zan yi da Yaya Habib kin kuma zauna"
"To rasa kunya ɓeran tanka, ai gara kiyi wayar ina ji, nima na tsinci abinda zan faɗawa Malam"
"Taɓ! Ba irin naku bane, haba kun tsufa ai"
"Gafara can waya faɗa miki soyayya tana ɓuya"
"Amma dai ba zaki iya yiwa Malam kalaman da zan yiwa Habib ba"
"Naki wasa ne yarinya"
"To na fasa wayar sai kin tafi"
"Ina nan kuwa sai dai karkiyi"
Dariya kawai suka yi, sai kuma duk sukayi shiru lokacin da suka ji Malam Yakubu na faɗin "Nazo ne kan batun auren Sadiya"
Umma kallon shi take kafin ta ce "Eh da yake baiko da saka ranar duk tare aka yi shiyasa ma baku ji da wuri ba"
"Eh ance jiya shi Baffa ya kawo kati har gida lokacin ni kuma ina gona"
Shiru Umma tayi, shi kuma ya cigaba da cewa "Akwai wani al'amari daya faru gab da rasuwar mahaifinta"
"Me kenan?" Umma ta furta tana kallonsa.
Bai ɓoye mata komai ba akan yanda ya ƙulla auren Muhasin da Sadiya ba tare da ko shi mahaifin Sadiya ya san cewa in aka yi auren ga abinda zai faru. Cikin tashin hankali Umma ta ce "Kenan so kayi ka kashe min yarinya?"
"Na san na aikata kuskure, kuma bana son aikata wani kuskuren shiyasa nazo, domin ko Sadiya za tayi aure dole sai an warware wancan auren."
"Mugu azzalumi, daga kai har mahaifiyar shi yaron ba zan taɓa yafe muku ba, kuma kai ne ka kashe 'yarka da kuma mijina, Allah ya isa ban yafe maka ba..."
Ƙaran Sadiya suka ji daga ɗakin, gaba ɗaya suka miƙe suka nufi can.
SaNaz Ce🌸🤘