Page 19
by @sanazty
*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
Page 19
__________🖌️"Na shiga uku, Umma gara kawai na mutu na huta, mene ke faruwa dani, meyasa rayuwata ta zama haka?"
Ita kanta Umma ta kasa magana sai hawaye kawai.
"Malam ai ka san gidan nasu ko?"
"Farin sani ma kuwa, ni kaina nayi niyyar kaisu kotu, amma kuma naƙi zuwa ɓe sanin cewa ni za a bawa rashin gaskiya ganin cewa suna arziqi"
"Ba zamu yi ƙasa a gwiwa ba insha Allahu gobe zamu Kaduna dani da kai, a nemawa yarinyar nan saki, saboda asibiti suka turo mana ita babu wani cikakken bayani, yaron nan Habibullah shi ne ya taimakemu, ya bata ƙoda hatta keken da take hawa shi ne ya saya mata, kuma koma ba haka ba, ba zamu lamunci wannan ba"
"Shikenan Allah ya kaimu goben" "Amin ya Allah"
A cikin gidan ya samu Umma da Sadiya suna ta kuka, Inna har ta gaji da rarrashi. Faɗa sosai Baffa ya yiwa Umma saboda ganin ita ce ya kamata ta rarrashi Sadiya amma kuma ta zauna suna kuka tare.
"Ke Sadiya kiyi shiru kin san mu ba zamu bari ki zauna da wanda baki so ba ko?"
Kai ta gyaɗa hawaye kwance a fuskarta. "To ki kwantar da hankalinki, gobe zamu je can Kaduna" Sallamar Ladi ce ta saka babu wanda ya sake magana sai amsa sallamar da Baffa ya yi.
"Wai mene ke faruwa ne, naji wani labari mara daɗi"
"Ladi matsaloli sun yi mana yawa, na rasa meye mafita, muna ganin Sadiya ta samu miji mai ƙaunarta wanda zata samu ta huta, duk da ya san abubuwan da suka faru da ita amma hakan bai hana shi daina son ta ba, sai kuma gashi an ɓullo da wannan lamari" Umma ta faɗa tana matsar hawaye.
Ita kuma Ladi ta ƙarasa kan katifar da Sadiya take tare da rungumota "Ki kwantar da hsnkalinki Sadiya, komai zai wuce da yardar Allah"
"Ai gobe zamuje can Kaduna gidan nasu, azzalumai kawai." Baffa ya faɗa rai a ɓace.
Shiru ya biyo baya, kafin Ladi ta ce "To shi Habib ɗin an sanar masa? Dan munyi waya shekaran jiya ya ce za a kawo lefe zuwa gobe ko jibi, dan akwai kayan da ba a gama ɗinkawa ba, ya ce yana so rabin kayan ya kasance a ɗinke saboda wanda zatayi fitar biki"
Jin haka ya saka Sadiya sake fashewa da kuka.
"Ban kira shi ba, amma zan kira na sanar dashi yanzu kuwa. Babu ya faɗa yana ɗauko wayarsa daga aljihu. Sadiya kuwa idanu ta ƙura masa gabanta na tsananta faɗuwa. Sau biyu yana kira tana katsewa ba a ɗaga ba. "Wataƙila baya kusa da wayar amma na san da zarar ya gani zai kira" Cewar Inna.
Ta ɓangaren Habib kuwa yana zaune a parlour kansa a ƙasa. Yayyan Mama guda biyu kuwa sun sako shi gaba sai faɗa suke.
"Haba Habib da hankalinka, duk yawan matan dake danginmu amma ka rasa wa zaka aura sai gurguwa, shikenan kai kaga baka da kwanciyar hankali, neman magani da kuma hidima sai sun gama zuƙeka tas"
"Aunty ba fa komai ne bata iyawa ba, tafiya ne kawai bata yi, saboda idan tana zaune ma ba zaki ce tana da ciwon ba, ƙafufunta suna motsawa"
"Dalla rufe min baki, ai wallahi ka bani mamaki, kuma ina nan akan bakana wallahi ba zan taɓa ƙaunarta ba, tunda dai mahaifinka ya goyi bayanka ka nuna ni ban isa da kai ba, gaka ga gurguwa Allah ya baku sa'a" Mama ta ƙarasa magana cikin ɓacin rai.
"Kar kuma ki masa baki, abi abun a hankali"
"Wane a hankali, biki ya ƙarato, ai koma me ta faɗa a kansa shi ne ya jawo, shikenan za ayi ta faɗa mijin gurguwa"
"Uhm! Ai gashi nan sai yaje ya yi aure, amma na faɗa masa bana so yarinyar nan ta tako gidana, dan haka kar ka sake ka kawo min ita"
Shiru ya yi bai ce komai ba. "Ka ga Habib, tashi kaje inda zaka je" Tashi ya yi ya fita, ita kuma ta kallesu "Har motarsa fa ya sayar saboda auren nan, tun kafin ma ta shigo har ta fara tsiyatashi"
"Kamarya ya sayar da mota"
"Wallahi ya sayar ya ƙarasa gini, ai ban taɓa ganin mutum irin Habib ba"
"Lallai Habib ya yi wauta"
"Shi ya sani, gashi yanzu yana ta fama da Lifan"
Yana ƙoƙarin hawa machine ɗin sa ya ga shigowar motar Najwa, ranshi ya ƙara sosuwa domin ita take ƙara zuga Mama akan batun Sadiya.
A jikin Lifan ɗin ya tsaya yana jiran fitowarta.
Tana murmushi ta ƙaraso inda yake "Ana ta fushi dani, ni dai ba zan yi fushi da kai ba"
"Ni ba fushi nake dake ba, amma bana son ki riƙa aibata abinda nake so muddin kina son zaman lafiyata"
"Kayi haƙuri kishi ne" Ta furta tana yatsina fuska.
"Wannan ba kishi bane, ke kin san babu aure tsakaninmu"
"Waye ya haramta auren?"
"Anyi miki miji, sannan kuma ko da ba a yi miki miji ba ba zan aureki ba, saboda ba zan auri wadda iyayenta basu ganin darajar iyayena ba" Yana gama faɗa ya haye machine ya tafi, da ido kawai ta bi shi.
****** ****** ******
Tana cire hijab ta janyo waya ta sake kiran Habib, sai dai har lokacin bata shiga ba. Ajiyar zuciya ta sauke tare da ajje wayar.
Ladi ce ta shigo ɗakin ɗauke da abinci, sannan ta ajje flask ɗin dake hannunta, sannan ta zauna a gefenta.
"Naga kamar ma fitilar bata da haske"
"Eh battery kamar ya yi sanyi, Baffa ya ce zai shigo da wani idan ya dawo daga masallaci."
"To bari na kunna ta wayata, sai kici abinci"
"Yakumbo Ladi na ƙoshi"
"Me kika ci da har ya ƙosar dake, bana son musu"
Shiru tayi bata ce komai ba.
"Hala har yanzu baki samu Habib ba"
"Ina ta kiran wayrshi baya ɗagawa ban san meyasa ba"
"Wataƙila baya kusa da wayar"
"Tunda yamma fa"
"Ki kwantar da hankalinki, insha Allah a wannan karon ba zaki faɗi ba" Hannu ta saka ta goge ƙwallar, ita kuma Ladi ta cigaba da tausarta. Har sai data tabbatr taci abinci sannan ta kwantar da ita ta fita.
"Wai har yanzu baki zauna ba kina nan tsaye?" Ladi tayi maganar lokacin data ƙarasa gaban Lami.
"Ladi na kasa sukuni, hankalina a mtuƙar tashe yake, wato so sukayi su kashe min Sadiya, me tayi musu?"
"Shi ne abin tambayar"
"Ladi har da laifin Malam fa, taya rana tsaka kawai a zo maka da batun aure baka san mutum ba ka ɗauki 'ya ka bashi sai kace bebin roba"
"Ni fa a tunanina aljanun nan sune suka kashe Malam kuma suka nakasa Sadiya"
"Ai ki daina wani tunani haka ma abin yake, dan haka gobe zamuje har da ita Sadiya kuma wallahi sai nayi masu Allah ya isa bayan sun bata takardarta, irin wahalar da yarinyar nan tasha a asibiti da irin wadda take sha a yanzu, rashin ƙafa fa Ladi, a ƙuriluciyarta, ke in ba dan Allah ya dubi maraicinta ba kina tunanin a yanda take da nakasar nan ga kuma talaucin da muke ciki zata samu miji kamar Habib? Ai bama zata samu mijin ba in ta samu kuwa sai dai nakasasshe"
"Hakane, ni kaina da ba dan Baffa ya hana ba, wallahi sai na ciwa Malam Yakubu mutunci, tsohon banza mara imani"
"Ai gashi alhaki ya faɗa kansu, da ace bai ga wannan sakayyar ba, da ba zai taɓa faɗar dalili ba, sai dai Sadiya ta mace ace ai lokacinta ne ya yi, to ni ban zauna haka ba, ina yiwa 'ya'yana addu'a kuma na tabbatar ko fyaɗen da aka mata a farko wanda shi ne dalilin lalacewar komai ƙaddara ce."
***** ***** ******
"A baya nayi tunanin na tono asirinsa a cikin mutane" Aziza ta faɗa gami da miƙewa tsaye, ita kuma Fa'iza tana zaune kan side drawer tana kallonta.
"Fa'iza wani tunani yazo min, na fasa tona masa asiri, a haka zan wajiga rayuwarsa kullum ya riƙa tunanin waye zan faɗawa, amma kuma a zahirin gaskiya ni ba zan tona masa asiri ba, sai dai na ɗauki alwashin ranar dana haihu a ranar zan kai masa 'yarsa, ruwansa ne ya tonawa kanshi asiri ko kuma ya san yanda zai yi da ita"
"To duk mene amfanin haka Aziza?"
"Ba zan yi laifi biyu ba, ga laifin zina ga kuma na kisan kai"
Ajiyar zuciya Fa'iza ta sauke, tare da faɗin "Amma fa kina jin abinda Mommy ta faɗa"
"Fa'iza ba zan zubar ba gara ta koreni" Ta furta tare da fashe da kuka.
"Ya Salam" Fa'iza ta furta gami da tashi ta riƙo Azizan.
****** ******* ******
"Kira daga Sadiya haka, lafiya" Ya furta tare da zama gefen gadon. Bayan kiran Sadiya yaga na Baffa sannan ya ga na Mama da Najwa, sai kuma wasu wanda suka bashi aikin waƙa, sai dai kiran Dadiya ya fara bi.
Har bacci ya fara ɗaukarta, saboda lokaci goma na dare ta gota, jin wayarta na ringing ya saka ta buɗe ido a hankali, tare da janyo wayar dake ƙasan pillow. Ganin sunan _Yayana_ na yawo akan screen ya saka ta miƙe zaune, tare da ɗagawa.
Bai yi magana ba, har sai da ta ce "Hello!"
"Wayar bata tare dani ne, a gida na barta" Jin amsar daya bata ya saka gabanta ya faɗi, tayi tunanin sun yi waya da Baffa ya faɗa masa tana da aure.
"Ina jinki Sadiya"
"Naji ka a wani yanayi, ko akwai abinda ya faru?"
"Babu. Fatan kina lafiya"
"Lafiya lau" Ta furta murya na rawa. "Haka nake son ji, sai da safe, yanzu bacci nake ji" Bai jira abinda zata faɗa ba kawai ya kashe.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya katse kiran. "Kiyi haƙuri Sadiya, raina a ɓace yake, ba zan iya sakewa muyi waya ba, na san zaki ji babu daɗi amma zan kiraki ko in ajje miki saƙo komin dare" Jin saƙo ya shigo wayarsa ya saka ya ɗauka tare da dubawa.
_Idan aka ce maka na mutu a daren yau kar kayi mamakin haka, saboda na kamu da son ka shiyasa ba zaka karɓi ƙaddarar da tazo min ba,da ka san yadda nake ji akan wannan maganar da baka amsa wayata a haka ba, kai nake ta kira ko zan samu sauƙi azabar da zuciyata keyi, sai dai kuma kiranka ya ƙara hura wutar dake ci a cikin zuciyata._ Sam bai fahimci saƙon nata ba, dan haka ya sake kiran wayarta, sai dai yaji wayar a kashe. Bai gamsu ba sai daya kira sau uku yaji a kashe, anan y tabbatar da ta kashe wayar, dan haka ya kira Baffa dan dama ya ga missed calls ɗinsa, amma gani sha ɗaya ta kusa ya saka bai kira ba.
Bayan sun gaisa ya duba jikin Sadiya ya ce masa da sauƙi. Shiru ya ɗan biyo baya kafin ya ce "Dama naga kiranka ne, na fita wayar a gida na barta"
"Ayya dama dana ga ba a ɗaga ba nayi tunanin haka" Ya ɗan yi shiru sannan ya cigaba da faɗin "Wani al'amarine kuma ya ƙara kunno kai, to sai naga ya dace a sanar maka"
"To Baffa ina jinka"
"Batun aurenka da Sadiya" Labarin zuwan Malam Yakubu ya bashi tare da abinda ya faɗa masu.
Abin ya matuƙar girgiza Habib dan haka yana zaune sai daya tashi tsaye.
"Gobe idan Allah ya kaimu gaba ɗaya zamuje Kaduna dan jin gaskiyar maganar, shiyasa nace kafin nan a ɗan jinkirta kawo lefen tunda ga kuma al'amarin daya shigo, shi ne ma nace ita ta kiraka sai dai itama bata sameka ba"
"Na kirata mun fara magana sai kuma naji shiru, na kira kuma naji a kashe."
"To wataƙila ko cajin wayarta ya ƙare, ko a kai mata" Ji ya yi kamar ya ce eh, amma kuma ya kasa. "A'a Baffa, goben dai ina so mu tafi gaba ɗaya har ni"
"Ba damuwa, kazo goben sai mu tafi gabaɗaya, mun yo shatar mota"
"A'a Baffa zan zo da mota"
"Habibu bana son kayi ta ɗawainiya haka"
"Karka damu Baffa"
Haka dai suka kashe wayar yana jin wani irin jiri na kwasar shi.
Zama ya yi tare da ƙara kiran Sadiya, sai dai still wayarta a kashe. Ranr sam bai runtsa ba, dama ga damuwar Mama, haka ya ga dare ya yi masa mugun tsayi.
Ta ɓangaren Sadiya ma kukan kawai take, sai dai ba a fili ba, sam batayi bacci ba, ta riƙa ganin dare ya mata tsayi,babban burinta bai wuce ta ganta a Kaduna ba gidan mutanen da suka ci mata mutunci a haɗuwarsu ta farko, har hangowa take mijin da aka aura mata wanda ko sunanshi bata sani ba ya bata takardarta mai ɗauke da saki uku..!
SaNaz Ce🌸🤘