...BASHI!

Page 20

by @sanazty

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

                   Page 20

__________🖌️Ta zaune akan tabarma ta ɗaura kanta a bisa gado, hawaye ne kawai ke kai kawo daga idanunta zuwa kuncinta.
Sallamar Umma ce ta saka tayi saurin saka hannu tana goge hawayen.

"Sadiya so kike ki kashe kanki?" Ta faɗa gami da zama, tare da ajje kofi da kuma plate ɗin da ke ɗauke da waina.

"Ga idanunki yanda sukayi jajir fa, kiyi haƙuri ki kuma rungumi ƙaddararki, Allah shi ne mafi sanin dai-dai, kuma ya riga ya gama tsara rayuwarki."

Bata ce komai ba, illah hannu da ta saka tana sharar hawayen. "Ga abinci nan kici, Baffa ya ce yanzu ba daɗewa zamu tafi, to bana so ki fita baki ci komai ba." Sai da Umma ta tsareta sannan ta ci abincin dan ji take gaba ɗaya komai na mata ɗaci a baki.

             **** **** ****

07:00am

Karɓar key ɗin ya yi, tare da kallon abokin nasa "Amma kuma Farouq sai nake ganin kamar wannan tayi girma, da ka bani waccan accord ɗin" Dafashi ya yi sannan ya ce "Haba Habib kafi ƙarfin haka a gurina, wannan Range Rover ɗin da ita zaka je, ai gidan su budurwarka zaka je, so dole a kankaro mutunci"
"To ai ni nafi so ta soni a yadda nake"
"Nima ba ina nufin kayi mata ƙarya ba, amma dai nafi so kaje da mutuncinka, shiyasa na ɗauki wannan motar na baka domin ni ɗinm a kayi min halacci sosai a rayuwata"

"Gidiya nake Farouq" 
"Baka da damuwa Allah ya kiyaye hanya"
"Amin mutumin"

Ƙarfe takwas na safe ya isa Gaya, kuma kai tsaye a ƙofar gidan Baffa ya parke motar sannan ya fita, gami da tura yaro ya yi masa sallama. Kusan tare da yaron suka fito. "A'a Habib har ka iso" 
"Eh Baffa" Har ƙasa ya durƙusa ya gaidashi.

"Bara kawai nace su fito dama duk mun gama shiryawa, sai mu biya mu ɗauko Malam Yakubu"

Bai iya cewa komai ba.

Yana tsaye jikin mota suka fito, Umma ce ta turo Sadiya daga kujerar, Baffa da Inna na biye. Habib ya ɗago yana kallonta sai dai ita sam taƙi yarda ma su haɗa ido, saboda idanunta gaba ɗaya sun canza, ga wani mugun ciwon kai da takeji.

 Umma ce ta ɗaga Sadiya ta saka a mota sannan Habib ya ɗauki keken ya kai boot. Yana dawowa ya gaida Inna da Umma sannan ya shiga motar Baffa na gefe. Inna tayi masu fatan sauka lafiya saboda ba da ita za aje ba.

Ko da suka je gidan Malam Yakubu, ita Sadiya hankalinta na gidansu, tana tuna irin rayuwar da tayi a ciki amma yanzu sai dai kallo.

"Ki shiga ku gaisa dasu sannan kiyi musu gausuwa"
"Baffa mutanen da suka nakasa min 'ya? Kuma in gaisuwa ce nima ai basu zo min ta Malam ba"
"Lami bana son musu kiyi abinda nace." Ya faɗa sannan shima ya fita.

Umma dai ranta bai so ba itama ta ɓalle murfin motar ta fita. Aka bar Sadiya da Habib a ciki.
"Wane laifi nayi miki kike azabtar dani haka" Jin kalamansa ya saka ta dawo da dubanta gareshi, ji tayi gabanta ya faɗi.
"Yayana baka yi bacci ba?"
"Ki faɗa min laifin da nayi miki Sadiya"
"Ni baka yi min laifin komai ba, ta faɗa idanunta cike da ƙwalla"
"To meyasa kika kashe waya dan kar na kiraki, tunda kin san dole zan nemiki, ni sam ban ma san mene ke faruwa ba har sai da mukayi waya da Baffa, taya kike tunanin zan yi bacci bayan ke kina cikin damuwa, har kina wani irin furuci, taya kije tunanin zan iya runtsawa Sadiya? To ki sani yadda naga rana haka naga dare"
"Kayi haƙuri ni ban faɗi haka dan ranka ya sosu ba"
"To dan me kika faɗa?"
"Dan ganin kamar zan rasaka, ni kuma ba zan iya jurar hakan ba"
"Ko babu aure ni Yayanki ne, bare kuma ni na san insha Allahu babu abinda zai hana aurenmu"
har zata ƙara magana taga fitowar Umma daga gidan, dan haka ta kwantar da kai jikin kujera tare da lumshe ido.

Malam Yakubu shi ne ya shiga gaba, Baffa da Umma kuma suka saka Sadiya a tsakiya, bacci ƙarya tayi dan kar ma ta gaidashi, saboda haushinsa take ji.

          ***** ****** ******

"Gashi" Fa'iza ta miƙawa Aziza bowl tare da zama.
"Nagode Sisy" Ta furta tana kai yankakkar kankana bakinta. "Wow amma haɗin ya yi daɗi"
"Ai Liquid milk na zuba shiyasa"
"Yayi" 
Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin ta ce "Kun gama WAEC ɗinku amma naji baki magana akan NECO ita yaushe za kuyi?"
"Ni ban zan yi ba, shiyasa naji daɗin Jumping so nake WAEC na fitowa in tafi can Florida inyi degree ɗina"
"Shi ne ba zakiyi NECO" 
"Ita NECO fa amfaninta a Nigreria ne, kuma a Nigeria ɗin ma idan kana da WAEC baka buƙatar NECO ni fa ko ban ci WAEC ba gara na sake next year amma gaskiya ba zan yi degree a ƙasar nan ba, Strike ya yi yawa"
"Kuma kina da tabbacin Daddy zai biya miki"
"Wallahi ko bai biya min ba sai naje"
"How?"
"Hanyoyi da yawa mana, ga Mommy ko kuma scholarship"

Har Aziza zatayi magana suka ji knocking.
Kallon juna sukayi kafin Fa'iza ta miƙe ta nufi ƙofa, ita kuma Aziza ta ɗauki Hijab ta zura saboda cikin jikinta ya fito bata son mutane su ankara.

"Bismillah ku shigo" Ta faɗa tana kallon Malam Yakubu dan shi kaɗai ta gane a cikinsu.

Aziza miƙewa tayi tsaye tana kallonsu. "Barka da zuwa Kawu" Ta furta tana ɗan rissinawa. Kallon tsana yake mata babu wanda ya amsa a cikinsu. Baffa ne kawai ya amsa musu da suka gaidashi.

Dukkansu sun zauna, dama ita Sadiya tana kan kujerar ta. "Fa'iza ki kira masu Mommy..." Sai ganin fitowar Mommy ɗin tayi bata ma ƙarasa maganar ba.

Kan kujera ta ƙarasa ta zauna, idanunta bama akan Malam Yakubu suke ba, suna kan Sadiya tana mamakin ganinta dan a tunaninta ta rasu.
"Bata mutu ba tayi rai,na san shi ne kallon da kike mata" Malam Yakubu ya faɗa ita kuma ta mayar da kallonta gareshi.

"Yanzu ke zakiyi farin ciki ki kashe ɗan wani dan naki ya rayu?" Umma tayi maganar cikin ɓacin rai. Mommy ta ƙara bin ta da ido ba tare da ta ce komai ba.
"Lami kar na sake jin kin yi wata magana, ba rigima ce ta kawo mu nan ba"
Shiru tayi rai a ɓace, shi kuma Baffa ya kalli Mommy ya ce "Dama mun zo akan batun aure da aka ce anyi na Sadiya da shi yaron gurinku, wanda mu bama mu san anyi ba. To sai yanzu yarinyar da ta samu miji har ma an saka biki sai mukaji wannan batu na aure, to kuma sanin kanki ne ba za a taɓa aure kan aure ba, shiyasa muka zo domin a warware wannan auren, saboda itama ta samu ta auri wanda take so"

Daga Fa'iza har Aziza baki suka saki suna kallon Sadiya da take zaune a wheel chair, sai a lokacin ne ma Aziza ta ganeta, lallai itace wadda suka taho da ita daga Gaya Mommy ta sanar dasu 'yar aiki ce"

"Ni bani da abinda zan iya akai saboda Muhasin ma yanzu baya nan kuma bamu san inda yake ba, sai dai idan ya dawo za a aiko muku da takardarku dan shi ma babu abinda zai yi da ita"

Habib ya ji zafin wannan furuci dan da ba a gaban manya bane da babu abinda zai han shi mayar mata da martani, sai dai kuma ba zai iya ba a gaban su Baffa.

"To ai dama mun san cewa kin haɗa auren ne saboda ki kashe Sadiya ɗanki kuma ya rayu, sai dai haƙonki bai cimma ruwa ba, to kamar yadda babu abinda zai yi da ita haka itama babu abinda za tayi dashi" Cikin ɓacin rai Umma ta faɗi haka, ita kuma Mommy ta mayar mata da "Me zai yi da gurguwa talaka fiƙirai irinku"
"A fiƙiran kika aurawa ɗanki, kuma ai gara cutar gurguntaka da cuta irin wadda ɗanki ke da ita" Umma ta mayar da martani a hasale.

"Mommy dan Allah kiyi dan Allah" Cewar Fa'iza, dan ita Aziza ta daskare a zaune, tausayin Sadiya take, tana kuma mamaki hali irin na Mommy.

"Ba zan haƙura ba, ki rabu dani Fa'iza, ba zan lamunci faƙirai kamarsu suzo har gida suna ci min mutunci ba"
"Kada Allah yasa ki haƙuri ki ɗauki duk matakin da zaki iya ɗauka"

Baffa dai ya zuba masu ido, ita kuma Sadiya jawaye kawai take, ta tsani a kirata da gurguwa domin har ranta kalmar tana bugunta.

Sai a lokacin Malam Yakubu ya saka baki "Wai ke Rukayya har yanzu ba zakiyi laushi ba, har yau bakinki ba zai daina aibata talaka ba, karki manta gidan da kika fito daga ciki bai ko taka ƙafar eanda suke ciki ba, su talakawa ne amma basu rasa cin yau da gobe ba, amma ke fa har kika yi aure gidanku wata rana kwana kuke baku ci ba. sai yanzu ne ma da suka ɗan samu tallafi amma kuma naga kina so ki manta asali"
"Kaga Yaya ina ganin mutuncinka, ba ruwanka da rayuwata"
"Dole zaki faɗi haka a yanzu tunda na gama yi miki rana a rayuwa"
"Rana? Tame? Ni ban ga abinda kayi min ba"
"Ai zaki faɗi haka, tunda ko ita yarinyar nan da kike kira gurguwa ai ke kika gurguntata tunda ba haka kika ɗaukota daga gidan ubanta ba, gashi ita ta raunata mahaifinta ya mutu duk a sanadin wancan ɗan naki"

"Dan Allah duk ba wannan ya kawo mu ba, abi komai a sannu, mu so muke kawai mu karɓi takardar Sadiya"
"To da Muhasin yana nan ai da tuni ya danƙara mata sakin, me zai yi da wannan yarinyar"

"Mu tafi dan Allah, Yayana mu tafi" Sai lokacin Sadiya tayi magana cikin hawaye. Ai kuma ta sayar da idanunta cak a inda yake, bama ta ƙara jin me suke faɗa ba saboda macen da ta gani zaune a gefen Habib, fuskarta a wani tsage, ga jini kamar ciwo a kumatunta, idanunta jajir sai kuma gashin taya zubo gaba da baya wani irin curkuɗaɗɗen gashi. 

"Naso na kasheki kamar yadda na kashe sauran" A ɗimuce ayi baya da kujerar ba tare da ta sani ba. Idanunta akan wannan mummunar halittar dake gefen Habib.
"Ƙarfin addu'arki ya saka na kasa sai kawai na ɗauki fansa akan mahaifinki, ke kuma ɓa mayar dake gurguwa da yadda zaki muzanta ki kuma tsani rayuwar. Sai dai tunda na gano kin fara wata soyayyar zaki bar Muhasin shiyasa zan ƙyaleki" Ta miƙe tsaye tana nufo inda Sadiya take, a lokacin ita kuma ta ƙwalla ƙara tare da rufe fuska.

"Lafiyarki Sadiya?" Suka faɗa tare da yowa kanta, sai dai tana buɗe ido ta ganta tsaye gabanta. "Zaki cigaba da tafiya tunda burina zai cika, amma ki sani muddin bai sakeki ba zaki dawo ruwa, so nake in ɗai-ɗaita duk wani wanda ya raɓeshi, sai dai shigowarki rayuwarsa ta saka bana iya aikina a kanshi yadda ya kamata." Hannu takai duka biyun ta shafa ƙafafunta aikuwa a furgice tayi baya, gaba ɗaya ta kife a ƙasa.

Ko da suka je kanta tuni ta suma. 

SaNaz Ce🌸🤘