Page 21
by @sanazty
*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
Page 21
__________🖌️ *Few Minutes Later*
A hankali ta buɗe idanunta, Umma ta fara haɗa ido da ita tana riƙe da hannayenta. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shi ne abinda ta furta a sanyaye, ta fara ƙoƙarin tashi zaune. "Sannu Sadiya" Baffa ya faɗa, a lokacin kuma Umma ta taimaka mata ta tashi zaune. Ɗakin ta kalla sosai, bedroom ne, dan inda take ma kan gado ne, sai dai bata san a ina bane.
Kowa take bi da kallon ɗai-ɗai, Habib yana jingine da wardrobe dake ɗakin ya harɗe hannayensa a ƙirji, koda ta kalleshi shima ita yake kallon, fuskarsa bata ɓoye damuwar da yake ciki ba. "Sannu...!" Jin muryar da bata sani ba ya saka ta kai dubanta ga gefenta. Aziza ce zaune da al-qur'ani da kuma carbi. Bata iya bata amsa ba sai kallon Umma da ta sake yi. "Umma mu tafi, dan Allah mu bar gidan nan" Ta furta tana fashewa da sabon kuka. "Sadiya ai jikinki babu ƙwari, ki bari ki ƙara warwarewa" Aziza ce tayi maganar, ita kuma ta girgiza kai tare da faɗin "Ni dai mu tafi" Haye wanke a fuskarta ta kalli Habib "Yayana dan Allah kace mu tafi, dan Allah tsoro nake ji" Ɗan takowa ya yi ya ƙaraso bakin gadon "Calm down, babu abinda zai sameki, duk muna tare dake"
"Ina ganin gara mu tafi ɗin tunda ta farfaɗo, Lami ki ɗauko kujerar a ɗorata" Sai lokacin Baffa ya yi magana. "Bari na ɗauko" Habib ya faɗa tare da fita da sauri.
"Mommy ki kwantar da hankalinki, dan Allah ki bar damuwa akan wannan matsalolin, ko da ciwo wallahi Yaya yafi ƙarfin waccan mai kama da mayun" Shi ne abinda kunnuwan Habib suka ji Fa'iza na furtawa lokacin daya fita ɗaukar Wheelchair ɗin Sadiya.
Tana ganinsa ta ɗanyi ƙasa da kai. Habib is one of her best musician sai dai kuma gashi a yanzu da ta ganshi free babu damar ta nuna ta sanshi ma saboda a yanayin da yazo gidan a yanzu. Sai dai sam bata ji daɗi ba da ya tarar tana wannan maganar, amma kuma sai ta basar tare da miƙewa "Amm... Me kake buƙata?" Ta furta tana kallonshi, kallonta ya yi sannan kawai ya ɗauki wheelchai ɗin ya wuce.
Baki ta taɓe ta koma kujera ta zauna, tare da saka hannu a kumatu tana tunanin anya wannan yana da kirki kuwa, kallon da yayi mata kaɗai ta gane yana jin haushinta, ko tantama babu ta tabbatar Habib yaji maganar da tayi da Mommy.
Gaba ɗaya suka fito parlourn, Umma na turo Sadiya akan kujerarta.
Mommy kallo ɗaya tayiwa Sadiya sai kuma ta ɗauke kai,ji take tsanar yarinyar ta kamata, lokaci guda kuma ta wurgawa Malam Yakubu kallon banza, domin shi ya bada shawarar a aurawa Muhasin Sadiya, sun yi abinsu cikin sirri amma gashi an fallasa komai. _Da na san zan ɓata goma ɗaya bata gyaru ba, da ban bari an yi wannan auren ba, ai abin kunya ne duniya taga na aurawa Muhasin wannan yarinyar, duk manyan masu kuɗi da muke hulɗa dasu haka. Ni tashin hankalina idan mahifinsa yaji maganar na san ba zamu kwasheta da daɗi ba._ Shi ne abinda ta furta a ranta tana kuma ƙara kallon Sadiya.
"To Hajiya mu zamu koma, muna fatan Allah ya bayyanashi, domin ita kanta yarinya kar tayi ta zama da auren shi a kanta" Mommy bata ce komai ba, sai Aziza ce ta ce "Amin ya rabbi, insha Allah zai bayyana nan ba da jimawa ba"
"To ko ke zan bawa lambar wayata in yaso idan ya dawo sai a taɓoni" Sai lokacin Mommy ta yi saurin cewa "Ba sai kun bayar da number ba, ai mun san gidan Malam Yakubu, dan haka za a aika muku takardarki can" Kallonta Aziza tayi kamar za tayi magana sai kawai ta ɗauke kai, ta kalli Sadiya ta ce "To Sister insha Allah zan kawo miki Yaya har gida Allah ya baki lafiya"
"Amin sauran suka amsa"
Har bakin mota Aziza ta rakasu, sannan ta sake yi masu godiya. Anan kuma ta karɓi number Umma da number Sadiya" Sai da har suka bar gidan sannan ta juya ta shiga.
"Bani wayarki" Kawai taji Mommy tayi maganar lokacin tana ƙoƙarin shiga side ɗinta. Kallon Mommy tayi, bata yi magana ba ba kuma ta miƙa wayar ba. Mommy ta miƙe a fusace ta fuzgi wayar Aziza kawai sai gani sukayi ta buga wayar akan tiles. "Mommy...!" Ta faɗa tana zaro ido, da kuma mamaki ɗauke a fuskarta. Fa'iza miƙewa tayi tsaye tana kallon Mommy tare da faɗin "Amma Mo..." "Ki rufamin baki Fa'iza, wannan yarinyar gaba ɗaya ta fitar min a rai, tayi cikin shege kuma yanzu tana bin maƙiyana har da karɓar number"
Aziza da Fa'iza gaba ɗaya babu wanda ya motsa daga inda yake, dukkansu suna mamakin abinda Mommy take, gaba ɗaya sims ɗinta sai data karya su ta watsar sannan ta miƙe tana kallon Aziza cikin ɓacin rai. "Mintuna goma na baki kije ki shirya muje a cire wannan tsinannan cikin" Rai a ɓace Aziza ta wuce, tana shiga ɗaki ta faɗa gado tare da fashewa da kuka.
Mommy na juyawa taga Fa'iza ta kafeta da ido "Ke kuma mene kika kafeni da ido kamar zaki cinyeni" Kai Fa'iza ta sauke ƙasa, ita kuma Mommy ta ƙarasa inda take tare da kamo kunnenta. Sai da ta cije lips ɗinta, dan yanda Mommy ta murɗe kunnen taji zafi. "Wallahi saura inji kin faɗawa mahaifinku cewar nayiwa Muhasin aure b tare da sanin kowa ba sai ranki ya yi mugun ɓaci" Tana sakinta ta ɗago ta kalleta "Mommy kiyi haƙuri, amma a yanzu zan faɗa miki gaskiya domin akwai haƙƙi tsakanin ɗa sa uwa, Mommy kenan kin so Sadiya ta rasu? Haba Mommy mu kanmu da muke cikin wannan bala'in jin mu muke a fargaba amma ita laifin me tayi miki, idan ta mutu Yaya ya samu lafiya shi ranta da kika salwanta fa?" "Ni kike faɗawa haka Fa'iza?" "Mommy gaskiya na faɗa, domin ni na fara zargin wannan kisan ma fansa ce, gashi kin ƙi faɗa mana komai game da labarinki da kuma asalinki, kina ta ɓoye mana abinda ya kamata ace mun sani tuntuni" Tana gama ta wuce kawai ta bar Mommy a tsaye.
Zama tayi kan kujera tare da dafe kai. _Ko dai alhakin Saifullahi ne ke bibiyarmu? To idan alhakinsa ne ai bai kamata ace ya shafi 'ya'yana ba. To waye ke yi mana bita da ƙulli? Tabbas maganar Fa'iza kusan gaskiya ce, ina Saifullahi a yanzu?_ Da sauri ta tashi ta lalubi wayarta ta kira Nizir Yayanta, sai dai yanzun ma kamar ko wace rana wayar sam bata shiga _Does not exist._ take cewa, kimamin shekara ɗaya har da rabi kenan bata ji komai daga gareshi ba, dan number ma bata shiga sam.
****** ****** ******
"Muna matuƙar godiya Habib, da irin ɗawainiya da kake yi damu, Allah ya biyaka" Habib kanshi na ƙasa ya amsa da amin.
"Sannan sai ka sanarwa da manyan naka a ɗan jinkirta bikin zuwa lokacin da shi wancan yaro zai dawo" Shiru ya yi bai iya bawa Baffa amsa a wannan karon ba.
Tana zaune a ɗaki, har lokacin bata ce a sauketa a kujerar ba, saboda so take sai sun yi sallama da Habib. Jikinta gaba ɗaya ciwo yake, haka rabin kanta ma, sai dai damuwarta kawai itace taga Habib, saboda akwai maganar da ke cin ta a cikin rai.
_Zaki cigaba da tafiya tunda burina zai cika, amma ki sani muddin bai sakeki ba zaki dawo ruwa, so nake in ɗai-ɗaita duk wani wanda ya raɓeshi, sai dai shigowarki rayuwarsa ta saka bana iya aikina a kanshi yadda ya kamata._ Maganar ce ta dawo mata a rai, taji gabanta ya faɗi.
_Me hakan ke nufi?_
Sallamar Umma ce ta katse mata tunani, ta ɗaga kai ta kalleta. "Sadiya ba zaki kwanra yanzu ba?"
"Jikina yana ciwo Umma kuma ina so muyi sallama da Habib sannan nasha magani na kwanta dan kaina ciwo yake"
"To ai Habib ya tafi" Kallon Umma nayi, da mamaki, saboda ni bai taɓa yi min haka ba, in dai zai tafi to sai mun yi sallama. "Baffa ne ya ce masa ya tafi kawai, saboda a yanzu akwai haramci kuyi magana bayan kina da aure" Ta jiyo sautin muryar Umma tamkr saukar aradu a tsakar kanta. "Umma aure kuma? Ni ban san anyi min aure ba, haka shima, to dan me za a hanani magana da Habib?"
"Haka musulunci ya tsara, saboda aurenki yake nema, a yanzu muryarki al'aura ce a gareshi" Suka ji muryar Inna, gabaɗaya suka juya suna kallonta.
"Kiyi haƙuri Sadiya, wannan ƙaddararki ce"
"Umma, Inna kenan ba zan ƙara magana da Habib ba saboda ina sa auren da yake kamar babu"
"Ke kike ganinshi a haka, amma mahaifinki ya karɓi sadaki kuma shaidu sun shaida"
"Kenan kuma kun amince da auren? Shikenan an rabani da Yaya Habib?" Ta furta ƙwalla cike a kurmin idanunta.
"Ba mu rabaki da Habib ba, amma a yanzu dole ku daina keɓamcewa sannan kuma babu doguwar waya ko kuma kalamai na soyayya da zasu ƙara shiga tsakaninku har sai lokacin da mijinki ya sakeki, ki dai cigaba da addu'a Allah ya bayyana shi lafiya, amma tabbas mutanen nan sun cucemu kuma Allah ya isa" Umma ta ƙarasa maganar tana hoge hawayen takaici data kasa riƙewa.
"Umma tunkafin na ganshi naji na tsaneshi, ki duba yadda mahaifiyaeshi ta riƙa ci mana mutunci, wallahi duk kuɗin da mutum zai yi ya riƙa wulaƙanta talakawa kuɗin shi basu da amfani, har gurguwa ta ce min bayan a gidansu na samo wannan nakasar"
"Ki rabu dasu akwai Allah"
Ɓangren Habib kuwa da ƙyar ya iya kai kansa Kano lafiya, domin damuwar da tayi masa katutu, jin sa yake kamar bashi ba. Kai tsaye gidan Farouq ya nufa. Yana isa ƙofar gate ɗin bai ma shiga da motar ba ya kirashi a waya ya ce ya fito.
A owners seat ya zauna tare da faɗin "Lafiya na ganka kamar ba daidai ba Habib"
"Farouq ina ganin na rasa Sadiya, na ƙyar na iya kawo kaina nan, ji nake zuciyata na raɗaɗi, ga wani duhu-duhu a cikin idanuna, ban taɓa tunanin haka nake son Sadiya ba sai yau"
"Mene ya faru da Sadiyar da kuma kai kanka?"
"Aure?" Ya furta da kasala a muryarsa.
"Aure kamar ya?"
"Dole sai an warware auren da mahaifinta ya mata ba tare da ta sani ba, kuma shi wanda aka aura mata baya nan,su kansu basu san ina ya nufa ba"
"Habib ni sam ban gane ba, kayi min yadda zan gane"
"Bani da confidence ɗin yi maka bayani a yanzu, amma babban takaicina shi ne da suka hanani ko sallama da ita wai yanzu ta haramta a gareni har sai lokacin da aka saketa, ji nayi kamar zan mutu"
"Calm down, koma back seat na driving ɗinka gida, dan ba zan barka a yadda kake haka ba."
*1 Week Later*
A parlour ta riƙa kwaɗa sallama amma shiru, sai da ta shigo har cikin parlourn sai ga Mama ta fito daga kitchen. "Najwa kece a gidan"
"Eh Mama ina wuni" Ta gaɗa tana rissinawa. "Lafiya lau, ya aikin naki"
"Alhamdulillah" Sai kuma tayi shiru. "Ki zauna mana" Murmushi tayi tare da faɗin "Dama naje can studio naga baya nan, ance min kwana biyu ma bai leƙa ba, to shi ne nace bari na sameshi a nan"
"Yana ɗakinsa ai ya zama kamar matar kulle, baya da aiki sai na barci kullum sai yamma yake fitowa ko dare, ai tunda wannan abu ya faru shikenan ya ɗauki damuwa ya ɗorawa kansa"
"Wane abu Mama?"
"Au bai sanar dake ba kenan, to ki ƙarasa ciki in kinci sa'a ƙofar a buɗe dan kullum kulleta yake"
Da ɗan sauri Najwa ta wuce, ita kuma Mama ta koma kitchen. Tana murɗa handle ɗin taga ya buɗu. Mamki da tsoro suka cikata a lokacin da taga kwalaben giya a gabansa ga ɗaya a hannu yana ta kurɓa idanunsa akan wayarsa.
Bai san ta shigo ba har ta ƙarasa gabanshi, tana leƙa wayar taga hoton Sadiya ne. Da ƙarfi ta fuzge wayar, a tsorace ya ɗago kai ya kalleta. "Keee...!" Ya faɗa cikin maye. Hannu ta saka ta toshe hanci saboda yadda warin giyar ta bugi hancinta a lokacin da ya yi magana.
"Rayuwar daka daina a baya tun a school itace ka dawo yi Habib saboda mace?"
"Ki bani wayata, ke dan baki san mene so ba shiyasa kike wannan maganar" Cikin maye yake miƙa mata hannu, idanunsa sai lumshewa suke gashi har sun ɗan yi ja.
"Ba zan bayar ba, idan kuwa ka matsa min zan je na sanarwa da Mama halin dana sameka a ciki"
"To kije ki faɗa mata sai me, ai dama itama bata ƙaunar Sadiya" Ya sake maganar da maye sannan ya langwaɓar da kansa bisa kujerar da yake zaune.
Tsaki kawai tayi sannan ta fara laluben number Sadiya, bata iya gano number ba sai da ƙyar ta cikin whatsapp ya mata saving da _Pearl_ Baki kawai ta taɓe sannan ta saka number a wayarta ta kira.
Sadiya na zaune a bakin katifar taji wayarta na ringing, daga inda take ba zata iya ɗaukar wayar ba, saboda tayi mata nisa tana jikin caji. A hankali ta riƙa ɗan miƙa hannu dan gidan babu kowa duk sun tafi barka.
_Zaki cigaba da tafiya tunda burina zai cika._ Ta tuno wannan maganar. Kusan sati biyu da zuwansu Kaduna amma bata taɓa tunanin ta taka ƙafar ba saboda ta san maganar ba lallai ta zama gaskiya ba, amma ganin yadda kira ke ta ƙara shigowa ya saka ta ɗan taka ƙafar a hankali, taji lafiya lau. Miƙewa tayi kawai sai gani tayi ta tsaya cak, a tsorace ta zauna tare da dafe ƙirji.
_Aljana ce kenan?_ Ta tambayi kanta, a lokacin kuma wani kira ya sake shigowa dan haka ta sake miƙewa tana ɗan takawa kamar mai koyan tafiya har ta ƙarasa gaban wayar. Ganin number ce ya saka ta ɗaga zuciyarta cike da mamakin ƙafafun nata. "Baƙar munafuka annamimiya to burinki ya cika kin kashe Habib, na rantse da Allah ba zan raga miki ba" Gabanta ya faɗi ta cire wayar daga kunne ta sake kalla taga dai tabbas bata san number ba.