Page 22
by @sanazty
*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
Page 22
__________🖌️"Wace ce ke?" Ta furta muryarta na rawa. "Ban sani ba, musaka talaka jahila kawai" Ƙit aka kashe wayar. Da ƙyar ta iya zama a kan tabrmar dake tsakar ɗakin, sannan ta sake kiran wayar. Sai dai tayi kiran ya fi a ƙirga amma ba a ɗaga ba, hakan ya saka ta ajje wayar tare da fashewa da kuka.
Kuka sosai tayi har ta godewa Allah sannan bacci mai nauyi ya ɗauketa anan kan tabarmar.
Ɓangaren Najwa kuwa kwalbar hannunsa ta karɓa sannan ta ɗauki sauran ma ta saka a leda kawai ta fita. A parlour ta tarar da Mama tana kallo. "Mama bara na wuce naga bacci ma yake, amma zan dawo anjima"
"To Najwa, sai kin dawo" Kai kawai ta gyaɗa sannan ta fita ta bar gidan.
_Wane irin so Habib yake yiwa wannan yarinyar? Shin me take dashi wanaita bata da har ya kasa ƙaunarta sai wannan gurguwar._
Kai tsaye gidansu ta nufa, tana jin wani irin ɓacin rai da kuma fargaba. Babu kowa a parlour har ta wuce side ɗinta, kai tsaye toilet ta shiga ta buɗe kwalaben ta zazzage ruwan giyar sannan tayi flushing.
***** ***** *****
Umma ta sandare a tsaye tana kallon Sadiya dake kwance kan tabarwa waya a hannunta tana bacci. A haka Inna ta shigo ta sameta. "Lafiya naga kin tsaya anan"
"Inna kin ga inda na ga Sadiya fa, kuma kin ga akan gado muka barta ai."
"To ko dai faɗowa tayi"
"Anya? Kuma har ta faɗo zuwa nan" Umma tayi maganar tana kallon Sadiya.
Jin kamar magana a kanta ya saka ta buɗe ido a hankali, ganin sune ya saka ta tashi zaune sai kuma ta fashe da kuka gami da saka hannunta cikin cinya. Umma ƙarasawa tayi ta zauna kusa da ita, tare da ɗagota. "Mene ya faru?"
"Umma na warke ina iya tafiya"
"Garin ya?" Bata ma san lokacin da tayi mata wannan tambayar ba. Hannu ta saka ta goge guntun hawayen sannan ta ce "Dama ina taso in faɗa maku amma ina tsoro, kuma na ɗauka ƙarya ne ma shiyasa, sai yau da aka kirani a waya na rasa wanda zai miƙo min kawai nace bari na gwada tashi"
"Sadiya duk ba wannan ba, ki bamu labarin abinda kike tsoron" Inna ta faɗa gami da zama gefensu.
Labarin matar da ta gani a gidan su Muhasin tayi da kuma abinda ta faɗa mata, da yadda ta shafa ƙafarta har ta tsorata ta suma. "Kenan ciwonki dama saka miki sukayi, ko shakka babu aljana ce, to amma Inna sun buɗe mata ido kenan?" Umma tayi maganar tana kallon Inna. "Bana ce ba, abin da rikitarwa gaskiya, sai dai idan Malam yazo a samu ya yi mata addu'o'i ko kuma a kaita wurin wani Malamin ya bincika mana ya bata maganin jinni"
"Umma ta faɗa min fa, yana sakina ta var rayuwata, kuma bama zata sake zuwa ba saboda ta san a yanzu bani da alaqa dashi"
"To shi mene tsakaninsa da aljana har take masa haka"
"Wannan bai shafe mu ba, fatan mu shi ne dawo ya sawsaƙe wannan auren da bamu san dashi ba, da yanzu muna nan ana shirin biki." Cewar Inna"
**** ***** ****
"Bana tunanin aljanune matsalarka Muhasin. Domin da aljanune da yanzu na gansu ko da ban yi maganin matsalar ba dole zasu bayyana" Zaliha ta faɗa tana kallonsa kafin ta ce "Amma ka san me?" Kai ya girgiza alamar a'a.
"Aure shi ne maganin matsalarka in har wannan abin bai yuwu ba"
"Ban gane ba"
"Maganin da nake maka, idan ya cika wa'adinsa zaka yi soyayya idan har yarinyar bata mutu ba to tabbas anyi maganin matsalar"
"Idan ta mutu fa?" Ya jefa mata tambayar. "Hakan na nufin matsalar bata kau ba"
"Zaliha ba zan iya soyayya ba, ina ji ina gani in yi kisan kai, ni gara na ƙare rayuwata anan dajin gurinku inda na san babu wadda zan gani har in so ko ta soni bare har ta rasa ranta"
"Kenan ka gwammace ka mutu da wannan ciwon?"
"Itace ƙaddarata"
"Kai baka son ka ga jininka, 'ya'yanka"
"Babu yadda na iya da yadda ƙaddara ta zaɓa min"
"Ni kuma ina mai tabbatar maka, zan maka maganin dana tabbatar zaka samu lafiya, idan har kaga baka samu ba, to sai dai kuma akwai wani zaɓi"
"Zaɓin aure kika ce, kin taɓa ganin inda aka yi aure babu soyayya, dole sai tana sona ko ina sonta kuma haka shi ne yake kashesu har lahira"
"Shi ne abu na ƙarshe da zamu jarraba, Arɗo yaƙi yarda ka aureni, ko kuma kaƙi yarda kayi auren sirri dani bare mu jarraba wannan a kaina."
"Kiyi haƙuri Zaliha..." Manyan idanunta blue su ta kafeshi dasu, tare da faɗin "Kana tsoron kar na mutu?"
"Ko baki mutu ba babu amfanin auren da babu albarkar iyaye a cikunsa, musamman wanda muke son kashe wata matsala dole sai mun samu albarka indai muna so mu samu nasara"
"Rabilu zo nan" Ta furta da fulatanci tana yafico shi da hannu. Da sauri yazo, ta miƙa masa ƙwarya ta ce "Kai ɗakina ka ajje" Ya karɓa sannan ya kalli Muhasin sai kuma ya tafi.
"Kamar ya san wani abu a kanka, ina zuwa" Ta faɗa sannan tashi taje gurin Rabilun.
Jiki a sanyaye ta dawo, shi kuma da tashin hankali ya kalleta "Mene ya faru?"
Murmushin yaƙe tayi sannan ta ce "Babu komai" Bai yarda ba, amma bai matsa mata ba saboda yadda yake cikin damuwa.
"Amma Muhasin..." Ta fara maganar kuma ta dakata. "Ki faɗi abinda kike son faɗa"
"Alfarma nake nema, ban sani ba ko zaka iya"
"Zan iya insha Allah" "Ina so ka daina fito ko ina har zuwa lokacin da zamu gama yi maka magani, zai ɗauki tsawon wata takwas zuwa shekara ɗaya" Kallonta ya yi sannan ya ce "Wata ce ta kuma mutuwa?"
"A'a, na dai fi so riƙa zama a gida, idan yawo kake so zamu iya ɗan fita bayan bukkokinmu amma bana son ka riƙa zuwa cikin gari, dan komai zai iya faruwa akwai ɓata gari a cikin gari" Kai ya gyaɗa duk da bai gamsu da dalilin data kawo ba.
****** ******
Juyawa tayi rai a ɓace, Mommy ta juyo da ita tare da kifa mata mari. Hannu ta saka ta dafe kuncin, Fa'iza kuma da sauri ta ce "Mom..." "Ki rufa min baki, baki fi ni son Aziza ba" Shiru tayi tana kallon Aziza wanda fuskarta har tayi ja saboda fara ce.
"Zaɓi biyu zan baki. Ko ki tattara ki bar gidan nan, kuma karki sake dawo mana, ko kuma ki yarda a fitar da cikin, dan na rantse ba zan zauna ina kallo ki haifi shege ba. Dangin ubanki kaɗai sun isheni kafin azo kan mutanen gari"
Hannu tasa ta goge kan hancinta da hawaye suka bi ta nan sannan ta kalli Mommy "Kiyi haƙuri, ba zan yi kisan kai ba, na yarda zan bar gidan"
"Yanzu ba anjima ba" Mommy ta furta tana kallonta.
"Mommy hukuncin nan ya yi tsauri ina Aziza zataje dan Allah Mommy ki taimaka kiyi haƙuri" Fa'iza ta furta tana hawaye.
"Duk inda zataje taje, amma ba zata zauna min da shege ba"
Tuni Aziza har ta janyo trolley ta fara zuba kaya, Mommy na tsaye rai a ɓace tana kallonta.
Fa'iza cikin kuka ta ƙarasa gurinta "Aziza dan Allah ki yarda a zubar"
Kallonta Aziza tayi sannan ta ce "Fa'iza ke ma kin yarda inyi kisan kai? In zubar da cikin da ya kai wata har biyar? Fa'iza zunubi biyu kenan fa, ga zunubin zina gana zubar da ciki, ba zan iya ba. Garin zubar da ciki zan iya mutuwa fa, to idan naje lahira me zan faɗawa Allah? Ko zan yi yawo da zagaggen zane gara in zauna in girbe abinda na shuka" Tana gama maganar ta zuge trolley sannan ta ɗauka.
A gaban Mommy ta tsaya tare da sauke kanta ƙasa. "Kiyi haƙuri, ban taɓa musa miki ba, sannan kin mana tarbiyya gwargwadon iyawarki, Mommy zan tafi kuma zan haife ciki na, na fi so Allah ya hukuntani a duniya, kiyi hƙuri na tafka babban kuskuren da har na mutu ba zan daina nadama ba. Saboda kina kunyar 'yan uwan Daddy shiyasa baki so na zauna ko? To na miki alƙawarin zan nisanta da duk inda na san zasu ganni" Tana gama faɗa ta wuce.
Mommy ta kasa motsawa. Amma Fa'iza har bakin motarta ta bita tana bata haƙuri amma taƙi ta saurareta, tana ji tana gani motar Aziza ta bar farfajiyar gidan maigadi ya wangaƙe gate ta fita. Babban baƙin cikin Fa'iza shi ne Aziza ba waya a hannunta Mommy ta fasa kuma ta karya mata sims ɗin.
Dawowa tayi jikinta a sanyaye, a parlour ta tarar da Mommy zaune kan three seater tayi shiru. "Mommy dagaske fa Aziza ta tafi"
"Ki bata sati biyu kacal zata dawo, saboda babu inda take dashi da yafi nan. Inda na zauna ina bata haƙuri kan ta zauna to ko ta tafi ba zata dawo ba, amma yanzu ina mai tabbatar miki zata dawo." Fa'iza dai sam bata gamsu da maganar Mommy ba, cikin baƙin ciki ta wuce ɗakinta tasha kuka kamar ranta zai fita.
Aziza kuwa kai tsaye ta nufi office ɗinsu, ta ajje rubuta takardar dakatar da aiki na tsawon shekara ɗaya. Sun yi mamaki sosai, data rubuta _Leave without pay._ amma sai ta ce masu wani course zataje na wata 9 a ƙasar Mali.
Bayan ta fito kuwa kai tsaye Hotel ta nufa dan ta huce gajiyarta, tayi booking ɗaki na kwana guda. Tana shiga kuwa ta zube a gurin tare da fashewa da kuka. Bata da wani abokin shawara ko kuma wanda zata faɗawa damuwarta face Muhasin gashi kuma baya nan. Kuka tayi kamar ranta zai fita kafin ta goge hawaye ta barwa Allah komai.
Washe garin ranar kuwa tayi deciding kawai ta koma Kano da zama, dan bata son tayi nisa sosai, domin tana ganin kamar Kano nan ne zata iya zama har zuwa lokacin da zata haife ɗan cikin nata. Bata yi wani dogon tunani ba ta zarce Kano. Sai dai ta ɗan sha wuya kafin ta samu masauki dan sai da ta ɗauki tsawon sti guda sannan ta samu madaidaicin gida da zata zauna.
Bata fita ko ina sai dai ta fara laluben yanda zata samu 'yar aiki dan bata saba da wahala ba ga kuma ciki da yake matuƙar wahalar da ita.
***** ******
Gabanta na faɗuwa ta sake kiran number Habib sai dai sam bai ɗaga ba.
Hijab ta ɗauka ta zira sannan ta fita. "Ƙafa ta samu ina zuwa kuma"
"Ina son zan sayo kati"
"To a dai tafi a sannu." Cewar Inna. Murmushi kawai Sadiya tayi sannan ta fita.
Tana zuwa shagon ta roƙeshi daya ara mata waya, ya kuwa bata dan ya sansu sosai suna mu'amala da Baffa. Number Habib ta kwafa ta saka a cikin wayar ta kira, tana fara ringing taji gabanta ya faɗi, har ta kusa katsewa sai ya ɗaga "Hello!" Yanayin yanda ya amsa ma ya tabbatar mata a cikin damuwa yake. "Nagode wannan shi ne tukwuicin soyayyar da nake yi ma, hakan kuma ya nuna kana ganin kirana kake ƙin ɗagawa, bayan cin mutunci da wulaƙanci da budurwarka tayi min,babu komai ina matuƙar godiya" Tana jin ya fara magana bata saurari me zai ce ba ta katse sannan ta miƙawa mai shagon wayar ta masa gadiya. Ta juya kenan taji yana faɗin "Gashi ana kira fa"
"Ka ɗaga kace na tafi ko kuma ka ƙyaleshi kawai" Tana gama faɗa ta juya rai a ɓace.
Tana shiga gida Umma bata tsakar gidan sai Inna. "Ke kullum ba zaki saki rai ba, kullum fuskarki a murtuke"
Zama tayi sannan kuma ta ɗora kanta a cinyar Inna ta ce "To ina har yanzu abin farin ciki bai sameni ba"
"Aikam ya samu tunda gashi kina taka ƙafafunki"
Ɗan murmushi tayi, sai kuma ta ɗsure ganin kuran Habib ya shigo mata. Kai tsaye tayi rejecting. Sai da ya yi mata kira uku tana rejecting sannan text ya shigo.
_Pickup my call please._ Shi ne abinda ta gani, kawai sai kashe wayar tayi.
Rai a ɓace ya sauke wayar lokacin da ya ji switched off kuma ya tabbatar da ita ta kashe dan kar ya dameta da kira, duk da ya san shi ne bai kyauta ba. "Wace budurwata data ci mutuncinta?" _Najwa?_ Ya tambayi kansa, "Tabbas Mama ta faɗa min Najwa tazo gida kuma dama ban ga kwalaben dana ajje ba" A fusace ya tashi sai kawai ganin shigowata ya yi.
"Ashe ka warware, ai jiya dana zo baka cikin hayyacin..." Bata ƙarasa ba taji saukar yatsunsa a kuncinta.
SaNaz Ce🌸🤘