...BASHI!

Page 23

by @sanazty

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

                   Page 23

__________🖌️Kallonshi take, hannunta na kan kuncinta. "Sadiya ta zama jinin jikina, a kanta zan iya aikata komai ga koma waye" Idanun Najwa sun ciko da ƙwalla take kallonshi. "Saboda na damu da kai shiyasa ka saka hannu ta wanka min mari?" Cire hannun tayi sannam ta goge hawayen "Babu komai in sha Allah ba zaka ske ganina ba bare har ka mareni saboda wata da baka daɗe da haɗuwa da ita ba." Tana gama faɗa ta juya ta bar ɗakin, shi kuma ya zauna kan gado yana jin ba daɗi a ransa.
Bata samu Mama a parlour ba, dan haka bata yi mata sallama ba ta bar gidan.

Kuka sosai take har ta ƙarasa gida, bata taɓa tunanin akwai ranar da zata zo a rayuwarta har Habib ya mareta saboda wata. Kai tsaye ɗakin Sister ɗinta ta nufa.
"Yau kuma kece kika shigo kina kuka?"
"Sis ina cikin matsala" Zama tayi tare da riƙo hannunta sannan ta bata labarin duk abubuwan da suka faru. "Haba Najwa, kin bani kunya, yanzu ɗa namiji kike wa kuka?"
"Ba zaki gane zafin da nake ji a raina ba"
"Najwa kawai ki haƙura da Habib, tunda already kina tare da Auwal kuma ma Dad kin san shi ya haɗaƙu saboda ya fi son ki auri Soldier" "Habib nake so, ke kanki kin sani" "Na sani amma kuma bana so kizo kiyi aure a inda bai dace ba, bana son ki auri mijin da zaki dawo gida ko zauna. Ko kin fi so kiyi aure ki fito mu zauna a gidan nan? Ko ni kaina ba zan ina so nake zaman gida ba, zaman gidan miji shi ne mutuncin 'ya mace Najwa" "Sis ina son Habib kuma dashi nake so muyi rayuwar aure, muddin ban samu 
Habib ba to itama ba zata same shi ba" Tana gama faɗa ta tashi ta fita "Ki dai bi a sannu."

Ɓangaren Habib kuwa ƙara kira ya yi amma still a kashe, ya ajje wayar tare da lumshe idanunsa.Ji ya yi kwanciyar ba zata yuwu ba, dan haka ya tashi tare da ɗaukar machine ya fita bai ko sanarwa da Mama ba san ya fita bata parlourn. A lifan ɗin nan tun daga Kano haka yaje har Gaya akan machine ɗinsa. Kai tsaye gidan Baffa ya nufa, yana isa ƙofar gidan kuma daidai lokacin Baffa ya fito zai tafi masallaci. "A'a wa nake gani kamar Habibullah" Ɗan murmushi ya yi yana gyara parkong ɗin Lifan ɗin sa kafin ya ƙarasa har ƙasa ya gaishe da Baffa. "Kai ne a yammacin nan, ince dai lafiya?"
"Eh Baffa, ai tun ɗazu na taho kuma sai machine ya samu matsala" Ya ɗan sadda kai ƙasa tare da cewa "Eh Baffa dama nazo naga lafiyarku ne" Murmushi kawai Baffa ya yi, dan ya gane inda ya dosa. "To bari a kawo maka ruwa kayi alwallah muje masallaci ko?" Bai ce komai ba, Baffa da kanshi ya shiga gidan ya fito masa da ruwa a buta ya yi alwallah sannan suka nufi masallaci.

Ko bayan da suka sawo a zaure ya saka aka shimfiɗa masu tabarma tare da kawo masu tuwan dare, anan ya samu damar gaisawa da Inna wadda ita ta kawo tuwan. Habib bai su ya ci ba, dan shi burinsa bai wuce na ganin Sadiya ba sai dai a wannan karon ko gidan ma ba a bashi damar shiga ba bare ya yi tozali da ita. A ƙarshe ma Baffa ko kula ya yi da hakan sai ce masa yayi, ya yi haƙuri a bisa wannan abu insha Allahu idan Sadiya rabonsa ce zai sameta, yaji ba daɗi ganin ko gaisawa bai barshi ya yi da Sadiya ba, duk da kasancewar ya taho ne daga Kano zuwa Gaya dan ya ganta.

Har zuwa bayan sallar Isha'i sannan ya yi haramar tafiya, Baffa ya yi masa godiya a bisa ziyara.

Tana makewayi ta jiyo Baffa na faɗawa Umma ai Habib ne yazo, kuma yanzu ma suka yi sallama zai koma, yaƙi bashi damar ganin Sadiya gudun kar a shiga haƙƙin aure.
Bata jira jin abinda Umma zata faɗa ba tayi saurin fitowa a hankali, dama banɗakin a kusa da ƙofar waje yake, dan haka da sauri ta sulale ba tare da sun sani ba, dan ma gyale ne ta ɗaura aka sai ta kunce ta yafa gabaɗaya.

"Wane aure? Auren da yake fankon aure, haba Baffa bai kamata a hana Habib su gaisa da Sadiya ba, saboda ko babu aure ya mana abinda ba zamu manta dashi ba"
"Hakane, amma ni na san haƙƙin aure kuma kema kin sani sai dai ki take"

Ta ɓangareɓMn Sadiya kuwa tana fita ta hangoshi yana ƙoƙarin tayar da machine ɗin,da sauri ta ƙarasa tare da faɗin "Jinin jikina" Juyowa ya yi tun ma kafin ya ga fuskar tuni zuciyarshi ta tabbatar da wacece, yana juyowa ya kalleta tare murmushi tare da sauke numfashi.
"Kayi haƙuri..." Shi ne abinda ta faɗa idanunta a kan nashi ya kasa daina kallonta. Sauka ya yi daga kan machine ɗin yana kallonta ya ce "Ya aka yi kika fito?" Hannu ta watsa yare da cewa "Ɓarauniyar hanya"
"Ban fahimceki ba"
"Basu san na fito ba, kawai naji Baffa yana faɗawa Umma yanzu zaka tafi shi ne sillo nayo nan ba tare da sun ganni ba" Shiru ya yi kafin ya ce "To ki koma gida kar kiyi laifi. "Zan koma amma ina so muyi magana da kai ne"
"To ina jinki" Ya faɗa yana daidaita tsayuwarsa. "Yaya Habib...! Ban sani ba ko gidanku zasu iya yarda su jira har lokacin da zai dawo ya sawwaƙe min"
Lumshe ido ya yi sannan ya buɗe a hankali ya kuma diresu a kanta. "Ni ne zan yi aure, ni zan zaɓo matar da nake so, haka zalika ni zan zauna da ita, dan haka hukuncin nawa ne"
"Zaka jirani?" Ta furta a sanyaye. "Sadiya zan jiraki har tsawon rayuwata, kawai ina fargaba ace ya dawo ya kuma ƙi sakinki" "Wallahi bai isa ba, kuma da kotu ce zata rabamu" Ta furta rai a ɓace. "Calm down a gabana kike ba a gabansa ba" Ɗan murmushi ta yi sannan ta ce "Yauwa Yaya dama ina so in ce maka dan Allah ka daina zuwa saboda ko kazo Baffa ba zai bari mu haɗu ba, kuma na san ranka bai zai so haka ba"
"Hakane" Ya furta yana ɗan jin zafin abin. "Yauwa kawai mu riƙa waya, kuma ma ai na kusa dawowa Kano tunda kace anan kake so nayi karatu, sannan kuma ina fatan kafin ma wannan lokacin ace waccan ya dawo ya sawwaqe min wannan auren nashi" "Sadiya kin kashe waya kina fushi dani dole in taho dan in ga lafiyarki" "Ba zan ƙara kashe maka waya ba, dan na san ita kaɗai ce hanyar da zamu riƙa magana, dan haka ina so ka kwantar da hankalinka, idan har kaga ban zama taka ba to mutuwa nayi" "Naji daɗin maganarki, amma ina so kiyi min alƙawarin duk faɗan da zamuyi ba zaki sake kashe min waya ba" "Nayi maka" "Ina godiya."Murmushi tayi sannan ta ce "Wai a machine kazo?"
"Eh yanzu ai bani da mota"
"Meyasa?" Tayi tambayar da mamaki a fuskarta. "Yanzu dai kije gida zamuyi magana a waya, saboda kin ga idan aka fahimci baki nan akwai matsala" "To shikenan, ina fatan Allah ya kaika lafiya, ka kula min da kanka" "Nima ki kula min da kanki" Murmushi tayi tare da gyaɗa kai.

Sai da har ya ga shigar ta gida sannan ya tayar da machine ɗinsa. Aikuwa a tsoro taci karo da Baffa sai da taji cikinta ya ɗuri ruwa, ta ɗan saukd kai ƙasa alamun rashin gaskiya sun bayyana ƙarara a fuskarta. "Daga ina kike?"
"Naje sayen kati ne" Ta samu kanta da yin wannan ƙaryar "Ban son yawon dare kin dai sani, idan baki da kati kiyi min magana ko kuma ki bari da safe ki saya" Kai ta gyaɗa. "Wuce ciki" Da sauri ta shiga tana addu'ar Allah yasa kar Baffa ya fita ya tarar da Habib a waje.

Akan katifar ta zube gami da sauke ajiyar zuciya. Rayuwarta ta baya ta faɗo mata tare da tuno lokacin da ta tafi sayen icce, sanadi na farko daya fara ɓarar da tanadinta na rayuwa. "Waye ya yi min fyaɗe?" Ta sake tambayar kanta a fili, sannan ta miƙe, tare da janyo bakkon da kayan sawarta ke ciki. Can cikin zip ta ɗauko zoben sannan ta ɗaga tana juyata a hannu. _Menen dalilinsa na saka min wannan zoben._ Ta ƙara tambayar kanta cike da mamaki _Hakan na nufin ko a ina ya ganki zai ganeki._ Zuciyarta ta bata wannan amsar sai dai tunaninta kuma ya ƙara karkata akan idan mai zoben ya ganta to mene zai mata dole akwai wata manufa tayi hakan. A manunuyar hannun hagu ta mayar da zoben "Saka zoben nan kaɗai zai saka in haɗu da mamalkinta, duk da bani da wani ƙarfin iko, amma tabbas ina son haɗuwa dashi." A fili ta furta tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi.

Zuciyarta taji tana kiran sunan Habib, hakan ya saka ta lumshe ido tana jin wani son shi na ƙara addabar zuciyarta.
Shi kuwa Habib bayan ya koma gida ya yi wanka ya yi shirin bacci sannan ya kira Sadiya wanda sai da suka raba dare suna waya ko wanne a cikinsu yana bayyanawa ɗan uwansa itin son da yake masa, tuni Sadiya ta ajje wannan auren ta manta cewa ita matar aure ce, ta riƙa bayyanawa Habib shauƙinta a gareshi.

_Bayan Sati Biyu_

Gabaɗaya Najwa ta ɗauke masa ƙafa, bata kiransa ba kuma ta ƙara nemansa ba, sannan ko Sadiya da ta ce zata ɗau mataki a kanta bata sake kiranta ba tun wancan kira na farko da tayi mata. Yan zaune a studio misalin ƙarfe 11 na safe kawai ya fara tunanin rashin adalci da ya yi mata, ta damu dashi tun lokacin yana makaranta bai kamata ace tashi ɗaya ya manta da ita ba. Wayarshi ya janyo ya kirata amma bata shiga sam hakan ya tabbatar masa da tayi blocking ɗinsa.

Tashi ya yi ya fita. "Oga kayi baƙi fa" Kallon Faisal ya yi ya ce a cikinku wani ya yi attending ɗin su, ina zuwa zan dawo ba jimawa. Bai jira amsarshi ya fita da sauri. Sanin working days ne ya saka shi kai tsaye ya nufi asibitin malam dan ya tabbatar acan zai sameta.
Kai tsaye ya nufi sashen maternity ya kuma nufi office ɗin nata, sai dai yana shiga ya ci karo da abokiyar aikinta Husna. "A'a wa nake gani kamar Habib" Murmushi ya yi mai ƙayatarwa sannan ya ce "Ni ne" "Babban mawaƙinmu sannunka da zuwa" "Yauwa, ina mutuniyar"
"Ta fita round amma na san ba zata daɗe ba, ka zauna"
"Okay" Ya furta gami da zama. Sun ɗan taɓa hira da Husna kafin Najwa ta dawo.

Sam bata nuna masa komai ba, ta ƙarɓeshi hannu biyu kamar babu abinda ya faru. "Najwa nima bari in ɗan duba wata patient ina zuwa" Kai Najwa ta gyaɗa alamar to, bayan fitarta ta mayar da kallonta ga Habib. "Kwana biyu, ya su Mama"
"Najwa..." Ya ambaci sunan nata a sanyaye, ita kuma da ido kawai take kallonsa. "Nazo ne na baki haƙuri a bisa abinda ya faru, na san ban kyauta ba, amma kiyi haƙuri"
Lumshe ido tayi, ta ɗan yi murmushi sannan ta ce "So! Karka damu na san so ne ya jawo maka, shiyasa nima na ɗan ja baya kamar yadda ka buƙata"
 "Idan kina faɗin haka sai in ga kamar har yanzu kina fushi dani ne" 
Kai ta girgiza sannan ta ce "A'a Habib karka damu" Ta faɗa tare da ɗaga idanunta sama ta saka yatsa tana goge hawayen da yake neman zubo mata.

"To mene na kukan?" "Babu komai ba kuka nake ba, kawai dai ina....".Sai kuma ta shiru kafin ta sake faɗin "Ya batun album ɗinka?" "Ana ta editing" Kai ta gyaɗa tare da faɗin "Allah ya taimaka." Dawowar Husna ce ta hanashi cigaba da bata haƙuri, da zai tafi kuwa ita ta rakashi har bakin machine ɗinsa, sai daya tafi sannan ta koma ciki.

"Meyasa baki faɗa masa batun aurenki ba?" Husna ta tambaya tana kallon Najwa "Babu amfani, Husna kawai dan yazo gurina ne ba zan iya wulaƙanta shi ba, amma Habib tun daya mareni akan macen da ba dukanta nayi ba, na san cewa bani da wani muhimmanci a cikin rayuwarsa, maganar bikina kuwa sai da yaji daga baya, amma ni bama zan faɗa masa ba bare nayi inviting ɗinsa, saboda shi ya janyo bikina dama ai Kamal ya shirya nice nake ta ɓata lokaci kawai saboda Habib amma abinda na fahimta shi ne Habib ba zai iya aurena ba saboda ina cikin 20's yafi so ya auri yarinya, dan haka na ƙyaleshi da ita" Tausayi sosai Husna taji ta dafa Najwa ta ce "Ita soyayya babu ruwanta da wani tsufa, kuma kema ai ba wata babba bace kawai kin yi karatunki ne da wuri a kuma ƙuruciya shiyasa." zMurmushi kawai Najwa tayi bata sake cewa komai ba.

*_2 Weeks Later_*

Habib na zaune a Studio bayan ya gama aiki, sun yi waya da Sadiya sun gama kawai yaga saƙo ya shigo masa waya. Ɗagawa ya yi ya duba. _Habib na tura maka saƙo ta Whatsapp amma naga baka duba ba har yanzu._ Ganin saƙon daga Najwa ya saka ya yi saurin shiga whatsapp.

Miƙewa zune ya yi daga kishingiɗe da yake, ya cigabada buɗe hotunan biki da kuma videos na events da akayi. Sai kuma saƙon da ke ƙasansu inda aka rubuta.
_Jiya aka ɗaura aurena da Kamal kuma a gobe in Allah ya kaimu za a wuce dani Abuja, kayi haƙuri Habib ba zan iya sanar maka bikina ba da kaina amma ganin har yanzu babu alamun ka sani shiyasa na faɗa maka domin ina so kayi mana fatan alkhairi dani da mijina._ Hankalinsa a matuƙar tashe ya kira number Najwa bayan gama karanta saƙon sai dai wayar still bata tafiya. Karɓar wayar Faisal ya yi, ya saka number amma kuma a kashe, zama ya yi tare da dafe kai. Tun lokacin da yaje asibiti bai sake kiranta ba, wai shi ma zuciya yayi har sai ta nemasa.

"Najwa tayi aure ban sani ba" Ya maimaita gami da dafe kanshi. Jikinsa a sanyaye rayuwarsu da Najwa a baya ita ta dawo masa.

SaNaz Ce🌸🤘