...BASHI!

Page 24

by @sanazty

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

                   Page 24

__________🖌️ *Waiwaye*

Yana zaune a plantation yana duba sasu takardu ta ƙaraso gurin tare da ƙawayenta guda biyu suka zauna.

"Wannan guy ɗin yana burgeni sosai, kuma bari ku ga yau dai sai nayi masa magana." Tashi tayi, Manal ta riƙota "Ke baki san halin mazan school ɗin nan ba, bare shi da yake handsome zaki sha wulaƙanci idan kika je" Ta fuzge hannu ta ce "Ni sai naje ko zai wulaƙantani" Da sauri ta ƙarasa gurin nashi "Sannunka da hutawa" Ya ɗauko manyan oily ice ɗinsa ya kalleta "Yauwa" "Zan iya zama kuwa?"
"Eh ki zauna mana bismilla"
"Ai ba zaman ba, so nake muyi magana, gurinka nazo fa"
Ƙara kallonta ya yi sannan ya ce "Za ki iya zama" Zaunawa tayi tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya. "Sunana Najwa kai fa?" "Habib" Ya furta a taƙaice. "Habib, suna mai daɗi, am ko zamu zama friends?" "Why?" "Just like that, dama na daɗe ina ganinka a cikin makarantar nan so ina ta so in maka magana but ban sani ba yanda zaka kalleni ko kuma kayi min wulaƙanci shiyasa ban iya tararka ba" Ɗan murmushi ya yi kaɗan da gefen lips ɗin sa sannan ya ce "Am sorry to say ni bana ƙawance da mata" Yana gama faɗa ya miƙe, itama da sauri ta miƙe tare da faɗin "Kar hakan ya fusata ka please" Juyawa ya yi ya kalleta "Baki fusata ni ba" "To idan haka ne kawai kayi zamanka mu zamu iya barin wajen ma" Ta faɗa tana kallonsa. "No karki damu kusha zamanku." Yana gama faɗa ya wuce.

"Ai na faɗa dama, na faɗa miki halin beautys ɗin school ɗin nan akwai dizgi." Manal ta faɗa rai ɓace. Ita kuma Najwa dariya tayi ta ce "Ni ban ji haushinsa ba" Amal ma dariya tayi tare da faɗin "Ai indai Najwa ce akwai shegiyar kafiya, dariya ta yi ta ce "Kwayi kwa gama."

 Najwa bata gaji ba, a haka ta riƙa bibiyar Habib, baya wulaƙantata amma fa yana nuna baya son mu'amularsu. "Kayi haƙuri please ni fa ƙawance kawai nake so muyi" "Mene amfanin haka?" "Saboda atlease zamu riƙa sharing ideas, kama daga karatu, da sauran rayuwarmu ta yau da kullum" "No need" Ya furta tare da wucewa.
"Saboda kana mawaƙi shiyasa kake wulaƙanci ko?" Juyowa ya yi ya kalleta bai ce komai ba. "Na sani ai hakane ko?" Ta sake tambaya tana kallonsa.
"Ka faɗa min hakane?"
"Ni bana wulaƙanci saboda ɗaukaka"
"Amma ni kuma ai gashi kayi min"
"Kema ban miki ba, kawai dai so nake ki gane bana mu'amula da mata"
"Waƙar ma ta maz kaɗai kake ba macece ke maka amshi ba?"
"Wannan sana'ace ta haɗamu"
"Kamar yadda nima makaranta ta haɗamu ba" Murmushi kawai ya yi, a wannan lokacin ne ya bata dama sukayi magana sosai har ma suka yi exchanging number.

Tun daga wannan lokacin suka zama best friends, ita ta saka ya zama celebrity a cikin makarntar, sannan kuma ita ta ce ta ƙarfafa masa gwiqa har ya kai matsayin da yake a yanzu. Najwa kusan zai iya cewa da ita aka haɗu aka gina wannan studio ɗin, ku san kuɗinta ma sun fi yawa a ciki. Ta rigashi gama school da shekara ɗaya sannan ya gama. Sai dai ita tana gama sevice ta samu aiki yayinda shi kuma dama already drama ya karanta shiyasa ma ta koma studio. A haka suna tare har ya zama celebrity aka sanshi sosai, a waƙoƙi da dama ta taimaka masa kasancewarta ɗiya ce ta masu kuɗi.

*Cigaban Labari*

Habib bai iya zaman studio ba, sai gida ya koma yana jin babu daɗi a jikinsa. wanka ya yi yana shirin kwanciya yaji knocking. Sanin Mama ce ya saka ya saka jallabiya tare da zuwa bakin ƙofar ya buɗe. "Mama..." Kallon shi tayi ta ɗan taɓe baki "Ka sameni a parlour" Ta furta gami da juyawa. Sai da yaji gabansa ya faɗi sannan ya ɗan daidaita nutsuwarsa ya nufi parƙourn. A zaune ya tarar da ita tana ta karkaɗa ƙafa, jikinsa ya yi sanyi dan ya kawo a randa a kan Najwa zata masa magana. "Ya batun aurenka?" Ta furta tana kallonshi ido cikin ido. Sosa kai ya yi sannam ya ce "Mama nayi miki bayani fa already, kuma Abba ma ya miki bayani" "Ni ban gansu da wannan bayanin ba Habib" Kallonta ya yi, sai kuma ya ƙara saukar da kai ƙasa.
"Habib kana nufin zamu yi ta jiran ranar da wani zai zo ya saki wannan gurguwar sannan ka aura? Shin itace autar mata da bazaka haƙura da aurenta ba. Na san kai ka fusata Najwa tayi aure dan haka nima ba zan lamunta ba sam, dole ka nemi mata ko a cikin dangi ko kuma a waje" "Mama baki taɓa ganin Sadiya ba, amma naga kin..." "Na tsaneta sosai sboda sanadinka gaka kana rayuwa da ƙoda ƙwara ɗaya rak, wannan wace irin masifa ce" Ta tari numfashin sa da faɗin haka. Shiru ya yi yana kallonta kafin ya sake faɗin "Kiyi haƙuri" "Haƙuri na shi ne ka fito da mace kayi aure na gaji da ganinka a haka" "Za ayi yadda kike so Mama" "Kuma dai" Ta furta tana kauda kai.

Tashi ya yi, jikinsa sam babu ƙwari ya koma ɗakin nasa, ya kwanta kan gado yana jin ƙunar zuciya. Yana jin kamar ya kira Najwa sai dai ya san ko ya kira ba zata shiga ba, sannan kuma bbu dacewar ya kirata bayan tana gidan mijinta. Haka dai kwana biyu ya yi shi ba cikin kwanciyar hankali ba kafin daga bisani ya ware ya manta komai, sai dai ya kan ɗan tuna wani lokacin.

                 ****** *******

"Wata ɗaya da kwana 6 kenan babu Aziza, dama na san ba zata dawo ba kika ce zata dawo Mommy" Fa'iza ta furta idanunta akan mahaifiyar ta-ta. "Fa'iza tuhumata kike yi ko kuma me?"
"Mommy ba tuhumarki nake ba, amma shiyasa ni sam ban so kika kori Aziza ba, yanzu fa bama mu san wata duniyar take ba, naje har gurin aikinsu ance min ta rubuta leave without pay, wai ta ce masu ƙaro karatu zata je" "Kin ga idan zaki mayar ɗa hankali a karatunki ki mayar idan kuma ba haka ba kin huta" Tana gama faɗa ta miƙe ta bar parlour. Da ido kawai Fa'iza ke bin ta kafin daga bisani ta miƙewa itama ta nufi nata ɗakin.

Tana kwance akan gado bayan ta gama shan kukanta ta miƙe tare da janyo wayarta. "Hello" 
Daga ɗayan ɓangaren Daddy ya amsa da "Auta ya kike" 
"Lafiya lau Daddy"
"Mene ke faruwa dan naji alamun damuwa a muryarki. Hannu ta saka ta goge hawayen idanunta kafin ta ce "Daddy when are you coming back?"
"Soon insha Allah"
"Daddy wai mene muka yi maka? Meyasa kake gudunmu? Daddy dan Allah ka faɗa min aibunmu"
"Baku da wani aibu Fa'iza idan dan kece ko Aziza ni bani da matsala daku, amma daga zarar nazo gidan sai naji duk wani irin yanayi wanda baya barina in rufa ko sati biyu"
"Daddy indai matslar nan ce duk muna fuskanta, kuma ko bayan tafiyar Yaya Muhasin akwai ƴar aikin da ta rasu yanzu haka a gidan nan fa sai sabbin ƴan aiki aka kawo, dan tunda waccan ta rasu duk guduwa sukayi mutum ɗaya ce ta zauna a ciki"
"Ki titsiye mahaifiyarki ta faɗa miki gaskiyar abinda ke faruwa ita ta san komai ai"
"Daddy ni na gaji da tambayar Mommy kan waɗan nan abubuwan ni kawai na kira in faɗa maka ka saka ayi min visa in bar ƙasar nan dan Allah"
"Ina kike son zuwa?"
"Ni ko ina ne kawai ina son barin Nigeria"
"Okay in zaki iya tahowa gurina fine, kin ga sai ki ƙarasa karatunki a nan"
"To Daddy, kayi hanzari please" Ta ƙarasa da muryar shagwaɓa.

Tana gamawa ta zauna, a ranta ta furta _Gara nima in tafi kawai, domin gidan sam baya min daɗi, babu Aziza babu Yaya, ga Mommy kullum hantara da faɗa._

Ta ɓangaren Mommy kuwa tana shiga shiga ɗaki ta kira ƙawarta Hajiya Karima. Har ta katse bata ɗaga ba sai da ta sake kira sannan ta ɗaga. "Karima akwai matsala fa" Ta furta tana share gumin dake fuskarta duk da da sanyin AC a bedroom ɗin nata. "Akwai matsala Karima na rasa yanda zanyi, yanzu babu Muhasin kuma babu Aziza, anya kuma rufaffan ƙwan da muke ɓoyewa ba shi ne yake son ya fara wari ba?"
"To ai komai ƙara jagulewa yake ban san ya zan yi ba wallahi."
"Kina ganin hakan zai zama mafita?"
"To shikenan zan cigaba da jarrabawa" Tana gama wayar ta ajje tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya.

*Bayan Wata Huɗu*

Kallon shi tayi ta ɗanyi murmushi, shima murmushin ya mayar mata tare da faɗin "Kin dai zama 'yar Kano" Murmushi ta sake yi, wanda har ya bayyanar da haƙoranta masu matuƙar kyau da haske, mai haɗi da 'yar siririyar wushirya. "Yayana a ina na zama 'yar Kano, Sati biyu kacal da zuwana fa" "A sati biyun fita nawa kika yi ba tare da na sani ba"
"Am sorry, ni fa kawai ina ɗan fita ne dan in san gari amma ba dan wani abu ba" "Ni ai yanzu sai dai nace Sadiya ta zo ta nuna min wasu gararen a Kano" "Haba Yaya kar kace haka to ni kam ina sani" Ta furta da shagwaɓa, idanu kawai ya ƙura mata kafin ya ce "Am eager to ga na mallakeki kin zama matata, wannan shagwaɓar a gidana ya kamata a riƙa yi min ita" "Soon ai" Ta furta a hankali. "Me kika ce?" "Nothing" "Ni fa ba komai nace ba, ta furta tana kama hannun machine ɗin cike da kunya. "Ina matuƙar ƙaunarki Sadiya" "Ni...." Sai kuma tayi shiru. "Say your mind mana" "Babu komai" Ta faɗa tare da kallon shi. "Ina son zuwa hostel saboda akwai assignment da nake son ƙarasawa"
"Ko dai kin gaji da ganina ne?" Ɗan zaro ido rayi kanta yana ƙasa, sannan ta ɗago ta kalleshi "Haba Yayana ya za ai na gaji da kai, kawai dai na tuna cewa akwai assignment kuma da wuri zai ƙarɓa gobe" "Okay to shi kenan, ina son mu fita outing yaushe kike free?" "Uhmmm! To ban dai sani ba, amma za muyi magana"
"Ina ganin saturday ya yi ko?" "Eh to ba matsala Allah ya kaimu" "Amin ya rabbi."

Tana komawa Hostel kwanciya tayi kan katifar, ji tayi kawai gabanta yana wani irin faɗuwa. _Na san kina son Habibu, kuma ba rabaku nake son yi ba, ina dai so na kare martabarki ne, tunda har aka ce kina da sure dole ne kuma mu kiyaye hakan, kiyi haƙuri, kar kiga kamar ina son zaluntarki ne._ Tuno da furucin Baffa a ranar da zata taho karatu shi ne abinda ya faɗo mata a yanzu. Ta tashi zaune tare da dafe goshinta da hannu.

"Ina ta sallama shiru" Shi ne abinda taji a dodon kunnata. Kai ta ɗago ta kalli Janan "Daga ina?" Ta furta a sanyaye lokacin kuma Janan ta zauna. "Naje department yanzu na dawo, amma kin daɗe" "Eh ai ban ma samu ganin Likita ba, cewa suka yi in bari sai Monday"
"Monday kuma, next week kenan?" "Haka dai suka ce, to ya zanyi" 
"To ba matsala Allah ya kaimu Monday ɗin" "Amin ya rahaman" "Yauwa Sadiya dama ina so muyi wata magana dake" "To ina jinki, Allah yasa na sani"
Murmushi rayi sannan ta ce "Kin san me, hotunanmu na Matrix Brotherna ya gani sai ya ce min kin masa kuma ma da aure yake sonki, shi ne fa tun ɗazu nake ta azarzaɓin kizo na faɗa miki"

Faɗuwar gaba ta kuma ji, sai dai ta maze, ta ɗanyi murmushi "Kin dai san Yaya Habib ai" "Wannan ai Yayanki ne"
"Ba iya Wa ba, shi ne wanda zan aura dan har anyi engagement" Ɗan zaro ido tayi sannan ta ce "Amma shi ne ko ki faɗa min"
"To ai bamu daɗe da haɗuwa ba, gaba-gaba zaki san komai daya shafi rayuwata. "Hakane kuma, aikam zan faɗa masa, Allah ya taimaka ma ban bashi number ɗinki ba"

_Dare_

Tana zaune kan abin sallah bayan ta idar da sallar isha'i, wayarta data fara ringing ta kalla, sai da ta shafa addua sannan ta janyo, ta ɗaga gami da manta a kunne. "Hello!"
"Ba dai kin yi barvi ba" Murmushi tayi kamar yana gabanta kafin ta ce "A'a idona biyu, yanzu ma na idar da sallah"
"Okay ni kuma ina studio ina tunanin anan zan kwana ma"
"Ayya ya aiki"
"Lafiya lau, kim gama assignment ɗin"
"Eh na gama" Shiru ne ya biyo baya kafin ya ce "Sadiya..." Yadda ya kira sunan ta tabbatar akwai damuwa. "Na'am" Ta amsa a sanyaye. "Ina sonki matuƙar so da ƙauna, ban san ya zan musaltashi ba, amma na san sodai ne. Sadiya ji nake idan ban sameki ba zan iya mutuwa" "Haba Yaya, dan Allah ka daina faɗar haka"
"Dole zan faɗa, kullum tunani nake ina ganin yaushe zai dawo ya sakeki, wata zuciyar tana faɗa min koda ya dawo ba zai sake ki ba"
"Ka daina biyewa wasiwasin zuciya"
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Sadiya kina sona kamar yanda nake son ki kuwa?" 
"Yayana kai mai bawa kanka amsa ne" Murmushi ya yi sannan ya ce "Na yarda da abinda kika faɗa, yanzu dai ya kike?"
"Ina lafiya" "Ma sha Allah"
"Yaushe za ayi min waƙa?"
"Nayi ai tuni"
"Amma ni babu ita a wanda ka turo min"
"Eh so nake yi nayi album me kamar series"
"Amma ni ce tauraruwar ciki ko?" Ta faɗa da sigar wasa.
"Sunanki dai, amma kishinki ba zai bari na barki kiyi ba"
"Su wanda kuke sakawa baku jin kishinsu?"
"No kar mu tafi wani maudu'in"
"Ai duk a ciki ne, so nake na sani dai"
"Okay na ji, to su ai sun zo ne a matsayin sana"a suyi a biya su, kuma daga zarar sun samu miji suma aure zasuyi su bar harkar, to ke kuma dama already na sanki ba zan so duniya ta ganki har ayi min ƙafa ba" Murmushi sosai tayi tare da cewa "To Yayana na yarda" 
"Ya kamata a canza min sunan nan"
Murmushi ta sake yi ba tare da ta ce komai ba. Sun ɗan taɓa hira kaɗan kafin daga bisani suka yi sallama.

Tana katsewa Janan ta kalleta ta ce "Love birds ana ƙaunar juna" Murmushi tayi bata ce komai ba.
"Ɗazu mun yi waya da Dr. Zahraddeen ya ce zamu iya zuwa gobe ƙarfe 8 na safe dan haka sai mu shirya da wuri in rakaki" "Okay babu damuwa Allah ya kaimu, nagode sosai, shi Zahraddeen ɗin waye?"
Murmushi tayi tare da cewa "Yanzu fa sai kice saurayina ne" Dariya tayi ta ce "Kin tona kanki kuwa" "To Sady kar ma ki saka cewa saurayina ne na faɗa miki. Kin ga ni ba wannan ba, ki ɗanɗana wannan kiji ya taste ɗin" Ɗebowa tayi a spoon ta miƙa mata. "Wow yayi sosai, yau dai zamu kwashi girki."

             ******* *******

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shi ne abinda ta furta tana ƙara jin wani zugi a cikinta, ga bayanta dama tun dare take jin yana mata ciwo, sam ta kasa komai, jira kawai take gari ya waye taje asibiti. Gani tayi dare ya mata tsayi sosai a yadda take jin kamar naƙuda take. Bata da kowa bata san kowa ba, ko awo da take zuwa bata bari tayi sabo da kowa ba haka ƴan unguwarsu ma basu mu'amula da kowa sai maƙotanta da ɗaya daga cikinsu take mata aikace-aikace, gashi ita bata da waya bare ta kirata, tunda Mommy ta karɓi wayarta bata sake yunƙurin sayen wata ba.

Gari na fara haske a daddafe ta ɗauki Key ɗin mota, dama tuntuni ta saka komai na haihuwa da zata buƙata a ɗan ƙaramin troley da ta saya dan zuba kayan Baby. Da ƙyar ta iya driving kanta zuwa asibitin Nassarawa wanda acan take zuwa awo.

Bata ƙarasa asibitin ba ta tsaya a gefen titi ta parker motar tana murƙuƙusu tana jin kamar a lokacin ɗan cikinta zai fito hawaye gaba ɗaya ya wanke mata fuska. Wani duhu ta fara gani yana mamaye mata bata ganin gabanta, daga nan kuwa bata sanin inda kanta yake ba.

Buɗe idonta tayi ta ganta a titi inda dai ta parker motar, mutane har sun fara hada-hadarsu, ga kuma rana ta fara fitowa hakanne ya tabbatar mata da ta daɗe da suma a gurin. Wasu zafafan hawaye taji ya zubo mata. "Rashin gata" Ta furta a raunane, kasala sam ta hana ta motsawa, ga kuma motarta tinted ce shiyasa ma kowa ya kasa ganinta.
Ta daɗe sosai kafin daga bisani ta tada motar, amma dai a hankali tke tafiya dan ba zata iya tuƙi da sauri ba.

Napep yana saukesu suka nufi cikin asibitin direct. "Allah yasa mu gama da wuri dan kamar muna da lecture ƙarfe 11"
"Insha Allah kafin 11 mun gam..." Basu ƙarasa ba suka juya da suri ganin yadda mota taci burki ta bayansu. "Wannan wane mahaukaci ne, su fa masu motar nan basu da hankali gani suke su wasu shegu ne" Janan ta faɗa rai ɓace. Sadiya ma kallon motar tayi, ta glass ɗin gaba ta hango wadda ke cikin motar ta kwantar da kai a jikin kujerar. "Anya lafiya kuwa?"
"Me kika gani ne?"
"Zo muje" Tana faɗa tayi saurin wucewa gurin motar. Hannu ta saka ta buɗe ƙofar, ganin jini tayi yana bin ƙafafun Aziza. "Subhanallahi" Ta furta tana zaro ido tare da ɗan matsawa baya.

SaNaz Ce🌸🤘