Page 25
by @sanazty
*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
Page 25
__________🖌️"Mene ne naga kina zare ido?" Janan ta tambaya daga inda take tana kallon Sadiya. "Kamar haihuwa za tayi, ki taimaka ki kira nurses ni zan kula da ita anan" Kai kawai Janan ta gyaɗa tare da wucewa da sauri, ita kuma Sadiya ta dafa kafaɗun Aziza dan taji daɗi, tana ta mata kallon sani amma sam ta kasa gane inda ta santa. Kallonta Aziza tayi sannan ta ƙyar ta ce "Ga key ɗin motana dan Allah ki riƙe a wajenki, sannan kayan baby na akwatin dake boot, ki kum...." Bata ƙarasa maganar ba ta damƙo Sadiya tana sauke numfashi da ƙarfi. "Sannu" Shi ne abinda Sadiya ta iya faɗa. "Ƙila mutuwa zan yi!" Ta furta a wahalce. "Za ki warware da yardar Allah" Ta furta jikinta a sanyaye.
Basu samu damar zuwa wurin Doctor akan ta ta matsalar ba, tana nan tsaye labour room tana jiran tsammani ga matar da bata ko san asalinta ba. Gashi lokacin da ta saka wani ya gyara parking ɗin motar dan kuwa ita bata iya ba. Addua kawai take Allah ya sa matar nan ta haihu lafiya, gashi ji tayi sam ba zata iya barinta a gurin ba. Haka Janan ta tafi ta barta nan tsaya saboda lectures da suke fama dasu bai kamata ace sun fara missing lectures ba, dan ma department ɗin su ɗaya shiyasa ta ce mata idan ta samu dama tayi mata attendance.
*04:00pm*
Tana zaune har lokacin amma bata haihu ba, hankalinta a tashe yake, dan ta shiga ta dubata taga har ta fara galabaita.
Tana nan zaune Likita ya fito "Doctor ya ake ciki ne?" "Gaskiya muna tunanin sai an mata aiki" Ya furta yana kallon Sadiya wadda tsananin damuwa da firgice ya bayyana a fuskarta. "Dole muna buƙatar sa hannun babba, ko mhifinta ko maigidanta ko kuma wani muharraminta" "Ni ba zan iya saka hannu ba? Saboda ba anan muke ba karatu ne ya kawo mu" "Amma tun safe aka ce an kawo ta, meyasa baki sanar da 'yan uwa ba, kamata ya yi ko daga ina ne sun zo zuwa yanzu"
"To yanzu mene mafita?" "Ai dole ne sai kin kira muharraminta da zai mata signing, gashi lokaci yana ta tafiya, ya kamata a hanzarta" Kai ta gyaɗa tana jin fargaba sosai a ranta, yana wucewa ta kalli wayarta. Zama tayi ta rasa mafita, dan haka kawai ta kira number Habib dan shi ne kaɗai wanda zata iya kira a wannan lokacin.
"My little princess"
"Yayana kana ina ne?"
"Ina studio ina recording ne yanzu ma mun yi break sai ga kiranki"
"Kuma da buƙatarka nake"
"Mene yake faruwa? Dan naga alamar damuwa a tattare da muryarki"
"Ina asibitin Nassara dan Allah kazo"
"Mene yake faruwa?"
"Kazo dan Allah sai ka gani"
"Shikenan ganinan zuwa yanzu"
"Okay" Ta furta a sanyaye.
Kusan mintuna talatin ya ɗauka kafin ya ƙaraso asibitin. Tana ganinshi ta taso da sauri ta ƙarasa inda yake "Mene ke faruwa na ganki a ƙofar labour room?" "Akwai matsala Yayana wata ce na kawo" Labari ta bashi, kuma tunda ta fara yake kallonta har ta kai aya.
"Sadiya wannan abin yana da matuƙar haɗari fa, gara dai a nemo ƴan uwanta"
"A ina? Yaushe suka zo har suka saka hannu? Dan Allah ka taimaka zata iya rasa rayuwarta dan likita ya ce ta zubda jini da yawa"
Da ƙyar tayi convincing ɗinsa ya yarda ya saka hannu sannan aka fara shirye-shiryen theater, sai da suka nemo jini har leda biyu, duk wannan abu da akeyi kuwa Sadiya da kuɗinta ake ta amfani sai dai kuɗin theater da taji an faɗo dubu ɗari har da sattin sai tayi laƙwas dan ita bama ta taɓa ganinsu a zahiri ba. Sai kuma ta tuna cewa dama ta ce mata idan tana buƙatar kuɗi taje mota.
"Yanzu ya za ai da kuɗin theater ɗin?" Habib ya tambaya yana kallonta.
"Bari na duba a motarta" Ta faɗa tare da barin gurin da sauri.
Kuɗi masu uban yawa ta gani abin har ya tsoratata, domin har da dollolin amurka. Haka ta ƙirgo dubu ɗari da sittin ta dawo ta biya kuɗin. Duk wannan zirga-zirgar da take Habib kallonta kawai yake yana ƙara tausaya mata, tana da tausayi da kuma jajirce, addua kawai yake da fatan samu Sadiya a matsayin mallakinsa.
*1 Hour Later*
Suna zaune ita da Habib a ƙofar theater suna ɗan taɓa hira jefi-jefi, ganin an buɗe ƙofa ya saka ta miƙe, shima Habib miƙewa ya yi. da leda ɗaya daga ma'aikatan gurin ya fito da ita, dukkansu suka bi ledar da ido.
"Yauwa ga uwa nan, sai a samu a binne"
Habib ne ya karɓa tare da cewa "Ina kuma Babyn?"
Ita Sadiya ta kasa magana ma tana jira ya faɗi abinda ya faru dasu ko anyi aiki lafiya ko akasin haka.
Murmushi ya yi tare da faɗin "An samu Baby Boy, dukkansu suna cikin ƙoshin lafiya, da an gama shiryasu za a fito dasu. Murmushi sukayi gaba ɗaya. "Alhamdulillah" Ta faɗa a hankali tare da lumshe ido.
*ƘASAR WAJE*
Tana zaune a ɗan gurin da aka tanada dan shaƙatawa, lemo ne a hannunta da stro a ciki tana ɗan sipping, hannunta riƙe da waya tana latsawa.
Kamar daga sama taji an wuce glass cup dake hannunta. Ɗagowa tayi, tana kallon yarinyar da take tunanin idan bata yi sa'a da ita ba, to da kaɗan zata girmeta
"Wane irin rashin mutunci ne wannan"
"Ke! Ki kiyayeni ni ba sa'ar yinki bace, kada ki mata am your father's have, so ki san da waye kike tare"
Dariya Fa'iza tayi har da tafa hannu "Ikon Allah sannu Father's wife, wai ma in tambayeki ke a wane ƙauyen ya kwasoki? Sai dai yaje Nigeria ya auroku ya kawo daga kun gundire shi ya sake ku, ke dan Allah ko kunya baki ji zaki dubi Daddy ki kirashi wai miji mtswww" Tayi tsaki tare da kana ƙugu.
"Oh na manta kina taya uwarki kishi ne tunda ita bata kusa ko?" Jin haka ya saka Fa'iza ɗaukar hannu ta wanketa da mari sannan ta fara kaɗa hannu "Mommy ba sa'ar yinoi bace, kuma a kan mahaifiyata wallahi zan iya ƙasƙantar dake a gidan nan"
"Ni kika mara?"
"Na mareki, banza shashasha" Tana gama faɗa ta fuzge lemon sannan ta bar gurin.
Ɗakin daya kasance nata shi ta shiga tayi locking, kan sofa ta kwanta ƙafarta ɗaya tana ƙasa. _Meyasa lokaci ɗaya komai na rayuwa ya canza mana, rashin kwanciyar hankali ya kutso mana lokaci ɗaya, ni nazo ƙasar nan ne dan in samu peace of mind, amma tun dana zo na kasa zaman lafiya da waccan 'yar iskar._ Tayi ƙwafa sannan ta miƙe zaune. "Wai Daddy ya rasa waye zai auro mana sai wannan kuciciyar yarinyar, thank god ma ba a Nigeria suke ba da wallahi bama zai yuwu mu barta har tayi kishi da Mommy ba"
Hannu ta saka a haɓa, tana tuno yadda komai ya juya masu kuma a gidansu kowa ya kama gabansa, tunani take yanzu wane hali Aziza da Muhasin suke, uwa uba Mommy da suka shaƙu da juna.
Bata fito daga ɗakin nata ba har sai bayan da tayi sallar isha'i, wanda da agogo kawai take kintata lokaci tayi sallah.
Yunwa dake addabarta ya saka ta miƙe ta nufi patlourn ƙasa dan ta samu ta ɗan ci wani abu. Dining ta hango wayam sai flower da akayi decorating gurin. Bata damu ba, kai tsaye ta nufi kitchen, shi ɗinma babu komai duk an wanke komai gurin neat. "Hmmm 'Yar wahala, daɗin abin ma nima na iya girki" Ta faɗa tana ɗauko frying pan.
Fried indomie tayi, tuni ko ina ya cika da ƙamshi saboda spices ɗin da ta zuba. Ta haɗo tea mai kauri sannan ta ɗauka, tana juyawa ta ganta a ƙofar kitchen ɗin ta kama ƙugu. Sai tayi kamar ma bata ganta ba kawai ta nufo inda take gadan-gadan dan nan ne dai hanyar fita parlour. "Tana zuwa gab da ita kawai ta turata tayi baya, da cup ɗin da plate ɗin gab ɗaya suka faɗi, ita kuma tayi baya, Allah ya sa ruwan zafin bai ƙona ta ba. Kallon ƙasan tayi, gaba ɗaya sun zube kuma kasancewar cup ɗin mug ne shima ya fashe haka plate ɗinma. "Wannan wane irin dabbanci ne, ke wace irin shashasha ce"
"Dabbar kuma shashashar kin barota a Nigeria" Jin maganar ya saka ta kalli ƙofar, daga bayanta Daddy ne. Ɗan juya ido tayi gefe tana jin zuciyarta na ƙuna.
"Yanzu Asiya kike kira da wannan sunan? To uwarki Rukayya ita kike zagi" "Amma Daddy kana ganin abinda tayi min fa"
"Ki rufa min baki, duk abinda kike mata ina sane kawai ina ƙyaleki ne amma wallahi zan yi mugun saɓa miki" Hawaye taji sun kwaranyo kumatunta, ta saka ya yatsa ta goge sannan ta nufi hanyar dai zata wuce. "Ki bata haƙuri" Taji Daddy ya faɗa. Shiru tayi batayi magana ba. "Ki bata haƙuri, ko kuma in tattara in mayar dake Nigeria, na gaji da halinki" "Na yarda na koma Nigeria ɗin da wannan abin" Sai kuma shiru. "Fa'iza ni kike kalla kina faɗa min haka?" "Amma Daddy kana ta ciwa Mommy mutunci a kan wannan yarinyar da bata fi sa'ata ba, Daddy me Mommy tayi maka da ka tsaneta? Tun muna yara na lura da haka" Ta ƙarasa tana ƙara fashewa da
"Ita zaki tambaya irin sharri da makircinta wanda har ya kai danginta babu wanda yake raɓarta, ko kun taɓa ganin wani a damgin uwarku? Sai dai ni nawa dangin. To baƙin halinta shi ne ya jawo mata" Fa'iza ta daskare a gurin ta kasa motsawa ban da hawaye da yake zubowa a idonta.
"Muje My Asy" Ya faɗa yana jan hannunta, sai da suka fita sannan Fa'iza ta durƙushe a gurin ta hau kuka a fili, tare da dana sanin zuwanta ƙasar.
Sai da tayi mai isarta ta gama sannan ta tashi ta koma ɗakinta. Trolley ta janyo ta fara ɗaukar kayanta tana zubawa, tana tsayawa tana share hawaye.
"Kowa yaci tuwo dani miya yasha"
Da sauri Fa'iza ta juya tana kallonta. Ta harɗe hannuwa a ƙirji tana murmushi. "Yarinya yanzu kika fara gani indai kika ce ba zaki barni nayi zaman lafiya da ubanki ba."
"Zan bar miki gidan idan kin ga dama ki ƙwaɗa ki cinye" Ta furta rai a ɓace.
"Zan fa ƙara kiransa in faɗa masa abinda kike faɗa a kaina, ba nisa ya yi ba" Juyawa kawai Fa'iza tayi ta cigaba da haɗa kayanta. "Kuma babu inda zaki je, anan zaki zauna ki cigaba da kwasar baƙin ciki.
"Zan iya miki dukan tsiya idan yaso Daddy in yazo ya kasheni" "Ni zaki daka?" "Ƙwarai kuwa, karki bar ɗakin ki cigaba da yi min maganganun banza kiga abinda zai faru."
Ƙwafa tayi sannan ta juya ta bar ɗakin.
***** *****
Kallon Sadiya take tana murmushi kafin ta ce "Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, sannan ta shafa Babyn hawaye cike da idonta ta ce "Allah ya raya ka"
"Tunda kin tashi bari na haɗa miki tea, ko kina buƙatar wani abu?"
"A'a bani buƙata, hakan ma nagode"
Sadiya ta haɗa mata tea ta miƙa mata, sannan ta ɗauki jaririyar tana kalla. "Ma sha Allah" Ta faɗa tana kallonshi.
Murmushi Aziza tayi tana shan tea ɗin a hankali.
"Gashi nan kamarsu ɗaya da babanshi" "Amma yana da kyau masha Allah. Amma yanzu ƙawata zata zo zata kawo abinci nasan kina buƙata, sai nace tayi tuwa dan naga maijego tana buƙatar tuwa, Yayana kuma shima ya tafi sayo kayan wanka"
"Nagode da wannan hidintawar" "Karko damu. Yauwa idan kin gama sai ki bawa jaririn zam-zam da dabino, naga akwai a. trolley ɗin."
"Okay. Sai nake ganin kamar na sanki" Cewar Aziza.
Kallonta Sadiya tayi ta ce "Ni kuma? A ina kenan"
"Bari na tuna" Ta faɗa tana ƙara kallon Sadiya, itama kallonta take, kafin ta miƙe tsaye da Babyn a hannunta.
"Lafiya?" Aziza ta tambaya.
"Kamar kune..." Sadiya ta kasa ƙarasawa sai hawaye daya fara zuba a idonta.
"Sadiya...!" Aziza ta faɗa a sanyaye tana kallonta tun daga ƙafa har zuwa fuska, dan ita sanin da tayi mata gurguwa ce duk da cewar a gidansu ta samu larurar.
SaNaz Ce🌸🤘