Page 26
by @sanazty
*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
Page 26
__________🖌️Jikinta tuni ya fara rawa, hakan ce ta saka tayi saurin ajje jaririn a gefen Aziza, ta juya hankali a tashe zata bar gurin. Aziza cikin azama ta riƙo hannunta, idanunta cike da ƙwalla ta ce "Ban taɓa nufinki da sharri dan Allah..." Kasa magana tayi ta fashe da kuka kawai. Itama Sadiya kuka ta fara, ta raɓe jikin bango tayi mai isarta sannan ta goge hawaye, har lokacin kuma Aziza bata bar kukan ba. "Ba zan hanaki yanke hukunci akan niyyarki ba, amma kuma ki sani wallahi dukkanmu bamu san cewa ke matar Muhasin bace, hatta shi kan shi Muhasin ɗin" Sadiya bata iya magana ba, sai dai ta saka hannu ta goge ƙwallar da take shirin sake zubo mata.
"Zan tafi" Ta faɗa tana jin zugi a ranta. Aziza bata ce komai ba har Sadiya ta fita.
Lumshe ido tayi ta sake fashewa da kuka, jikinta gaba ɗaya ya fara rawa, a gadon tana kwance jikinta ya fara jijjiga, wanda har gadon nata jijjigawa yake, ga Baby akai, ga kuma bata cikin hayyacinta, gashi a Amenity suke.
Sadiya kuwa a farfajiyar gidan ta hango Habib yana buɗe boot, da sauri ta ƙarasa gurinsa. "Yayana ka dawo kenan" Ɗagowa ya yi ya kalleta "Eh me kika fito yi?"
Kai ta ɗan sosa kafin ta ce "Zan ɗan je hostel na dawo"
"Amma ba dai ita kaɗai kika bari ba, ko 'yan uwanta sun zo?"
Kai ta girgiza, sannan ta ce "Har yanzu babu wanda yazo"
"Okay to ai kin ga yanayi na C.S da aka yi mata bai kamata ki bar ta haka ba, nima naje na karɓi motar abokina ne saboda kayan ba zasu ɗebu a machine ba. Yanzu mu fara ragewa ɗauki, wanda zaki iya" Matsawa tayi ta ɗauka, sam bai gane tayi kuka ba saboda sinne kai da take tayi.
Ɗaukar sauran kayan suka koma, suna shiga hankalin Sadiya ya yi matuƙar tashi, ta ajje kayan da sauri ta ƙarasa inda Aziza take. Tana kwance a ƙasan gadon ta faɗo garin jijjigar nan, shi kuma Babyn yana kan gadon yana bacci abinshi.
"Mun shiga uku Yayana kaga halin da take ciki" Bai ma bata amsa ba ya juya da sauri. Ita kuma ta saka hannu tana ɗago Aziza wadda har idonta ya fara ƙaƙƙafewa.
Habib tare da Doctor da nurses guda biyu. "Ku ɗan bamu guri" Suka faɗa suna ƙarasawa inda Aziza take. Sadiya ta ɗauki jaririyar suka fita.
Akan kujerun wajen suka zauna sai dai ta kasa faɗa masa su waye, duba da yadda hankalinsa ba a kwance yake ba, kullum maganarsa kar Muhasin ya dawo yaƙi sakin Sadiya, to tabbas ta san idan ta faɗa masa zai iya tashi ya yi tafiyarsa ma.
Kallon Babyn tayi sannan ta kalli Habib "Yaron yana da haƙuri, gashi ya buɗe ido, kuma baiyi kuka ba, tunda aka kawo shi duniya ba a saka masa komai a bakin shi ba." "Meyasa?" Habib ya faɗa da mamaki, yana miƙa hannu ita kuma ta bashi Babyn.
"Ka san da aka kawota allura bata saketa ba, to kuma lokacin da na fito ai tana karyawa ne nace idan ta gama ta bawa yaron zam-zam da dabino, to kuma ka ga halin da muka tarar da ita. "Ya kamata gaskiya ko kece ki bashi" "Ai naga mahaifiya ke bayarwa" "To kin ga halin da take ciki ai, kawai ki bashi da zuciya ɗaya" Yana gama maganar sai ga Doctor da nurses ɗin sun fito.
"Karku damu, insha Allah komai lafiya" Cewar Doctor.
"To amma mene ya jawo wannan jijjigar?" Aziza ta tambaya tana kallonsa.
"Zuwa yanzu bamu sani ba, saboda ba irin jijjigar masu haihuwa bane nata, ban sani ba ko tana da mutanen ɓoye" Kallon Habib tayi sannan ta kalli Doctor. "Kenan sune?"
"Haka dai muke tunani, dan haka idan tana da magunguna sai ku fara yi mata amfani dasu, saboda ni na yarda da maganin hausa"
Suna shiga suka tarar an saka mata drip tana kuma bacci.
Kan kujera Habib ya zauna da jaririn a hannu. Ita kuma Sadiya ta ɗauko trolley ɗin ta buɗe ta ɗauki zam-zam da dabino. Karɓar yaron tayi daga hannun Habib sannan ta tauna dabinon tayi addu'a ta bashi, haka zam-zam ɗinma.
A kafaɗa ta sakashi tare da sauke ajiyr zuciya. A lokacin kuma Janan ta turo ƙofa ta shigo. "Ya na ganku haka cikin damuwa" Ta faɗa tana kallonsu. Murmushin ƙarfin hali Sadiya tayi shi kuma Habib ya ce "Wallahi kuwa bata jindaɗi ne"
"Ayya Allah ya sawwaƙe." Ta kalli Sadiya tare da ajje basket ɗin "Sady karki damu dama dole sai a hankali musamman ma daya kasance C.S naga kin damu sosai"
"Dole na damu, na santa fa" Ta faɗa cikin damuwa, ba Janan ba hatta Habib kallon neman amsa yake mata.
"Haba nima dama kamar kallon sani nake mata" Habib ya faɗa yana kallon Aziza dake kwance. Sadiya kuwa ji tsyi gabanta ya faɗi.
"Na tuna" Ya faɗa yana miƙewa. "Ƙawar wannan yaron ko? Gidan da mukaje a Kaduna" Kallonshi Sadiya take ta kasa magana. Shi kuma ya zauna kawai ranshi a ɓace sosai, ji tayi ta tsince kanta a tsananin faɗuwar gaba, bata da buri daya wuce taga ta samu guri ta kwanta dan samun nutsuwa amma kuma babu damar yin haka.
Shiru babu wanda ya yi magana, har daga bisani Habib ya miƙe tare da faɗin "Babe ina da aiki a studio" Ji tayi wani iri, dan in ya kirata da sunan gabanta na yawan faɗuwa. Miƙawa Janan Babyn tayi "Bari na taka masa" "Okay" Janan ta faɗa tare da karɓar Babyn.
"Naga kamar ranka a dagule" Ta faɗa lokacin data fita tare da jerawa ta gefensa.
"Kawai raina ne ya ɓaci, duk da ita a cikin 'yan gidan nasu ta fita zakka" "Nima a lokacin dana gane ita ce kai na tuno irin cin mutuncin da suka mana, sai na fita shi ne ma haɗuwar da mukayi da ksi har muka dawo, amma kuma halin dana ganta a ciki, ya saka naji ba daɗi dama ban tafi ba, ni dai da zuciya ɗaya zan taimaka mata" "Ki taimaka mata, amma kuma karki saki jiki da ita" Ya faɗa yana kallonta. Ita kuma ta gyaɗa kai.
"Ina tunanin a satin nan zan sayi mota, dama ginin gidanki ne ya saka na sayar da ita" Murmushi tayi tare da yi masa fatan alkhairi.
***** ***** ******
Hannu ta saka ta goge hawaye tare da kallon Daddy "Ina so na koma Nigeria"
"Saboda muna takura miki ko me?"
"A'a Daddy kawai ina so na koma gurin Mommy"
Asiya da take kwance a jikinsa tasowa tayi zaune ta ce "Hmmm! Kawai dai ki faɗi gaskiya, kin fi son komawa can" Ji tayi kamar ta mareta, amma dan dai a gaban Daddy ne shiyasa ta ƙyale.
"Kin fasa yin karatu kenan a nan?" "Daddy ga KASU nan zan yi, nafi son zama tare da Mommy"
"To shikenan, dama ke kika ce kina son zuwa nan, tunda baki so kuma yanzu shikenan sai ki koma ai, zan gama miki komai daga nan zuwa ƙarshen satin nan."
Bata sake cewa komai ba ta tashi kawai ta tafi, tana shiga bedroom ɗinta ta kwanta kan gado tare da sauke ajiyar zuciya. Ta rasa me zatayi tunani ko kuka, kawai sai jin shigowar Asiya tayi.
"A tafi a bamu space" Ɗagowa Fa'iza tayi ta kalleta. "Na baki watanni kaɗan indai Nigeria ce zaki dawo kema, amma zan baki wata 'yar shawara ki daure ki ƙoƙarta kar ki samu ciki, domin samun ciki shi ne ƙarshe alaqarki da Daddy"
"Oh baƙin ciki kike min nima kar in samu magaji?"
Dariya Fa'iza tayi tare da cewa "Oh wai ke har magaji kike nema? Okay Allah ya kawo magaji lafiya, amma ki tabbtar a gidan tsohonki zaki haifo magaji, ki rubuta ki ajje"
"Yarinya ki sani nida mahaifinki mutuwa ce zata rabamu, aurena dashi tamkar auren zobe ne"
Tsaki kawai Fa'iza tayi, ta shareta har ta gama ɓaɓatunta ta fita.
****** ******* *****
Miƙo madarar tayi, ta karɓa sannan ta fara bashi. "Sadiya nagode sosai, kina ta ɗawainiya dani, ga karatu kuma"
"Babu komai krki damu"
Murmushi tayi ta kalli Babyn sannan ta ce "Na san kina da tambayoyi da yawa da kike son yi min, amma kuma kawaici ya hanaki"
Murmushi Sadiya tayi bata ce komai ba. "Na san zakiyi mamaki dana haihu babu wanda yazo ko?" Ta faɗa tana kallonta. Shiru Sadiya tayi ta ɗan sauke kanta ƙasa.
"Sadiya ina tausayin yaron nan idan ya tashi ya tambayi waye mahaifinsa ni kuma ban san wace amsa zan bashi ba"
Ji tayi gabanta ya faɗi, ta dafe ƙirji, tare da lumshe ido.
"Sadiya nabi soɓ zuciya da ruɗin shaiɗan na kwaso abin kunya, Mommy tayi ƙoƙarin a zubar ni kuma naƙi yarda, to shi ne dalilin da yasa ta koreni, Sadiya ban gane ina da ciki ba sai daya kai wata huɗu, ba zan iya zubar da cikin da har ya zama ɗa ba, domin ban sani ba ko shi ne kaɗai ɗan da zan haifa a duniya" Ta fashe da kuka. Sadiya ta taso ta ƙaraso inda take kan gadon ta zauna. "Kiyi haƙuri, ƙaddarace, nima irin wannan ƙaddarar ita ta fara ruguza rayuwata" Tuni idanunta ya yi jajir sai dai bata zubda hawayen ba sai raɗaɗin da take a zuciyarta
"Kina nufin kema kin taɓa samun kanki a wannan yanayi?"
"Eh, amma ni ban san waye ba, ban san dalilinsa ba, kawai dai sn gusar min hankali aka min fyaɗe sannan aka saka min zobe a hannu" Ta ciro zoben "Wannan itace zoben da har na ajje, kuma da Habib yaso karɓa amma kuma nayi imani duk runtsi komin daɗewar lokaci ta wannan zoben ne kaɗai zan haɗu da wannan azzalumin"
Ajiyar zuciya Aziza ta sauke tare da faɗin "Ki yafe mana Sadiya, na san a gidanmu kika samu wannan larura, kuma sai na ganki kin warke mene ya faru?"
Shiru Sadiya tayi, bata son ta faɗawa Aziza abinda yake faruwa. "Ko baki so ki faɗa min?"
Murmushin ƙarfin hali tayi kafin ta ce "Ban san komai ba, na san dai na br gidanku da kwana biyu kawai na tsinci kaina a wannan yanayi, na tashi naga ina tafiya"
"Naji daɗin ganinki a haka, Allah ya ƙara lafiya"
"Amin ya rabbi"
Shiru ne ya ɗan biyo baya kafin Aziza ta ce "Za ki gane kamannin Muhasin kuwa?" Murmushi tayi tare da faɗin "Waye Muhasin?"
"Shi ne wanda aka aura miki a bisa rashin saninki"
"Ba zan gane kamarshi ba"
"Sadiya, Muhasin baya da wani aibu ban da wannan larurar, ba dan kin faɗa wata soyayyar ba, da nayi miki sha'awar zama dashi, sai dai kuma..." Sai tayi shiru.
"Sai dai kuma Muhasin duk wacce ya ce yana so ko ta ce tana son shi mutuwa take, bamu san dalili ba"
Shiru tayi jin cikinta yana kartawa, ta ɗan runtse ido tana cije baki, kafin ta buɗe. "Ina so Muhasin ya samu lafiya, Sadiya ni na san Muhasin mutumin kirki ne, shiyasa nayi ma Baby huɗuba da sunanshi" Sai kuma ta riƙo hannun Sadiya "Idan babu raina za ki iya kular min da Baby?"
"Meyasa kike faɗar haka?"
"Saboda gani nake kamar zan mutu, ba zan rayuwa dashi ba, bana so ayi masa gori ko nan gaba"
Hannu Sadiya ta saka tana share mata hawaye "Za ki rayu dashi, insha Allahu"
"Kenan zai tashi ya titsiye ni na faɗa masa wate ubansa? A lokacin waye zan nuna?"
"Komai zai zama daidai, insha Allah ba zaiyi kukan rashin mahaifi ba"
"Kin min alƙawarin haka?" Shiru Sadiya tayi.
"Zamanki da Muhasin shi ne kaɗai zai tabbatar min da haka"
"Kina so in mutu?" Sadiya ta faɗa a sanyaye.
Shiru Aziza tayi tana sauke numfashi "Idan na auri Muhasin mutuwa zan yi, kiyi haƙuri ina da future a gaba"
"Ba damuwa, Allah ya zaɓa abinda yafi akhairi."
"Amin ya rabbi"
Shiru ne ya biyo baya kafin Sadiya ta ce "Amma ya kamata a yanzu gida au san halin da kike ciki"
"Bana son na koma gida"
"Meyasa?"
"Saboda ɗana na san ba zasu ƙaunace shi ba"
"Amma zamanki anan ba mafita bace"
"Ina da gida da kuma 'yar aiki"
"Kulawar da za ki samu a gida sai tafi wadda zaki samu anan, kuma na san suna mararin ganinki a yanzu"
"Zan koma in har za ki yi min alƙawari"
Ju tayi gabanta ya faɗi alƙawarin.